BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   2 / 53

3K to 6K   out of 156.9K words

na kawo maku saboda ni ne namiji, ina kunyar ranar da zan fita na dawo ban samo komai ba bayan kuma nasan kuna da buqata, dan haka ki barsu kawai dan ALLAH kar kice ah ah".

"Shikenan tashi kaje Kayi mana cefane ko shi ɗin ma baza Ka iya karbar kudin ba na soke kaya na?"..........Murmushi yayi dan ko ba a fada ba yasan taji haushi ne. "Me dame zaa siyo?".

Taɓe baki tayi sannan ta ce, "taliya ce da kayan miya ita zata fi sauqin bararrakawa a yanzu dai, sai Ka samowa Shazeen ko cornflakes ne dan nasan baza ta iya jira na gama ba". Ta ƙarashe tana miqa masa kuɗin.

Karɓa yayi sannan ya tashi ya zura takalmin sa ya fita, ita kuma ta fara kwala kiran Shazeen. "Shazeen Shazeen wai me kikeyi a dakin nan ne? karfa ki cinye min caji kinsan ba kaiwa zanyi ba tunda wanna yayan naki ya sake musu baki sun gille wayar wutar ai shikenan sai kowa ya zauna".




------------------------√




"Kamal in mun ƙarasa motar mu kaɗai ce zata shiga ciki, su Aram su jira mu a waje ba dadewa zamuyi ba"........Ya faɗa da sanyayyar Muryar sa. Kallo na na dawo dashi gareshi, a yanzu ya cire p cap, sunshades da kuma noes mask din. kyakyawa ne ajin ƙarshe dan irin caramel skin ɗin nan ne dashi mai kama ido sai wani fidda annurin haske yake, bashi da saje amma gemun nan da gashin bakin sun sha gyara sun wani kwanta gwanin sha'awa, yana da dogon hanci tare da madaidaicin lips da suka kasance pink, idanun sa irin sleepy eyes ɗin nan ne masu saukarwa da mutum kasala, dole ma in Ka kalle Shi Ka ƙara saboda shi ɗin ƙarshe ne.

"Okay boss an gama". Shi ne abinda kamal ya furta tare da dannawa su Aram ɗin kira.

Tafiyar minti goma ce ta ƙarasa dasu inda zasu kamar yadda ya faɗa motar su ce kawai ta shige cikin gidan bayan an bude musu gate ɗin, bayan kamal yayi parking ya fito da gudu ya buɗe masa kofa sannan ya wuce booth ya dauko wani sabon loafers black, ciro shi yayi daga kwalin sa sannan ya zare ledar tare da cire soso ɗin dake ciki, ya wuce ya zura masa shi a foot space.

Takalmin ya sanya sannan a hankali ya ziro kafarsa guda, komawa yayi ya jingina da headrest ɗin tare da lumshe idanun sa tsawon seconds ya bude su sannan ya yunqura ya ziro ɗaya ƙafar tare da dukkan jikinsa, compound ɗin gidan ya bi da kallo kafin ya doshi hanyar da zata sadashi da cikin gidan, door bell ya danna sannan ya zube hannuwan sa cikin aljihun rigar sa.

Kusan minti biyu aka ɗauka kafin a buɗe ƙofar, wata budurwa ce tsaye sanye da vest da legging wanda ya tsaya iya guiwarta kanta ya sha kitso da gashin doki da ya sauka har kan mazaunanta, fara ce amma irin farin nan da aka hada da na kanti. Bashi hanya tayi tana faɗin, " Wai wai wai , Ya Amjad da gaske kai ne yau a gidan mu".

Saida ya karasa cikin falon ya zauna sannan ya ce, "Ni ne mana khadeejatou, ykk?".

Ɗan ɓata fuska tayi, "Haba ya Amjad Kai dai har yanzu khadeejatou nan sai kace a ƙauye, zamani fa yanzu ya canza, ina laifin deeyyah".

Taɓe baki yayi da faɗin, "Khadeejah ai shi ne suna, ko baki san sunan matar Annabi Muhammad ta farko bane Nana Khadeejah macen data fara Musulunta ta kuma yi imani da Annabi Muhammad tun farkon bayyanar wahayi, why zaku dinga bata sunayen ku da sunan wani zamani bayan ga sunaye masu asali, sai kunje garin canje canje kun sanyawa kanku sunan aljanu, ni ba wannan ba sauri nake ina mommy?".

Tura baki tayi gaba tare da faɗin, "Yanzu ta hau sama bari na faɗa Mata"....... Ta ƙarashe tana wucewa da sauri har tana haɗawa da dan gudu dan zuwa sanar da mommy.

Jingina yayi da headrest ɗin tare da ɗan ɗage kansa sama yana kallon pop ɗin, a ahankali ya shafo fuskar sa tun daga goshi har zuwa wuyansa tare da furzar da wani zazzafan numfashi sannan ya ɗago, bin komai na falon ya fara yi da kallo kamar mai haddace su kafin ya zaro wayar sa kirar iPhone 17 white in colour ya fara latsawa, minti biyar tsakani ya fara jiyo motsin saukowar su, bai daina abinda yake ba har saida ya tabbatar da bayyanuwar su cikin falon sannan ya dago Yana kallon su, dattijuwar macece da akalla zata yi shekaru 56 - 57 a duniya, Amma yadda ta suturta jikinta da kayan ƙawa da kyale kyale zai sa ka dauka she's in her early 40s, Khadeejah biye da ita.

"Barka da fitowa mommy".

"Haaa'aa Kaga yaron ummun sa, gabaɗaya ta hana Ka zuminci da mu ko sai ita da danginta kawai?".

"Ko daya mommy whl ba haka bane, abubuwan ne sai a hankali". Ya faɗa yana saukar da kansa ƙasa.

"Kai ba aiki ba, Kai ba iyali ba miye abubuwan da zai hana ka zumunci bayan kuma gari ɗaya muke, kai ko koyi da yan uwan ka baka yi duk wani taro su na kokarin halarta amma kai Ka ware Kan Ka daban ko?". Ta ƙarashe tana zama ta ɗora da faɗin, "deeyyah kawo masa ruwa".

" Afuwan mommy in sha allah za'a gyara". Ya faɗa still kansa na kallon ƙasa.

"To ai shikenan, ya gidan ?".

"Lpy kalau alhamdulillah".

"Ya su ummun ta Ka da su hajiya zunaira, ya kuma jikin yayan?"......... Shuru yayi na wasu daqiqai kafin ya ce, "dukkan su lpy, jikin dada da dama alhamdulillah".

" ALLAH ya kawo masa karshen wahalar nan shi ma Whl, in sha allah ni ma zan shigo na ga jikin nasa. Ya batun aure kuma Amjad? Ko shi ma an yafe shi? To Kaga idan ma har na waje suna tsoron abinda kaje yazo ne, mu sai mu shiga qauye mu bincika a dangi, mu ai dole haka zamu rufa asiri tunda hannun Ka baya taɓa rubewa Ka yanke Ka yar, dan nasan a dai bare ba wanda zai dauki ƴa' ya baka. Wai ma Amjad wani tsautsayin ya kaika jefa kanka a matsala irin wannan ne kana zaman ka lafiya ba abinda ka nema ka rasa".

Dan siririn murmushi yayi kwata kwata baza ka iya cewa ga yanayin da yake ciki ba. "Mommy a yanzu bani da bakin magana domin duk abinda zan faɗa mutane zasu ga kamar ina ƙoƙarin kare kai na ne amma lokaci alkali kuma shi zai bayyana gsky ko akasin ta".

Zuba masa ido tayi tana son gano yanayin da ya ke ciki amma ta ƙasa, hakan yasa ta ɗan yamutsa fuska da faɗin, "Kayi hakuri fa in maganar tawa ta ɓata ma rai, Amma gsky ce ni dole na faɗa ma a matsayina na ƙanwar mahaifin ka dan bazan jin tsoron idonka ba. Sai sa ake so mutum ya kasance nagari mai aikata ayyukan kwarai ba wai amfani da fuska biyu ba saboda akwai ranar qin dillaci, kuma masu iya magana na cewa rana ɗaya ta barawo rana ɗaya tak ta me kaya, In wani yayi rawa an bashi kudi in wani yayi duka zaici, zaren ba kalar yadin bane sai kaga Kai ALLAH yayi using dinka as example, shiyasa ake so a dinga sara ana duban bakin gatari. Ni whl banji dadin abin nan ba sam sam Amjad banso kayi wasa da damar da mahaifin ka ya baka ba".

Tun da ta fara magana ya janyo wayar sa yana ɗan latsawa duk da kuwa kana kallo kasan ba wani abun kirki yakeyi a ciki ba, har sai da ta ƙare maganganun nata masu kama da shagube sannan ya miqe yana gyara rigarsa daidai lokacin da deeyyah ta dawo falon riqe da tray data shiryo refreshments a ciki. "Nagode Mommy, ni zan wuce".

"Haba Amjad har zaka wuce kuma, yaushe ma Ka shigo ko minti talatin fa bakayi ba sannan kace zaka tafi, ka kusa shekara biyu fa rabon Ka da gidan nan".

"Haka ne mommy Amma yanzun ina sauri ne , in sha ALLAH in an kwana biyu zan dinga zagayowa".

"To shikenan Amma ga ruwa yar uwarka ta kawo ma ai ko shi ka tsaya ka sha"..........dan shafa kansa yayi tare da ɗan kaɗashi kaɗan ya ce, "in na sake zuwa zan sha in sha ALLAH".

" To ba damuwa ka gaida mutanan gidan".

Ƙasa ƙasa ya ce, "zasu ji". Tare da sa Kai ya fice. Juyawa deeyyah tayi wurin mommy kana ta ce, "Mommy meya faru ? na ga kaman ba haka ya shigo ba" .

"Ke da kika iya lura da wannan hargitsatsen ma kenan, shi da ba gane farin cikin sa ko akasin sa ake ba, dama a haka ya shigo ai. Tashi ki je shirya ki zo na aikeki ki karbo Min saqo wurin deedy".

"Mommy Amma ya Amj....."

"Keee zaki tashi ki bani wuri ko zaki tsaya min kinibibi". Mommy ta katseta a tsawace dan tasan nacin deeyyah ɗin.

Sai da ta sake kallon ƙofar falon nasu sannan ta tashi tana tura baki ta bar falon.

Mommy kuwa deeyyah na barin falon wata number da akayi saving da Hajiya zunaira ta dannawa kira, sai da ta kusan tsinkewa aka amsa. "Hello Hajiya zunaira!".

"Naam ƙawata, mun wuni Lpy". Faɗin Hajiya zunaira........."Lpy kalau ya mirrah?"

"Whl tana nan lpy, ina Deeyyah tah?"..........."Tana nan lpy yanzun ma ta hau sama. Yanzu fa shegen yaron nan ya tashi daga nan"......... Shiru Hajiya Zunaira tayi kafin ta ce, " wani yaro kenan?".

"Matsala ta dake bakya harbo jirgin da wuri wannan yaron kishiyar taki mana Nadeera"..........."Auho Amjad wai?"

"Shi dai, kinsan ai ada kilibabbar uwar tashi ta hanashi zuwa sai da ranar nan muka hadu a gidan yaya Maheera sunan yarinyar wurin ta data haihu baki samu zuwa ba, ai kuwa na mata tas shi ne yau ta turo shi".

"Hmmm ai hajiya Fareeha karki taɓa ganin laifin yaran nan dan ba ruwan su duk wani iya shege uwar ke daura su akai, sai sa ni kinga yaqi na da baqar algunguma nake yi ba abinda ya sha min kai da ya'yan ta ".

"To ai kuma kina nunawa ya'yan soyayya ai baza taji zafin duk abinda zaki mata ba".

"Hajiya Fareeha kenan". Hajiya zunaira ta faɗa tare da yin wata yar bazawarar dariya.

"Tsaya nan kallon ruwa ƙwaɗo ya Miki ƙafa, ki cigaba da dariya". Mommy ta faɗa.

"To ni yanzu me ya rage min hajiya Fareeha, ɗan nata ma da suka dauki burin duniya suka ɗaura masa ita da Alhajin gashi nan ya ɓata rawar sa da tsalle, uban ma duka daya ya kwantar dashi to sai mai kuma? ya'yan nawa dai su ne yanzu akan komai to miye kuma zai tada min hankali ni yanzu ALLAH na tuba".

"Shegiyar gari Ke fa kin dafe ƙasa saisa kika koma gefe kika yi shuru abinki ko. Ai bake kaɗai abun nan ya wa dadi ba har dani, ashe dai yaro Musa ne a fuska firauna a zuci, ai yanzu kafin ya fita saida na tabbatar ya shaqa da zafi dan ma dai kinsan yaron wani irin juyayye ne kwata kwata ba'a taba karantar facial expressions ɗin sa". Ta ƙarashe tana kwashewa da dariya.

" Kuma whl yaron yana da biyayya Hajiya Fareeha kawai dai kinsan in an budewa yaro ido da kuɗi sai kiga ta kowacce hanya neman su zaiyi ba tare da yayi tunanin me zai faru gaba ba".

" Kaji Hajiya zunaira da wata magana da ALLAH, yanzu har zakiyi zancen kudi a cikin zurriyar Hashim Darwin, ai ke kinsan yaya ba ƴaƴan sa ba hatta jikokin jikokin sa ba zasuyi talauci ba, su dai kawai dama can basu gaji arziki ba, yaya ya kwaso mana jaraba ya kwaso mana jinin tsiya".

Dariya Hajiya zunaira tayi da faɗin, "Baki da dama ƙawata ya kamata ki samu ki shigo fa".

"Yanzun nan nake maganar Whl, in sha ALLAH zan samu na shigo mu sha hira dai"........."To shikenan zan zuba ido saura ki jirgani".

"Habaa ke kuwa ai kinsan Bama haka, in sha ALLAHU kafin alhaji ya dawo daga tafiyar nan zanzo mu wuni ".

"To shikenan Allah ya kawoki lpy". Daga haka sukayi sallama, tashi Mommy tayi tana kiran masu aiki da suzo su kwashe refreshments ɗin da deeyyah ta bari a wurin sannan ta wuce saman itama.


SHIN WAYE AMJAD?

MIYE DALILIN MOMMY NA JIFANSA DA IRIN WANNA ZAZZAFAN KALAMAN?

MEYSA YAYI TUNANIN AIKO HUSHAIMA AKAYI?

WACECE HUSHAIMA, SAHNISH DA KUMA SHAZEEN?

SANNAN INA IYAYEN SU SUKE?

MIYE DALILIN DA YASA SUKE RAYUWA SU KADAI?

KU CIGABA DA BI NA DOMIN MU SAMO AMSOSHIN WANNA TAMBAYOYI TARE.


NOTE: THIS IS A WORK OF FICTION , NAMES, CHARACTERS, EVENTS AND OTHER ELEMENTS ARE THE PRODUCT OF THE AUTHOR'S IMAGINATION, ANY RESEMBLANCE TO ACTUAL PERSONS LIVING OR ACTUAL EVENT IS PURELY COINCIDENT. NO PART OF THIS BOOK MAY BE REPRODUCED OR SHARED, INCLUDING ON YOUTUBE WITHOUT THE AUTHOR'S PERMISSION.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd Sultywrites22



STEP 1



PAGE _______ 3



Fitowa yayi cikin tafiyar sa me cike da kwarjini da kuma nutsuwa kansa a ƙasa wanda hakan ya hanani gane yanayin da ya ke ciki. Tun kafin ya ƙaraso kamal ya bude masa ƙofar motar, yana zuwa ya shige, shi Kuma ya rufe ya koma mazaunin driver yaja suka fice, sauran motocin na ganin fitowar su suka rufa musu baya.

A karo na biyar wayar sa take ta faman tsuwwar neman Agaji dauka yayi da niyyar kasheta gabaɗaya idonsa ya sauka akan sunan dake yawo kan screen din, " My Ninie". tare da wani maroon heart emoji da Kuma emojin padlock da key. Ganin Kiran na kokarin tsinkewa ya sashi amsawa tare da Kai wayar kunnen sa idanun sa kan titi yana kallon hanya. " Amour dama kana kusa nake ta Kiran ka baka dagawa ".

Saida ya lumshe idanun sa da a yanzu suka dan sirka da red saɓanin lokacin da suka shiga gidan mommy da suke a washe kamar madara. "Ina hanya ne Ninie". Ya faɗa a sanyaye.

"To kuma kana hanya ai ba Kai kake driving din ba, amour ko dai ina takura ma ne". Ta ƙarashe kamar zata fashe da kuka.

Yanayin yadda tayi maganar ya sashi furzar da zazzafan numfashi tare da faɗin, "I'm sorry Ninie".

Shuru tayi kafin ta ce, "I'm the one who's supposed to tell you that".

"Why?". Ya tambaya.

"Shirme na ya sa ina ta ma surutai ba tare dana tsaya na tantance yanayin ka ba, meke faruwa ne amour, waya bata ma rai?".

"Nayrah!"......... "Naam rabin ran Nayrah".

"Nayrah!"..........."Naam Habiby nah".

"Nayrah!".......... Ya sake fada a karo na uku.

Dariya tayi tare da faɗin, " Whl Yadda kake Kiran sunan nan sai naji kamar na bayyana a gaban ka amour, na kalla cikin idanun ka domin na gano abinda ya bata ma gwarzo na rai dan na ɗauki mataki ba tare da bata lokaci ba".

"Ji ki, sai kace iyawa zakiyi".

Cike da confidence ta ce, "Zan iya mana, a kanka ai ko aljani ne ina iya faɗa dashi talkless of mutum da ina ganin sa yana gani na".

Wani killer smirk yayi Mai sauti har saida jerarrrun fararren hakoransa na gefen dama suka bayyana, Wanda ni kai na saida zuciyata ta buga da wanna tsadadden murmushin saboda kyawun da ya masa. " Abinda ni ke nufi shi ne zaki iya gane me ya ɓatamun rai idan kin kalla cikin idanun nawa ne?".......... Dan shuru tayi can kuma ta ce , "to ai Kai ɗin ne ma duk hasashen mutum sai ka maida shi karya ko da na canka ma zakace ba haka bane".

"Ai bakya canka daidai din ne". Ya sake faɗa cikin taushin murya.

"Dama kullum haka kake musawa ai, Amma kasan dai ina ganewa daga Muryar ka ko".

"Ehen shi ma saboda kinsan kina sani surutu ne ai, saisa in bakiji na Buɗe baki sosai ba kike iya fahimta".

"Naji amma with time kuma zan baka mamaki".

"Ya kamata ki bani mamakin nan da wuri, dan Gsky bazan auri matar da bata iya fuskantar yanayin da nake ciki ba har sai na buɗi baki na faɗa mata". Ya faɗa cikin sigar tsokana.

"To dama wa yace ma nima zan iya auran mutum mai wuyar sha'ani irinka, dama maneji zanyi kawai".

"Kyaji dashi dai, kinga dan saurayi kin rikice a kansa. Bari In na koma gida zan kiraki".

Dariya tayi kana ta ce, "To, ALLAH ya kaika gida lpy, ALLAH ya karemin kai, ka kula min da kanka kaɗan".

"Ameennn ya Allah, and zan kula Miki da kai na da yawa ma". Ya faɗa yana ɗan murmushi.

Ajje wayar tayi bayan ya kashe tare da janyo pillow ta rungume tana murmushi ɗaga kan da zatayi idon ta ya sauka kan mahaifiyarta dake tsaye ta zuba mata ido, "laa mumu yaushe ki..kika shigo". Ta tambaya cikin yanayin dake nuna alamar rashin gaskiya a tattare da ita.

"Nayrah da wa kikayi waya?". Mumu ta tambaya ba alamun wasa a tattare da ita.

Sake rikicewa tayi duk da kokarin saita kanta da take saboda sanin halin mahaifiyarta ta, "Mumu ba kowa fa, ba waya nake ba". Ta faɗa duk da tasan kallon da taga tana mata da wuya ace bata ji ta ba.

"Tambayar ki nake da wa kikayi waya?". Ta maimaita tambayar a kausashe.

"Amm, dama dama Amla ce, Kuma ma network ya hana naji ta ma sosai".

"Baki da gaskiya Nayrah, wato har yanzu baki rabu da wanna annobar ba ko? Kin dage sai kin janyo mana bala'in da daga mu har dangin mu za'a shafe tarihin mu ko?".

Idanunta ne suka ciko da kwalla ta ce, "mumu Dan ALLAH ki daina cewa haka,

2 / 53