Author : Young Writer Category : Tknovels
with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______58
Reeslan na shigowa ɗakin su ya tarar da jakadiya dake zaune kan shag rug ɗin ɗakin nasu tana tsiyayawa Rouslan ruwan addu'ar da Ummu tace tazo ta bashi wanda Imam ya aiko, Wani irin ɓaci yaji ransa bai san lokacin da ya katsa mata wata tsawa ba, da faɗin, "Me kikeyi Anan, tashi ki fita kafin na saɓa miki kamanni"......... Take jikin jakadiya ya ɗau rawa har cup ɗin hannun ta na suɓucewa ya faɗi. " ALLAH ya huci zuciyar Maleekh dama Sheikha ce ta buqaci nazo na bashi "..........Ta ƙarashe tana tashi zata fita, ciki ya ƙarasa in da take tsugunne tare da ball da kyakkyawan Jug ɗin yana faɗin, "Su wannan uban wa kika barwa ? tattare tsiyarki ki fita da ita "..........." Habiby p......."
"Kaiiiiii Shut".......... Ya faɗa yana ɗaura yatsan sa kan ɗan mitsitsin lips ɗin nasa. Harara Rouslan ɗin ya watsa masa ta gefen ido yadda shi kaɗai kawai zai gani sannan ya ɗauke kansa, Wucewa jakadiya tayi jikinta na ɓari ta shiga tattare kayan dan Jug ɗin tuni ya tarwatse ruwan addu'ar ya zube, haka ta tsitsince sannan ta nufi ƙofar fita. "Kuma ki turo wadda zata gyara ɗakin nan"........ Ya faɗa Yana matsawa wurin two seater sofa ɗin da Rouslan ke zaune a kai. Zama yayi yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Sai a lokacin Rouslan ya sake cewa, "Haba Habiby ruwan Addu'a ne fa Imam ya aiko kazo ka zubar, ayoyin ALLAH ne fa"........ Wani kallo ya watsa masa Amma baice komai ba shi kuma ya cigaba da faɗin, "Kuma jakadiya ko ba komai tayi ya'ya damu, ka tuna tun bamu fi shekaru huɗu ba a duniya take tare da mu, ya kamata ace kayi limiting actions ɗinka toward her".
Hannunsa ya kai goshin Rouslan ɗin yana faɗin, "Me kake ji yanzu? Ummu tace min bakaji daɗi ba bayan fita ta?".......... Ɗan sauke numfashi yayi dan maganar da yake ma ƙarfin hali ne shi kaɗai yasan me yakeji a jikinsa wani irin turirin zafin zazzaɓi ne kawai ke fita.
"Shi Abyan ɗin da yazo ya baka magani ko kuma kawai iyayi yazo yayi ma? Meysa ma tukunna baka kirani ba har ka bari suka kira wani Abyan"........ Ya faɗa wannan karon a tausashe da kuma kulawa . Lumshe idanun sa yayi ya buɗe kana ya ce, " Ya min Allurai dai, ga sauran can ma ya bari ya ce in kazo sai ka duba yaso ka cigaba da yi min. Kuma banaso ne na tashi hankalin ka a inda kake saisa ban kiraka ba"........ Jijjiga kai Reeslan ɗin yayi tare da tashi ya wuce gaban gadon nasu, bedsheets ɗin dake kai ya cire gabaɗaya sannan ya wuce ya ɗauko wani sabo ya dawo ya shimfiɗa ya canza pillow case ya gyara gadon tsaf tsaf, sannan ya dawo ya kamo hannun Rouslan ɗin kamar wani yaro, miqewa yayi ya bishi har zuwa bakin gadon, nuna mashi kan gadon yayi da faɗin, "Kwanta ka huta".
"Ina zaka ?".......... Rouslan ɗin ya tambaya yana kallon sa. "Ba inda zani wanka ma zan shiga, nima in na fito kwanciyar zanyi na huta ai"........... Rouslan bai Ƙara cewa komai ba ya hau ya kwanta, wata na'ura Reeslan ɗin ya kunna ita kuma iyakarta zagayen gadon kawai zata sanyaya, in kuma sanyi ne zata baka dumi kamar dai Ac amma Ac in Ka kunna duka ɗakin zata game ita kuma wannan iyaka gadon ne kawai. Saida ya seta ta sannan ya sauke wasu ƙayatattun transparent curtain dake zagaye da gadon. Daidai lokacin akayi Knocking, "Waye ?"..........Ya tambaya a daƙile.
"Khadimah Jamila ce jakadiya tace nazo na gyara ɗakin"......... Saida yaja tsaki sannan ya Ƙarasa ya buɗe ya koma tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da riqe waist ɗinsa da hannayen sa, "ki nannade rug ɗin ki fita dashi ki canzo wani karki ɓatamun lokaci kiyi sauri"......... Duk wannan maganar yana yin tane cikin faɗa faɗa a qage irin wanda ya ke jira ayi kuskure kaɗan ya kaiwa mutum duka.
Duk da nauyin rug ɗin haka ta nannaɗe shi sannan ta shiga ƙoƙarin ja amma duk da haka bai ga ƙoƙarin ta ba ya ce, "Da ALLAH ki sa ƙarfi kiyi maza ki fice dashi, ki zo kiyi abun dake gabanki, kina abu sai kace wanda ake rainon ku da yunwa"......... Bata ce komai ba sai saka dukkan ƙarfinta da tayi ta ja shi waje sannan ta kira wata khadimar tace ta janye wannan ta sa a ɗauko wani a store yanzu yanzu, Kasancewar sun san aikin Reeslan ɗin yanzu yanzu ne shi bai san wani abu wai sai anjima ba yasa cikin hanzari ta kira wata ta tayata ɗauke wannan ɗin.
Dawowa ɗakin khadima Jamila tayi tana haki ta tattare Wurin sannan tayi mopping, lokacin aka shigo da wani sabon rug ɗin tare suka haɗu ita da wadda ta kawo suka shimfiɗa sannan suka zube a gabansa tare da faɗin, "Ko da akwai abinda za'a yi wa maleekh?".......... Tsaki yaja da faɗin, "Dama ku biyu na kira ne ?".......... Da sauri wadda ta kawo rug ɗin ta tashi zata fita har ta kai ƙofa ya ce, "keehhhhh"......... Datse hakwaran sa yayi tare da kallon gadon da Rouslan ke kai yana bacci, cikin ƙoƙarin yin ƙasa da Muryar sa ya ce, "Nace ki fita ne ko kuwa na sallame ki ne? ba tambaya na muku ba? "......... Jikinsu ne ya ɗau rawa a tare suka ce, "ALLAH ya huci zuciyar Maleekh ".
"Ku bace min da gani kafin nayi pieces da miskinan ƙasusuwan ku"........ Ai kafin ya ƙarasa sunyi waje tare da rufo ƙofar, kwafa yaja sannan ya wuce wurin bedside drawer ya jawo burner ɗin sa ya jona ya wuce ya ɗauko turaren wutar su, dan shi takanas yake zuwa ya kwaso na Ummu daga an haɗa mata sabbi, kaɗan ya zuba dan already ɗakin nasu ya riga ya kama da kamshi dan ko pillown su ka ɗauka in Ka ajje to kai ma kamshin ya kama jikin ka kenan. Bathroom ya wuce domin watsa ruwa ya zo ya kwanta ya huta.
------------------√
Ranar ko da ya tashi bai fita ko falo ba daga ɗakin sirrinsa sai normal ɗakinsa, gyaran ɗakin ma yana ciki akayi, haka abinci a ɗakin yaci sama sama saboda hankalin sa na kan aikin da yake, ko su Ace bai haɗu dasu ba sai Philip da ya sanya ya dubasu ya Kuma tambaye su ko da akwai abinda suke da buqata. Ba abinda yake sai bincike a kan shadow tun 11am yake Abu ɗaya har 3pm Amma ba wani labari domin Shadow Yana da mutane a kowani ƙasa Wanda suke masa safarar mutane, Saidai Kuma a duk binciken sa mutanen nasa ko wuqa zaka sa musu a wuya su faɗa ma inda za'a samu shadow to fa Saidai ka datsa musu wuqar nan bama inda yake ba hatta kamannin sa basu sani ba fari ne? Baqi ne? ah ah yellow ne baza su iya faɗa ba kamar dai yadda BB LALO ya faɗa masa, tashi yayi daga gaban table ɗin yanajin kamar kansa zai kama da wuta, tunda ya fara aiki Matsayin jami'in sirri Ba'a taɓa bashi aiki yayi failing ba hakan yasa ko da aka danqa masa aiki kan Shadow baiji ko ɗar ba dan gani yake kamar ƙaramin aiki ne, tun da ya tashi ko wanka baiyi ba daga shi sai short nicker yake ta dirzar wannan uban aikin. Kai kawo ya shigayi a ɗakin sirrin nasa yana tunane tunane har baisan iya tsawon lokacin da ya ɗauka ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fice zuwa master room ɗin nasa, toilet ya wuce ya ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya zira kawai ya tada sallah. Yana idarwa ya miqe ya koma ɗakin sirrin ya sake dasa sabon zama gaban system ɗin ya ɗaura daga inda ya tsaya, Amma still ba wani labari kawai dai matsayar da ya tsaya itace dole wa'anda zasu ɗauki mutanan da zasu basu zasu kaisu inda ake tara mutanan, Kuma dole ne shadow ya kasance a kusa dasu koma ta Ina yake. Da haka ya yanke nasa hukuncin kawai zasu Kira suce musu sun gama aiki su faɗa musu inda zasu Kai musu mutanan, numfashi ya furzar tare da kashe system ɗin da duk wasu abubuwan da ya kunna lokacin da ya shigo sannan ya fita daga ɗakin ya koma master room.
Miqa yayi tare da langwashe hannayen sa baya suka bada sauti ƙas ƙas haka wuyan sa ma, direct bathroom ya wuce tsawon 30 minutes yayi a ciki sannan ya fito lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib, wata jallabiyar ya ɗauko ya sanya ya tada sallah, yana idarwa ya cire ya wuce gaban mirror can ma sai da ya ɓata kusan minti ashirin ba dai sai na fada ba kunsan mutumin naku da sluggishness ya fiya lakwai lakwai tu. Tashi yayi ya wuce gaban sip ɗin nasa ya ciro kaya maras nauyi, wani army green cargo shorts da black armless t shirt Mai laushi kamar auduga ya feshe jikinsa da turaren sa me kamshi. Saida ya gama duk abinda zaiyi ciki harda sallar isha Sannan ya fito daga ɗakin.
Haka take a wurin su Kiara tunda suka tashi sukayi wanka suka fita sukayi breakfast Kiara ta koma ɗakin da suka sauka ita da Ash, ta fara aikin binciken Shadow, Ash kuwa Philip tasa ya zagaya da ita gidan ta ɗanyi kalle kalle sannan ta koma ɗaki ta samu Kiara ta tasa system ɗin ta a gaba, itama wucewa tayi ta ɗauko ta ta ta jona a caji tana faɗin, "Kin samu wani info ne Kia?".......... Ba tare data ɗago ba ta ce, "Ash kinsan abinda ke ban mamaki a duk ƙasar da yasa a samo masa mutane to a bakin border wanna ƙasar ake ajje masa wa'anna mutanen".
Cikin alamun rashin fahimta Ash ta ce, "kamar ya kenan ? Ban fahimta ba ?".
Ɗagowa kiaran tayi tare da cire hular dake kanta ta wulla kan gado Sannan ta ce, " Hakan na nufin bashi da takaimemiyar ƙasa, su kawai yaran nasa aikin su su kawo masa mutanen bakin border daga nan Kuma su juya suyi tafiyar su".
"Kenan akwai mutanan sa a bakin kowace border?"........." Yes that's the fact, to Amma yanzu ta Ina kike ganin zamu soma kamashi ?".
Ash na kunna system ɗinta ta ce, "ki daina Abu kamar ba jami'ar bincike ba idan dama taqi sai Abi hagu, zamuyi amfani da na'urar tracker ne kawai".
"Yes yes Ash kin kawo idea, dole idan da tracker a jikin mutanan mu, duk inda sukaje zamu san takunsu da Kuma motsinsu har mu sameshi".
Wata bazawarar dariya Ash tayi hankalinta akan system ɗin ta da take caccaka da zara zaran yatsun hannunta kamar wata typewriter ta ce, "Wai kina tunanin dan munyi amfani da tracker shikenan zamu samu inda shadow yake?"
............"What do you mean? Kin sake sani a duhu?". Kiara ta tambaya tana sake haɗe rai.
"Kinga shikenan daga na haske ki da fitila kema naki shadow zai bayyana".........."Stop joking Ash it's not time for that".
"What I mean shi ne in munyi amfani da tracker zamu San inda ake Kai mutanan, sannan zamu San me akeyi dasu sai muje mu ebe su, dole hakan zai girgiza shi Kuma duk inda yake zai motsa wannan shi ne target ɗin mu, motsin sa muke so daga inda yake kawai, Amma fa karkiyi depending kan magana ta do your own investigation, that's just my own idea and perception"........... Ta faɗa tana cigaba da aikin ta, Shuru kiara tayi tana kallonta tsawon 2 minutes kafin tayi focusing back Kan nata aikin, suna a haka ne Ace ya shigo tare da musu excuse Ash ce ta ɗago tana kallon sa, bakin gadon ya zauna tare da ɗaura tasa system ɗin a gefen gadon Yana kallon su, Dan suna opposite ne dashi a kan wasu kujeru guda biyu da wani table a tsakiya, Ba tare da Kiara ta ɗago ba ta ce, "Ace how far ?".
Dan watsa hannayen sa yayi tare yana ɗan taɓe baki ya ce, "Not too far, daga nayi gaba sai nayi baya, sai sa kawai na taho nan, dan Philip yace har yanzu Amjad ɗin Bai fito ba".
"To muma hakan take, Amma fa Ash ta kawo wata idea......." Nan ta faɗa masa yadda sukayi da Ash ɗin. "Yes wannan idea ce me kyau, Amma Kuma inaga me zai hana mu datsi duk wayoyin Yaran nasa domin musan ta ya suke waya ? Shi yake Kiran su da kansa ko kuwa dai ya abun yake? Mutane nawa ne suke Kiran su? Sannan daga wace ƙasa aka fi Kiran wayoyin ?".
Kallon Kiara da hankalin ta gabaɗaya yana kan system ɗin ta tayi kana ta ce, "Ace ma fa ya kawo idea shi ma, Dan daga inda aka fi kiran wayar nan zamufi focusing akai".
Ace ne ya sake cewa, " But baza mu yanke hukunci ba har sai Amjad ya fito, Amma kunyi waya da widad ne?".......... Wani dogon tsaki Kiara taja tare da faɗin, " Wanna Ɗan wulakancin bame Kiran sa saidai Amjad ɗin dake iya haƙuri dashi, dan ni bazan Kira mutum mu tsaya breathe competition ba, sai kace baisan aikin sa ba"......... Ash kuwa taɓe baki tayi ba tare da tace komai ba, Ace ya ce, " Ni fa na rasa wannan Yar tsamar da ke tsakanin ku da Widad, especially ma ke kia ko dai ko dai?"......... Ya ƙarashe cikin salon zolaya. Wata banzar harara Kia ta wurga masa da manyan idanuwan nan nata. "To kunga ko tun da na shigo bata ɗago ba sai da nayi Maganar sa"......... Ya sake faɗa yana dariya. Ashley ta ce, "God forbid, me Kia zatayi da wani Widad ai sai a rasa waye mijin waye matar".........." To ni dai bari kuga na kirashi dan inajin dukkan ku kun kyasa ne saisa kuke ta cece ku ce a kansa"........... Ya faɗa yana ɗage musu gira ɗaya. A kufule Kiara ta ce, "Kuma a rasa wanda za'a kyasa sai widad, me yake dashi da zaija hankalin".......... Ashley ta ce , "Ke da kike kallon shi ma har kika lura bashi da abun jan hankalin, ni ai ko kallo ma bai isheni ba"..........wani irin kallo Kiara ta watsa mata kafin ta ce, "Me kike nufi?"..........Shi dai Ace dariya yake kawai dan ya san ya haɗasu kwafso. Har tayi ringing ta gama Jey bai yi picking ba, Kiara kuwa kamar ita ta Kira, rai a ɓace ta ce, "Dan ALLAH ka rabu da mutumin nan Ace, yanzu gani zaiyi kamar baza mu iya komai ba in ba shi shiyasa zai tsaya yiwa mutane yanga"........ Girgiza Kai kawai Ace yayi tare da ɗaukan system ɗin sa ya ce, "Ummm bari kuga na koma inda na fito sai anjiman ku".
Shi kuwa Jey lokacin da Ace ma ya Kira bacci yake sharba Abun sa, dan bai samu yin bacci ba saida yayi sallar Asuba shiyasa bashi ya tashi ba sai 12:00pm, wanka ya shiga ya fito sannan ya shirya cikin white jeans da royal blue shirt ya fito, dinning ya nufa ba komai akan dinning ɗin dan tuni sun manta da yin breakfast har an gyara wurin, a madadin ya Kira masu aikin sai ya gwammace ya wuce kitchen ɗin da kansa, Yana shiga ya tarar da maids ɗin na faman aikin girka abincin rana, suna ganin sa suka fara gaishe shi, amsa ɗaya ya basu wato, "lpy". Sannan ya buɗe fridge ya ɗauka natural madarar shanu da ake kawo masu jarka guda duk bayan sati biyu zuwa uku daga ƙauyen mahaifin su, tsiyaya yayi a Tumbler sannan yayi waje, a dinning ya zauna tare da zaro wayar sa nan yaga missed call ɗin Ace Amma bai maida Kiran ba, ya cigaba da scrolling ɗin wayar yana kurɓar madarar har ya gama sannan ya tashi ya bar tumbler ɗin a wurin. Sama ya wuce ɗakin mahaifiyar sa saboda yadda yaji gidan nasu shuru yasan Azhar tana wurin aiki, kasancewar ta babbar yar jarida a BBC, Najmah kuwa yasan tana makaranta itada Bushra.
Kamar yadda yayi tunani kuwa hakan ne zaune ya sameta a ɗaki tana waya, wuri ya nema ya zauna har ta gama sannan ta kalle shi tana ƙara faɗaɗa fara'ar fuskarta ta ce, "Jawaad ka tashi".
A hankali ya ce, "Na tashi Ammie jiya na dawo late kunyi bacci".
"Eh kwarai Kam Najmah ta gaya min, dan lokacin Da muka tashi nake tambayar ta Bushra tace ai a wurin ka ta kwana, shine nace ta je ta ɗauko ta tazo su shirya su tafi makaranta, ya aikin naka Ina fatan ba wata matsala".
"In Sha ALLAH Babu Ammie saidai ki tayamu da addu'a Dan muna kan wani aiki ne me wahala sosai".
"Karka kirashi me wahala Jawaad domin duk yadda ka ɗauki Abu haka zai zo ma, in ka ɗauke shi da zafi to fa a tafashe zai zo ma haka in ka ɗaukeshi da sanyi to fa a kankara zai zo ma. Kawai abinda zakayi shi ne ka sanya a ranka zaka iya, ka sani Kai ɗin fa jinin soja ne sojan ma kamar mahaifin ka brigadier general Aleeyou barkidɗo, Wanda ya bada ransa wa ƙasar sa Wanda ya sayar da rayuwar sa akan ya bari a cigaba da yaɗa ɓarna, Wanda ya zaɓi mutuwa akan ya take gaskiya kuma ya bari a cutar da Al'ummar sa, Wanda ya zaɓi yin fito na fito da duk me shirin kawo tashin hankali