BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   21 / 53

60K to 63K   out of 156.9K words

ya kulla alaqa dashi ya Kuma samu irin gold da diamond ɗin HD, tare da bashi offer ɗin zuwa ya kafa brand a ƙasashen su, Amma yaqi yace yafi son yan ƙasar sa su amfana wanda hakan ya janyowa ƙasar farin jini a idon duniya, a hankali ya mallaki rijiyoyin man fetur yana refining ɗin sa tare da fitarwa ƙasashe mabanbanta.

Yana da mata biyu matar sa ta farko Hajiya Zunaira ƴaƴanta Huɗu Julaybin shine na farko sai Nuhail mai bin sa sannan Awais sai Kuma autarsu Mirrah. Duk kan su sunyi aure har da yayansu Mirrah ce kawai take karatu. Sai Kuma ya'yan amarya wato Anah, lokacin da ya auro Anah mahaifiyarsa da danginsa basa sonta kwata kwata dan daƙyar ma suka bari akayi auran abunka da rabo dan da cewa sukayi ba zaa yiwa Hajiya Zunaira kishiya ba. Anah ma ya'yanta huɗu Afiya itace babba sai Durrah sai Amjad sannan Auta Adla .

Alhaji Hashim mutum ne dake son ya'yansa a jikinsa Amma Hajiya Zunaira ta janye ya'yanta ta ɗaura su akan cewa su gina nasu karsu bi mahaifin su su tayashi ya kafa kansa alhalin suna da yan uba, komai ya tara tare zasu raba, hakan yasa yanaji yana gani ya'yan hajiya Zunaira suka gagare shi dole ya haƙura ya bar mata su ya kuma ja bakinsa yayi shuru ya zuba musu ido, har zuwa lokacin da Anah ta haifi Amjad, Alhaji Hashim ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaura masa ko bacci a jikinsa Amjad yakeyi hakan yasa ya taso kamar wani abokin sa, a lokacin da Amjad ya girma ya mallaki hankalin kansa sai mahaifin nasa ya ɗaura shi akan komai nasa dan ko abokan kasuwancin sa da yawa sun ɗauka Amjad ne kaɗai ɗansa namiji dan shi suka sani. Ba wani sirri tsakanin sa da mahaifin sa dan basa boyewa junan su komai harta mahaqar golds ɗin sa da ba kowa ya sani ba Amjad ya sani. Lokacin da su Julaybin suka buɗi ido suka kuma farga da yadda Amjad ke tsaye akan komai na dukiyar mahaifin su ga kusancin dake tsakanin su, a lokacin ne wutar ƙiyayyar sa ta huru a zuciyar su, nan suka fara Neman hanyar da zasu matsar dashi su dusashe taurarin sa sannan su ɓata shi a idon duniya, har suka nemo wasu mutane suka biyasu suka fito suka shaidawa duniya cewa Amjad ya yaudari yarsu ya mata fyaɗe, ɗan iska ne bashi da aiki sai lalata qananan yara, harda shigar da ƙara a kotu, basu barshi haka ba suka bi ta ƙarƙashin ƙasa inda aka fara raɗe raɗin cewa Amjad ɗin na safarar mutane ƙasashen duniya, wanda hakan ya sanya jinin mahaifin su ya hau sosai har ya yanke jiki ya faɗi inda ya kamu da cutar locked in syndrome wadda aka fi sani da paralysis . WANNA KENAN.

Alaqar dake tsakanin su da Ahuoyzah kuma Kan batun kasuwanci ne, shi Ahuoyzah yana da nasa matatar man fetur ɗin Amma kwata kwata baiyi sunan da HD refinery tayi ba, haka yasa suka shirya poisoning din Alhaji Hashim ta hanyar haɗa baki da na kusa dashi domin a sanya masa gubar dake ƙone jini ya mutu, ALLAH bai basu Sa'a ba, sai suka sa aka laqabawa Amjad sharrin fyade da Kuma kasancewar sa ɗaya daga masu masu safarar mutane, domin Ahuoyzah ya samu Inganta nasa refinery ɗin a idon duniya ya maye gurbin HD refinery, su Hajj zawaad Kuma duk yaran sa ne . WANNAN KENAN.

Ramphant juwaira sabon Dan kasuwa ne me tasowa, dan a yanzu ne ya kafa tasa refinery ɗin shima Kuma yakeson gogawa cikin wa'annan manyan a lokaci guda.

Akwai number yabo da kasashe ke bawa duk ma'aikatun man fetur ɗin da suka fi kowa fitar da mai a duk ƙarshen shekara, shine tsakanin Ahuoyzah da Ramphant yanzu suke takarar karɓar wanna number yabo dan yanzu Babu HD refinery a lissafi .


TO KUNJI YADDA ABUN YAKE, SHIN WAYE ZAI KARƁI WANNA NUMBER YABO TSAKANIN WA'ANNAN BIYU? KUMA MA WAI A CIKIN SU WAYE YA AIKATAWA ALHAJI HASHIM DA ƊANSA WANNA AIKIN ? KO KUMA DUKKAN SU NE? IN DUKKAN SU NE YA AKAYI TUNANIN SU YAZO ƊAYA NA ABUNDA ZASUYI ?



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd



STEP 1


PAGE _______28 & 29



Ko da ta shiga ɗakin Sahnish ɗin bacci ta sameshi yanayi saboda harda maganin bacci suka bashi dan ya samu hutu, fitowa tayi ta jawo masa ƙofar sannan ta koma ɗakinta. Ranar bata samu wani baccin kirki ba kawai dai tana kwance ne ita ba ido biyu ba ita ba bacci ba, hakura tayi ta tashi ta zauna tare da dauko wayarta ta duba lokaci 3:03am, maida wayar tayi ta ajje tare da tashi ta fito mutum ta gani tsaye a bakin rijiya Yana ɗiban ruwa daga shi sai shortnicker wanda hakan ya bayyana murdaddun tsokar jikinsa wanda ke shafe da gargasar lallausan bakin gashi, shagala tayi da kallon sa saboda akwai wuta a lokacin har bata san lokacin da ya gama ɗiban ruwan ba ya ɗauka ya wuce ɗakinsa, da kallo ta bishi dan sarai tasan ya ganta ɗauke Kai kawai yayi, ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa zuwa ɗakin Sahnish da har lokacin yake bacci dan haka ta ɗauki bokitin sa dake gefe a ɗakin taje ta dibo masa ruwa ta dawo ta ajje masa sannan ta koma ɗakin su ta ɗauki nasu ta ɗaibo rabi saboda ciwon dake hannunta idan ta ciccika baza ta iya ɗauka ba.

Komawa tayi ta zauna har aka Kira sallah ta tashi taje ta ɗauro alwala, ta tashi Shazeen ma taje tayi. Raka'atanil fajr suka farayi sannan suka tada sallah, tashi tayi ta fita bayan sun idar ta bar Shazeen na azkar ɗin safe, ɗakin Sahnish ta koma har lokacin bacci yake ƙarasawa tayi tare da fara tashin sa, "Sahnish! Sahnish!!"......... Wani irin fargaba tare da tsoro ne ya dirar mata ganin ko motsi baiyi ba, hakan ya sa ta daddage ta Kai Mai duka a dantsen hannun sa tare da Kiran sunan sa da dan karfi.

Bude ido yayi yana kwaɓe fuska alamar zafi ya ce, "Me na Miki da sassafen nan zaki fara duka na?"......... Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi kana ta ce, "Tashi Ka makara har an idar da sallah". Tashi yayi zaune ai da sauri ya saki yar Ƙara, "Wayyooo ALLAH"............saurin riqeshi tayi tana faɗin, " sannu har yanzu kafadar ce?"...........Daga Mata Kai yayi alamar eh.

Cikin tausayawa ta ce, "Sannu, zaka iya tashi ko in samo ma botiki kayi alwalar anan basai kaje waje ba eh?".......... "To ". Ya ce kawai tare da jingina da bangon ɗakin.

Tashi tayi ta fita tana waiwayen sa harda cin tuntube bata dade ba ta dawo da wani ɓantararren bokiti da buta, a tsaye ta same shi yana ƙoƙarin fitowa. "Ana Kai da na tafi ɗauko ma kuma Ina zaka".

"Zan Kama ruwa ne, zan iya ai karki damu".........." Muje to ". Ta faɗa tana taimaka masa suka fita daga ɗakin , tana tsaye a tsakar gidan har ya gama abinda zaiyi suka koma ɗakin nasa yayi sallar sannan ya koma ya kwanta, sannu ta dinga jera masa har ya koma bacci kamar ba ita bace jiya take cewa gwara ya mutu kowa ya huta.

Tashi tayi ta fita, ta rasa me zatayi zuciyar ta gabaɗaya a cinkushe take, haka duniyar ma juya Mata take dan abin da zasu karya ma in tayi wasa sai ya gagare su, Dan kuɗin da take jalalawa bai kai ya kawo ba Shazeen ta fara zazzabi sukayi jigilar allura daga nan Sahnish shi ma ya amsa shikenan dan ragowar kuydin shi ma yabi ruwa sai abinda ba'a rasa ba yan canjin da basu fi dubu daya da ɗari biyu ba, gashi har yanzu wata baiyi ba bare ta karɓa albashin ta.

Ɗaki ta koma ta zauna tare da zubawa Shazeen ido wadda ta koma bacci akan abun sallah, a zahiri Shazeen ɗin take kallo Amma a baɗini hankalin ta yayi wani wurin, har saida rana ta fara fitowa sannan ta tashi Shazeen dan tayi Wanka tayi shirin makaranta saboda ita yau batajin zata fita aiki kawai zata kira hajiya ta sanar da ita baza ta samu zuwa ba.

Tana nan zaune har Shazeen ta shiga wanka ta fito ta sanya Kaya anan ne tasan dole fa saita tashi ta samowa mata abinda zata karya.

Hijabinta ta ɗauka tana faɗin, "Zanje na samo miki abinda zaki karya, zaki zauna nan ko zaki tafi ɗakin yaya?"........."Zanje ɗakin yaya ". Shazeen ɗin ta faɗa.

"To muje".......... Hushaima ta faɗa tana fita daga ɗakin Shazeen ɗin tabi bayanta, saida taga ta shiga ɗakin nasa sannan ta juya ta fita waje da mamakin jin yau gidan nasu yayi tsit kamar an sauya mutanan ciki, duk wanna karaniyar da hayya hayya ɗin nan babu ita, wurin jamcy me abincin yan gayu ta nufa a nan Yar kasuwar dake ƙofar gidan nasu.

Jamcy ɗaya daga cikin masu hayar gidan ne dake sana'ar siyar da abinci a kofar gidan, ta yi da safe tayi da yamma kuma kullum a wurin ta Hushaima ke siya musu abun Kari haka abincin dare dan tunda sukazo basa girki.

" Sannu Jamcy". Washe baki Jamcy tayi da faɗin, "Hajiya Hushaima har an fito kenan?".

"Eh whl, Danwake zaki bamu".

"To take away nawa ? Sannan me kwai ko marar kwai?".

"Marar kwai, take away biyu"........... Da saurin ta ta amsa da to sannan ta hau zubawa, ta gama ta miqa Mata .

"Amma Jamcy yanzu babu kuɗi a hannuna in na fito anjima zuwa dare zan baki"...........Ta faɗi haka ne saboda bata son taba kuɗin hannunta duk rintsi bata yarda ta bar hannunta ba komai tunda har tasan ba wani suka ajje da zasuje ya basu ba in wani abu emergency ya taso, dama jiya da ba dan abinda ya faru ba ta ƙudindi ne su ne ta bawa me tuktuk nasa ta maqale ragowar dan ko shi Sahnish ɗin baisan ta rage wannan ƴan kuɗin ba.

"A'a Hushaima kinga Kar muyi haka dake, in kina da kuɗi ki biya ki tafi, in baki dashi ki ajje min kayana akwai masu saya ". Ta faɗa dan tasan irin su Hushaima idan kayi bashi dasu kun dinga rigima kenan, ballatana ita da take ganin rigimarta ta girmi ta kowa ba kuma zata iya ja da ita ba.

Shuru Hushaima tayi can Kuma ta ce, " Shikenan naji, yanzu abinda za'ayi bari in na shiga ciki sai na ɗauko miki kuɗin, yanzu na bar Shazeen ciki tana jira kuma makaranta zata kar ta makara".

Miqewa Jamcy tayi cikin rashin mutunci ta ce, "In kin isa na zama titi mota ta dinga bi ta kaina, Nima fa bar gani na haka duk wani salon tantiranci na sanshi dan haka in kinga kin bar nan to kin ajje min kayana ko kuma kin bani kuɗi na, ina ruwana da wata Shazeen , Shazeen ɗin banza Shazeen din wof........" Bata ƙarasa ba taji wani Abu me dumi a bakinta ɗagowa tayi tana kallon Hushaima dake tsaye tana huci ta ƙanƙace birkitattun idanun nan nata ta da lpy lau ma rikita mutum suke bare kuma zuciyar ta motso.

Tofar da abun daya taru a bakinta tayi sai ganin jini tayi guda guda tare da hakori guda ɗaya . "A duk Ranar da wanna ƙazamin bakin naki ya sake furta wani abu marar kyau Kan Shazeen to dukkan wa'annan jerin hakwaran naki saina wargaza su wawiya kawai" .............Ta Ƙarashe tana wurga mata ledar ɗan waken a fuska ta juya ta bar wurin ranta a bace.

A soro ta haɗu da Baba ilerika da alama yau a gida ya kwana, ya sha sabuwar shadda sai kyalli take harda kafa hula aka wani karkaceta gefe, tafiya yake yana wani cilla ƙafa irin duniya daɗi ɗin nan tare da raira yar wakar sa ta mamman shata, fura me nonooo gyadar da sai in ka sauka cikin daji........"

Ganin Hushaima ta shigo rai bace ko ganin gabanta batayi ya sashi kaucewa ya bata hanya ta wuce, "tou ALLAH yayi dare gari ya waye, yau kuma wani me Iftila'in safen ne ya taɓo wanna ruwa biyun?"............ leqa cikin gidan yayi kamar zai bita sai kuma ya fasa, "Kai gwara dai nayi tafiya ta kawai, bari ma kaga kashe wayar nan zanyi Kar ma a neme ni dan yau nisan zango zanyi "......... Ya faɗa Yana zaro wayar tasa ya kashe bai gama maidata aljihu ba yaji sautin wani ihu a kunnen sa.

A lokacin da Jamcy ta gama gane me ya faru da ita wani irin ihu ta zunduma ta Ƙara kurma wani, tsirarrun mutanen gidan nasu da suka maida layin ƙaramar kasuwa suka yo kanta da gudu dukda yau ko rabinsu Babu a wajen.

Da yawa sunga ganin abinda ya faru wasu Kuma basu lura ba, da sauri Baba ilerika ya fito ganin jamaa zagaye da Jamcy ya sashi ƙarasawa da sauri Yana tambayar, "Meya faru?"........ Ɗaya daga cikin yayansa ne me suna Bagimba ya ce, "ita da wanna yar hau ɗin daka kwaso mana ce".

"Ashsha ashsha subahanallahi meya faru haka? Me ya hada su?".

" A gsky Baba ilerika Ka kawo mana bala'i da masifa a cikin gidan nan, shikenan yanzu kuma an fara daga waje, wasa wasa abun ya fara dawowa cikin gida, to whl ko ka sa su bar gidan ko mu mu barshi, Ina dalilin wanna Abu". Faɗin lady Cyama.

Yar charas ta ce, "Ni fa duk kallon su nake yadda suke tsayawa take musu illa, ai whl dani ta taɓo Bala'in mu bazai ƙare ba saidai mu tona rami mu binne Kan mu, ita ɗin banza in aljanu take ji dashi Ni bishiyar kuka ma a kai na ta ƙarƙace".

"Yanzu kun tsaya kuna ta magana ku taimaka Ku kamata a kaita chemist mana ko bakwa ganin har yanzu bakinta jini yake ne".......... haka dai aka kwashi Jamcy aka wuce chemist da ita, Wanda suke da abun sayarwa kuma a wurin suka koma bakin kasuwancin su suna maida zancen yadda akayi.

Ita kuwa Hushaima ko da ta koma ciki, ɗakinsu ta shiga ta ɗauko ragowar kuɗin ta nufi ɗakin Sahnish, a zaune ta same su shi da Shazeen dan sakin fuskarta tayi dan kar Sahnish ɗin ya fahimci wani abu ta ce, "Saida kika tasheshi ko Shazeen?".

"Dama baccin nawa baiyi nisa ba naji shigowar ta".........." To tashi muje na miqaki makaranta karki makara, nan basu fara komai ba, ko ƙosai na siya Miki a hanya".......... Tashi Shazeen tayi ta yiwa Sahnish sallama suka fito, ɗakinsu ta shiga ta ɗauko jakarta sannan Hushaima ta kulle ɗakin, wayarta ce tayi ƙara, Ɗan tsayawa tayi ganin Amla ke Kiran, picking tayi ta maqala a kunne, "Hello Amla?".

"Hello bestie kina gida ?".

"Eh Amma zan Kai Shazeen makaranta yanzu na dawo".

"Okay thom gani nan zuwa ki turomin address ɗin naku, Sahnish Yana nan ai?".

"Eh yana nan baya ma jin daɗi ne ".

"Subahanallahi ALLAH ya bashi lpy, turomin ɗin kawai sai nazo"......... Da "To". Ta amsa sannan sukayi sallama ta kashe, ajiyar zuciya ta sauke tare da kama hannun Shazeen ɗin sukayi waje.

Saida ta tsaya ta siyawa Shazeen da Sahnish ƙosai a leda daban daban sannan ta tsare musu abun hawa suka wuce, Saida taga shigar Shazeen ɗin cikin makaranta sannan tace da me tuktuk ɗin ya juya da ita, daga hanya tace ya ajjeta sanin in tace ya maidata inda ya ɗauko su kuɗin zaiyi yawa.

Da ƙafarta ta taka har gida tana shiga ta wuce ɗakin Sahnish, Yana kwance Amma ba bacci yake ba kamar dai me tunanin wani abu, ajje masa ledar tayi a gabansa da faɗin, "Ɗauki kaci ka samu ka sha magani". Kallon ta yayi da faɗin, "ke kuma fa?".

"Naci".........Ta amsa ba tare data kalle shi ba. Bai sake cewa komai ba, ita Kuma ta juya ta fita ɗakinta ta koma ta share ta kimtsa komai a muhallin sa, Kira ne ya sake shigowa wayarta ta, da sauri ta ɗauka da faɗin, "Hello Amla!".

"Gani a kan layin kizo ki shigo dani".

Da "To". ta amsa sannan ta tashi ta fito gaba da gidan kaɗan ta hango wata mota mai huci duk da ba motar da Amlan tazo rannan bace Amma ta san dama Amla bata hawan mota ya wuce wata ɗaya bata sauya wata ba, Dan haka ta nufi wurin, tun kafin ta ƙaraso Amla ta buɗe motar ta fito tana wani yauqi kana ganinta kaga model, sanye take da farin jeans da riga doguwa data kai mata har qauri tana da yanka daga both side tun daga kan faffaɗan waist ɗinta har ƙasa red colour, sai wani dan ƙaramin veil data yafa Wanda ya zame daga kanta ya koma kan kafaɗarta, gashin nan daya sha kuɗi sai ɗaukan ido yake, ga ƙafarta tasha wani arnen heels.

Rungume juna sukayi Hushaima ta ce, "Yanzu nake shirin kiranki in ji ALLAH yasa ba kwantaccen nawa kika kasa ganewa ba, Kar naje na ɓatar da yar mutane azo a naɗeni".

Ɗan dukan kafaɗarta tayi tana dariya ta ce, "ke kin fiya Neman Magana, yanzu mu ƙarasa ciki dai, ya jikin Sahnish ɗin".

" Da sauki fa "........... Ta faɗa tana wucewa suka ƙarasa ciki, da wani irin kallo Amla ta dinga bin gidan da mutanan cikin sa dan bata saba ganin irin wanna rayuwar ba, saboda ita banda dalilin Hushaima Amla duk mu'amalarta da masu hannu da shuni takeyi.

A ɗakin Sahnish ta musu masauki, yana zaune

21 / 53