Author : Young Writer Category : Tknovels
nutsuwar ta cikin rawar murya ta ce , "Amour Kai ne gabana"........... Gyada mata Kai yayi alamar eh, kuka ta fashe dashi tare da faɗawa jikinsa, riqota yayi yana shafa bayanta a hankali yace, "Stop crying I'm here okay ?".......... Cikin kuka ta ce, " Amour bansan meysa Mumu da Dad canza ba gabaɗaya sun daina so na, haka jiya suka kwace min waya, sannan suka canza min asibiti duk dan su nisanta ni da kai, kuma su kace wai anzo an tafi dakai saidai in prison zan bika mu zauna "............." Ya isa Ninie, ai na riga na faɗa miki in har kin shirya aure na to sai kin shirya ɗaukan duk wani qalubale kika ce kin amince, wannan shi ne abinda na guje miki tun a baya Ninie ba wai ina jan lokacin auran mu bane haka kawai ina da dalilin yin haka saidai a lokacin ke kuma kin kasa ganewa, ba ƙarya su dad sukayi ba wanna sojojin da kika gani an sasu ne su dinga tsaro na, har sai sun kammala bincike saboda suna gudun a neme ni a rasa, amma ki kwantar da hankalin ki".......... Wani sabon Kukan ta sake fashewa dashi. Tausa murya yayi da faɗin, "Ninie kin fa san baki da lpy ko ? shi ne kike nema ki ƙarawa kanki damuwa ni ma Kuma ki samun, meysa baza ki kwantar min da hankali bane ninie, meysa bazai zama in nazo wurin ki na samu sauƙi ba, ya kamata ace ki zama jaruma"........... Ɗagowa tayi daga kirjinsa tare da goge hawayen fuskarta tayi murmushin da bai Kai zuci ba, sai faman gyada masa Kai take amma ta ƙasa cewa komai, tashi yayi ya ɗauko gorar ruwa ya dawo ya zauna tare da buɗewa ya sanya mata a baki, ba musu ta buɗe bakin ta fara sha ba wai dan tanajin ishirwar ba sai dan wanna shi ne na farko da zai shayar da ita wani abu da hannunsa. Ta shagala a kallonsa har Saida ruwan ya kwareta. "Ufff sorry". Ya fada yana hura mata iskar bakinsa a fuskar ta tare da ɗan bubbuga bayanta a hankali, gyada masa kai tayi alamar she's Okay sannan ya rufe gorar ya ajje ya jawo kanta ya kwantar a kan shoulder ɗinsa, wayar sa ya ɗauka ya Kira kamal yana ɗagawa, ya ce, "Kamal turomin Dr ɗin".
Ba'a fi 3 minutes ba Dr ya shigo, ba tare da ya motsa ba ya ce, " Ya jikin nata?".
"Ai ba wani internal injury ranka ya dade sai dai bruises ɗin da muke treating"........... Gyada kansa yayi sannan ya ce, "kaje ka rubuta min sallama sannan ka rubuto duk wasu abubuwan da zata buqata, ka Kuma sama mana nurse ɗin da zata kula da ita a gida, Kar a wuce 15 minutes"............ Yana kaiwa nan ya miqe tare da kamo hannu Nayrah ɗin data bi shi da kallon rashin fahimta, ƙoƙarin tashi tayi da taimakon sa, Dr ya ce, " Ai ranka ya daɗe yanzu ba zai yiwu ta taka ƙafar sosai ba saidai ko a kawo wheel chai........." Kasa ƙarasawa yayi saboda wani kallo da Amjad ɗin ya watsa masa tare da rankwafowa ya ɗauke ta kamar wata yar baby, waje ya nufa da ita a haka, su Kamal na ganin sa suka rufa masa baya, ɗan dakatawa yayi sannan ya ce, "kaje ka taho da wancan sister ɗinta ta "............ Ya ƙarashe yana cigaba da tafiya, a cikin motar da yazo ya sanyata sannan ya rufe ya zagaya shi ma ya shiga, ita dai Nayrah da kallo kawai take binsa har Kamal ya ƙaraso shi da Nashwa, rage glass ɗin bangaren sa yayi tare da faɗin, "Ita ta shiga gaba shi Kuma Masood(ɗayan sojan) ya koma wancan motar tare da su Joseph, akwai nurse ma da Dr zai bada ta shiga wadancan motocin tare dasu"..........." Okay boss"......... Kamal ya amsa tare da buɗewa Nashwa gidan gaba ta shiga sannan ya koma wajensu Joseph.
Bayan an gama komai suka dawo tare da Dr ɗin motar da su Amjad ke ciki. "Zaka ga saqo"........ Shi ne kawai abinda ya faɗa sannan ya rufe glass ɗin, Dr kuwa sai godia yake wa Kamal kamar shi ya masa albishir ɗin ko kuma shi zai bashi kyautar, buɗe mota kamal yayi kawai ya shige mazaunin sa na driver. Nashwa ce ta ce, "Nayrah baba jamilu fa yana nan yana jira"........... Ɗan murza yatsu Amjad yayi kafin ya ce, "Da ALLAH Kamal yi sauri kaje ka sallame shi kace ya tafi gida kawai, karka daɗe". Ya faɗa a qage yana duba agogon hannunsa, da sauri Kamal ya sake fita yaje ya sallami drivern sannan ya dawo suka tafi.
"Bluevielle". Ya faɗa a takaice . "Okay boss ". Kamal ya amsa.
A bakin gate ɗin wata haɗaɗɗiyar Estate suka tsaya, Saida akayi searching ɗin motocin nasu sannan suka shige. Estate ne na bugawa a jarida ya haɗu iya haɗuwa, an ƙawata shi da wasu irin shuke shuke ta ko ina. Gidaje ne a jere amma kowani gida zagaye yake da wasu dogayen bishiyu sai yar hanyar shiga da suka bari, manufa babu katangar data yanka wa mutum iyakar yankin gidan sa, sai dai bishiya kawai, estate ɗin tsit ba hayaniya sai kukan tsuntsaye da suka kafu a bishiyoyin. Gaban ɗaya daga cikin su Kamal yayi parking sannan ya fito ya buɗewa Amjad ɗin da har sojoji sun zagaye motar tasu, Saida ya fito sannan ya miqawa Nayrah hannu ta kama tana ƙoƙarin ɗaura ƙafarta kan ƙasa yayi sama da ita, cikin gidan ya wuce ba tare da ya kalli kowa ba. Kallon Nashwa da tayi tsuru tsuru Kamal yayi sannan ya ce, " ki shiga mana, ke ma nurse ku shiga tare, ai kin ɗauko jakar magungunan ko?".
"Yes sir"........... Nurse ɗin ta amsa sannan tabi bayan Nashwa suka shige .
Bai direta a ko Ina ba sai cikin wani ƙayataccen bedroom da ya gaji da haɗuwa, a bakin gadon ya ɗaura ta sannan ya ɗan rankwafo kamar me raɗa ya ce, "Zanje wani wuri yanzu in dawo, maybe anjima ki ganni amma in baki ganni ba karki damu zansa a kawo maki waya da Kuma duk abinda zaki buqata ga Nashwa ga kuma nurse nan okay?".......... Riqo hannun sa tayi tare da faɗin, "Ina zaka tafi Kuma? sannan nan ɗin ina ne ?".
"In har baki na so a kame mijin ki bane to dole sai na tafi yanzu, nan kuma shi ne gidan ki kece matar gidan".......... Ya karashe yana mata wani sassanyar murmushi cike da bata kwarin guiwa. Idanun ta ne suka ciko da hawaye, ba tare data saki hannun nasa ba ta shiga jero masa addu'o'in tsari da kariya, Saida ta gama sannan yayi hugging ɗinta cike da zallar soyayyar ta dake neman sauya masa tunani, After his parent ba ya jin akwai wanda yake so sama da Nayrah saboda ita ɗin abar so ce a gareshi, ta bashi dukkan soyayya da yarda ta kuma riqe masa alqawari.
After some minutes yayi breaking hug ɗin yana kallon cikin idonta da gashin idon e jiqe da hawaye sai wani far far take dasu wanda haka ya kara Mata kyau, one side smiling yayi tare da kamo fuskarta ya manna mata wani light kiss da ya sata kallonsa ba shiri saboda yadda taji abun unexpected, da sauri ya miqe ya nufi ƙofar fita yanajin kamar ya fasa tafiyar, saidai bashi da wannan damar a yanzu Wanda shi ne dalilin da ya hanashi yin aure tun a wancan lokacin saboda manyan ayyukan dake jiransa sam bayaso ya shiga hakkin ta, saidai kuma wannan nasa tsarin da tunanin ne ga tsarin da ALLAH ya masa dan haka bashi da ikon canza hakan.
A falo ya tarar da Nashwa tare da nurse ɗin nan sunyi tsumu tsumu kamar shege a rabon gado. " Ina wayar ki?". Ya tambaya yana tsareta da ido, ba musu ta miqa masa, karɓa yayi ya zura a aljihu sannan ya ce, "Zansa a kawo maki wata da Kuma duk abinda zaku buqata, Akwai me gyaran gidan a waje idan kuna da buqatar wani abu kafin su Aram su ƙaraso"........... Da "to". Ta amsa sannan tayi masa fatan dawowa lpy, ta wuce ɗakin da taga ya fito dan tafi tabbacin Nayrah na ciki.
Jama'a kuna ganin Dad ba zai tada bomb ba kuwa idan labari yaje masa? Ga Amjad da ƙarfin hali ka ɗauki matar ka amma tsabar neman magana harɗa ƙarawa da sister ta. Eh kwarai akwai ɗan ƙaramin yaqi kuwa dan Amjad yazo da bidi'a.
---------------------√
A cikin wasu yan lokuta shaquwa me ƙarfi ta shiga tsakanin Hushaima da Jey, Dan yanzu kwata kwata jinsa suke kamar wani baban yayan su, tun ranar da abin nan ya faru Jey ya karance alqiblar Hushaima ya kuma ke binta yadda take so ɗin, a bangaren masifar ta kuwa ba abinda ya sauya sai ma gaba da abun yake sake yi, dan duk wanda ya tabo ta ko waye gatansa sai yaji a jikin sa, sai tai ma shegen duka ba abinda ya dame ta, bata shakka kuma bata tsoro wanna abun shi ya sanya Jey Ƙara janta a jiki saboda wata manufa tasa da ya barwa kansa sani, yanzu sun samu saukin rayuwa dan wani abun shi yake musu. Tun mutanan gidan na adawa da ita har ya zama kowa tsoron ta yake Kuma binta suke duk abinda take so shi akeyi kamar ita ce me gidan, rigimar da ada ake yi a gidan yanzu kaso 70% ya ragu saboda tsoron Hushaima, yanzu duk wasu yan tasha tsoron gidan su Baba ilerika ake.
Sahnish kuwa dubu ashirin ɗin nan data bashi yaje wurin masu turare suka hada masa yazo yake siyarwa Kuma ba laifi yana samu sosai, ganin haka yasa Jey ya ƙara masa jari. Ita Kuma uwar gayyar tana aikin ta a Starlight beauty Co. akan batun Amjad kuwa bata hakura ba tana nan akan bakarta ɗan Hushaima akwai naci ga kafiya da taurin Kai, Saidai duk wani Binciken ta kan Amjad amsa ɗaya ake bata na ƙarfin dukiya da matsayi na mahaifin sa, sai Kuma laifukan sa da ake faɗa, saidai ita duk ba wannan take son ji ba, kwata kwata bata yarda da abinda ake faɗa mata ba gashi tana neman hanyar da zatayi ramuwar da ta ɗau alwashi ba tare data shiga matsala ba, duk da tasan inda yake da kuma inda zata sameshi amma tasan bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane, dan haka ta cigaba da faɗaɗa tunanin ta kafin ta waiwaye shi.
Sahnish ne tsaye a shagon juma shi da Shazeen sanye da uniform da alama daga makaranta ya ɗauko ta, jira yake juman ya gama sallamar wanda suke a kan layi, wani ne ya ce, "Malam juma tun dazu fa nake tsaye kazo ka auna min shinkafar mana"..........."ya hakuri malam Audi bari nazo, irin wacce za'a baka royal ko tomato rice ?".
"Babu irin ta mu ta gida ne?"............ Mutumin ya tambaya.
"Gsky yanzu bamu cika ɗauko ta gida ba, babu ma su da yawa a kasuwa, kuma mutane ma sunfi sayan wa annan ɗin".........."Kai bawa bai san ina zai sanya kansa a ƙasar nan ba wato mutanan nan ƙarfi da yaji nema suke su raba mu da abincin mu na gida domin su tasu kasuwar ta buɗe "............. Wani mutum da ya gama sayayya yana duba canjin sa da malam juma ya bashi ya ce, "Ai ka bari kawai Malam, in baka dashi kuma saidai ka mutu, tunda gashi dai wasa wasa zuwa gona da kiwo fa yanzu yana nema ya koma tarihi, saidai a shigo mana da komai amma mu baza mu iya fitar da namu ba, saboda kawai an raina mana wayo".
Shi dai malam Audi ce wa yayi, "ALLAH ya kyauta, Malam juma zuba min royal din shakaɗeka guda".......... Dan baya so maganar tayi nisa saboda yanzu abu kaɗan zaka furta, za'a cafke ka dan baka san da wa kake tare ba wasu ma jami'an sirri ne suke basaja.
Sunkuyawa juma yayi yana ɗaibowa Malam audi shinkafar ya amsa da, "To in Banda abinka malam waye zai fita kiwo a kashe shi a banza, ba saisa kaga dabbobin sun ƙara tsada ba, haka zalika nomar yanzu kana cikin gona saidai kaji an zagayeku da bindigu in baka da tsawon kwana daga nan kai taka ta ƙare, dole hakan dai za'a dinga lallaba rayuwar"............ Ya ƙarashe yana miqawa Malam Audi ledar ya bashi kuɗin ya miqa masa canji ya fita. "Malam Sahnish me za'a baka?"............" Sabulun wanka zaka bani da omo". Ɗaukowa yayi ya miqa masa shi kuma ya bashi kuɗin ya ɗauki kayansa ya masa sallama ya fito yana tariyo hirar su Juma me shago, duk da dai shi ma yana da abin faɗar amma ya zabi yayi shiru ɗin.
______________ A kofar Starlight beauty Co. ɗin ya umarci me tuk tuk ɗin da ya tsaya sannan ya sauka tare da faɗin, "Dan jirani yanzu zan fito". Ya ƙarashe yana nufar ƙofar gate ɗin wurin ya tsaya tare da Kiran number Hushaima amma bata yi picking ba, ɗan tsaki yaja ya maida wayar sannan ya nufi ciki yana turawa gate ɗin ya buɗe, da ido yabi compound din kafin ya wuce ciki, yana shiga reception din Jumayma dake haɗa kayanta ta ɗago tana dubansa, dan already sun riga sun tashi, "Malam lpy dai?"............"kalau, wuri na yazo kina da matsala da hakan ne?". Hushaima data fito daga ciki ta faɗa tana watsawa Jumayma harara, Jey baice komai ba ya juya ya fice, Jumayma Kuma taja tsaki, bin bayansa tayi tana faɗin, "tsaka ma da tayi ALLAH ya tsine mata, ba dai yadda zakiyi dani".
A cikin tuk tuk ɗin ta sameshi, tana zuwa ta shige ba tare data dube shi ba, shi Kuma ya bawa me tuk tuk ɗin umarnin tafiya, kallon ta yake har saida ta juyo suka haɗa ido harararta yayi kafin yayi magana ta ce, "Dai na kallo na ni ma".........."Me zan kalla anan?"..........."Kai kafi kowa sani ai"............yar dariya yayi tare da ɗauke Kansa ba tare da ya sake cewa da ita komai ba, hakan yasa ta buga tagumi tare da zuba masa ido kawai, a duk lokacin da Jey yayi dariya har kumatun sa suka lotsa sai ta samu kanta cikin yanayin data kasa fassara shi, yana jinta yayi banza da ita suna zuwa kusa da layin su yace me tuktuk ɗin ya tsaya sannan ya sauka. "Ya dai?"........... Hushaima ta tambaya. "Zan siya wani abu ne ku ƙarasa ka sauke ta"..........."Nima zan sauka anan ". Ta faɗa tana saukowa kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya bashi kuɗin ya yi gaba, da sauri tabi bayansa suka cigaba da tafiya can kuma ta ce, "Ni kuwa Jey Ina da tambaya?".
Kallon ta yayi ya ɗauke Kai baice komai ba . "Yau dai ka daure ka amsa min tambayar nan kullun na tambaye ka game da yan uwanka ko garin ku sai ka ƙi bani amsa meysa baka so na sani, ko baka yarda dani ba ne"..........." Me sa ba zanso ki sani ba, ai kin cancanci ki sani ko ?". Ya ƙarashe cikin sigar tambaya me ɗauke da rainin wayo, bata bashi amsa ba dan taji haushin yadda yayi maganar sai kawai ta cigaba da tafiyar ta, tama yi gaba abunta, dan takaitaccen murmushi yayi tare da tsallakawa kan wani dakali in da wani shirgegen mutum ke zaune kan bencin dake kan dakalin ya zubawa hanya ido.
Jin baya binta yasa ta juyo ganin inda ya nufa ya sa ta dan tsaya Tare da ƙuresu da ido.
Miqa masa hannun mutumin yayi bayan ya miqe a lokacin da ya ƙaraso yana washe baki, zama gefen bencin Jey yayi ba tare daya miqa masa hannun ba ya bige da faɗin, "Na danji ciwo ne saisa "........ Dan shi mutum ne me tsananin kyankyami ga mutumin kuma rigar jikin sa ma har tashi take, komawa yayi ya zauna tare da faɗin, "Alhaji kazo lpy?".........."lpy kalau Alhamdulillah, batun aikin nan da mukayi magana ya samu in sha ALLAH gobe zanzo muje su ganka su ma interview sai ka fara aikin". Godia ya fara zuba masa kamar zai sunkuya, "No bakomai karka damu". Ya faɗa yana ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya miqa masa, da sauri ya sa hannu zai amsa kamar walkiya yaga an warce kuɗin .............
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd SultyWrites22
STEP 1
PAGE _______42
Godia ya fara zuba masa kamar zai sunkuya, "No bakomai karka damu"............ Ya faɗa yana ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya miqa masa, da sauri ya sa hannu zai amsa kamar walkiya yaga an warce kuɗin, ɗagowa yayi tare da kallon Hushaima da fuskarta ke ɗaure tamau kamar an aiko mata da azarailu, zaiyi magana ta miqawa mutumin da faɗin, "Nima barin samu wannan ladan "........... Kallon ido cikin ido sukeyi ita dashi, irin kallon kar ta san kar ɗin nan. Sosai ta Ƙara haɗe girar sama data ƙasa tare da faɗin. "Karɓa mana, ni da shi ai duk ɗaya ne yayana ne"............ Yaqe mutumin ya fara, "Ahh Ranki ya daɗe, kina iya ajje min, whl nauyin ki nake ji ne"............" In zaka karɓa ka karɓa". Ta sake faɗa a dake.
"Ke wai meye hakan"........... Jey ya faɗa a fusace dan ransa ya fara ɓaci ganin aika aikar da Hushaiman ke kokarin yi, Itama a tsawace ta ce, "ka tashi