Author : Young Writer Category : Tknovels
muna waya, shi ne take ta fada, Amour na rasa taya zanyi na shawo kan mumu ta fahimtar da dad game da sharrin da akai maka, gabaɗaya taƙi yarda da duk wani abun da zan faɗa mata, nayi iyaka koƙarina amma kullum ma kamar ƙara tunzirasu ake".........Ta ƙarashe cikin yanayin dake nuna tana jin ɗacin maganar da take furtawa.
"Hakan ba laifi bane Ninie, domin abinda mumu da dad sukayi shi ne abinda kowani iyaye nagari zasuyi akan ƴar su, kuma suna sonki ne saisa suka kasa fahimtar duk wani bayanin da zaki musu a kai na".
"Bann... Bangane ba Amour me kake nufi?".
"Ke yarinya ce baza ki fahimta ba, Abinda nake so dake kar muyi gaggawa domin gaggawa daga shaiɗan ne jinkiri kuma alheri ne. Kiyi haƙuri ki sa musu ido kiga abinda zasuyi".
Unexpectedly yaji ta fashe masa da kuka, cikin kukan take faɗin, "Amour kai ma yanzu ka goyi bayan a rabamu kenan? Shikenan dama nasan ni kaɗai nake faman zubin adashin da ba ranar ɗauka. Na riga na san ba so na kake ba, kawai dai ina takura ma ne. Sai ka wani dinga dauka na a banza a banza, an gaya ma in na rabu da kai mutuwa zanyi ne, kai ɗin banza ai da bansan ka ba nake rayuwa, dan haka yanzu ma in na rabu dakai ba abinda zai far...u".........ta ƙarashe Maganar a rarrabe saboda kukan da yaci ƙarfin ta, kashe wayar tayi tare da yin wurgi da ita. Haɗe kai da guiwa tayi ta shiga raira kukanta bilhaqqi da gaskiya dan tana matuqar son Amjad, shi ne first love ɗin ta Kuma da shi take fatan ƙare soyayyar ta.
A bangaren Amjad kuwa kafin yayi yunqurin cewa komai ta katse kiran. Dafe goshinsa yayi da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana riqe da wayar sa, sam baiji zafin Maganar ta ba takaicin sa kukan da takeyi, yasan irin yadda suke ƙaunar Junan su shi da Nayrah domin ba dan Abubuwan da suka faru ba da kuma wanda ke kan faruwa a yanzu to da ba zai wuce wata biyu ba auran su saboda har baiko an musu, to amma ya zaiyi? Zaije ne ya nunawa iyayen ta ƙarfi ko kuwa zai iya canza abubuwan dake faruwa dashi ? Hakurin dai shi ya kamata suyi har komai ya daidaita saidai ita ta kasa fahimtar hakan, gani take kamar bai damu ba saboda shi mutum me zurfin ciki, da wuya ya fito ya faɗi damuwa ko yanayin da yake ciki, wannan yasa Nayrah ke ganin laifin sa. Tashi yayi riqe da wayar sa ya zura mule slippers din sa ya fice daga dakin.
__________sosai ta sha kukanta har ta godewa ALLAH sannan ta tashi da niyyar shiga toilet ta wanke fuskarta kawai taji an turo ƙofar ɗakinta an shigo, saurin waigowa tayi kasancewar ba wadataccen haske a ɗakin yasa a tsorace ta ce, "Nashwa?"..........Shiru taji sai ma locking ƙofar da akayi a tsorace ta bude baki da niyyar yin ihu. "Shiiiiiii"..........Ya faɗa yana ɗaura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tayi shiru.
A tsorace taja baya tana binsa da wani irin kallon tuhuma saboda matsowar da yayi yasa ta gane shi ne, cikin rawar murya ta soma tambayar sa, "Amour y..ya ya akayi ka shigo gidan nan? Taya ma ka wuto duka kofofin gidan nan har ka hawo sama ka shigo ɗaki na bayan ko ina a kulle yake? Na shiga uku! ALLAH yasa ba wanda ya ganka"......... Gabaɗaya a hargitse take jero masa tambayoyin kamar wadda taci kai.
Harɗe hannuwan sa yayi a ƙirji yana jifanta da wani irin narkakken kallo mai cike da tsantsar ƙauna, ya buɗi baki da faɗin, "A kanki ba irin kasadar da bazan iya ɗauka ba Ninie, ko da kuwa sanadin hakan zan rasa rayuwata ne. Ki nutsu muyi Magana".............. girgiza masa kai ta shigayi tare da faɗin, "Bazan iya ba, I'm afraid ina tsoro Amour wani zai iya zuwa ya gan ka".........Ta ƙarashe ko ina na jikinta na rawa.
Fisgota yayi tare da riqo kafaɗunta da hannayen sa idanuwan su cikin na juna sai dai ita kallon firgici take masa, sake kwantar da murya yayi wurin faɗin, "Ina son ki ninie, duk duniya ALLAH ne kaɗai zai iya rabamu saboda dama shi ya haɗamu, ita soyayya a zuciya take ba wai a baki ba, domin daɗin baki in yayi yawa ƙarya da yaudara ne ke shigowa ciki. Ina son ki ninie, ki yarda dani, ki kuma yarda da cewa ina tare dake duk rintsi saidai idan kece kika gujeni"...........a hankali jikinta yake saki, maganganun sa suna ratsa ta, nutsuwar ta tana dawowa Ajiyar zuciya ta sauke tare da zamewa daga riqon da ya mata ta koma ta jingina jikin bangon ɗakin tana kallon sa. "Ka tafi to, ina tsoron kar wani ya ganka a sake samun matsala".
"Kin fiya tsoro da yawa, in ma an ganni ai kece sila, in dai zaki kashemin waya kina kuka to kuwa a duk inda kike a kuma kowani lokaci zaki iya gani n........" Kafin ya ƙarasa sukaji Knocking, da sauri ta matso wurinsa tana yarfa hannu da faɗin, "Shikenan kaga abinda nake gaya maka ko, yanzu ya kake so nayi"..........shiru yayi idonsa akan Ƙofar ya ce, "Wa kike tsammani a wannan lokacin?".
"Wace irin tambaya ce wannan amour, mutanan gidan mu ne mana, kuma kasan in suka ganka kashi na ya bushe".........ta faɗa cikin raɗa, wucewa yayi bakin gadon ya zauna tare da faɗin, "jeki ki duba".
Ƙara rikicewa tayi sai ta nufi ƙofa ta dawo wurin sa, gashi har lokacin Knocking akeyi. "Ki nutsu kije ki duba". Ya sake faɗa a dake.
Daurewa tayi ta nufi ƙofar ta buɗe tana waiwayen sa, ido huɗu tayi da Mumu dake tsaye tana binta da kallon tuhuma kafin ta ce, "Yau kuma wani munafurcin ne yasa kika kulle ƙofar?"..........Dan Susa kanta tayi, cikin alamu na rashin Gsky ta ce, "Am dam..a dama naji tsoro ne saisa na rufe".
"Ban hanya na wuce"........... Mumu ta faɗa tana kokarin sa kai cikin ɗakin, da sauri ta tare da faɗin, "Mumu dan ALLAH karki shiga ɗakin a hargitse yake gyara nake duk na fito da kayan ".......... Ta ƙarashe tanawa Amjad alama da hannu da ya tashi ya shige toilet.
"Zaki ban wuri ko sai na gaura Miki Mari, uwar me kike boyewa cikin ɗakin"......... Mumu ta ƙarasa tana ture ta tare da shigewa ɗakin. Wani irin tsuma jikinta ya ɗauka, ta kasa ko da ƙwaƙwaran motsi ballantana ta juya jira kawai take taji me zai biyo baya.
Bin ɗakin Mumu tayi da kallo Kafin ta ce, "Me kike shiryawa ?"..........Yadda taji Mumu tayi tambayar ya sata ɗan juyowa, waro idanun ta tayi gabaɗaya ganin ba Amjad ba alamar sa a ɗakin, wurga ido ta shigayi ko zata ga inda ya ɓoye ta ma manta da Mumu dake binta da kallo har sai da ta ce, "Whl ki kiyayeni, idan na gano akwai abinda kike ɓoyewa sai naci ubanki a gidan nan, ki wuce mu tafi Nashwa bata jin dadi kije ki kwana a ɗakinta".
"Ni me zan ɓoye Mumu, dan ALLAH ki yarda dani mana".........juyawa tayi ta fita tana faɗin, "Ni dai na gaya miki, kuma karki ɓatan lokaci ina jiran ki a ɗakin nata, ina so in je in kwanta".
Wata gauron ajiyar zuciya ta sauke bayan fitar Mumu, bincika ɗakin ta shigayi lungu da sako har toilet amma bata ganshi ba, tsayawa tayi tana tunanin ina ya shiga to, tsuwwar da wayarta ta fara yasa ta nufeta tana zuwa taga shi ne cikin sauri ta ɗauka kafin tace wani abu ya riga ta da faɗin, "Karki wahalar da kanki wurin bincike na, ni na riga na tafi, ki wuce ki tafi kinsan Mumu na jiran ki, Kuma ki kula ki kuma rage tsoro dan zaki tonawa kanki asiri ne kawai".
"To wai yaushe ka fita? Ta ina ma ka bi?"........ Ta tambaya cike da tsantsar mamaki.
Ba tare da yabi takan tambayar ba ya ce, "good night, have a sweet dreams of me"..........Yana kaiwa nan ya kashe ya barta saqalo riqe da waya.
---------------------√
Sai da ta Kintsa komai na gidan sannan ta shiga wanka dan tuni Sahnish ya tafi kai Shazeen makaranta, ko da ta fito shiryawa tayi ta dauki Jakarta ta fita tare da kulle gida ta saka maqullin a jaka. Abun hawa ta tara sannan ta shaida masa inda zai Kaita. A gaban wani ratsatstsen wuri da a saman aka rubuta STARLIGHT BEAUTY CO. Suka tsaya, sallamar me tuktuk ɗin tayi sannan ta shiga wurin. Babban wurin ne da ya gaji da haɗuwa, kallo ɗaya zaka masa kasan wuri ne na masu hannu da shuni, ba abinda ba'a yi a wurin kama daga kan su saloon, spa, pedicure, manicure, henna da sauransu. A reception ta tsaya suka gaisa da receptionist ɗin sannan ta ce, "Mai wajen fa?"..........Dan kallon tuhuma matar ta mata kafin ta ce, "baiwar ALLAH lpy dai?".
Ƙasa ƙasa ta watsa mata wani kallo sannan ta ce, "lpyr ce ta kawo haka, gyaran jiki zata min, ni amarya ce Amma bana son aikin yara kuma bana son wasa saisa nafi buqatar nayi magana baki da baki da ita"......... Sai da receptionist ɗin ta sake ƙare mata kallo sannan ta ce, " Bata zama yau, Amma kinyi sa'a yanzu nayi waya da ita tana hanya, kina iya zama ki jira ƙarasowar ta".
"Eh to, ALLAH yasa karta daɗe dan ina da uzuri"........ Ta ƙarashe tana wucewa ɗaya daga cikin kujerun dake reception ɗin ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya kamar wata shegiya, bin wurin ta shigayi da kallo tare da jinjinawa samun wuri irin na masu kuɗi, kawai mutum yazo ya biya dubunnen kuɗaɗe dan kawai a yanke masa farce ko kuma a wanke masa ƙafa.
Bata daɗe da zama ba wata babbar mata ta shigo. "Barka da zuwa Hajiya"........ Receptionist ɗin ta faɗa tana fitowa daga wurin da take wanda wani gajeren gini da akayi ya kewaye tare da barin wurin shiga da fita kamar kofa, an yi plan din abun ne kaman zagayayyen table tare da sanya kujera daga cikin cycle ɗin saidai shi ba table bane hasali ma da gini ne aka manna masa tiles.
"Yauwa jumayma, ya kokari?" .........Ta faɗa cikin sakin fuska. "Lpy kalau Hajiya"..........."To masha ALLAH"........ Ta faɗa tana wucewa ciki, jumayma ta rufa mata baya.
Bata jima ba ta dawo hannunta dauke da tumbler da kwalin exotic, stool ta janyo ta ɗaura akai tare da faɗin, "Ga lemo Ki sha, na faɗa mata, ki ɗan jira kaɗan".
"Ba damuwa"............Ta faɗa cikin tsare gida kamar wata uwar masu gida, sannan ta ƙara da fadin, "AC Nan naku baya aiki sosai fa".
"Bari a Kara ".......... Jumayma ta faɗa, har hannunta na rawa wurin ɗaukan remote ɗin ta kara mata, sannan ta koma wurin zamanta ta zauna.
Ko kallon tumbler ɗin batayi ba bare lemon, gabaɗaya hankalin ta ma naga TV dake manne a bango tana aiki inda ake nuno labarin wani shahararren wanda ake zargi da laifin safarar mutane zuwa ƙasashen waje, mai labaran ta ƙara da , "Wanda ake zargi da wannan laifi ba kowa bane face Amjad Hashim Darwin, wanda a yanzu duniya gabaɗaya ta zubawa ƙasar nifaz ido ne domin ganin hukuncin da zata ɗauka. Kamar yadda kuka sani shi ɗin ya kasance hatsabibi mai aiki da fuska biyu, ya dau tsawon lokaci yana aikata wannan laifi ba tare da an farga ba. Ruhotanni sun sake bayyana cewa a dukkan record na laifukan da ake samu dangane da laifin safarar mutane shi ne number 1 suspect, Amma kuma ba'a kamashi dumu dumu ba sai dai har yanzu jami'an mu suna iya bakin kokarin su wurin bincike. Yanzu zamu bawa Mutanen mu damar fadar ra'ayoyin su dangane da wannan case ɗin daya rikita ƙasa gabaɗaya akan Number waya kamar haka 091.........." Tana ƙarashewa kira ya shigo, " Hello salamu alaikum".
"Wa alaikum salam".........." Da wa muke tare?" Mai gabatar da labaran ta tambaya.
"Kuna tare da Alfah Zuhair, daga babban birnin Nifaz".
"To Malam Alfah mai zaka iya faɗa game da wannan case ɗin ?"..........."A gsky muna kira ga gomnati data ɗau tsautsauran mataki akan wannan mai laifi ba tare data duba matsayin da mahaifin sa yake dashi ba a ƙasa da kuma duniya bakiɗaya, domin a halin yanzu al'ummah sun shirya tsaf domin ɗaukan doka da hannunsu idan har suka ga gomnati zatayi musu wasa da hankali kamar yadda aka saba banbanta doka a tsakanin talaka da Mai kuɗi, saboda jama'ar gari sun alaqanta wannan jan Lokacin da ake tayi da sunan binciken domin a janye hankalin su daga kan case di......."
"Ranki ya dade, Hajiya ta ce ki shiga"........ Maganar Jumayma ta katsewa Hushaima kallon labaran da take. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta miqe tare da ɗaukan kwalin exotic ɗinta ta wuce ciki. Saida ta tsaya ta jefa kwalin lemo a jaka tana fadin da ganin wannan mai zubin munafukan kasan zatayi baqin hali, ALLAH dai ya ɗaura ni akan oganniyarta ta. Ni kuwa nace ke dai komai akayi ba'a fita a wurin ki Hushaima.
A wani karamin falo ta samu hajiyar zaune, tana ɗaura ido a kanta dariya taso subuce mata ganin fuskar matar kamar kwarya ta sha bille ta ko Ina, sam a shigowar ta bata lura ba ko dan ita tana daga side na kofar shigowar ne. Fisgewa tayi abun ta sannan gaishe ta. Amsawa tayi ba yabo ba fallasa sannan ta ɗaura da fadin, "Sorry na barka kina ta jira, na tsaya wani lissafi ne".
" Bakomai hajiya, dama dai wani dan taimako nazo nema wurinki".
"Taimako Kuma?"......... Ta tambaya tana Ƙare mata kallo ganin batayi kama da mabaraciya ba balle tace bara take katse mata tunanin tayi ta hanyar faɗin, " So nake ki taimaka ki ɗaukeni aiki anan wurin dan ALLAH, ni din bazawara ce miji na ya mutu ya barmi da marainiya, hajiya ga matsin gari na rasa in da zan sa kai na".
Shuru matar tayi kafin ta ce, " Toh baiwar ALLAH ba wai naqi bane amma a qa'ida bama ɗaukan mutum haka daga sama b......" Kafin ta ƙarasa Hushaima ta riqo hannayen ta kamar zata fashe da kuka ta ce, "Hajiya ki taimake ni Dan ALLAH, duk wanda ya taimaki wani ALLAH zai taimake shi, Hajiya tunda har ALLAH ya baki dama da kuma halin yin taimakon Wannan ma soyayya ce da rahama ta musamman, idan kuma har kayi amfani da wannan damar da aka baka don taimakawa, to kai ma zaka samu sakamako mai kyau na lada a wajen ALLAH".
Shiru hajiyar tayi tana tunani kafin ta ce, "Shikenan ka tashi kaje reception wurin Jumayma ka cike form, ba damuwa in sha ALLAH. ALLAH zai kawo mafita"..........Ta Ƙarashe tana bin Hushaima da kallon tausayawa ganin da ƙarancin shekarunta ɗawainiya irin wanna ta hau kanta. Ni kuwa nace an kai wata sharaton.
" In ka cike, ko zuwa gobe ma zaka iya farawa. ya so in kazo sai muyi maganar albashi".......Godia ta fara mata kamar zata ari baki har saida ta tsaida ita da fadin, "karka damu ai duk yiwa Kai ne"........Sai da ta sake mata godia sannan ta fito cike da farin ciki.
Reception ɗin ta dawo, samun Jumayma tayi tana waya kuma ga dukkan alamu hajiyar ce ta kira take sanar mata. Ja gefe tayi ta tsaya har saida ta gama sannan ta ce, "Hajiya tace nazo wurin ki na karɓa Form"........ba tare data kalle ta ba, a wulaƙance ta ce, "Na ji".......Saɓanin ɗazu da ta tarɓe ta da rawar jiki. Drawer dake wurin ta bude tare da zaro Form ɗin ta ɗaura mata pen ta tura mata gabanta , ta koma ta zauna tana sake haɗe girar sama data ƙasa kamar a kanta Hushaiman zatayi aikin.
Zubawa paper ido Hushaima tayi kamar mai irgen rubutun, jin shirun yayi yawa yasa Jumayma kallon ta da fadin, "Ya dai?".........." Kinga kamar fa an samu kuskure a rubutun nan."
Wani kallon rainin wayo tai mata kafin ta taso ta janyo paper da faɗin, " kinga Malama cewa akayi ki rubuta sunan ki, number wayar ki, Adreshin ki, email address, NIN number, Acc number, sunan guarantor din ki, number wayar sa da Adreshin sa. Ai ba wani dogon turanci bane ballantana har ki nemo wani kuskure a ciki".......... Ta ƙarashe tana sake tura mata paper gabanta.
Bata ce komai ba taja biron ta ɗaura kan paper saidai ta ƙasa rubuta komai, sai sake bin rubutun take ɗaya bayan ɗaya, can kuma dai ta ɗago da faɗin, "zan iya tafiya da ita gida gobe in zanzo sai na taho da ita?".
"Zaki iya miss"....... Jumayma ta fada cikin izgilanci tana dariya.
Bata bi ta kan dariyar da Jumayma ɗin ke yi ba ta dauki paper tayi waje, duk da kuwa tasan me takewa dariyar. Da Ƙafa ta shiga takawa saboda akwai ƙarancin abin hawa na haya a unguwar kasancewar layi ne na masu kuɗi.
Saida ta tsaya ta musu cefane sosai wanda zai ɗan musu kwana biyu sannan ta tari abun hawa ta wuce gida cikin farin cikin samu aikin yi.
Wuraren Sha biyu ta tashi ta shiga kitchen domin ɗora musu sanwa, Sahnish ne ya shigo jikin sa duk jini, ga hannun sa a ɗaure da rigar sa da ya cire ya daure hannun da ita. Fitowa tayi daga kitchen din tana faɗin, "Albishir........." Maganar ce ta maqale mata sakamakon ganin sa haka a ruɗe ta shiga jero masa tambayoyi. " Meya faru da kai Sahnish? Meya sameka? Hadari kayi?".
Wucewa yayi bakin Ƙofar ɗakin su ya zauna dakyar ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Ba komai bane fa ɗan ciwo ne naji kawai".......... girgiza masa kai tayi da faɗin, "Baka saba min ƙarya ba, dan haka in kayi dole in gane, taya zaka ce ba komai, ka kalli kanka kuwa "..........."Nace Miki bakomai kawai"..........Ya faɗa still kansa a ƙasa.
Baya baya ta fara kafin ta ce, "Whl idan baka fadamin ba sai naje har garejin naku naji abinda ya faru, in na dawo kuma sai naci qaniyar ka billahillazi. Ya zaka fita lpy ka dawo min haka ga hannunka a daure sannan ina tambayar ka kace min bakomai, Ni zaka maida sauna, ko ka manta na rigaka zuwa duniyar ne".
Ɗan kallon ta yayi kafin cikin ƙarfin hali ya ce, "ki min alqawari ko