BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   8 / 53

21K to 24K   out of 156.9K words

ko ina ba sai police station.......


TO JAMAA ME HUSHAIMA TAJE YI POLICE STATION KUMA?




-------------------√




"Hello julaybin"........"Awais kana ina?".

"Yanzu na ke shiga family house, ina ta neman wayarka ana ce min line busy, ance jikin dada ne ba daɗi, shi kuma wannan Baba Sufi ɗin yanata neman wancan matsiyacin yaron, kasan abinda ake ciki, in ya same Shi a waya har ya rigamu zuwa za'a iya samun matsala, saisa ma na hanzarta isowa".

"Nima gani daf da gidan, ALLAH yasa ina kusa da gidan, Ka kirawo nuhail kuwa?".

"Yes inajin ma yana ciki, dan tun dazu yace min ya shigo shi ma".

"Shikenan kaje Ku tsaya kan komai kafin na iso, kasan shi Nuhail ya fiya sanyi sai a gama damu bai sani ba".

"Baka da damuwa Julaybin"........ Da haka sukayi sallama sannan suka tsinke Kiran daidai lokacin da drivern Awais din yayi parking ƙofar shiga part ɗin dada, Buɗe masa akayi ya fito da sauri ya wuce ciki sai faman baza babbar riga yake, a falon cikin ya tarar da Nuhail tsaye shi da Hajiya zunaira mahaifiyarsu. " Hajiya ya na ganku anan kuma? Kai Nuhail ba cewa nayi komai za'ayi karka bar wurin ba, ya zaka dawo Waje ka tsaya".

"Cewa tayi a bata wuri tayi aikin ta fa, to ya kake so nayi da ita".........Tsaki Yaja zai wuce ciki Dr kinal ta fito, Nuhail ne ya nufo ta yana tambayar, "Ya jikin nasa Dr?".

Tana ƙoƙarin basu amsa Julaybin ya shigo shi ma sai hayya hayya babbar rigarsa takeyi. "ya na ganku a tsaitsaye meke faruwa"........ Ya faɗa yana binsu da kallo.

"Amm Ku kwantar da hankalin Ku, muna Kan aiki ne, yanzu nayi wa abokin aiki na Dr Hazeem waya zai kawo min wasu kayan aiki, Amma muna san Ku kasance a kusa gsky incase ko zaa buqace Ku".

"To Dr ko za'a biku dashi hospital ɗin kawai in a gidan abun zai bada wahala"........ faɗin Awais.

"Nop a gidan sai anfi gajarta masa wahala gsky, in sha ALLAH zamu shawo Kan matsalar yanzun ma saboda akwai allurar da ya kamata nai masa to ban taho da ita bane".

"To ba damuwa kuyi aikin naku"....... Nuhail ya faɗa yana cire hular kansa.



__________A guje ta faɗa falon kamar an jeho ta tana faman kiran Anah, "Anah! Anah! ".

"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun, haba Adla irin wanna Kiran har kinsa gabana ya fadi whl, meke faruwa?".

"Anah jikin Dada ne ba daɗi, wai ana ta neman ya Amjad kuma ba'a samun sa, yanzun naga duk su ya julaybin sun iso".

"Subahanallahi tun yaushe?"...... Anah ta tambaya tana tashi daga kishingiɗen da take.

"Yanzun nan! An kira likitoci ma suna kansa har yanzu, kuma su hajiya ma duk suna can bangare".

"Shi ne mu kuma sai yanzu muke ji? Ni dazu ai lafiya na barshi, wuce muje"........ Ta faɗa cikin tashin hankali tana tashi ta wuce gaba. Ta hanyar da zata sadata da bangaren ba tare da sun bi ta compound ɗin ba.

A zaune suka samu hajiya zunaira yayin da su Julaybin ke tsaye suna ta Kai kawo kamar gaske, shigowar su Anah yasa su ɗagowa su duka, Awais ne ya dakatar da Adla dake ƙoƙarin shiga ɗakin, " ke da ALLAH dakata nan, ko duk Baki gan mu tsaye bane, Doctors ne a ciki suke aikin su, kika taho kina neman kutsa kai".

A ɗarare ta ce, "Ya Awais please inaso na shiga naga jikin dada ne dan ALLAH".

"To uwar kinibibi ke kaɗai ya haifa ne, baga Mirrah can ba a bangaren hajiya, ai ko daga can kika zauna kika masa addu'a ta wadatar ba sai kun zo Kuna ƙara tayarwa da mutane hankali ba. koma can ki zauna"........ Julaybin ya faɗa.

Anah ce ta ce, "Hajiya zunaira saboda ALLAH muna gida daya jikin Alhaji ba daɗi a kasa sanar mana".

Wayar da Hajiya zunaira ke latsawa hankali kwance kamar ba abinda ke faruwa ta ajje da faɗin, "Ha'a yau naga ikon ALLAH, ƴaƴana suka kirani suka sanar min ke ina naki ɗan? ina cewa shi aka fara nema ba'a samu ba, saisa dadin Ka haifa da yawa kenan saboda baka san waye me jin ƙanƙa a cikin su ba, kuma in ɗaya bai tsaya ma ba saura zasu tsaya ma, yanzu ba ga sauran ƴaƴan nasa zagaye dashi ba, shi kuma Wanda ya fifita ɗin ya zubar dashi kamar baisan darajar sa ba"....... Jin martanin da Hajiya zunaira ta mayar yasa Anah jan bakinta tayi shuru, ba wai dan bataji zafin maganar ba, sai dan ta san in ta tanka mata hakan zai iya haifar da mummunar bacin rai a tsakanin su bayan kuma a yanzu ba hakan bane yafi cancanta dasu. Gwada layin Amjad ta cigaba da yi amma baya shiga bama network gabaɗaya a Kan wayarta ta.

"Wai Awais ya akayi ba network ne a part ɗin nan tun dazu nake gwada Kiran wanan Dr ɗin har yanzu bai ƙaraso ba".........Julaybin ya faɗa yana ɗan jijjiga wayar sa.

"Whl ni ma na gwada baya tafiya inajin daga MTN din ne"....... Awais ɗin ya bashi amsa shi ma yana faman hawa da sauƙan jirgi (wato flightmode)

Sun daɗe tsaye kafin Dr Hazeem ya iso, Haƙuri ya basu tare da shigewa ciki da sauri, kusan mintuna bakwai suka fito tare shi da Dr kinal ɗin, tashi Anah tayi ta nufe su dan jin yadda Ake ciki. " Ku kwantar da hankalin Ku, jikin da sauƙi dan har ya samu bacci ma, ba kuma wata matsala, kuna iya ma zuwa Ku ganshi"........ Ta faɗa tana nuna musu Hanyar ɗakin da hannu.

Ajiyar zuciya Anah ta sauke yayin da Awais ya bi bayan Dr kinal da Dr Hazeem zuwa waje shi kuma Julaybin ya wuce gaban hajiyar su, yayin da Nuhail, Anah da Adla suka shige ɗakin Dada.

Bayan su Dr kinal sun tafi Awais na ƙoƙarin juyawa ciki, Kira ya shigo masa, ɗagawa yayi Yana faɗin, "Badar ya Ake ciki ne?".

"Ranka ya daɗe Amjad ya tashi zuwa Belgium yanzu".

"Whatttt?"........ Ya faɗa cikin karaji da tashin hankali, "How taya?".



___________Dukan hannun kujerar da yake kai yayi da faɗin, "Taya zaku bar hakan ta faru, kun kuwa San me hakan ke nufi, in har kun tabbatar da tashi Amjad Hashim Darwin to tabbas plan ɗin mu na daf da rushewa, abinda muke gudu yana shirin faruwa, abinda muka binne yana shirin bayyana".

" Shakka babu maganar Ka abun dubawa ce Alhaji Abid".......... Ɗaya daga cikin mutanan dake zaune a ɗakin ya faɗa sannan ya ɗaura da. "Dan kamar mun yiwa Kura sarƙa ne ta warware, kasan kuwa Kan mu zata nufo".

"To ai abinda ya ban mamaki Alhaji hammoud shi ne, taya duk idon da muka baza a garin nan ace har yaron nan ya shirya tafiya bamu samu labari ba saida ya tashi anya kuwa, anya kaiiiiiiiiii da sake, abun nan da mutukar ɗaure kai yake gsky".




------------------------√



Bata jima a cikin police station ɗin ba ta fito ta shiga tuk tuk ɗin data ajje yana jiranta, suka wuce ya maidata wurin aikin nasu, bata samu kowa ba sai su Elijah. Bunayna ce ta ce, "Hushaima kinyi missing bayan tafiyar ki ba ƙaramin rikici aka sha ba"........ Elijah ta ce, "ai tana nan aka fara".

"Amma bata nan ai lokacin da matar tace zata kira police in bata biyata ba daƙyar Hajiya ta bata haƙuri, amma yarinyar nan tayi mirsisi tace bata ɗauka ba wala ALLAH kuma kunyar fito dashi tayi, daƙyar dai nake gaya Miki aka samu tayi wa matar nan transfer ɗin kuɗin sannan aka rabu lpy".

Hushaima ta ce, "Ta dai biya ɗin kenan?".

Wata abokiyar aikin su itama me suna irepa ta ce, "To abun mamaki har tana kuɗin me zaisa tayi sata tunda gashi har tana da kuɗin da ta iya biyanta a Acc ɗin ta".

"Nima dai abun ya ɗaure min kai gsky"....... Bunayna ta faɗa.

Itadai Hushaima bata ƙara cewa komai ba ta nemi wuri ta zauna tare da faɗin, "ALLAH ya kyauta"........Haka suka cigaba da attending customers har zuwa lokacin tashin su wato karfe Shida. Tare suka fito dasu Bunayna, sallama suka yiwa Jumayma a lokacin da suka ƙaraso reception ɗin, ita kuwa ko kallon ɓangaren da take ma take batayi ba dan kwata kwata jinin su bai haɗu ba.

saida suka fito titi sannan suka rabu kowacce ta tsari abun hawa ta wuce gida. Ko da Hushaima ta isa gida, a nan tsakar gidan ta same su, Sahnish na kwance akan tabarmar da suka shimfiɗa ya tada kansa da pillow da ya ɗauko daga ɗaki hannunsa marar ciwo riqe da wayarsa yana scrolling, Shazeen kuma na gefensa tana zane zane jin sallamar ta yasa ta taso da gudu ta rungume ta tana faɗin oyoyo oyoyo.

Riqeta tayi tana ɗan murmushi ta ce, "To ai zaki kada ni kuma, mu zube ƙasa gabaɗaya ".........ta ƙarashe tana riqo hannunta suka ƙarasa wurin
Sahnish, zama tayi tana faɗin, "Sahnish ya jikin naka?".

"Na ji sauki fa, ya wurin aikin naku ?".

"Ahh aiki ba laifi fa, dan daga zuwa saida nayi gamdakatar......" Tsayawa tayi tare da kallon Shazeen sannan ta ce, "Ungo shigar min da gyalen na ciki, ga wayata ma ki haɗa ki kai min ɗakin ki zauna ki jirani yanzu zan shigo kar kuma kimin danne danne a ciki"........ Ta ƙarashe tana miqa mata gyalen da wayar.

"To"........ Ta faɗa tana tashi ta tattare takardunta sannan ta karɓi Kayan ta wuce.

Tashi zaune Sahnish yayi da faɗin, "Inajin ki wani irin gamdakatar kikayi? Ba dai kinyi sabon kamu ba".

Harara ta watsa masa sannan tasa hannu a jakarta ta fito da Kuɗaɗen ta ajje a gabansa tana faɗin, " kalla nan".

Ɗauka yayi Ya jujjuyasu sannan ya maida ya ajje yana kallon ta ya ce, "To ina jinki, ya akayi?".

Labarin abinda ya faru ta bashi kaf, shiru yayi harta gama sannan ya ce, "Sata fa kenan Hushaima".........."AHH sata!, to ni nayi satar?".

"Amma meysa baki maida gabaɗaya ba, kika maida abun hannun kika ɓoye kuɗin".

"Dana zama wawuya ma, ni fa taso qalawa Sharrin satar ALLAH ya ceceni, sannan kuma kace na maida duka, wato ta tafi ma a banza kenan. Amma yanzu da nayi hakan ai gashi an sa ta biya a aljihun ta kaga in da daɗi gobe ma ta ƙara. Ni kuma banyi sata ba, satar min akayi aka bani dan haka ni bani da laifi".

Buɗe baki yayi zaiyi magana ta ce, "karka ƙara ce min komai. kasha maganin Ka?".

" Eh".......Ya faɗa yana komawa ya kwanta ita kuma ta tashi ta shige ɗakin su.

Wuraren takwas na dare ta fito tsakar gidan tana sanɗa kamar ɓarauniya ganin Sahnish baya nan yasa ta riqo Shazeen sukayi soro, tsayawa tayi sannan ta dan rage tsawon ta tare da riqo kafadun shazeen ɗin ta ce, "kinaji, idan yaya ya nemeni kice kai na ke ciwo na sha magani na kwanta. yanzu zan dawo ba zan daɗe ba ki kulle ƙofar ki koma ciki wayata tana ɗaki ki ɗauka kiyi game kafin na dawo kinji"........ Ɗaga Mata Kai tayi alamar toh.

"Yauwa Shazeezee ta, zan kawo Miki bobo in zan dawo"......... ta faɗa tana buɗe Ƙofar ta fita, sai da ta tabbatar Shazeen ta rufe gidan sannan ta ɗaga wata yar baby Nokia ta Kira wata number bayan an ɗaga ta ce, "Saga kunje ne?".

"Yanzu muka fito, kina ganin flashing ɗina to kawai komai ya kammala, mun gama namu".

"Nagode saga sai na jika"......... Ta faɗa tana kashe wayar ta fara tafiya har ta fita daga Kan layin abun hawa ta tsara sannan ta faɗa masa in da zai kaita.

A ƙofar police station ɗin nan ya ajje ta, sauka tayi ta shige ba jimawa ta fito tare da ƴan sanda mutum uku, ganin ta nufi motar Yan sandan yasa mai tuk tuk sauqowa yana faɗin, "Hajiya ya zaki tafi kuma baki bani kuɗi na ba"........ Kallon Sama da katsa ta masa kafin ta ce, " kamar ya ban baka kuɗin ka ba, salon cutar da Kuka koyo Kenan kuma".

"Ahh ke kinga tsaya a ƙofar police station muke whl kika min gargar ina iya shigar da karar ki".

"Kar Ka fasa shigarwar Dan ALLAH, ko ina za'aje ina da gaskiya ta tunda ban shiga ciki ba saida na baka kuɗin ka"........ Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya ce, "ku tsaya wai meke faruwa?".

"Ranka ya daɗe na ɗauko ta na kawo ta nan ne, muna tsayawa ta fice ta shige ciki ba tare data bani kuɗi na ba, na ɗauka jiran ta zanyi saita fito, yanzu kuma ta fito tana neman raina min hankali".

"Ƙarya yake ranka ya daɗe sharri kawai yake son yi min saboda yace min sai ɗari biyar nace ban yadda ba ɗari uku zan bayar shi ne yanzu yake son ya juya zancen".

"Kai miye shaidarka na cewa bata baka ba?".

"Amma dai ranka ya daɗe kasan da ta bani bazan tsaya ba saboda Kan aiki na nake".

"To ke miye shaidar kin bashi".

"Ni nasan na bashi dari uku ƴan dari dari sabbi, kuma a duba in da suke ajje kuɗi a cikin tuktuk ɗin tasu in karya nayi"......... Ƙwafa me tuktuk ɗin yaja tare da faɗin, "Ni bani da sabbin kuɗi ma a kudaɗe na gabaɗaya amma bari za'a ƙure ƙarya".......... Sargeant ne ya ce, "Muje in gani sai in tabbatar"....... tsayar dasu tayi da faɗin, "harda ni za'aje, dan whl bazan yarda ya qala min sharri a banza ba".

" Corpor Hambali Ku shiga mota bari na kashe wanna case ɗin tukunna"........Ya faɗa Yana sasu a gaba zuwa wurin tuk tuk ɗin .

"Ni zaki cuta ko to bari a kure ƙaryar me ƙarya, kikayi wasa sai kin shiga cell ba dai taƙamar ki 419 ba".

"Ayya in baka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama Ka, Ka sani a cell kace ko? to ni in har ta tabbata sharri kamin sai na sa an rufe Ka, azzalumi kawai".

"Kai! Kai! kusan a gaban wa kuke. Bude Ka duba mu gani"......... Buɗewa yayi ya ɗauko kuɗaɗen da yayi ciniki gabaɗaya ranar sai ga sabbin yan ɗari ɗari guda uku da sauri ta ce, "Ka gani ko ranka ya daɗe, bana faɗa ma ba to nima Whl bazan yadda ba ni zai ɓatawa suna ya biyo ni yana min tijara a bainan nasi"........ Shi dai Mai tuk tuk sakin baki yayi kawai Yana kallon ta saboda tsananin mamaki da ya kusa halakashi a tsaye, shi dai yasan bata bashi kuɗi ba, kuma tunda ya dauke ta bai ɗauki kowa ba sannan wannan sabbin kuɗin ba kuɗin kasuwanci bane hasalima a aljihun sa suke ya akayi suka koma cikin abun da suke tara kuɗi a tuk tuk ɗin, tirkashi Anya kuwa mutum na dauko? Yayiwa kansa tambayar da bashi da amsar ta.

Waya sargeant yayi saiga wani dan sandan ya fito, "Constable ka shiga dashi ciki a shigar da tuk tuk ɗin tasa ma sai mun dawo tukunna, saboda sauri muke yanzu akwai aikin dake gaban mu".

"Ranka ya dade ya za'a min haka kuma ? Ni ne fa me gaskiya"........ Harara ta galla masa sannan ta juya ta wuce zuwa motar yan sandan ta buɗe ta shige, sargeant ya shiga shi ma suka wuce, yayinda aka shige da me tuk tuk da tuk tuk ɗin sa zuwa cikin station ɗin.

Sai da suka biya headquarter din Drugs law enforcement agency suka dau jami'an su mutum biyu sannan suka wuce, A hanya taga flashin ɗin saga hakan yasa ta ce, "ranka ya daɗe mu ɗan ƙara sauri Kar su bar wurin fa".

"Ke dai ba kinyi naki ba, ai shikenan yanzu kuma ki barmu muyi namu aikin. Da ace akwai irin Ku a cikin al'umma da bata gari basuyi yawa ba"........ Jami'in da suka ɗauko ya faɗa.

Murmushi tayi kawai bata Ƙara cewa komai ba har suka shiga layin , "Yallabai Ku tsaya na sauka saboda Kar su gane fuskata".

Sargeant ne ya ce, "Eh ai dama ba tare zamu ƙarasa ba, amma kinsan akwai case ɗinki da me tuk tuk ɗin can, saidai ki biyomu a motar hayar".

" To ranka ya daɗe zan biyo bayan ku in sha ALLAH"........ Daga haka suka sauketa sannan suka wuce majalisar su karafiya daga ɗan nesa suka faka motar sannan jami'an nan biyu suka sauka su sargeant kuma suka tsaya kan hanyar.

Suna zaune suna yan bushe bushen su karafiya ya ce, "Jagwa wai ina mutumin naka yayi ne, dan ina ga ni zan nausa nayi yar wawura dan nayi tass ko na cloud babu"........... Zandam ne ya ɓuɗe baki zaiyi magana aka kaiwa kugunsa cafka, "innalillahi wa inna iiii... Ilaih......" Marin da aka wanka masa ya hanashi karasawa, "Zaku wuce mu tafi ko zaku tsaya mana gardama" .

"Ahh ranka ya daɗe tsaya kaji, whl tlh ba komai bane yar jigaret ɗin nan ce kawai muke busawa".

"Ehn zakuje can ku bada bayani ai".

"Qaluuuuuuuuu innalillahi wa inna ilaihir rajuun jagwa hattara, hattara dai"..........Karafiya ya faɗa yana raba ido.

"Kuna yunqurin guduwa ina tasar ƙafafunku aiki"........ Jami'in ya faɗa yana fiddo da bindingar dake bayan wandon sa.

Haka suka tisa keyar su karafiya zuwa mota, tana tsaye taga wucewar su, tsayawa tayi neman abun hawa, saida tayi mintuna kusan ashirin sannan ta samu mai tuk tuk ɗin da ya ɗauketa ta faɗa masa inda zai Kaita.

Ko da ta ƙarasa su Sargeant basu dawo ba da alama suna headquarter ne, haka ta zauna suna ta aikawa junan su da saqon harara itada me tuk tuk , basu jimaba su Sargeant suka shigo, basu umarnin biyoshi office yayi sannan ya shige.

Office ɗin nasa suka bishi, wurin zama ya nuna musu baya ya zauna. Nan ya buqaci su sake masa cikakken bayani, amma a maimakon hakan sai suka kacame da cacar baki ganin suna kokarin tara masa mutane a office ya sashi faɗin, "Ku dakata nan ba tasha bane ko gidan karuwai, nan police station ne kuma kuna gaban hukuma ne".

"Ranka ya dade sharri fa ya min whl sai ya biyani tara"..........kafin sargeant yace komai me tuk tuk ya ce, " Ai ke dama daga ganin ki kinyi zubin yan damfara".

"Ahhhh kwarai ba shakka, to bari kaji nama fasa sai anje kotu, an bi min hakki na".

Har wurin 11pm ana rikici tsakanin Hushaima da me tuktuk, a lalle ta tubure sai ta shigar da ƙara kotu, daƙyar dai Sargeant ya tausheta ta karbi ɗan kuɗin da me tuk tuk ya haƙura ya bayar matsayin tarar sannan ya samu ya sullube ya

8 / 53