Author : Young Writer Category : Tknovels
ba ta wuce ɗakinta tare da gabzo ƙofar.
Bai fi minti huɗu ba ya dawo cikin gidan inda ya samu mutanan gidan ana ta maida zance, wurin Sahnish ya wuce direct yana faɗin, "Baba ka taimaka min mu kai yaron nan asibiti Dan inaga kamar sun ji masa ciwo a shoulder ɗinsa " .
Baba ilerika da hankalinsa bai yi wurin Sahnish ba sam, ya nufo wurin da hanzari yana faɗin, "Subahanallahi Sahnish, ashsha ashe Kai tsautsayin ya faɗawa kuma, taimaka masa muje, kai rayuwar nan ta zama Abun tsoro"........... Da taimakon baba ilerika Jey ya kai Sahnish asibitin kusa dasu, ALLAH ya taƙaita babu karaya kawai buguwa ne, nan suka basu magungunan suka masa allurar pain reliever Sannan suka taho, a hanya Jey ya ce, "i think itama taji ciwo a hannu ku ƙarasa kawai, ni zan tsaya chemist na taho da Nurse da zaiyi treating hannun nata".
"To ba damuwa Jawaad ALLAH yayi albarka kaji, ai kayi taimako whl ba kaɗan ba".
"Ka kula dashi baba bari naje"...........Ya faɗa Yana wucewa ya barsu.
Ko da ta shige ɗaki wuri ta nema ta zauna tare da zubawa hannayen ta ido, ji take kamar ba lpy take ba, kamar akwai abinda ke juya rayuwarta, komai na neman rikita mata tunani, wani abun bata sanin tayi sai bayan ta gama. Cikin wanna yanayin taji knocking a hankali ta ce, "Waye?"..........Mai makon ya amsa sai kawai ya shigo ciki, gyara zaman ta tayi tana kallon sa dan bata taɓa zaton gani sa ba, daga ƙofar ɗakin ya tsaya tare da karewa ɗakin kallo a ƙasa da second 60, idonsa ya tsayar a kanta kamar wanda aka tilasta ya ce, "Na zo da Nurse zai Miki dressing hannun ki fito waje".
Kallon hannun tayi har lokacin yana fitar da jini kaɗan kaɗan ga wasu har sun daskare, miqewa tayi dankwalin kanta ya zame sunkuyawa tayi da niyyar ɗauka gashin kanta ya kunce, warwarewa ya dingayi daga daurewar data masa in a sleek bun style har ya baje a gadon bayanta gabaɗaya, harta ɗauki gyalen Kuma ta fasa ta ɗauko hijab ta zura, har tazo zata fice sai ta ɗan ɗago da niyyar satar kallon sa ganin bai motsa ba, karaf idonta ya shige cikin nasa, kallon ta yake kawai irin kallon nan me cike da tarin tambayoyi da sauri ta ƙarasa ficewa, ya rufa mata baya yana tunanin yanayin gashin kanta da ya gani sai kace aljana.
Tana fita ta samu baba ilerika da wani me lab coat zaune sai first aid box a gabansa Wanda tafi tunanin shine nurse ɗin da Jey ya faɗa mata, kujerar tsugunno data gani ta ja ta zauna tare da miqa masa hannun. "Sannu Hushaima ALLAH ya tsare gaba".........Baba ilerika ya faɗa.
Akan labban ta ta amsa da Ameen Dan gabaɗaya bata jin ƙarfin jikinta .
Spirit ya dangwalo a audugar ya fara goga mata. " Sorry"......... Ɗagowa tayi ta kalle shi tsaye yake a wurin kanta hannayen sa zube a aljihu dukda fuskarsa a hade take ta nuna alamun tausayawa, murmushi ta masa kawai ba tare da tace komai ba. Har aka gama aka naɗe hannun da bandage bata motsa ba, miqewa tayi bayan an gama ta ce, "Nagode baba ALLAH ya Kara girma".........Juyawa tayi bangaren sa inda idanunsa ke yawo a kanta kamar me nazari, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke Kai a zuciyar ta kuwa faɗi take shi sai yace baya son kallo shi Kuma yaita ƙarewa mutane kallo, "Nagode". Ta faɗa cikin sanyin murya .
"Kije ki duba shi"............ Shine abinda ya faɗa yana nufar hanyar fita daga gidan tare da nurse ɗin, bayan sa ta bi da kallo tanajin wani abu na taso mata a rai kafin ta juya ta kalla ƙofar ɗakin Sahnish ɗin a hankali taja ƙafarta zuwa ɗakin.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______ 27
Yana shiga dad ya nuna masa hanya da hannu yana faɗin, "Na faɗa na Ƙara maimaitawa ba kai ba ya' ta, karka kuskura Ka je inda take, in ba haka ba whl sai na wulakanta Ka saidai ni ma Ka sa a kashe ni"........... Mathew da ya fusata ne ya boqaro, tare shi Amjad yayi ta hanyar ɗaura hannunsa a ƙirjin Mathew ɗin ya maida shi baya, sunkuyar da Kai Mathew yayi zuciyar sa na tafarfasa ya ce, "Sorry Boss".
Idonsa akan dad ya ce, "kaci albarkacin ƴarka daga lokacin da ka sanyo ƙafarka cikin asibitin nan zuwa yanzu, zan tafi ba kuma zaka sake gani na a inda kake ba har sai ka neme ni da kanka".
"ALLAH shi sitira na neme Ka, me zanyi dakai me zaka min, in kuma gori kake son min ne sai Ka zauna Ka lissafa abinda ka min a baya in biyaka, kai kasan waye ni ada ai ba matsiyaci bane gaba da baya, ALLAH ne ya qaddara min hakan har Ka samu damar taimaka min ɗin, kuma wannan tsohon baikon babu shi na warware shi ko da Farshad ɗin ya mutu kuwa"............ Girgiza Kai Amjad yayi tare da yin one step backward sannan ya juya ya fita, su Kamal suka rufa masa baya banda Mathew da saida ya sake komawa wurin dad ya nuna shi da yatsa yana huci kamar zakin daya fito farauta, kwafa yaja sannan ya juya yabi bayansu.
" To ko duka na zakayi ne, kaji Dan iska qaton banza".......... Ya faɗa shi ma tare da jan kwafar sannan ya juya ya koma ɗakin da yasa aka canzawa Nayrah ɗin.
Ko da suka fita gidan su ya nufa, Kamal na yin parking aka buɗe masa, da sassafar ya fito wanda ba halinsa bane Ada dan Amjad komai nasa a hankali yakeyi cikin nutsuwa, saisa in kana sauri to karka neme shi dan shi acewar sa duk abinda aka sa gaggawa za'ayi dana sani ne daga baya.
Ko lura da Julaybin da kuma Alhaji fuad bin talib tsohon abokin kasuwancin Dadan su baiyi ba yayi shigewar sa ciki, kallon Julaybin alhaji fuad yayi cikin harshen turanci ya ce, "Wannan ba Amjad bane?"........ Murmushi Julaybin yayi Yana gyara tsayuwa ya ce, "Shi ne, ai kasan duk wanda ya sai rariya yasan zata zubda ruwa, tun bayan tonuwar asirin sa haka yake kullum cikin tashin hankali da firgici da kuma tsoron abinda zai biyo baya".......... Jijjiga kai Alhaji Fuad yayi tare da furta. " ALLAH ya kyauta"........ Yana sake kallon inda Amjad ɗin yabi sannan ya wuce Julaybin ɗin na take masa baya zuwa mota.
A falo ya samu Anah da jikokin ta sai Durrah da Adla dake dinning masu aiki na serving ɗinsu, gaisheshi da yaran suka farayi yasa duk hankalin su ya dawo kansa, kusa da mahaifiyar tasa ya zauna. "Yanzu na gama waya da Hunaiz, ina ƙoƙarin kiranka sai gaka kuma ".
"Eh Anah"............Ya faɗa fuskar sa ba annuri ko kaɗan .
"Ya min bayanin komai amma nace yayi magana da mahaifin sa, su suje saboda kasan bangaren Dadan Ku baza su taɓa shiga ba ko dan wanna laifin da aka qaqaba maka, saidai ko yayyin naka ai kayi magana dasu ko?".
"Bana buqatar su anan bangaren".
"To wai ma me yayi zafi ne haka naga dai tsawon lokacin da aka yi baikon nan, ni nake binka ma kana cewa ba yanzu ba, sannan yau kuma kwatsam kace gobe kake so a ɗaura aure ba shiri ba komai ana tsaka da wannan tashin hankalin ".
Saida yaja numfashi sannan ya ce, "Anah ban taɓa faɗa Miki abinda ke tsakanina da mahaifin Nayrah bane, tun bayan faruwar abun nan saboda bana so hankalin ki ya tashi dad ɗin Nayrah Y.........." Duk abinda ya faru daga lokacin da aka bayyanawa duniya cewa yayiwa wata ƙaramar yarinya fyade zuwa faɗin da ake cewa yana da hannu a cikin masu safarar Mutane ƙasashen duniya, har zuwa yanzu da suka rabu a asibiti.
"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun ²" .............Shi ne abinda Anah ke maimaitawa, "To yanzu miye abinyi kenan? Su Akram ɗin wurin wa zasu je bayan uban yarinya yace bazai baka ba".
"Gidan kakanninta zasuje su samu uncles ɗinta".
"Kana tunanin su zasu iya aurar da yar ɗan uwansu ba tare da izinin sa bane?".
Gyada kansa yayi alamar eh sannan ya ce, "Abinda na sani kawai a gobe za'a ɗauramin aure da ita bayan an sauko daga masallaci".
"ALLAH ya kawo ma sauki a lamarinka Babban mutum, amma naso Juraysh ka ɗaura akan Maganar, ko ba komai ai shi ne gaba da Hunaiz abinda zai yi Hunaiz bazai iya ba, kuma shine kuke haɗa kai dashi".
Kafin yace wani abu su Durrah suka shigo falon da niyyar tsokanar sa amma ganin yanayinsu su duka yasa jikinsu yayi sanyi, zama sukayi durrah ta ce, "Anah meke faruwa na ganku haka? Akwai matsala ne?"......... Zazzafan numfashi Anah ta furzar sannan ta zayyane musu halin da ake ciki, cikin qunar rai Adla ta ce, "Whl ya Amjad karka yafewa duk wanda ke da sa hannu a wanna qazafin da aka maka, kasa a binciko ma su sannan ka tozartasu a idon duniya".
Durrah ta amsa da, "Tabbas an cutar damu Anah dan ba karamin giɓi aka mana ba ta hanyar ɓatawa Amjad suna, saboda an san dukda kasancewar shine ɗa namiji ƙarami a cikin gidan, shi ne ke tsaye a gidan nan, shi ke jagorantar abinda manyan suka ƙasa saisa aka shirya masa haka".
Dagowa yayi yana bin kowaccensu da kallo kamar wanda baya gane abinda suke faɗa. Anah ce ta ce, "Zato zunubi Durrah a yanzu baza mu ɗaurawa kowa ba, Ni kawai fatana ya wanku a idon al'umma, so nake zargin da ake masa ya kauce, batun a nemo wanda sukayi a tozarta su duk bai taso ba, Mun barwa ALLAH tunda ALLAH baya bacci Kuma sai ya saka masa"........Miqewa yayi yana duba agogon hannunsa ya nufi hanyar fita, Durrah ce ta ce, "Ina zaka Kuma ?".
"Ina zuwa"............Ya faɗa tare da ficewa cikin sauri. Dawo da dubanta tayi wurin Anah da faɗin, "Anah fuskar Amjad bata cika bayyana halin da zuciyar sa take ciki ba amma yau ta nuna, tabbas ba batun yarinyar nan bane kaɗai, akwai wani Abun da ya ɓoye mana"..........Shuru Anah tayi itama ta lula duniyar tunani can Kuma ta ce, "Kar dare ya muku durrah ya kamata ku wuce gida".
"Ah ah Anah bazan iya tafiya na barku a wanna halin ba, Dama kuma daddyn su Arzan ɗin ma baya nan, kawai zan sanar dashi a waya zan kwana anan zuwa gobe muga abinda ALLAH zaiyi"...........Anah bata Ƙara cewa komai ba sai tashi da tayi ta wuce ɗakin ta.
Yana fitowa kamal dasu Mathew suka taso a ɗarare amma ganin baice komai ba ya bawa kamal ƙarfin guiwar shiga driving seat dan already an budewa Amjad ɗin har ya shige, su kuma Aram da Mathew suka shige ɗayar mota suka rufa musu baya, saida suka hau hanya ya ce, " Asibiti zamu koma"...........ya ƙarashe yana sake duba agogon hannun sa. Da "to". Kamal ya amsa masa.
Lokacin da suka isa ɗakin da Nayrah ɗin take yan sanda suka samu guda biyu tsaitsaye ƙofar ɗakin, girgiza Kai kawai Amjad yayi tare da zuwa ya wuce ta gabansu ya ratsa ta tsakiyar su ya shige ciki ba tare da ya ko ɗaga ido ya kalle su ba, su Kuma su Kamal sukaja suka tsaya daga nan waje.
Kallon juna yan sandan sukayi ɗayan ya ce, "Kai Awsaf cewa fa yayi Kar mu bar wani namiji ya shiga in ba likita ba. ko Kuma a Kira matar sa ta tantance mutumin".......... Hararar sa Awsaf yayi da faɗin, "To Kai me yasa da yazo shiga ɗin baka hana shi ba sai nine me tsautsayi a ka".
"To ai Kai naga baka yi magana ba".......... Tsaki yaja ya ɗauke kansa da faɗin, "In ya fito kana iya tsaidashi ka tambaya waya bashi izinin shiga ko kuma ka bishi ciki ai baka makara ba".
"Ai saidai in mu bishi tare".
"Kai da wa ?"........... Awsaf ya tambaya yana masa irin kallon nan na baka da wayo.
"Ni da Kai mana".
"Kaga da ALLAH Sargeant ƙarami kayi min shuru kaji".
Shi kuwa Amjad ko da ya shiga ɗakin bai samu kowa ba domin Mumu tana toilet sai Nayrah dake kwance tana bacci, gaban gadon ya matsa daidai lokaci wayar sa ta fara haske alamar shigowar kira, sake kallon Nayrah ɗin yayi ya kalla me Kiran wayar, lips ɗinsa na ƙasa ya kamo ya dan ciza sai Kuma ya juya da niyyar fita yaji an riqo hannun sa, juyowa yayi dan ganin waye idanun sa suka gauraya da nata, kallon sa take da sirkakkun idanunta, hannun sa dake cikin nata ya kalla sannan ya maida kallon sa kanta kokarin cire oxygen ɗin ta fara ya riqe hannun, kwacewa tayi ta cire, ciki dasasshiyar muryarta na marassa lpy ta ce, " Meke faruwa?".
Kamar bazai faɗa mata ba sai Kuma yace, "wata waya zaki amsa"...........Da ido ta masa alamar to......."Zaki iya?" ...........Ya sake tambaya yana kallon ta, nan ma da ido ta amsa masa da eh.
Amsa Kiran wayar dake ta shigowa yayi tare da maqala mata a kunne, amsa sallamar da akayi a cikin wayar tayi sannan ta yi shuru can Kuma ta ce, " Da sauki iyani"...........Banji me aka ce a ɗayan bangaren ba ta ce, "Ameen nagode Iyani"..........Shuru tayi tana sauraron abinda Iyanin ke faɗa a ɗaya bangaren, a hankali ta ɗaga ido ta dubi Amjad ɗin da Shi ma ita yake kallo, "Eh iyani haka ne Kuma na amince"........Shuru tayi can Kuma ta ce, "to".
Zare wayar yayi sannan ya maida mata oxygen ɗin da sauri ganin tana jan numfashi da kyar. " zan tafi sai gobe in sha ALLAH zan dawo, ALLAH ya baki lpy My Ninie ALLAH ya tashi kafaɗun ki".......... Sansanyan murmushi ta masa tare da ɗan daga masa kai, shi kuma ya juya ya fita da sauri .
" A sauka lpy".......... Sargeant ƙarami ya faɗa yayinda Sargeant Awsaf ya Maka masa harara. Shi kuwa bai ma san sunayi ba yayi gaba abinsa su Kamal suka rufa masa baya.
Ko da mumu ta fito bin ɗakin tayi da kallo saboda tsarabar kamshin turaren sa da ya bari a ɗakin, kallon inda Nayrah take tayi taga bacci take, zuwa tayi ta buɗe ƙofar ɗakin tare da kallo su Sargeant ta ce, " Akwai Wanda ya shigo ne?"......... Da sauri Sargeant ƙarami ya ce, "Kai ah ah, ai ko aljani bai shiga ɗakin nan ba bare mutum".
Tsaki Sargeant Awsaf yayi da faɗin, "Ba Wanda ya shiga ma'am".
Komawa tayi tana tunani ko ta window ne iska ya ɗauko kamshin wani turaren.
____________A bangaren Julaybin kuwa bayan ya raka Alhaji Fuad ya tafi, bangaren mahaifin nasu ya koma cikin farin cikin yana zuwa ya samu su Nuhail a inda ya barsu zama yayi, Awais da ya kasa hakuri ya ce, "Ya ake ciki ta faɗa ne?".
"Kai bari, wancan yaron naga ya shigo a fusace, tunda nake ban taba ganin fuskarsa a irin yanayin dana ganta yau ba".
Nuhail ya ce, "To me ya faru haka".......... Awais ya cafe da, " koma me ya faru ba ƙaramin abu bane gsky".......... Julaybin ya sake cewa, "ko ma dai miye nayi matukar jin dadi dan da ya tsaya wurin Alhaji Fuad da an samu matsala dan kasan bansan ya dawo ba saisa da ya min batun zaizo duba jikin Dada ban hana shi ba, to ashe munafikin yana nan".
"To yanzu ya kukayi dashi?"........... Nuhail ya tambaya cikin zumuɗi. "Yace ba damuwa zai neme mu ".
"To batun HD AURUM MINING ɗin fa?".......... Nuhail ya sake tambaya.
"Kana da son dawo da magana baya ai kasan Babu ita a yanzu dama Dada Amjad kawai ya ɗaura akai to shi Kuma yanzu gabaɗaya ƙasashe sun rushe Alaqa da duk wani abu da zai sanya suyi mu'amala dashi, so kaga babu batun ta koma sunyi kayan sai dai a karyar dasu a banza a cikin qasar Nifaz".
Awais ya ce, "kasan ko a labarai yanzu an daina sakota Amma ba wanna ba kasan yadda irin aikin nan yake, kana da kuɗi isassu a wajen ka dai ko?"...........Ya faɗa yana kallon Julaybin ɗin.
"Eh to da a tunani na so nake nayi exporting wasu crude oil yaso sai na canza account ɗin da zasu sa daga na dada zuwa nawa, amma ina tantance mutumin da zamuyi harkar dashi ne ba tare da yaron can ya sani ba".
"Hakan yayi ka fidda da dan yawa dan nima Ina bukatar ɗan wasu personal kuɗaɗe gsky"........... Awais ya faɗa yana gyara zama.
Nuhail ya ce, "kamar ka shiga raina Awais, kawai ka fidda duk Wanda suke a ƙasa yaso in an tura kuɗi sai ka ɗauka abinda zaiyi a harkokin buɗe ma'aikatun namu sauran sai kowa ya ɗan riqe a hannu ko ya kukace?".
"Ba damuwa, Amma a sirrance zamuyi saboda
In yaron can yayi magana mu tuhume shi kan hakan kun gane plan ɗin ai?". Faɗin Julaybin.
"Hakan ma yayi"........... Nuhail ya faɗa, da haka suka rufe zancen suka shiga wata hirar.
WAYE HASHIM DARWIN?
Hashim Darwin cikakken hamshakin Mai kuɗi ne da duniya gabaɗaya take ji dashi, Yana da ma'adanai na tono gold da Kuma sauran precious stones wanda ba kowa ya san dasu ba sai masu masa aikin Wa'anda suka kasance amintattun sa, abinda kawai duniya ta sani yana da ma'aikatar dake sarrafa gold, diamond da sauran precious stones din da duk duniya a HD AURUM MINING (Hashim Darwin aurum mining) kawai ake samun irin su, nan ne fa duniya ta masa ca kowa burin sa