BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   26 / 53

75K to 78K   out of 156.9K words

dake iyakar ruwan da kayan HE suka saba shigowa dan sanar dasu saboda kar a samu matsala. "Hello jibrin"..........."ranka ya daɗe Barka da dare".

"Barka Jibrin ya aikin?"............."Da godia ranka ya daɗe".

"To madallah, ammm akwai kayan da zasu shigo anjima da tsakiyar dare ka sanar da abokan aikin ka banaso a tsaya wani bincike ku barsu su wuce kawai".

"To ranka ya daɗe yadda kace haka za'ayi in sha ALLAH".......... "Nagode sai ka ji Ni". Daga haka sukayi sallama ya kashe wayar. Tashi yayi ya sauya kayan Sannan ya nufi hanyar fita daga ɗakin wayarsa da ya ajje bakin gado tayi ƙara alamar shigowar saqo, fasa fitar yayi ya koma ya ɗauka, dubawar da zai yi yaga wani nannauyar alert ne, wata yar ƙarar jin daɗi yayi dan kuɗin da HE ya tura masa a yanzu yafi na ko yaushe, bai yi ƙasa a guiwa ba shi ma ya kira jibrin yace ya turo masa acc number ɗinsa zai saka masa wani abu su sha ruwa shi da abokan aikinsa. Daga nan ya zura wayar a aljihu ya fita cike da wani energy da naunauyan alert da irin wannan ne kawai ke bada shi.



-----------------------√



"Kasan tun ɗazu naso mu haɗu, to naje wuri sir Ramphant ne kuma na tarar yana da baqi ban ma samu ganin sa ba".......... Faɗin Hajj zawaad.

"Meke faruwa ne ? Ni tunda na shigo Naga kamar baka cikin nutsuwar Ka".......... Faɗin Alhaji Huzaif. Zama Hajj zawaad yayi sannan ya ce, "Bari kawai Alhaji Huzaif wa'annan yaran Alhaji Hashim ɗin ne suke ƙoƙarin fitar da crude oil me ɗinbin yawa domin suyi amfani da kuɗin wurin kammala gyare gyaren sabuwar ma'aikatar su ".

Cikin Rashin fahimta Alhaji Huzaif ya ce, "To miye aibun hakan?" .

"Matsalata dakai rashin saurin fahimta, shin ko Ka manta yaqin mu akan miye ne? ai fitarwar da zasuyi a yanzu kaɗai zai iya Kai percentage ɗin da dole mu haƙure musu lambar yabon nan, kasan su ma ɓarayin kansu ne ballatana yanzu sun samu dama kawai yadda suke so sukeyi".

"Kaiiiii inaaaaa hakan ma bamai yiwuwa bane ai, to yanzu me kayi akai?"............" Shi ne abinda nake faɗa ma Ka kasa fahimta ai, ni abinda nayi na aikawa dashi Amjad ɗin bayanin komai saboda nasan bashi da masaniya akai ko zaiyi wani Abu amma shegen sai yace yasan komai ai da sanin sa, saboda shi bazai iya cigaba da running din komai kai tsaye bane a yanzu saisa ya miqawa brothers ɗin sa ".

"To wai ba ance an daina karɓar ko sayan komai daga garesu bane ma?".

"Haka dai wasu suke faɗa".........." Bangane haka wasu suke faɗa ba?". Girgiza Kai Hajj Zawaad yayi tare da faɗin, "Mu dukkan mu haka muke zato Amma kuma sir Ramphant juwaira ya tabbatar min da ba hakan bane domin suna fitarwa kawai dai an daina zuwa a karɓa ne a wurin su, shi ma ya sanar min batun cewa su Julaybin ɗin na shirin fitar da wani gwagwaban crude oil ɗin".

"Kenan wasa da hankalin mu ake ?".

"Ko kuma muke wasa da hankalin mu da Kan mu ba, kasan iya adadin kuɗin da Ahuoyzah ya zubar kuwa, duk a Kan ɓacin sunan yaron nan In har suka tashi a banza ai inajin sai ya kwanta ciwo, kasan yan jaridu da gidajen television nawa aka saya kuwa ko dake Kai lokacin baka cikin mu sai sa baza ka sani ba".

"To yanzu me ake ciki?"........... Kafin Hajj Zawaad yace komai wayansa tayi Ƙara duba wa yayi tare da faɗin, "kaga Yan halak yanzu nake shirin Kiran su".

"Waye ne?"........... Alhaji Huzaif ya tambaya. "Alhaji Abid ne " ............ Ya faɗa yana amsa wa tare da sanya wayar a handsfreee. "Hajj zawaad ya akayi kana ina ne?". Faɗin Alhaji Abid Muryar sa wasai wasai, ɗaga Kai Hajj zawaad yayi suka kalli juna shi da Alhaji Huzaif sannan ya ce, "Ina gidan gona, ta samu ne naji muryar Ka normal".

"Ai Ka bari abubuwan farin ciki sai faruwa suke, labarai biyu ne amma dai bari na fara da wannan ɗin, kasan burin mu na daf da cika kuwa?".........."Kai da ALLAH fa, shaqa min mana?". Hajj zawaad ya faɗa cike da zumudi.

"Yau Allah yayi fa, mutanan ne suka aiko azo a naɗe yaron can Amjad dama nace muku ai bincike sukeyi suna haɗa bayanai, to fa shi yanzu tasa ta ƙare dan saidai ya ƙare rayuwar sa a babban kurkukun ƙasa, kuma daɗin daɗawa gashi gobe za'a shiga koto nan ma ga yarinya da iyayenta babu. Shi kuwa kaga yau dashi da duk wani masoyan sa basu ba bacci"........... Ya ƙarashe yana gaggaba dariya, dariyar shima Hajj zawaad yayi ransa fess yayinda Alhaji Huzaif ya ɗan murmusa dan bayaso Alhaji Abid yasan suna tare da Hajj zawaad.

"To yanzu zyaa wallafa ne ko kuwa?". Hajj Zawaad ya tambaya.

"Waya Gaya ma , ai sai an gama da kotu gobe idan an naɗe shi anyi gaba, sai kuma mu sanar wa duniya da namu labarin ".

"Kai Amma naji dadin wanna batu naka alhaji Abid gobe sai mu haɗu da wuri ko saboda a Ƙara tattaunawa".

"Eh zanyi magana da Sir Ahuoyzah ma abinda yace dani zan turawa kowanne ku saqo yanzu ma ina kashewa Alhaji Huzaif zan Kira".

"To kace labarai biyu ne........" Kafin ya ida Alhaji Abid ɗin ya riga shi da faɗin, "Anjima cikin dare kayan mu zasu sauka fa "............"Kayi magana dashi ne?".

"Shi wa?"......... Alhaji Abid ya tambaya.

"Ka fa san wanda nake nufi"........Dariya Alhaji Abid yayi kafin ya ce, "Tun ɗazu fa, yace dai na saurari kiransa, idan an kai inda aka saba kai wa zai kirani".

"To amma Alhaji Abid wani hanzari ba gudu ba, dukkan mu munsan kuɗin kwayoyin nan sunfi haka, amma sai a wani ce mu rabasu a mafi ƙanƙantar farashi baka ganin anan ma baza mu haɗa wata yar camama ba".

"Ah ah Hajj zawaad, mutamin nan fa ido ne dashi a ko ina, kuma kaga biyanmu yake da kuɗaɗe masu nauyi, inaga kamar in munasan ribatuwa dashi to kawai mu masa yadda yake so, shi ma ya mana yadda muke so, kowa ya zauna lpy".

"Wai shi miye ribarsu da yake zubda wannan miliyoyin kuɗin ba tare da samun wata riba ba sai ma faɗuwa?"......... shuru Alhaji Abid yayi can kuma ya ce, "ALLAH masani, amma su ai ba mahaukata bane da zasuyi abun da babu riba".

"Zaiyi ko zasu yi?"........... Hajj zawaad ya sake tambaya.

"Hajj zawaad bari na amsa wata waya da ALLAH "......... Alhaji Abid ya faɗa ba tare da yabi ta kan tambayar Hajj zawaad ɗin ba. Sallama sukayi ya kashe, sautin hmmm Hajj zawaad ya fitar sannan suka cigaba da magana da Alhaji Huzaif.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._




@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______35 & 36



Lokacin da labari ya zo wa Anah tana ɗaki wurin Dada tana bashi abinci, Kiran Adla ya shigo wayarta ajje bowl ɗin macaroni salad ɗin dake hannunta tayi tare da ɗaukan wayar tayi picking call ɗin, kuka adla ta fashe mata dashi, cikin Muryar kukan take faɗin, "Anah dan ALLAH kiyi sauri ki zo"............. Sosai gaban Anah yayi wani irin faɗuwa Amma ta daure saboda Dada bata so ta yi wani abu da zaisa ya zargi wani abu, dama gashi tun ɗazu yake mata kallon tambayar ina Amjad tace dashi yana lpy yayi tafiya ne Saboda bataso ta tada masa hankali wurin faɗin irin kaikawon da Amjad ɗin yake kan yi Yanzun, amma duk da haka bata ga alamar ya yarda da abinda ta faɗa masa hundred percent ɗin ba. "Shikenan Ina zuwa"........... Duk da idanun Dadan da takeji a kanta bata nuna ta sani ba sai kawai ta ɗauki bowl din da niyyar cigaba da feeding ɗinsa amma sai ya datse bakinsa alamar ya isheshi, kallon sa tayi da faɗin, " ka Ƙara mana ai bakaci sosai ba".

Da ido ya mata alamar a'a ya ƙoshi, tashi tayi ta ɗauko ruwa ta bashi sannan ta goge masa bakin sa, ta kunna masa TV Dan ta rage masa kewa, "Bari na shiga ciki na dawo yanzu"........... Da ido ya amsa da to sannan ta ɗauki bowl ɗin ta fice, duk taku ɗaya da zatayi daidai yake da ƙaruwar bugun zuciyarta, masu aiki ta bawa bowl ɗin sannan ta wuce samanta, tana shiga falon Adla dake waya tana kuka ta saki wayar ta nufo ta da gudu tare da faɗawa jikinta.

Riqe ta tayi ta shiga tambayar, "Adla meke faruwa ne meya faru kike kuka?".........." Anah ya Amjad ya Amjad...." Shi ne abinda take ta maimaitawa.

Ture ta Anah tayi cikin dauriya ta ce, "ke dallah in zakiyi magana kiyi kinji ko, me ya samu Amjad ɗin? Yana Ina ?".

"Anah sojoji aka turo su tafi da ya Amjad kan zargin da ake masa wai an gama bincike za'aje a tsare shi kafin a yanke masa hukuncin "............ Wata hajijiya ce ta ɗauki Anah har saida Adla ta riketa tana faman Kiran sunan ta, da gudu esham taje ta ɗauko ruwa me sanyi. Da taimakon su ta zauna, sannan Esham ta miqa mata bottle ɗin ruwan tana mata sannu amma sai ta ture alamar batason ruwan. "innalillahi wa inna ilaihir raju'un"............ Shine abinda bakinta ke iya furtawa, sai hawaye sharr. "Yana Ina ne yanzu Adla ? Sun tafi dashi ne? Sun sameshi?".......... Duk a jere take jerowa Adla wa'annan tambayoyin Muryar ta na rawa.

"Bansani ba Anah, ai baya gida, inata neman wayan sa bana samu, ya Awais ne ya shigo yana neman ki dan ya sanar Miki abinda ke faruwa a waje amma bai same ki ba, nace masa kina wurin Dada shine ya fadamin wai an baza sojoji ana neman ya Amjad wa......"

" Ya isa haka Adla barni haka, nemo min wayar Juraysh".

Wayar ta ɗauko ta fara kiran number juraysh, Kira ɗaya ya ɗaga, cike da barkwanci ya ce , "Hello Adeedyn Anah, Amaryar Ya Jurays....... ".......... Katseshi tayi daga wasan barkwancin da ya fara kamar yadda suka saba ta ce." Ya juraysh kana Ina dan ALLAH".

Jin yanayin muryar ta ya sashi miqewa ba shiri kamar tana gaban sa ya ce, "Adla lpy? Meke faruwa?"........... Anah ce ta karɓi wayar, "Juraysh hukuma na neman ɗan uwanka ido rufe yanzu, wai zasu tafi dashi wurinsu".

"Anah karki ce min Amjad, su waye suka zo Kuma?".

"Sojojin gomnati mana, wai sun kammala bincike".

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Anah kin gani ko na faɗawa Amjad mu ɗau mataki tun lokacin amma yaqi yace gsky zatayi halinta, Anah in har da gaske anzo tafiya dashi kenan zargin da akewa Amjad tabbatacce ne ya kasance ɗaya daga cikin international human traffickers, saboda hukuma baza ta aiko a tafi da mutum ba ba tare da tayi ƙwaƙwaran bincike ba".........Wani hawayen baƙin ciki ne ya sake zubowa anah Dan ta rasa amsar da zata bawa Juraysh ɗin, ya akayi Amjad ɗinta ya kasance ɗaya daga cikin su? ita ta yarda da Amjad bazai taɓa aikata hakan ba, haka zalika ta yadda bazai yiwu hukuma ta ɗau mataki akan abinda batayi ƙwaƙwaran bincike ba, Wai meke faruwa ne? Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsa sai kawai ta sake rushewa da kuka tare da faɗin, "Sake gwada kiransa mu gani "............ Adla da ta cire wayar daga kunnen Anah ta kashe kiran Juraysh ta shiga neman number Amjad ɗin.


_______________Zaune yake shi da philip gabaɗaya Hankalin sa yana kan Philip ɗin, yana sauraren abinda yake faɗa masa cikin nutsuwa, sanye yake da 3 quarter da vest smooth caramel skin ɗinsa sai sheqi yake. Philip ne ya ce, "Boss a yanzu haka maganar da nake ma ya canza musu asibiti zuwa city clinic"............ Murmushi yayi da faɗin, "Manta dashi yanzu ba tashi nake ba, ya batun mutanan kuwa kasan so nake kafin lokacin da ya eba mana mu gama nasa aikin?" .

"Nayi magana da su danny ai sunce an haɗa 70%".

"Kiramun shi ".......... Ya faɗa yana cigaba da danna normal system ɗinsa, bayan Danny ya ɗaga Philip ya miqo masa wayar, "Hello Danny". Da sauri danny ya nutsu jin muryar Amjad a maimakon Philip, "Good evening Boss".

"How about the people?"........." An haɗa 70 percent out of 100 na mutanan da ka buqata Boss".

"Have you contacted Ace or Ash or kia?"

"Yes Boss, munyi magana"........... Shuru yayi can Kuma ya ce, "kunsan ba aikin mutum ɗaya bane a gabanmu ya kamata ku hanzarta mu gama da wannan"........." Noted Boss".

"Wait danny how about widad?". Ya tsayar dashi daga ƙoƙarin kashe wayar da yake.

"I haven't heard from him yet Boss, you know how he's, sometimes he doesn’t even pick up the call"..........."Don't mind him. Just make sure you check how it's going with him". Daga Nan ya miqawa Philip wayar tare da cigaba da Abinda yake yi.

Bayan philip ya kashe ne ya gyara zama da faɗin," Boss daman"............. Dakatawa yayi tare da faɗin, "uhmmm what's it?"........... "batun su Oga Julaybin"........." Inaji go ahead".

" Accountant ya kirani ya shaida min cewa kuɗaden da suke Zara ya wuce misali, har ya kai yanzu kuɗin da ya kamata ya shiga account ɗin Alhaji nasu yake shiga"........... Ture system ɗin yayi tare da faɗin, "Abinda duk ma'aikatan can suka kasa fahimta shi ne no matter how much they collect, Dada’s wealth won’t end, they just grab what they can and leave the rest. I told Baba Hakim to tell them that Aurum mining’s low‑key now, business stopped. But regarding the refinery, it’s almost that time of year. Since they can get the countries to collect crude oil from them it’s pure profit for us all, as our export percentage would goes up. Kai wai ko daga yadda yaran Ahuoyzah suke son nayi wani abu na tsaida su bai isa shaida ma so suke kawai su zama sune a farko ba wannan year ɗin".

Murmushi Philip yayi yanajin ina ma shi ne da brain din Boss ɗin nasa, in dai wayo ne duk ta inda ka biyo Amjad ya san ta ina zai ɓullo ma.

"Boss yanzu sai batun yarinyar"........... Ɗan ƙurawa wani wuri ido yayi alamar tunani kafin ya ce, " Which girl?" ............ Buɗe waya Philip yayi tare da nuno masa hoton Hushaima tsaye a ƙofar gida sanye da wata yaloluwar riga marar nauyi, ta ɗaure kanta da dankwalin Atampa fuskar nan a haɗe tana hararar wani wuri, gefen ta kuma group ne na maza da matan gidan nasu zaune suna poker kamar yadda suka saba duk dare. Ya ɗan dauki lokaci yana kallon hoton kafin ya ɗauke kansa ya mayar kan Philip cike da neman Ƙarin bayani amma bai ce komai ba.

"Boss a du bayanan dana haɗa a kanta an tabbatar da su uku suke rayuwa ita da kannen ta biyu, mace da namiji, domin har gidan wanda suka fara haya a wurinsa an kaini yace shi ya fara basu gida a garin nan dan a lokacin kowa ya hana su gida ganin dukkansu ba wasu manya bane, sai shi ne ya basu gida haya amma ba wanda ya san daga inda suka zo ko Ina iyayen su, a dukkan bayanan dana samu Kuma ita ke ɗaukan nauyin kanta da Kuma na yan uwan nata, tayi aiki daban daban amma Kuma duk inda ta fara aiki bata daɗewa suke korarta saboda zafin Kai irin nata, an tabbatar min bata da tsoro domin ba ta shakkar kowa da komi, sannan daka zagi ƙannen nan nata biyu gwara ka zagi iyayenta, an shaida min ƙaramar kanwar tasu ce kawai take karatu domin su ko bindiga zaka sa musu a ka baza su iya faɗa ma ɗauko wancan ba da harshen turanci, nayi iyakar bakin kokari na ko zan samu wani bayani na inda suka fito ko iyayen su amma ban samu ba, saidai tana da ƙawa guda ɗaya, yarinyar alhaji zawaad ce ma, ance sun daɗe tare amma kamar ita mahaifiyar yarinyar bata san alaqar su saboda talakawa ne kuma basu da asali".

Numfashi ya furzar tare da furta, "Miye alaqar ta da Alhaji zawaad da Kuma Mahaifin Nayrah?"

"Gsky a bincike na basu da wata alaqa, shi dai Alhaji zawaad mahaifin ƙawar ta ne".........Girgiza kansa yayi da faɗin, "Baka taɓa min binciken abu sau biyu ba, amma a wanna zan baka umarnin yin second round, domin duk wannan info ɗin da ka bani wrong ne". Yana kai wa nan ya maida kallon sa kan kofar da ake knocking tare da ba da izinin shigowa, Aram ne ya shigo tare da durƙusaqa cikin girmamawa ya ce, "Boss kayi baqi fa a waje".

Duba agogon dake manne a bango yayi kafin ya ce, " Baƙi Kuma? Philip akwai Wanda yace zaizo ne?"......... Aram ne ya amsa shi da faɗin, "Boss inaga ko akwai matsala ne domin sojoji ne".

Shuru yayi yana tunani can Kuma ya miqe ya ɗauki system ɗin ya wuce ɗaki yana faɗin, "kaji dasu Philip ina zuwa"......... Yana isa ɗakin ya hango wayarsa dake kan gado tana haske alamar shigowar kira, ƙarasawa yayi ya ɗauka inda yaga sunan Juraysh yana yawo akan screen ɗin, zama yayi bakin gadon tare da faɗin, " Juraysh ya ake ciki ne?".

"Amjad kana Ina ? Hankalin Anah ya tashi saboda an sanar dasu cewa ana Neman ka, an aiko a tafi dakai bisa laifin da ake zargin ka akai"............ Sake gyara zama yayi tare da ɗaga ido yana kallon kansa a mirror dake facing ɗinsa, baka isa gano halin da yake ciki ba a wannan lokacin

26 / 53