BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   41 / 53

120K to 123K   out of 156.9K words

suke mana, a yaushe ma akayi hakan, Ina ita Anooshan take ma? Kawai dan sunga kwana biyu mun saurara musu, bafa zasu mamaye mana wuri ba sannan ace za'a ɗinga nuna mana iko kuma. Inati ya kamata mu nuna musu har yanzu fa muna nan ba abinda ya sauya"........ Take aka fara bata baki ana mata kirari Matsayin ta na babbar Ya' a wurin Queen Hirut Kuma magajiyar Crown ɗin sword of fire kingdom, kasancewar Queen Hirut ya'yanta biyu ne kawai a duniya Azal itace babba sai Anoosha.

"Kai Azeeb maza ɗauko kayan rubutu ka maida musu raddi".

Cikin wata ƙasaitacciyar murya dake nuna Mai ita yana ji da iko da Kuma izzar mulki Queen Hirut ta ce, "Za'a tura musu amma ba yanzu ba, domin yanzu in aka tura musu sunyi nasara a kan mu kenan in har dama sunyi hakan dan su tabomu ne,  Amma shurun mu shi zai fi firgita su ya Kuma sasu a cikin fargabar rashin sanin menene shirin mu, Dan haka zamu tsahirta da maida musu raddi har zuwa kwana biyu ba dai kwana goma suka ce sun bayar ba to barsu"......... Jijjiga Kai Azal tayi alamar ta gamsu da maganar mahaifiyarta ta sannan ta juya ta nufi hanyar barin fadar saboda ranta ya baci sosai baza ta iya cigaba da zama ba, dan a ganinta hakan rainin hankali ne da zubda qima a wurin su, Siberian tiger ɗin ta guda ɗaya ta rufa mata baya suka fice daga fadar.




----------------------√



                WIDAD (JEY)



A Daren nan yana fita Bai tsaya ko Ina ba sai gida sau ɗaya yayi horn wani security ya leqo ganin motar sa yasa ya wangale masa gate ɗin, da hannu ɗaya ya murza steering motar ya shige ciki gabaɗaya tukin ma yanayin sa ne a kasalance kamar bayaso, dan kamar yadda yake motsa steering wheel ɗin da hannu ɗaya haka ma da kafa ɗaya yake amfani wurin break da clutch dan ɗayar ma tuni ya naɗeta akan seat. Saida yayi parking jikin jerin jibga jibgan motocin dake parking lot ɗin sannan ya buɗe motar ya fito a hankali, gyara zaman rigar dake jikinsa yayi sannan ya doshi building ɗin gidan nasu cikin takun nan nasa na yanga. Key ya zaro a aljihun sa ya buɗe ƙofar ya shige, duhu ne ya mamaye ganinsa dan duk an kashe wutar falon alamun mutanen gidan sun kwanta. Amfani yayi da hasken screen ɗin wayarsa don ganin hanya, direct upstairs ya nufa, tun daga kan stairs yake jin kukanta hakan ya sashi ƙara ɗan sauri, yana zuwa ƙofar ɗakin ba tare da yayi knocking ba yasa hannu ya murda handle ɗin ƙofar ya shiga.

Wata budurwar yarinya na hango zaune bakin gadon kwata kwata baza ta wuce 17 years ba tana sanye da silky pj's silver colour, hawaye ne ke zuba akan fuskarta tasa wata baby da baza ta wuce shekaru uku ba a duniya, kuka yarinyar take shaɓe shaɓe da hawaye, kyakyawar gaske ce dan kallo ɗaya zaka mata ka hango tsananin kamannin ta da Widad har ma ta ɗarashi a kyau dan ita farace sosai kumatun ta har wani ja ja yake. Tana ganinsa ta fara miqa masa hannu tana Kiran baba tare da ƙoƙarin sauka, ƙarasawa yayi yasa hannu ɗaya ya ɗauketa ya sabata a kafaɗar sa tare da kallon budurwar ya ce, "Me haka Najmah, dama in tana kuka haka kike sata gaba kina kallo, baza ki iya lallashin ta bane ko bakisan in Kukan ya mata yawa zai iya sata ciwon ciki ba, ina ma wancan lalatacciyar take?"........ Magana yake a fusace cikin faɗa Amma muryar sa sam ba hayaniya ko kaɗan.

"Ni ya Jey na rasa ya zan mata ne ina ɗaki ina bacci na jiyo kukan ta, shi ne nazo na dubata kuma tun ɗazu nake lallashinta taqiyin shiru".........."To meysa baza ki tafi da ita ɗakin ku ba".

"Ya Jey kasan halin ya Azhar, yanzu sai tace munzo mun hanata bacci da hayaniya".......... "Okay good yayi kyau"..........Ya faɗa tare da juyawa ya fita, ƙasa ya sauka inda ɗakin sa yake, ko da ya duba har ta koma bacci dan haka ya shinfiɗe ta saman gadon sa sannan ya rage kayan jikinsa ya shige wanka.

Bai jima ba ya fito kugunsa daure da towel Ash colour sai wani ƙarami dake hannun sa yana goge wuyansa dashi, da alama wanka yayi. Gaban mirror ya nufa ya ɗanyi shafa sama sama sannan ya wuce ya zaro PJ's ɗin da zaisa. Sai da ya gama shiryawa sannan ya haye kan gadon tare da ɗauko wayarsa ya shiga dubawa saboda tsawon lokaci bai samu wannan damar ba kasancewar in yana kan aiki ajje duk wani personal abu nasa yake, WhatsApp ya fara shiga messages ne rututu, wata number da akayi saving da emojin heartbreak ya tsurawa ido kafin can kuma ya buɗe message ɗin, video ne aka Turo masa hakan ya sashi rage volume saboda kar ƙaran ya tashi yarinyar sannan yayi playing, lokacin da ya gama kallo gabaɗaya yanayin sa ya sauya tsananin ɓacin rai ya bayyana a fuskarsa in banda huci ba abinda yakeyi, cilla wayar yayi gefe tare da ɗaga kansa sama, Adam apple ɗin sa sai sama da ƙasa yake, wani Murmushin takaici yayi kafin ya dawo da kallonsa kan babyn dake kwance a gefensa a hankali yakai hannu kan lallausan gashin babyn yana shafawa, Ji yake inama zai iya dawo da hannun agogo baya, inama ina ma, ganin tunanin sa zai karkata wani wurin ya sashi tashi ya fice parlour tare da zama ya kunna TV duk dan ya ɗaukewa kansa wancan tunanin dan yasan ko yace zaiyi bacci ma bazai taɓa iyawa ba a wannan yanayin.




-------------------------√


                 AMJAD


Kwata kwata ranar bai samu bacci ba yadda yaga dare haka yaga rana, black tea kawai yake dirkawa cikin sa yana murzar aiki, sai da yayi sallar Asuba sannan ya Kira Nayrah, sun yi kusan minti talatin suna waya kafin sukayi sallama ya ɗan kwanta domin ya rintsa.

_____________A bangaren su Alhaji Abid kuwa haɗuwa sukayi domin sake tattaunawa bisa jagorancin Hajj zawaad da Alhaji Huzaif. Hajj Zawaad ya ce, "Kunsan meysa na nemi mu haɗu mu sake tattaunawa kafin isowar mutumin nan nasu Awais, inaso mu danyi wani cuwa cuwa ne domin muma mu ɗan fita da kaurin mu"........ Alhaji Malayin ya ce, "Kamar ya kenan Hajj Zawaad?".

"Kunga ai cewa yayi mu ce dasu za'a cire musu 30%, to ni abinda na gani mai zai hana mu ce wa mutumin za'a ɗauke masa 25% mu Kuma 5% ɗin sai mu rabeshi a tsakanin mu, kunga ai mun ƙaru ko ya kukace?"........... Alhaji Hammoud yayi saurin faɗin, "Maganar ka haka take Hajj Zawaad nima nayi wanna tunanin Kai ko 20% muka ce an cire masa amincewa zaiyi wa yaqi sauqi saboda kunga whl sir Ahuoyzah yana samun abinda yake so, to mu fa ya zubda mu kenan tunda dama amfanin mu Kenan, shekara nawa muke aiki a ƙarƙashin sa bacin albashin mu me muke samu, mutumin nan fa ko wayar mu baya ɗagawa direct ballatana ya saurari wata matsala ta mu".

Alhaji Huzaif ya ce, " Tabbas maganar ku haka take kawai ayi hakan tunda a tsakanin mu ne, mu kashe mu binne Kar kowa yaji ko ya kace Alhaji Abid?".

"Ai ni duk yadda kukace to fa daidai ne kawai ayi sha'ani".......... Haɗa ido Hajj zawaad da Alhaji Huzaif sukayi wani makirin murmushin nasara Hajj zawaad yayi tare da gyara zama aka wani ɗage ƙafa ɗaya aka ɗaura kan kujera tare da faɗin, "Ni fa Kun sani ne ? har na fara tunanin shiga siyasa da zarar komai ya tafi yadda nake so takarar minister man fetur zan fito kawai ayi me gabaɗayan".

Dariya Alhaji Abid ya kwashe da ita tare da faɗin, "Kai Ka rufawa kanka asiri, in dai baso kake ka zama ministan yan kurkuku ba, Dan whl kana shiga siyasa sunan duk wasu asirin mu ya tonu ne, kaiiiii Hmmm siyasa fa ? Lalle ma Hajj Zawaad me ya shiga kanka da yawa haka ko dai kai ma kabi layi ne".

"Kai ai kaji Baka faɗan alkhairi Alhaji Abid, amma fa da gskyr ka dan abu na farko ma da za'a fara tonowa shi ne batun harqallar ƙwayoyin nan"......... "Ah to ina baka kana ki".

"Ah ah to ai in hakane Wanda yake shigo dasu har yake raba mana ai shi za'a fara kamawa"........ da sauri Alhaji Abid ya ce, "ka.. ka sanshi ne?"........ "Ina zan sanshi bayan duk kabi ka kididdibe shi gani kake zamu kwace ma hanya ".

"Ahh haba Hajj Zawaad ai duk mun zama ɗaya ai ba wannan a tsakanin mu, Ka gane shi ɗin ne baya so mutane da yawa su san fuskarsa saboda shi ɗin babba ne, hakan zai iya jawo masa matsala, jiya ma yace min akwai wani babban contract da za'a kawo zai kuma sanya sunan mu a ciki".

Alhaji Malayin ya ce, "kaiiiiii mutumina harka sai faɗawa take ". Ya ƙarashe yana bawa Alhaji Abid ɗin hannu suka tafa cikin jin daɗi.




*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
            

_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._

⭐MALLAKIN⭐
               *SULTYWRITES*
                         A-K-A
               [YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._

  

@wattpadd sultywrites22


           STEP 1


PAGE _______56 & 57


____________zaune suke dukkan su a falon mahaifiyar su hajiya Zunaira suna fira cikin nishaɗi, Mirrah ce ta shigo bayanta maids ɗin gidan ne ɗauke da warmers. A kan Chinese rug ɗin suka yada zango, saida suka fara shimfiɗa leather mat sannan suka shirya warmers ɗin dasu plate akai suka juya suka fita. Kallon Hajiya Zunaira dake hakimce kan kujera ta wani zaquɗo glasses ɗin rashin mutunci kan hanci Kuma tana kallo ta samansa a maimakon ta cikin sa, wayarta take latsawa hankali kwance. "Hajiya ni zan shiga bangaren Anah akwai wani assignment da ban gane bane zanje muyi da Adlah".......... Ba tare data kalle ta ba ta ce, "Sai kin dawo".

Cikin faɗa Julaybin ya ce, "Ba inda zaki dawo ki zauna, ke kenan baki da wurin zuwa sai wurin Adlah sai kace ƙanwar uwar ki ce ita. Ke jakar inace da kanki baya ɗaukan abinda aka koya Miki a class, Okay sai su Adlah ne kaɗai masu kwakwalen ɗaukan karatu ko? Ku Kuma dake taku kwakwalwar ta kifi ce?"......... Dariya Nuhail yayi da faɗin, "Julaybin ka rabu da yarinyar nan Dan ALLAH taje duk inda zata in ma cikin Anah zata koma ta sake haifota ya rage nata, ai ita ba yarinyar goye bace da za'a ce har yanzu sai an haska mata hanya".

"Baza ka gane ba Nuhail abun akwai haushi ne. Duk gamu mun haɗu anan ta zauna ayi hira da ita a'a ita baza ta zauna tayi nishaɗi cikin yan uwanta ba sai wurin ƴar uba ko? to jeki, kifi ruwa gudu"......... A sanyaye Mirrah ta wuce ta zauna kusa Hajiya Zunaira tana faɗin, "Ya hakuri Yaya na tuba bansan Ranka zai ɓaci ba".......... Tsaki yaja Awais ya ce, " Ku da kuka iya magana ma kenan ai ni in Mirrah tayi wani abun ji nake kamar na kamata na nada mata na jaki ko zata dawo nutsuwarta".

"Kaiiii ka maida hankalin ka kaji ko, ƴar tawa zaka naɗawa na jaki, a gaba na ma kake faɗa?".......... Hajiya Zunaira ta faɗa tana ajje wayarta a gefe. " To Hajiya yarinyar ce da Abun haushi Ke kuma Bakya tsawatar mata".

"Ku tsawatar muku nakeyi? kaji yaro, kaga ka barmin Ya' tayi rayuwarta yadda take so, kowa da irin rayuwar da ya zaɓawa kansa Kuma kowa yana da ƴancin yin abinda yaga dama".

Julaybin ya ce, " To ai shikenan yanzu dai duk ba wanna ba, ga abinci ya sauka ya kamata Ku sauqo mu zauna muci, ke Mirrah matso ki zuzzuba mana"......... Sauqowa Mirrahn tayi ta fara serving ɗin su. " A tray ɗaya zaki zuba"....... Nuhail ya faɗa, haka kuwa tayi ta haɗa su gabaɗaya a tray ɗaya tana ƙoƙarin zuba nata ya sake faɗin, "Kema tare zamuci, Hajiya ce kinsan bata zaman ƙasa dan haka zuba mata nata ita"........ Da "To". Ta amsa sannan ta zubawa Hajiya Zunaira nata a plate daban ta tashi ta ɗauko stool ta ɗora mata akai, ta sake dawowa ta zuba mata sanyayyar watermelon and pawpaw juice ɗin da ya sha sanyi har raɓa yake ta suke mata a gefe sannan su ma ta zuzuba musu ta zauna suka faraci.

Ba wanda yayi Magana har suka gama sannan ta kirawo masu aikin suka kwashe suka gyara wurin kamar ba'a ci abinci ba. Julaybin ne ya nisa da faɗin, "Hajiya akwai wasu kuɗaɗe masu ɗan nauyi da zasu shigo ko kina da buqatar wani abu?"........... Ba tare data damu da jin ta ina ko Kuma ta yaya kuɗin zasu shigo ba ta ce, "Ai kasan bamu da buqatar komai a gidan nan ".

"To ke fa?"......... Ya tambaya yana kallon Mirrah. "Nima ba komai Yaya waya ne Kuma jiya aka kawomin 17pro sabuwa, haka mota ma last month Ya Amjad ya sa aka kawo mana sabbi ni da Adlah so babu abinda nake buqata".

Taɓe baki yayi saboda sunan Amjad data ambata sannan ya ce, "To shikenan dama shine abinda muka ce bari muzo mu tambaye ku, tunda ba abinda kuke da buqata zamu shiga mu tambayi Anah itama ko da akwai abinda suke buqata a matsayin mu na manya Kar azo ana ƙananun maganganu ko ba haka ba?".

"Yadda ya muku "............ Hajiya Zunaira ta basu amsa dismissively tana kurɓar juice ɗinta . Tashi sukayi suka musu sallama suka fice suna maida zancen yadda zasu kasa kuɗin da bai shigo hannunsu ba.

A falo suka samu Anah tana kamawa Esham gashinta, ɗagowa tayi tana kallon su cikin wani yanayi dan basu cika haɗuwa su shigo Mata a haka ba indai ba wani abun bane marar daɗi ya faru, Amma dukda haka saita aro jarumta tayi murmushi da faɗin, "Bismillah Julaybin Ku ne tafe"........ Saida sukayi masauki Kan tsadaddun cushions ɗin sannan Nuhail ya ce, "Mu ne Anah, mun sameku lpy?".......... Gaishe su Esham tayi suka amsa Awais ya ɗaura da cewa, "Ya wurin mamanki kuwa ? Su suna can kuma ba'a ganin su, dukda nasan batayi niyyar zuwan bane kawai"........ Anah ce ta amsa da, " Nuhail ai zaman aure take dole sai mijinta ya yarda, kuma already ai duk karshen shekara suna zuwa Hutu hakan ma ai yafi, Amma ta dinga yawo daga wanna ƙasar zuwa wanna ni kaina hankali na bazai kwanta ba"........."Eh duk da haka, ai ko dan rashin lpyr Dada, tunda sukazo sau ɗaya fa bata sake zuwa ba".

"To Nuhail da zuwan Afia da rashin sa ai duk ɗaya ne, dan zaifi amfani ma in ta zauna a inda take tana masa addu'a kawai, kaga ko da sukazo farkon rashin lpyr wurin watan ta biyu amma me hakan ya ƙara?".........Taɓe baki Julaybin yayi kana ya ce, "Anah dama abinda ya kawo mu munzo muji ko kina da buqatar wani Abu ne saboda kinga yanzu duk wasu abubuwan Dada a hannun mu yake, so ya kamata ace mun bincika muji ko da abinda kuke buqata saboda mu sauke nauyi ko ba haka ba?"......... Murmushi Anah tayi duk da a zuciyarta tasan ba wai tsakani da ALLAH sukazo tambayar ta ɗin ba sunzo ne saboda su nuna Mata yanzu fa ba ɗan ta a kan duk wani abu na Dadan. Bata nuna musu komai ba ta ce, "Duk abinda zamu buqata to kafin mu buqace Shi Amjad yayi Shi dan haka bama buqatar komai, ALLAH ya bada Sa'a".

Awais ya ce, "To ai ganin halin da yake ciki yasa muka ce Kar a ɗaura masa nauyi da yawa, in har da wani abu sai ki faɗa ayi ko ba haka ba Julaybin?".......... Girgiza Kai tayi tare da faɗin, "Ko da ace Amjad baya tsaye yanzu a kan duk wani abu na mahaifin sa ba hakan na nufi in yana buqatar kuɗi bazai iya zara bane, daku dashi ai duk ɗaya ne, kuna da iko shi ma yana da iko kawai dai a yanzun Ku ke tafiyar da abun ne sai sa"......... Ta ƙarashe tana murmushi Wanda hakan ba ƙaramin qona ransu yayi ba, Nuhail ya ce, "Well tafiyarwar ma ai da shi yakeyi Amma yazo ya bata rawarsa da tsalle, ni na rasa me muka rasa na dukiya da Amjad zai janyo mana zagi da cin mutunci irin wanna, ai abun da takaici ace qanin Ka na jini wai shi ke safarar mutane, ɗa ga Hashim Darwin fa wadda duk duniya ake yi dashi. Anah abinda baki sani ba fa duk hour ɗaya yawan adadin kuɗaɗen dake shiga Acc na Dada ba'a san yawan su ba amma a haka saboda rashin godiyar ALLAH Amjad ya jefa kansa a wahala, abun kunya whl".......... Miqewa Anah tayi da faɗin, "To Julaybin in kun gama ku gaida gida, ni zan shiga na shirya akwai inda zani ne"........ Tana faɗin haka ta wuce ciki Esham ma ta rufa mata baya.

Kallon Nuhail Awais ya yi da faɗin, "Kaga ni ko ba'a

41 / 53