BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   16 / 53

45K to 48K   out of 156.9K words

ba wani kayan kirki take sanye dashi ba domin wani guntun custard colour mini skirt ne, sai yar ficiciyar riga data tsaya iya cibiyar ta itama custard colour ta ɗaura wata jacket da tsayin ta zai kai har guiwa grey colour, ta tattare curly golden brown hair ɗinta ta daure in a ponytail style, ƙafarta sanye da high heel René caovilla da igiyoyinsa suka kusan kai guiwarta su ma.

Wata Mata ce ta shigo kallo ɗaya zaka mata kasan ko zata girmewa ta zaunen ba zaifi da shekaru biyu zuwa uku ba, saidai ita fara ce sosai irin farin turawan nan mai kauu ɗin nan kamar takarda, gashinta orange colour Amma ita ba curly bane straight ne itama irin style ɗin wancan ɗin tayi saidai ita ta tufke shi ya sauka har kusan ƙarshen bayanta, sanye take da irin leather skintight ɗin nan black yabi fatar jikinta kamar wanda aka liqa, sai wata halter neck blouse milk da tabi jikinta itama, kunnen ta maqale da bud, ƙafarta Kuma sanye da wani high heel me masifar tsini na Company Versace Kai zaka ce in an taka karyewa zaiyi, cikin harshen turanci me fita da European accent ɗin su ta ce , "Kia you still haven't gotten ready yet, you know we are the ones to pick the boss up from the airport"...... Saidai har ta ƙaraso ta zauna kusa da ita bata sani ba tayi nisa a wata duniyar bata jin Kira, warce wayar tayi tare da yiwa screen ɗin kallo ɗaya ta fice a gallery, ta rufe wayar ta bata tana da girgiza kanta kaɗan ta ce, "Reeslan still? common get up let's go"........... Ta ƙarashe tana tashi ta nufi ƙofar fita tana faɗin, "The boss's flight will land in the next 30 minutes".........Kamar wadda aka tsikara haka ta mike jikinta har ƙyarma yake tabi bayanta tana haɗawa da dan gudu ta ce, "Ashley wait for me please".

Wata orange Lamborghini suka shiga Ashley ce ta shiga mazaunin driver ita kuma kia ta shiga passenger seat, da wani irin gudu ta ɗauki hanya, cikin salo da kwarewa take murza steering kamar me juya spoon a pot.

Ko da suka ƙarasa airport ɗin basu fito ba, a cikin mota suka zauna, kusan 7 minutes sai gashi ya fito kamar ba Amjad ɗin mu ba, dan saida na kalla na sake kalla dan tabbatar wa, ya sha wani shegen aski da ya mugun fito da kyawun fuskar sa, sanye yake da ash suit da tayi mugun karɓar body structure ɗin sa, idonsa manne da wani munafikin black sunshade, fuskar nan baza ka taɓa karantar yanayin da yake ciki ba, hannunsa ɗaya riqe da wani suitcase. Wasu sojoji ne sun kai wurin su bakwai suka nufo wurin sa, tsayawa yayi jim yana bin kaf ilahirin airport ɗin da kallo kamar me shirin aiwatar da wani abu, a maimakon ya miqo da tafiya akan right side ɗin da yake sai ya yanke yabi left side ɗin sa.

Su Ashley da suka firfito daga motar lokacin da suka hango fitowar sa, suka kalli juna Ashley ta ce, "Where's he?"........... Ta ƙarashe tana waige waige amma ko me kama dashi bata hango ba, ita kuma kia gaban bonnet ɗin ta koma tare da ɗage ƙafarta ɗaya ta ɗan lankwasata ta jingina da motar tare da harɗe hannuwanta a kirji saidai ita ƙasa kawai take kallo.

Ashley data gama dube dubenta ta juyo da niyyar zuwa wurin kia wayarta tayi ƙara, dakatawa tayi da tafiya tare da sanya hannunta a aljihun wandon ta dauko wayar ba tare data duba sunan me kiran ba ta ce, "Hello Ace!"........bansan me akace ba daga ɗayan bangaren ta ce, "Okay!".......... Tare da kashe wayar.

"Kia!!!"..........Ta kira ta da dan karfi tare da nufar motar tana faɗin, "let's go, let's go!"...........Bata bawa kia damar tambayar ta ba saboda kunna motar da tayi ta na bata wuta, da sauri kia ta faɗa motar ko gama rufewa batayi ba Ashley Taja motar da mugun gudu suka bar airport ɗin, sai a lokacin kia ta kalleta da faɗin, "Meke faruwa?"

"An dan samu matsala, Ace yace muje zasu zo daga baya".

"Boss fa ake magana?"............Kia ta sake tambaya tana kallonta. Hankalinta na bisa titi ta sake cewa, "Suna tare".......... Daga Nan duk shuru sukayi har suka koma gida.

Suna shiga kia ta wuce daki ita kuma Ash ta zauna anan falon tare da kunna TV, ta bawa masu aikin umarnin kawo Mata kayan taɓawa, time to time take duba agogon dake manne a bango har 12am ta buga, tashi tayi tana hamma ta bi bayan kia da tuni tayi bacci, ruwa ta shiga ta watsa sannan ta fito ta sanya PJ's ta kwanta.

My people nasan kuna cike da tunanin ko ƙasar Nifaz ne nan to ba ita bace, zaku san wace ƙasa ce nan gaba kaɗan.

Misalin 3:00am Kia ta buɗe ido saboda Knocking ƙofar ɗakinsu da akeyi dan dama sam ita bata da nauyin bacci, "who's that?" ..........."you guys should wake up and come out, we are waiting for you in the living room"........... Muryar wani namiji ya daki kunnenta, sai da ta makawa ƙofar harara kamar yana gabanta sannan ta ce, "Mu na zuwa, tun kafin ka fasa mana kunne da bugu"...........Ta ƙarashe tana jan tsaki sannan ta tashi zaune tare da fara tashin Ashley, buɗe ido tayi tare da tambayar, "what?"..........." Get up, they are waiting for us in the living room".

Tana kaiwa nan ta tashi ta fita, tashi itama Ashley tayi tana mirtsika idanunta tabi bayanta, tare suka shiga falon inda wasu maza biyu suke zaune Amjad cikon na Uku, ɗaya kana kallon sa kaga Italian kyakkyawa ne aji karshe, sai kuma dayan da in baifi Amjad fari ba to zasu zo ɗaya, kallo ɗaya zaka masa kasan akwai class.

Duk ɗagowa sukayi suna kallon su Kia da suka shigo, saida suka ƙaraso suka zauna sannan suka farawa Amjad sannu da zuwa. "Thanks"....... Kawai ya ce sannan ya gyara zama da faɗin, "let focus on what brings us here, Ace explain to them yanayin yadda aikin yake".

Dan zakuɗowa Ace yayi sannan ya fara musu bayani dallah dallah banda Amjad daya gama kwashe komai a brain box ɗinsa tun daga Denmark, Har Ace ya gama bayanin sa ya rabawa kowa aikin da zaiyi. Ashley ce ta ce, " What about akil?"........ Ido Amjad ya zuba mata yayin da su kuma suka zuba masa suna jiran jin me zaice, tsawon mintuna biyu suna a haka can ya Miqe yana gyara rigarsa ya ce, "Widad will tell you everything"......yana Kai nan ya sa kai ya fice daga falon wanda yayi daidai da karar shigowar saqo a wayar widad ɗin.

Minti talatin suka ƙara a falon sannan suka tashi kowa ya nufi makwancinsa dukda kuwa lokacin 4:30am na dare kenan.

Misalin karfe 6pm na agogon ƙasar, tsaitsaye suke dukkaninsu a airport ɗin, Amjad na sanye da thaki colour jeans da black t shirt sai black p cap daya dora ya Janyota ta rufe rabin fuskarsa da take tsuke kamar kullum hannayen sa zube cikin aljihun wandon, gefen sa widad ne shi kuma sanye yake da combat jeans army green da sage colour t shirt. Amjad ne ya fara magana ba tare da ya kalle su ba. "Ya kamata mu maida hankali muyi masa aiki fiye da na kowa saboda mu ma mu sami yadda mukeso, especially ke Kiara kina ban matsala a tafiyata ya kamata kisan wannan aikin daban yake da sauran, kuma ni kinsan a hal.........." Bai karasa ba aka fara Kiran pasinjoji masu tashi, dunƙule hannuwansu sukayi su ukun Amjad, Widad da Ace suka nausa da junansu Amjad ya sake cewa ku kula, sannan suka wuce. Saida suka ga shigewar su Sannan suka koma mota suna jiran jin tashin jirgin su sannan su bar airport ɗin.

Bayan an kammala duk wani Abu da ya kamata suka shige cikin jirgin, baza Ka taɓa kallon su kace tare suke ba yadda kowa ya sha murr, ana saura 2 minutes jirgi ya tashi aka fara sanar da cewa an tsaida tashin jirgi saboda samun sanarwa da akayi cewa Akwai criminals a ciki da ake zargin cewa sun shiga da miyagun kwayoyi.

Kallon kallo akayi tsakanin Amjad da widad kafin kowannen su ya ɗauke kai, jami'ai ne suka fara shigowa suna bincike tare da karbar passport ɗin kowanne suna dubawa, tashi Amjad yayi ya wuce cikin toilet ɗin jirgin, hakan yasa Widad shi ma tashi da sauri sai............



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1



PAGE _______21 & 22



Kallon kallo akayi tsakanin Amjad da Widad kafin kowannen su ya ɗauke kai, jami'ai ne suka fara shigowa suna bincike tare da karɓar passport ɗin kowanne suna dubawa, tashi Amjad yayi ya wuce cikin toilet ɗin jirgin, hakan yasa Widad shi ma tashi da sauri sai wani jami'i ya sha gabansa da faɗin, "Your passport?"............ Komawa yayi ya zauna tare da miqa masa passport ɗin, karɓa yayi yana dubawa yana kallon sa har ya gama sannan ya miqa masa, tare da sanya portable millimeter wave scanner yayi searching ɗinsa sannan yayi gaba.

Amjad kuwa yana zuwa toilet din ya shige ko kula ma'aikaciyar dake tsaida shi baiyi ba ya shige ya rufo, buga masa ta farayi Amma shuru ba alamun zai buɗe, zuwa lokacin jama'ai uku ne a wurin, kallon su tayi da faɗin, "Make an emergency call"..........daidai lokacin Amjad ya buɗe ya fito yana gyara belt ɗin wandon sa. "Hands up"............ ta faɗa tana nuna shi da pistol ɗin ta, ko alamar yaji bai nuna ba sai da ya gama gyara zaman wandon sa. "Search him "...........Ta sake faɗa tana kallon wasu jami'an mutum biyu.

Bai motsa ba haka Kuma bai ɗago ba har suka gama caje shi tare da miqa Mata passport ɗinsa da wasu ID'S ɗin da suka samu a jikinsa, karɓa tayi ta duba da sauri jikinta ya fara rawa, ba tare daya ɗago ɗin ba ya saki wani killer smirk da shi kaɗai yasan ma'anar sa, ita kuwa faɗi take, " I'm very sorry sir, we misunderstood you da ALLAH kayi hakuri akan aikin mu muke ne"....... Baice komai ba ila hannu da ya miqa mata, da sauri ta saka miqa masa abubuwansa, karɓa yayi yana sake janyo P cap ɗin sa ya har wurin.

Komawa yayi wurin zaman sa ya zauna ba tare da ya kalli inda Widad yake ba Wanda shi ma a lokacin ya zauna ko daga Ina yake Kuma oho.

Daga nan aka fara sanar da cewa an bawa jirgin izinin tashi saboda an kama masu laifin.

A bangaren su Ace kuwa sunji sanarwar da akayi hakan yasa hankalin su yayi masifar tashi sai Kai kawo suke, kiara ta ce, " I need to go inside....."

"To do whattt?". Ace ya amsa yana baza hannu cikin gashin kansa cikin yanayi na rashin nutsuwa.

"You know there's gonna be a problem if we don't do something, so let's go do something about it"............. ta amsa masa a zafafe tana wucewa, cikin zafin nama ya fisgo hannunta tana kokarin faɗuwa ya sanya mata ƙafa ta tsaya cak jijjiga mata Kai yayi da faɗin, "kinsan waye boss sannan kinsan waye Widad har meysa zaki tashi hankalin ki".

"But A......"

"Shiii, mu tafi kawai"............. Girgiza masa Kai tayi ta buɗi baki kamar zatayi magana sai Kuma tayi shuru, sanarwa suka faraji cewa jirgi zai tashi a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, ɗagowar da zasuyi suka hango Kia na fitowa daga cikin airport ɗin tana tura wani Abu cikin aljihun jacket ɗin dake jikinta taku take kamar ba mace ba, tana zuwa ta wuce su ta shige mota tare da ja ta bar airport ɗin gabaɗaya dan dama da mota biyu suka zo Ace da Amjad da widad, sai kiara da Ashley.

"Ni ka hanani amma Kuma gashi ita taje tayi abinda ya kamata"........Rasa me zaice da ita Ace yayi saboda bai san ya akayi ma ya tsaya riqe Ashley ba a maimakon kiara da duk suka san halinta in ta furta Abu to fa sai tayi gata da brain, she's very smart saidai in bataga dama ba Wanda hakan ne yasa Amjad ke warning ɗinta da Kar ta bashi matsala. Tare Ace da Ashley suka shiga mota ya jasu suka wuce gida su ma.

Tafiyar 6 hours 30 minutes sukayi a sama kafin su sauka a babban birnin Nifaz, ko kallon juna basuyi ba kasancewar Widad shi ma haifaffen ƙasar Nifaz ne. Amjad kuwa yana fitowa ya tarar da kamal yazo ɗaukan sa shiga yayi tare da faɗin, " Livy Street".......... Hakan yasan Kamal gane ainahin gidan sa suka dosa.



--------------------√



Kamar yadda ta saba Kiran sallar farko akan kunnen ta akayi dan daman batayi wani baccin kirki ba saboda duk da maganin sauron data sa abun yaci tura kasancewar yanayi na damuns sauraye sun yawaita, kusan kwana tayi tanawa Shazeen firfita. Miqewa tayi ta wuce toilet ɗin nasu dake cikin ɗakin ta ɗauko buta ta fito tsakar gidan, Duhu ne dan haka tayi amfani da hasken wayar ta wurin haskawa ta daibo ruwa a rijiyar data gani a tsakar gidan daga can gefe ta zuba a butar sannan ta ɗauka ta wuce, tana kokarin komawa ɗakin nasu Sahnish na fitowa daga nasa ɗakin, miqa yayi tare da faɗin, "Har kin tashi ashe? na ɗauka zaki makara ai saboda gwajabniyar jiya".

"Wace gwajabniya kuwa, kaji ka kamar jiya muka fara".......... Ta fads tana shigewa ɗakin.

"Yanzu dai na jiraki kenan ki miqomin butar?"........... Tsayawa tayi da faɗin, "Ba toilet a ɗakin ka ne?".

"Ahh lalle jiya a ruɗe kika shigo gidan nan, Saida fa kika shiga kika duba kowani ɗaki duk a lokacin baki lura ba toilet ba".

"Ina fa na lura, ka shigo to in na gama sai na baka".

"Barni in sha iska kinji ɗakin nan kamar kurkuku Yasin, ke dai in kin gama miqomin ai naga ma ga toilet nan a waje".

Wucewa tayi ta barshi, Saida ta ɗauro alwalar ta dawo ta tashi Shazeen taje tayi itama da ragowar ruwan data rage mata, sannan taje ta ɗauko butar ta leqo ta miqa masa ta koma, hijaban su ta ɗauko musu ta shimfiɗa darduma suka tada raka'atanil fajr sannan suka ɗan zauna har aka Kira sallah sukayi, suna gama azkar Shazeen ta koma bacci ita Kuma ta tashi ta fita, samu tayi rabin mutanen gidan duk sun firfito masu ɗiban ruwa sun bi layi dan guga ɗaya ce haka zalika da yawa daga ɗakunan basu da toilet sai wanna na waje guda ɗaya, ɗakin Sahnish ta wuce inda ta tarar dashi zaune kan Abun sallar da ya idar da sallah zama tayi da faɗin , "Sahnish dole fa mu nemi stove kaga dai ba zai yiwu na kunnawa mutane gawayi a ɗaki ba a zo a samu akasi na babbakawa mutane guda".

"Nima tun jiya nayi wanna tunanin amma Kuma kina da kuɗin ne a hannun ki ?".

"Babu whl dan abinda ke hannu na baifi na ɗan Abun da zamuci ba a hakan ma inaga ba zai Kai mu wata ba, har Ina tunanin ko zan tambayi wani abu daga cikin albashi na, sannan Kuma ga batun canzawa Shazeen makaranta".

"Canjin makaranta Kuma ?".......... Ya tambaya yana jifanta da kallon mamaki.

"Eh suna Ƙare zango nan kuwa tunda dama zangon karshe suke zasuyi canjin aji, zan nema mata wata me haɗe da islamiyya kawai Wadda in ta tafi tun safe sai 6pm ko 5 ".

"Meysa to?"

"Ni da Kai ba yara bane munsan daidai da ba daidai ba amma ita fa? zaman gidan nan zaiyi matukar tasiri akan tarbiyyar ta ya Kuma gurɓata tunanin ta".

Ajiyar zuciya Sahnish ya sauke da faɗin, " ALLAH ya kawo yadda za'ayi, nima yau zan fita lalube na ALLAH yasa na dace".

"Amma kasan Kai zaka ɗauko ta daga makaranta ko, Kuma in ka ɗauko ta karka fita ku zauna a ɗaki sai lokacin islamiyyar su yayi ku fita tare".

"Aiki sabo kenan".

"Haka zaka daure, ni bari kaga naje na shirya ban ma san inda zan samu ruwan ba naga sunyi layi kamar masu karɓar sadaka gwara nasan nayi tun wuri "........... Ta ƙarashe tana tashi ta fice, layin data gani yanzu yafi na ɗazu dan haka tayi saurin shiga ɗaki ta ɗauko bucket ɗin su tazo ta sa a layi sannan ta koma kan wani benci tana kallon masu Kai kawo daga masu ɗaura kirji sai masu vest Kuma harda matan aure wai, wani mutum ne ya fito daga wani ɗaki hannu maqale a kirji sai wani gatsina yake, "Rama ke rama kina Ina ne fatan dai kin samun bokiti na dai, Dan nace Miki yau sammako zanyi zamuyi tafiya da Alhaji".

Rama dake ebo ruwa ta ce, "Da ALLAH Shamsy karka dameni ni, ladanka na samu ma da zan ebo ma ɗin".

Sake noke hanci yayi da faɗin, "To yar masu gida, kema kinsan ko banza da bazata kike rawa, in kika min rashin ta ido kuwa ki gani a ƙwaryar ki".......... Ya ƙarashe yana murguda baki tare da dafe hanci sama.

Ita dai Hushaima dariya take a zuciyarta amma a zahiri wani ɗan guntun murmushi me siririn sauti tayi tare da tafa hannu a zuciyar ta ta ce yau Kuma ga inda rayuwa ta juyo daku Hushaima.

"Wace shegiyar ƙafar ke mun dariya ne anan, ni whl ƙaramin aiki na ne in kwaɓe mu daku da kowace shegiyar karuwar da takejin ita balagaggiya ce, ba abinda ya Sha min Kai

16 / 53