BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   17 / 53

48K to 51K   out of 156.9K words

, to in banda ma iskanci taya mutum yana magana ana masa dariya dan dai anga mutum bai shiga harkar kowa ba".

Taɓe baki Hushaima tayi tare da duba wayar ta ganin suna neman yin late especially Shazeen me makaranta gashi su kuma sun tsaya kace nace basu iba ruwan ba basu bar wasu sun ɗiba ba, tashi tayi ta ɗauki bucket ɗinta ta matsa gaban rijiyar ta ajje, gugar da wata mata ta danne da ƙafa ta janye tare da ƙoƙarin zurawa cikin rijiyar, wata irin danka taji ta bayanta tana juyowa sukayi ido hudu da wata budurwa kana ganin ta kaga tatacciyar Yar duniya. "Ke wani kikafi ne anan wurin da baza ki iya jira layi yazo Kanki bane saboda ke gaki shafaffiya da Mai, to baki isa ba kauce ki ban wuri".

"kiyi hakuri uzuri ne dani ba wani me yawa zan iba ba ".

Dukan kafaɗar ta tayi cike da tashen iskanci dake fisgar dusar kwakwalwarta ta ce, "ke baza ki iba ba har sai na ɗiba yaso su sokayen in sunga dama su hakura su zuba Miki ido ki ɗiba".......... ta ƙarashe tana matsar da ita ta warci gugar ta jefa a rijiyar.

Girgiza Kai Hushaima tayi tare da ja baya ta bata wurin, "Duduwa kawomin kapilas ɗin nan na Ƙara dashi".

"Ke kin ma isa"........ Wadda take Kan layi ta faɗa tana watsa Mata wani kallon banza.

"Wani irin na isa ni da gidan uba na, ke zan tambaya ma kina yar kale"..........Ta faɗa tana riqe kugu.

"Ke da ALLAH dakata uban naki ai ba kyauta muke zaune a gidan nasa ba, zaman kuɗin mu muke yauwa".

"Ke kowa layi yazo kansa sai ya iba iya adadin abinda ya ke so, Dan haka baki isa hana ni iban ruwan nan ba whl"........Hayaniya ce ta barke a tsakanin su kamar zasu bawa hammata iska kowa na mayar da martani cikin zafi.

"Tou Tou ALLAH yayi dare gari ya waye tsoffin guzmaye an tashi za'a fara halin da aka Saba "......... Da mamaki Hushaima ke kallon Baba ilerika da ya shigo ashe ba'a gidan ya kwana ba dan baiyi kama da wanda ya kwana gida ba, yana hangota tsaye ya ƙaraso yana faɗin, " Hajiya kece nan tsaye, ba dai hanaki ɗiban ruwan sukayi ba".

Ba yabo ba fallasa ta ce, "Layi ne baizo Kai na ba ai, mun tashi lpy?".

Wani ashar ya lailayo tare da faɗin, "Duk Ku gyara ku bawa hajiya wuri ta ɗiba"....... A tare sukace bamu gane ba ita hajiyar wankakkiya ce data fi kowa kenan".

Warce gugar yayi Yana faɗin, "Ke ban wuri dan uwar ki, bana son tumasanci ".

"Amma dai Abun da kake yi kasan ba daidai bane ko"........... Yarinyar da ya warci gugar a hannunta ta faɗa tana harararsa ƙasa ƙasa, fasa zura gugar yayi tare da ɗaga ta da nufin buga mata da gudu ta bar wurin. "Na dauka kin girma ai, to ko uwarki bata isa in tsaya ta tsaya Ina magana tana ce min ba haka ba dukda nasan duk wani iskanci uwayen ku ke koya muku, to whl ku shiga hankalin ku dani a gidan nan kafin na shata muku tsagwaron rashin mutuncin da yafi naku, ƙananun yan iska kawai".

"Bari na ɗiba ruwan Baba ilerika"........... Hushaima ta faɗa a ƙoƙarin ta na karɓar gugar ganin Baba ilerikan ya buɗe wata sabuwar chapter magana.

"Bari na ɗaibo Miki mana".........Ya faɗa Yana katse masifar da yakeyi ya ja ƙwafa ya zura gugar. Cikin jin daɗi Hushaima tayi masa godia tare da komawa gefe ta tsaya, Nan fa yan ƙananun maganganu da habaice habaice suka fara tashi dan dai ba yadda zasuyi da Baba ilerika ne saboda tijirarsa tafi ta kowa a gidan mutum ɗaya yake tsoro shi ma wato babbar yar sa wadda ta kasance uwar dakin duk wata me bakin uwa ita Kuma ba cika zama tayi a gidan ba sai tayi wata nawa bata leqo ba gidan ba.

Saida ya cika Mata ruwan a bokitin taf sannan ya ɗauka Yana faɗin, " Muje a Kai Miki, Ina aka taɓa tarbar bako haka, banda ma mutanan gidan nan da ba mutunci suka sani ba"......... Ita Hushaima ma nauyin abun ta fara ji ganin sa babba Wanda zai iya haifar Wadda ta fita ma amma shi ko a jikinsa da alama ya saba irin wanna fadancin, a ƙofar ɗakinta tace ya ajje mata zata ƙarasa dashi sannan ta sake masa godia ta ɗauka ta shige.

A gurguje tayi Wankan ta tashi Shazeen ta shiga , kaya tasa ta fita ta kaiwa Sahnish kuɗin da zai siyo musu waina da kunu, sannan ta Koma ɗaki ta ƙarasa shiryawa. Tana cikin maqalawa Shazeen igiyar takalmi Sahnish ɗin ya shigo ya miqa Mata ledar sannan ya zauna yana faɗin, " wai me ya faru naga duk inda na gifta a gidan nan daga masu nuna ni da hannu sai masu yi da baki sai kace wanda yayi wani abun kunya".

Sai da ta juye wainar a kwanu sannan ta ce , "Kai yanzu miye abun faɗa ma, in kana da damuwa da hakan zuwa zakayi Ka samu duk Wanda ya nuna Ka ɗin ya nuna ma abun nunawa a jikin Ka"..........Ta faɗa hakan dukda kuwa tasan ko za'a sa masa wuqa a wuya bazai iya ɗin ba. Hararar ta yayi tare da dauke Kai bai Ƙara cewa komai ba harta turo masa nasa cup ɗin gabansa tare da ajje Kwanun wainar a tsakiya ta miqawa Shazeen nata cup ɗin kunun ita Kuma ta riqe nata da ɗayan hannun tana fadin, " Shazeen shaf shaf (sharp) fa Kar mu makara".

A gurguje suka gama sannan ta ɗauki Jakarta suka fito gabaɗaya, kulle ɗakin tayi ta miqawa Sahnish makullin, "Gashi nan Ka Kula saura kazo Ka cemin ya ɓata".

"Ba zance ba, a dawo lpy"..........."Sai mun dawo yaya". Shazeen ta faɗa tana ɗaga masa hannu.

" To Shazeey a dawo lpy, ayi karatu sosai".

Tunda suka fito bata ɗaga ido ta kalla kowa ba harta fice a gidan dukda kuskus ɗin dake sauka cikin kunnenta. A kofar gidan ta tarar da wata sabuwar kasuwa kowa da abun da ya kasa me awara, me kosai, me waina , me dankali, me kunu, me shayi kowa na Kai kawon sayan abinda zai karya, jijjiga kanta tayi kawai taja hannun Shazeen suka wuce bakin titi, kasancewar babban titi ne yasa basuyi wahalar samun abun hawa ba, saida ta Kai Shazeen makaranta sannan ta wuce wurin aikin nasu.

Tana shiga da Jumayma ta fara cin Karo, ko nuna ta ganta batayi ba ta fara ƙoƙarin wucewa, tsayar da ita jumayma tayi, "Hey wait tsaya Nan".......... Ja tayi ta tsaya fuskar nan ba sauki Amma bata ce komai ba. "Jiya me ya hanaki zuwa? sannan kuma baki yi report ba".

"Kece me wurin ko ke zanwa refot din?".

"Amma ni ke da alhakin supervising ɗin Ku ai tare da sanin ya performance ɗin ku yake, Amma ke daga farawa kin fara skipping Kuma a haka in wata ya cika ba'a baki salary ɗinki daidai ba kice an miki rashin adalci".

Dukda bata fahimci English words ɗin ba amma a jimlar da sukazo yasa ta ɗan fahimci wani abun. Dan haka ta gyara tsayuwa da faɗin, "Ashe kin samu qarin matsayi bayan gadin masu shige da fice da aka baki, to in kina da hannun jari a wurin nan karki barni na wuce sa'o'i 3 kinji, ɗaya biyu uku "........... Ta ƙarashe tana irgawa da yatsunta. "In kuwa har sa'a uku ta wuce ina nan wajen to kin cika banza marar abun yi me gadi". Tana gama faɗa ta wucewar ta ciki ta bar Jumayma baki Buɗe.

"Ni kika fadawa haka ? lalle talaka bai san samun wuri ba, ni kuwa nace har tulu yayi dariyar tukunya bayan duka ƙasa ne. "To Bari hajiyar tazo zakuwa kisan ni ba banza bace, jaka me kwakwalwar kifi bata gane komai sai iskanci".......... Ita dai Hushaima ko juyowa batayi ba tayi shigewar ta.

Lokacin da hajiya tazo da baƙi suka shigo hakan yasa Jumayma bata samu damar Mata magana ba har saida suka tafi sannan ta samu shiga office ɗin nata, saidai me tana shiga ta samu Hushaima ciki suna magana, turus taja ta tsaya yanayin ta na nuna rashin jin dadin ganinsu ɗin a haka. "Yauwa gwara da ALLAH ya kawo ka Jumayma, ƙaraso".........Hajiya ta faɗa.

Cikin sanyi jikin da bata San yadda akayi ya lullube ta ba ta ƙaraso tana harara Hushaima ta nemi wuri ta zauna. "Jumayma meke faruwa ne tsakanin ke da Hushaima?".

"Me tace Miki hajiya?".

"To ai ke na tambaya ko, tunda ita naji nata?......... Abinda ya faru da safe ta faɗa Mata tare da maganganun da Hushaima ta faɗa Mata sannan ta ɗora da, "Hajiya tunda ta fara aiki haka takeyi min, Kuma ko ba komai duk ma'aikatan wurin nan suna bani girmana, Amma ita sai tai ta wani jijji da Kai kamar wata yar sarki".

"Ya isa to, ke Hushaima kinji haka ne?".

"Ko kusa ba haka bane ranki ya daɗe, abinda dai da na gaya Miki Shi ne daidai, don ni tunda na fara aiki wurin nan Jumayma bata so na kamar na tare mata wani Abun, ƙarshe ma cewa tayi taci alwashin sai tasa kin koreni, hajiya bansan abinda zai faru ba a gaba gwara tunda mutunci na kawai na hakura na bar wurin nan, na nema a wani wurin tunda abun ba zai yiwu ba".

"Baza ayi haka ba Hushaima, ka kwantar da hankalin ka ai ni ke da wurin ko, ba Jumayma bane ke da ikon korarka dan haka karka damu, kai kuma Jumayma dan ALLAH Kar naji Kar na gani, Bana son irin wa annan ƙananun zancen masu Kai kawo. Ba sanin juna kukayi ba ba komai ba anan fa kuke haɗuwa kawai daga an tashi Kuma shikenan, Kuma in ma Hushaima ya bar aiki anan miye ribarka Jumayma, wani ai baya tarewa wani Abun da ALLAH ya bashi. Da ALLAH Kar na ƙara jin Abu makamancin haka".

"In sha ALLAH Hajiya". Jumayma ta faɗa Amma a zuciyar ta kuwa wani haushin Hushaima take ƙara ji.

"Haka nake son ji, kuna iya tafiya, Jumayma kai kuma ka kawomin lissafin nan"........ Da "To"......ta amsa sannan ta tashi ta fita, gyara zama Hushaima tayi da faɗin, "Ranki ya daɗe dama ina da wata yar magana ne?".

"To inajin ka"......... Hajiya ta faɗa tana bawa Hushaiman duka hankalin ta.

"So nake a bani wani Abu daga cikin albashi na a karshen wata sai a Zara"...... Shuru hajiya tayi kafin ta ce, " Gsky there's no way da zan iya Baka wani Abu daga albashin ka, saboda kai sabuwar ma'aikaciya ne ko albashin farko baka fara karɓa ba, ka dai yi hakuri ko ka nemi rance wani waje in watan yayi saika biyasu".

"Shikenan Nagode Hajiya ba damuwa"....... Daga haka ta miqe ta fita ta koma bakin aikin ta .



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️


___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______23 & 24



Haka rayuwa ta cigaba da miqawa yau da dadi gobe babu, da buga buga suke cigaba da gungurawa Amma duk da haka sun rufawa kansu asiri, haka zalika ta bangaren Baba ilerika sosai yake mutunta su tare da nuna musu kulawa tun mutanen gidan na kuskus akan cewa saboda yaga yar budurwa kyakyawa ne har suka fito fili suna faɗin ai karuwar sa ce dama saisa ya fitar da ya'yansa ya basu ɗakunan.

Mu ɗan waiwaya baya abinda baku sani ba shi ne lokaci da Baba ilerika yace wa Hushaima akwai ɗakunan haya, ya'yan sa ne a ciki ya fitar dasu ya maida mazan ɗakin soron ƙofar gida, matan kuma ya ce su koma su raɓe ɗakin yan uwansu, a faɗin sa basu da amfani tunda basa kawo masa komai dan haka in sukayi wasa duk sai yayi waje dasu ya zuba yan haya a gidan dukda yanzu ma rabin ɗakunan yan haya ne a ciki.

Yau ta kasance lahadi su Hushaima basu da aiki, Shazeen kuma da Sahnish zai fita ya wuce ya kaita tahfeez da suke zuwa tun 10am sai 5pm a duk ranakun weekend. Zaman ɗakin ne ya isheta taji gwara ta fito ta sha iska duk da kuwa bata san zaman tsakar gidan, saboda har yanzu bata shiga sabgar kowa harkarta tsakanin ta da Baba ilerika ne sauran mutanan gidan kuwa saidai in ta kama, dan tunda ta karanci duk ba wanda ke kallon kan ɗan uwansa da gashi taja mutuncin ta.

Sanye take da ɗaya daga cikin rigunan da Amla ta kawo masu tsaraba, miqewa tayi tana neman Abinda zata rufe gashin kanta wanda na lura shi kaɗai Hushaima ta damu data suturta a duk inda take zakaga kanta a ɗaure da dankwali, ganin zata wahala yasa ta zari dankwalin atampa kawai ta kafa daurin ture sannan ta dau wayarta ta fita.

Kusan yau duk kowa na gida ga kuma alamar hadari dake haɗowa wanda yasa zafi ya yawaita, yawanci kowa na waje yana shan iska ƙarƙashin manyan bishiyun mangwaron dake cikin gidan, wanda suka yiwa kusan rabin filin tsakar gidan rumfa, kowa da abinda yakeyi wasu kuma zaune suke kawai suna gulmar junan su.

Fitowar Hushaima yasa ido ya dawo kanta aka fara kuskus ɗinta, bata kalli kowa ba ta Ƙarasa Kan wani table data gani an ɗaura qullin kayan wanki akai, ture kayan tayi gefe ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya Kan ɗaya, ta buɗe game a wayarta tanayi amma kusan duk hirar da suke tana ji , kunnen ta ne ya ɗauko Mata maganar da wata da Ake Kira da Sa'a super keyi da ƙawarta Wadda tafi tunanin ba a gidan take ba, saboda ita har yanzu tsabar yawan mutanan gidan baza ta iya ware su ba, faɗi take, "Kee kowa ya iya takunsa ustazi ne, amma wanna da kike ganinta akuya ce me fatar kura, karuwar Baba ilerika ce ai har kawalcinta yake yana haɗata da wasu manyan alhazawa a waje yaga yar kyakyawa, ke ai kinsan Baba ilerika baya zubin adashin da ya san ba ranar ɗauka ".

Cikin bacin rai ta ɗago da Niyyar maida martani idanunta ya sauka cikin na wani kyakyawan matashin saurayi da ya fito daga wani ɗaki, yana sanye da t shirt me ƙaramin hannu sea blue da Ash wando, fari ne amma ba irin kau ɗin nan ba, fatar jikin sa a murje take kamar ta wani ɗan jariri, lips ɗin bakin sa pink dasu sunyi shar suna shining kamar ya shafa lipgloss suna zagaye da sirrin gashin Baki, hancin sa ɗan karami haka idanun sa irin Magnetic eyes ɗin nan ne masu kyawun kallo, baya tara gashi amma Wanda ke kansa a kwance yake baki siɗik ga laushi, kunnensa ɗaya maqale da earpiece. Kallonta yake shi ma kamar yaga wata sabuwar halitta, ganin ido na ƙoƙarin dawowa kansa ya sashi basarwa yana ɗan kashe idanun saboda ranar data hasko ƙofar ɗakin nasa, sai da yabi gabaɗaya mutanan dake tsakar gidan da kallo sannan ya Ƙarasa fitowa, A tsaye yake dan duk inda ake buqatar namiji wanna gayen ya Kai, ga six packs din sa da shatinsu ya fito dar ta cikin t shirt ɗin saboda fitting ɗin gymnastics body ɗinsa da tayi.

A bangaren Hushaima kuwa ganin ya dauke kansa yasa itama sauke nata ƙasa da mamakin wannan kyakyawar halittar data gani a yanzu a kuma cikin gidan da kwata kwata bai Mata kama da irin mutanan dake rayuwa a ciki ba, take ta manta da martanin da taso yiwa Sa'a super, jama'a duk fa wanna kyawun da Hushaima ta rude a Kai baikai rabin kyawun ta ba. " May I sit"........... Ta juyo wata murya, ɗagowar da zatayi kawai ta ganshi tsaye a kanta ba tare data san lokacin da ya ƙaraso ba, sai dai kuma ko da ta kalle shi bai mata kama da shi yayi maganar ba. "Stop looking at me before I poke your eyes out"............ Sai a lokacin ta tabbatar da eh lalle shi ɗin ne yayi magana, voice ɗin sa is so deep gata very clear sannan gata da low sound dan ko ita badan idanunta na kansa ba taga motsawar ɗan bakin nasa da baza tace shi yayi maganar ba, amma kuma duk wannan abun a banza tunda bata san me yace ba hakan yasa ta sake ɗauke kanta kawai.

"Ya jey zaka zauna ne ta tashi ko Kuma na kawo ma wani Abun zaman ?"............ Baheelah yarinyar kawu Adamu ta faɗa tana tasowa cikin salon dake nuna neman shiga take.

Ko kallon ta baiyi ba ya sanya farar ƙafarsa dake sanye cikin slippers ya ture kayan wankin dake gefen Hushaima qasa sannan ya zauna, matsawa Hushaima tayi can karshen bencin, har yasa hannu zai ɗauko wayar sa a aljihu ya tsaya ɗagowa yayi yana kallon space ɗin data bada a tsakanin su fuskarsa dauke da dimbin mamakin da ya gaza ɓoyuwa ya ce, "Are you in this house ? "............ Ya tambaya idonsa a kanta, kallon sa kawai ta tsaya yi kamar wata doluwa dan kwata kwata bata fuskanci abinda yake faɗa ba. " A gidan Nan kike?"........... Ya sake tambaya da wannan daddadar muryar tasa . "Eh". Hushaima ta amsa.

"Sabuwan zuwa?".............Ya sake tambaya, Kai kawai ta gyada masa alamar eh, still idon sa a kanta ya sake faɗin, " Bana son kallo".

"Ikon ALLAH, to Kai da wani idon kake kallona har kasan Ina kallon ka?"........... Tayi karfin halin faɗa duk da yadda takejin zuciyarta

17 / 53