Author : Young Writer Category : Tknovels
koya Miki sabo"............."Denmark ka tafi ko? Naga code number ɗin can".
A ɓoye ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi Magana ta riga shi da faɗin, "Kar fa kayi tunanin zan faɗawa wani".
"To Ni yanzu kinji nace ki faɗa ko Karki faɗa ne"............"Nasan ai tafiyar sirri kayi so baza kaso wani yaji ba".
Shiru yayi yana mamakinta duk da ba abun mamaki bane dan yasan duk wanda yasan yayi tafiya a wannan halin yasan tafiyar sirri ce saboda already bashi da ikon fita ko ina a yanzu har sai an gama bincike, saidai kuma gefe ɗaya dariyar zallar ƙuruciyarta yake data ƙasa wani further thinking akan tafiyar, sai kawai ya basar da faɗin, "kaga wife material me riqe sirrin mijin ta, i know you will make a good wife".
Dariya tayi me sauti wanda ya sake sanyashi murmusawa shi ma tare da faɗin, "ko kunya "........... Daga haka suka cigaba da hira yana sake tabbatar mata da ita ɗin tasa ce kuma ba mai rabasu sai ALLAH.
Sun daɗe suna wayar kafin suyi sallama, juyawa yayi da niyyar ajje wayar akan bed ya wuce bathroom dan tashin sa kenan daga bacci ya kirata, text message ne ya shigo wayar tasa, dakatawa yayi tare da buɗewa, Address ne tare da time, Saida ya gama dubawa sannan ya rufe ya cilla wayar Kan gadon ya wuce bathroom ɗin.
Tsawon minti 30 ya ɗauka kafin ya fito waist ɗinsa ɗaure da milk towel, caramel skin ɗin nan tasa sai wani glowing take ruwa na darewa kamar wani jikin kifi, gaban mirror ya tsaya Yana goge jikinsa, kusan minti goma sha biyar ya ɗauka yana shafe shafe kafin ya miqe ya Ƙarasa ya bude wardrobe ɗin ya ɗauko kayan da zaisa Wanda suke cikin ledansu alamun sabbi ne, Kan gadon ya cillasu su ma sannan ya rufe sip ɗin ya bi bayan su. Wata oversized t shirt ce white me karamin hannu tare da wani sky blue ripped jeans, safa ya saka tare da white canvas ya ɗauko white nautilus watch din sa na Company patek Philippe ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa sannan ya ɗauki wayarsa da keyn ɗakin ya fita.
Sanyi ake tafkawa na bugawa a jarida dan kankara ce kawai take zuba ta ko wani angle, sai dai duk yawanci mutanen dake Kai kawo kananun Kaya ne a jikinsu hakan ya nuna sun saba da irin wannan yanayin garin, da ƙafarsa ya dinga takawa ba tare da ya tsaida abun hawa ba sai da yayi tafiyar kusan 15 minutes sannan ya tsaya a wani cafe shop, coffee da cookies kawai yayi order, ba jimawa aka kawo masa.
Kaɗan kaɗan yake kurɓa kamar baya so yana kalle kallen yadda kowa ke harkar gaban sa can kuma ya jawo wayar sa ya shiga contact kamar zaiyi dialing contact ɗin Anah sai kuma ya fasa, WhatsApp ya shiga ya danna mata Kira saida ta kusan tsinkewa ta ɗauka, "Assalamu alaikum Anah".
"Wa alaikum salam, Amjad ya kake?"...........Ta faɗa Muryarta a dake, take yasha jinin jikin sa jin yadda ta ambaci sunan sa kai tsaye da kuma yanayin Muryarta da yaji.
Kwantar da murya yayi dan yasan laifin sa amma sai ya waske da faɗin, "Anah meke faruwa? Lpy dai?" ............."Bakomai. Me kaji?".
"Anah Dan ALLAH"..........Shuru tayi, ya sake cewa, "kiyi hakuri to in na Miki laifi a rashin sani".
"Ina ka shiga tsawon kwanakin nan ana ta neman ka, na kira su Aram sun shaida min rabon ka da gidan wurin kwana huɗu, haka mahaifin ka jikin sa ya motsa akai ta neman ka ba'a samu, tukunna ma ina kaje? Kana sane da cewa satin nan za'a shiga kotu da mutanan can"..........."Anah wanna shi ne kaɗai damuwar ki?".
"Babban mutum bana so Ka ƙara shiga matsala, wadda kake ciki ma ina roqon ALLAH ya kawo mana mafita, duk da nasan baza ka aikata duk wa'annan abubuwan ba, amma na rasa Mesa hankali na ya ƙasa kwanciya, mutane sun sakoka gaba babban Mutum".
Cikin son ƙarafafa ta yayi murmushi da faɗin, "Anah ɗanki fa jarumi ne in sha ALLAH ba abinda zai faru ki kwantar da hankalin ki, sannan kuma batun wannan kotun fa babu ita".........."Ya zakace babu ita".
"Ba zan iya ce dake komai ba Anah amma dai nace Miki baza a zauna kotu a satin nan ba, sannan kuma batun In da nake na danyi wata ƴar tafiya ne amma ba nisa nayi ba, ai kinsan a yanzu bani da ikon barin ƙasa so naje KM ne nan da kwana biyu zan dawo, na takura ne da yawa Saisa na danje na sha iska".
"Ah ah babban mutum karka yi sake, ka kula sosai tunda kaga har sun tunkari kotu da Batun ai kasan sun shirya hujjojin su ko da na ƙaryar ne saboda in basu da su abun zai dawo kansu ne, kotu ai ba wurin wasan yara bace. Bana goyon bayan ka gana da alkalin ko ka nuna sanayya ko dukiya, kawai dai inaso a bayyana gaskiya su kuma ko su waye ke da hannu a ciki a toni asirin su dan nasan tabbas sayansu akayi".
"To Anah duk abinda kikace za'ayi, amma Anah meysa bazan auri yarinyar ba kawai, a gani na hakan shi zai rufe ƙofar duk wani cece kucen mutane".
"Whattttttt Baka da hankali ne Amjad, me kake faɗa haka, karuwar da akayi haya ita da iyayen ta suka maka sharri ita kake so Ka aura anya baka fara shaye shaye ba kuwa".
Dariya ya fashe da ita. "Sorry Anah da wasa nake fa, yi hakuri maida wukar"........... Ajiyar zuciya ta sauke Amma dukda haka hankalin ta bai kwanta ba, kafin tace wani Abu ya tare ta da faɗin, "Anah zamuyi magana anjima ki cewa Dada na ina gaishe shi, anjima zan Kira video call ki hadamu".
"Allah ya kaimu, Ka Kula da kanka"............ Ta faɗa a hankali. Ko da ya kashe wayar tunanin maganar tasa ta shiga yi, tasan halin danta ciki da bai tunda har yayi wannan maganar to akwai wani abu a ƙasa, Ni kuwa nace Anah kin dai san wasu halayen sauran kuma baza aji mutuwar sarki a bakina ba.
Wata number da akayi saving da Juraish ta kira, Anah ɗagawa ta ce, "Hello Juraish.........."
----------------------√
Sauri take ta zabgawa kasancewar yau sun makara shiyasa a maimakon su tsaya girka wani abu kawai ta fita siyo musu kosai, saidai me tana shiga gidan ta samesu sunyi cirko cirko, Sahnish ne tsaye da wasu manyan mutane su uku suna magana, ƙarasa shigowa tayi da sallama tana binsu da kallo kafin ta maida kallon ta ga Sahnish ɗin tare da tambayar, "Sahnish lpy dai? meke faruwa?".
"Wai Malam Ado ne ya saida gidan nan, su kuma suna buqatar mu tashi daga yau zuwa gobe dan ya daɗe da saida musu duk zaman da muke ma a cikin notis (Notice) ɗin da suka bayar ne".
Maida dubanta tayi Kan mutanen kana ta ce, "Malam baku san cewa ya karɓi kuɗin hayar mu bane?".
Ɗaya daga cikin su ne ya ce, " Wannan mu ba damuwar mu bace tsakanin Ku ne dashi, mu abinda muka sani mun saya gida ya kuma karɓi kuɗin mu da shedu da komai, dan har munzo munga gidan ma yace da akwai mutane a ciki amma mu baku notice zuwa lokacin da kuɗin hayar ku zai ƙare, yanzu kuma lokaci yayi munga shiru, Alfarmar da zamu iya muku kawai daga yanzu ne zuwa dare, gobe da sassafe zamu zo karɓar makullin gidan mu".........Ba tace komai ba sai jijjiga Kai da take . Sahnish ne ya ce, "bakomai to, ALLAH ya Kai mu".
"Ameen"............ suka amsa sannan suka juya suka fice. Miqawa Shazeen dake ɗaura igiyar takalmin ta ledar kosan tayi sannan ta ce. "Sahnish ina takardar da malam ado ya baka Lokaci da ka bashi kudin hayar?"..........."Tana ɗaki".
"Dauko mun ita kayi sauri kuma"........."Me zakiyi da ita?". A fusace ta ce "Nace kaje ka ɗauko min Ka tsaya tambaya ta me zan yi da ita to haɗiye ta zanyi ko ma cinna mata wuta kaji".
Bai Ƙara magana ba ya shiga ɗakin sa ya ɗauko mata, karɓa tayi ta wuce ɗakin su ta ɗauko handbag ɗinta ta nufi soron gidan tana faɗin, "Ga ƙosan nan wurin Shazeen in ta gama Ka miqata makaranta".........Kasa cewa komai yayi har ta fice.
Bata tsaya ko ina ba sai gidan Malam ado, dutse ta ɗauka ta shiga buga ƙofar dashi, wata budurwar yarinya ce ta fito tana faɗin, "waye ne da sassafen nan ".........."Ubanki yana nan ?" Ta Tambaya a fusace.
Kallon Sama da ƙasa ta Mata sannan ta ce, "Malama lpy?".
"Yana nan ko baya nan?".........Ta sake maida Mata tambayar.
"In yana nan uwarki zaki masa "........ Wani matsiyacin tsaki Taja sannan ta ce, "Eh ita zan masa, sallamo min Shi".
Shuru tayi tana kallon ta, Hushaima na shirin sake magana ta juya ta shige cikin gidan, ba Jimawa suka fito yana gaba tana bayansa, yanayin tozali da Hushaima ya sha mur da fadin, "ke lpy zaki zo ki damu mutane da sassafe ".
"Kai Asararren tsoho, macuci saurara kaji zuwa nayi Ka dawo mana da kuɗin hayar mu daka karɓa tunda Ka saida gidan".
Wata matsiyaciyar dariya ya kwashe da ita. "Yarinya bari kiji ai ni kuɗi baya shigowa hannu na ya fita, kuma qanin ki ne ya tilasta min na karɓa, dan haka da ALLAH bar kofar gidan nan Kar nasa yarana su miki shegen duka".
Murmushin gefen Baki tayi tare da juya kanta ta ce, " Ina cewa Ka dai karɓa kuɗin hayar?".
"Na karba kuma naci banza, ba ubanda kika isa kiyi".........."Haka kace?"
"Nace na Kara cewa ma kuwa "........... Ya ƙarashe Yana sake gyara tsayuwa, gyada kanta tayi sannan ta juya ta fara tafiya tana jinsa yana ta faman kuri cewa yaci banza tare da aibata su amma ko juyowa batayi ba ballatana ta san yanayi.
Tana shan kwanar layin taji ana kwala mata Kira daga bayan ta, "baiwar ALLAH baiwar ALLAH"......... Tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon mutumin dake Kiran nata dattijo ne amma irin wanda bariki tayi aman su ɗin nan ne dan kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan tasha ne cikakke kuma an buga duniyanci, asuwakin dake bakin sa ya cire tare da tsiyayar ruwa a butar dake riqe a hannun sa ya kuskure bakin sannan ya ce, " Da farko ni sunana Junaidu amma anfi sani na da ilerika, matasa kuma na kirana da Baba ilerika, Dama cewa zanyi meya haɗaki da Malam ado ne tun daga farkon layi nake jin yadda yake ɗaga miki murya".
Saida ta gama Ƙare masa kallo tsab sannan ta ce, "Muna haya ne a gidan sa, ya karɓi kuɗin mu kuma ashe ya daɗe da saida gidan har ma notis ɗin da masu gidan suka bayar ya ƙare, sunzo sun bamu iya yau kawai gobe zasu zo su karɓa makullin gidan su, kuma nazo nace ya dawo mana da kuɗin mu yace yaci banza".
" Tirkashi, indai Malam ado ne zaiyi fiye da haka, cikakken ɗan 419 ne ai, yanzu wani mataki kika dauka?".........."Ka sanshi ne?"
"Farin sani ma kuwa, abokina ne ada kafin tamu ta hadomu muka raba gari, yanzu ke ya zakiyi kin samu gidan ne".
"Ai bazan yadda ba ƙara zan kaishi ko zan tashi sai ya biyani kuɗi na".
"Yauwa yar albarka hakan shi ne daidai ni zan ma yi Miki shaida in kina so".
"Nagode".......... ta faɗa tana cigaba da tafiya , saurin shan gaban ta yayi, "Ya zaki tafi bamu gama magana ba ai, akwai ɗakin haya idan kina buqata a cikin gida na ne ba a wani wuri ba".
Ɗan Jim tayi kafin ta ce, "Bani kaɗai bace mu uku ne saidai idan zaka iya samo min gida me ɗaki biyu".
Washe Baki yayi da faɗin , "Ai indai baza ki damu ba a gidan nawa ma zaki samu ɗaki biyu kuma babu takura, kowani ɗaki dubu 35 ne harda bayi a ciki".
Shuru tayi kafin ta ce, " Zanyi shawara da qanina tukunna".
"To ba laifi, bani lambar telephone dinki"........Karanto masa tayi ya saka sannan ya kirata tayi saving nasa. "To zan saurari kiranki ba"........ Gyada masa Kai tayi alamar to sannan ta koma gida.
A Buɗe ta samu Ƙofar gidan tana sa kai Amla na ƙoƙarin fitowa hakan yasa sukayi Karo, baya kowaccen su ta ja, "Haa basu tafi makarantar bane ko kuma ya dawo?"............"Su waye kuma ?" Amla ta tambaya tana kallon ta. "Su Sahnish mana".
"To ai Nima nayi mamakin ganin gidan a buɗe na ɗauka kuna ciki na shiga kuma naga ba kowa, dama na fito ne zani wani wuri na biyo na karɓi form ɗin nan, Amma meke faruwa na ganki kamar a birkice".
"Bakomai whl ina sauri ne kawai muje na baki Kar na ɓata miki lokaci "...........Ciki suka koma ta shiga ta dauko Mata form ɗin ta dawo, riqo hannunta tayi cikin nata kana tace, "Amla ke kin wuce ƙawa a wurina kin zama yar uwa, ina godia ga dukkan alheran ki garemu bakiɗaya, Dan ALLAH ki cike takardar nan da sunan Sahnish, ina fatan hakan be ɓata Miki rai ba".
Shuru Amla tayi tana kallon ta kafin tayi Murmushi da faɗin, "Ko ɗaya whl raina bai ɓaci ba sai ma jin dadi da nayi, kawai takaicin na da ban karɓo guda biyu ba bansan haka bane ai".
"ALLAH ne bai qaddara Miki asara ba Amla, Dan ni abinda ya shafi karatun ne gabaɗaya bana so domin bashi da amfani a wuri na".
Buɗe baki Amla tayi zatayi magana tayi saurin girgiza Mata Kai , "Dan ALLAH Kar muyi haka dake, bana son ki tambayeni abinda bani da amsar sa, kiyi hakuri".
"Shikenan Hushaima tunda hakan kike so, wani surname da other name zan sa tunda naga ko waiwayar Form ɗin ma bakuyi ba".
"Duk abinda kika sa".........." Ina nufi sunan mahaifi da kaka fa?". Amla ta sake tambaya tana kallon ta, Shuru Hushaima tayi tana kallon wani gefe can kuma ta ce, "SAHNISH HUSHAIMA SHAZEEN".
Cikin rashin fahimta Amla ta ce, "Bangane Sahnish Hushaima Shazeen ba, sunan uba da kaka fa nace Miki ko kin kurmance ne"........... Ta ƙarashe tana aika mata da hararar wasa.
Ba tare data kalle ta ba ta ce, "Bashi da sunan da ya wuce wannan, in kuma wani daban kike nema to saidai fa a hakura"........Tana kaiwa nan ta shige ɗaki ba tare data bari sun haɗa ido ba. Saqale Amla tayi da takarda a hannu tana maimaita sunayen da Hushaiman ta fada Mata kamar me hadda har Sahnish ya shigo kamar wanda aka koro turus yayi ganin Amla, ƙaƙalo murmushin dole yayi da faɗin, "Amla ina kwana?"
"Ina kwanan mu Sahnish".......... Ta faɗa tana ɗan kawar da mamakin dake kan fuskarta. "Ta dawo ne?"
"Eh ta dawo, gwara ma da ALLAH ya kawoka zancen form ɗin nan ne tace a cike ma shi to Amma bansan sunan da zanyi amfani dashi ba wurin baba da Kaka".
"Kai Hushaima akwai kafiya har Yanzun dai ta kafe sai ni ɗin kenan"......... Ya Ƙarashe Yana nufar ɗakin nata saidai kafin ya Kai ga shiga Amla ta dakatar dashi, "karka damu Sahnish hakan ba damuwa bane Kai dai fadamin sunan kawai, ina so in tafi saboda ina da wani uzuri ne".
"SAHNISH HUSHAIMA SHAZEEN".
"Kuma?"..........Ta faɗa cikin daurewa Kai, kallon ta yayi da tambayar, "Wani Abun ne?".
Saurin girgiza kai tayi, "Ah ah ba komai bari naje ɗin, kace Mata na tafi sai munyi waya"........ Ta Kai Ƙarshe tana nufar ƙofar gidan. Binta yayi da kallo ko zai gano dalilin canzawar yanayin fuskar ta amma ya gagara, can kuma ya taɓe baki tare da dage kafaɗun sa ya shige ɗakin Hushaiman Yana Kiran sunan ta.
A tsaye ya sameta ta bawa ƙofar baya tana jin shigowar sa ta juyo tare da faɗin, " yauwa ungo, ga wannan kuma"........ta miqa masa takardar da ya bata ta shaidar biyan kuɗin hayar tare da dubu ɗaya. "Kaje Ka bayar a maka irin wanna rubutun, a wajen kudin asa dubu ɗari maimakon sittin ɗin nan"........."Me zaayi wai?"
"Da hausa fa nake ma magana"........."Eh naji ai me sa zaayi hakan."
"Zaka sani daga baya, sannan mun samu wasu ɗakunan haya guda biyu Amma ba gida guda bane, to nacewa mutumin sai nayi shawara tukunna".
"In dai ke baza ki takura ba sai a kama ɗin, ni bani da matsala, saboda kinga bamu da lokaci daga yanzu zuwa dare ne, Amma kuma kinsan bamu da kuɗi isasshe a hannun mu ko?".
"Kai dai yanzu kayi sauri kaje a maka irin rubutun yanzu Ka kawo min ina jiran Ka".........a aljihu ya saka sannan ya juya ya fita .
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______16 & 17
"Barka da rana Anah".
"Yauwa juraish, yakeka ya gidan?"..........." Lpy kalau Alhamdulillah Anah ya jikin Dada?".
"Da sauki Alhamdulillah, da ALLAH tambaya nakeso na ma"............Sake nutsuwa yayi tare da bata dukkan hankalinsa ya ce, "To Anah ALLAH yasa na sani".
"Baka da wani labari game da abinda dan uwanka yake shiryawa kuwa?"............ Dan gajeren Murmushi yayi kafin ya ce, "Anah Whl Amjad ko ruhin dake jikinsa bai isa yace ga next target ɗin sa ba balle ni, nasani duk a family ni da shi munfi kusa amma ni ma Akwai limit ɗi na dan kwata kwata bai bani irin damar da zan shiga jikinsa ba ballatana nasan duk wani moves nasa, infact ni a fahimta ta mutum ne shi da a zuciyar sa kawai yake ayyanah Abu sai dai ya aiwatar dashi, bashi da alqibla ko ada bare a yanzu da abubuwa suka tabalbale sosai, kwata kwata bashi da abokin shawara. Amma me ya faru ne?".
Zazzafan numfashi ta