BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   6 / 53

15K to 18K   out of 156.9K words

na gaya Miki baza kiyi komai ba".

A tsawace ta ce , "Dan ALLAH Ni ka fadamin ka daina min kwana kwana kana bata min lokaci".............Shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba can Kuma ya ce, "Su karafiya ne".

"Suka ma me?" Ta tambaya cikin zaquwa. "Duk wanna abinda kika gani"......... Ya bata amsa cikin fargaba. "Me ka musu?"..........." Me kuwa zan musu ai kinsan ba abinda zai haɗani dasu, faɗan ki ne ya shafeni sunce wai sun daki kuɗinsu".

Wata ashariya ta lalubo ta kwantsama sannan ta ce, "In kuwa haka ne lalle sun Kawo karshen iskancin su da kansu, wa yace musu ana irin haka Dani, whl in duk duniyar nan gatan su ne sai zaman unguwar nan ya gagare su, dabar ma in ance musu ga hanya baza suyi ba".

Kafin yayi magana ta zari gyalen ta dake kan igiya tayi waje yana kiranta Amma ko juyowa batayi ba, Cikin karfin hali ya fara kokarin tashi ya bita amma jikin sa ya masa nauyi hakan ya sashi dafe Kai yayi shuru kawai cikin tsananin tashin hankalin abinda Hushaiman zataje tayi.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22




STEP 1




PAGE _______7 & 8




Zaune suke gabaɗayan su a dinning suna breakfast dad, Mumu, Nayrah da kuma kannen ta uku Nashwa, da majeed sai kuma Nashmi. "Nashwa ya jikin naki?".......Dad ya tambaya yana kai Mug bakin sa.

"Naji sauƙi dad Alhamdulillah".........." Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara sauƙi, amma in kinji zazzaɓin ya dawo kuje asibiti".

"In sha ALLAH dad"..........kallon Mumu yayi da faɗin, "to Hajiya Latifa ni zan fita ba wata Matsala ko?"......... tissue ta ɗauka ta goge bakin ta sannan ta ce, " Akwai abu ɗaya, batun Farshad gata nan ka faɗa mata da bakin ka saboda ni ta raina ni, ban isa nayi magana ɗaya ba saita maida min goma".

Rufe Nayrah da faɗa dad yayi kamar zai haɗiye ta ɗanya har abin yaso ban mamaki, cikin zafin rai ya ce, " kin san dai abinda ya faru dangane da wancan baragurbin da kika kawo mana dalilin jajiɓe jajiɓan ku na tsiya, sannan na riga na muku iyaka ke da shi kuma batun baikon ma yanzu babu shi na warware. Akwai yaron Aboki na Farshad, kuma na riga nayi magana da mahaifin sa na kuma bashi auranki saboda bana ma so aja Lokaci, zaizo ku gaisa sauran naji wani abu marar daɗi sai na mugun saɓa Miki whl".

Cikin rawar murya ta ce, "Haba dad, haba dad dan ALLAH karku yiwa Amjad haka, shi ɗin bai cancanci hakan daga gare ku ba, dad nasan kai ɗin babban mutum ne kuma ka riqe muqamai da yawa, amma ka tuna halaccin Amjad a gareka ba wai ina ma gori bane, kawai ina ma tuni da baya ne, a lokacin da dukkanin abokan naka suka gujeka suka daina yi da kai saboda kawai ka samu raunin arziki ba tare da sun duba kai ɗin waye bane ada, amma shi fa ? Yana tare da mu . Dad zuciya me halacci bata manta alheri dan ALLAH dad karka rufe idanun ka ".

Mumu ce ta amshe da, "A lokacin ai bamu san ainahin ɗayar fuskar tasa ba, waya sani ma ko dan ya gan mu da yara ne yayi cinikin su ya bamu kuɗin idan ya samu sarari ya yi gaba dasu, ko kuma ke da shegen rawar kanki in ya samu dama ya ɓata Miki rayuwa ya cucemu. Kin shiga zuciyar sa kinga niyyar sa ne a lokacin da ya taimake mu? ba'a isa ayi magana ba sai kice a dinga tuna alherin sa".

"Ko ɗaya Mumu Amjad zuciya ɗaya ya taimake mu, kuma nayi mamakin yadda zantukan mutane suka samu wurin zama a zuciyar ku, whl Mumu! dad!, in kuka tsananta akan Amjad zakuji kunya, Ni nasan waye shi kuma nasan bazai taɓa aikata wa'annan abubuwan ba, kawai dai mutane ne suke son masa ƙazafi saboda shi ɗin sananne ne, ko kuma masu son yin amfani dashi su ɓatawa mahaifin sa suna, amma Gsky zatayi halinta nan bada jimawa ba".

"Ke Nayrah saurara duk wannan maganganun naki bashi zai wanke shi daga zargin laifu......."

"Kaji ko dad kai ma zargi kace".......... Ta katse shi, tashi yayi bata ankara ba ya wanke ta da mari sannan a dake ya ce. "Keee dakata min haka kinji ko, dan mun baki damar magana ba shi yake nufin zaki dinga ja in ja damu ba, har kina ikirarin zamuji kunya, akan wani banza can da baki haɗa dangi dashi ba kike fatan iyayanki suji kunya tsabar baqar zuciya, to bari kiji ko ya aikata ko bai aikata a yanzu bamu iya bashi auran ki saboda sunan sa ya riga ya ɓace a idon duniya, in kuma ɗan taimakon da ya mana ne ada a yanzu zan iya linka masa na maida masa, kuɗin ma da bamu san na halal ne ko haram ba, wawiyar banza wawiyar wofi".

Bataji zafin Marin da dad ya mata ba sai zafin maganganun da yake jifan Amjad dasu. Cikin dacin rai ta ce, "Dad sai dai kuyi hakuri ban taba qin wani abu da kuke so ba Amma in dai kuka hanani auran Amjad to whl bazan auri kowa ba, saidai ku kai gawata"......... Tana kaiwa nan ta miqe ta bar dinning ɗin da gudu tana fashewa da kuka.

"Sai dai kuwa ki mutu shashashar banza shashashar wofi, dan kin mutu zan damu ne". Dad ya faɗa cikin tsananin fushin da ya sake ɗauremin kai.

"Ka gani ko Alhaji, kana dai gani, yarinyar nan nema take tafi ƙarfin mu anya yaron nan ba asiri ya mata ba, yarinya lokaci daya ta birkice ".........….. Mumu ta faɗa tana tana nuna hanyar da Nayrah tabi da hannu. A hankali Nashwa ta ture plate ɗin abincin dake gabanta ta miqe tabi bayan Nayrah ɗin. Majeed ma miqewa yayi tare da faɗin, "Nashmi tashi mu wuce school kar muyi late, dad mu zamu wuce".

"Ku sauka lpy".........Ya faɗa har lokacin sauke numfashi yake da zafi zafi alamun akwai abinda ke cin ransa. Ba tare da Mumu ta lura da yanayin sa ba ta ce, "Alhaji yaran nan duk sun zama munafukai fa, ka duba duk sun tashi sun bar abincin saboda kawai an yiwa wannan me shegen taurin kan faɗa"..........."To laifin waye?"........ Ya tambaya a kausashe.

"ban gane laifin waye ba?"............itama ta maida masa tambayar tana zuba masa ido, kallon ta yayi na tsawon seconds kafin ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, "laifi na ne. Bari naje sai na dawo".........kwafa taja ta bishi da kallo har ya fice sannan ta tashi ta bar dinning ɗin itama.

____________Nayrah na shiga ɗaki gaban mirror ta wuce ta tsaya tana kallon kanta yayin da hawaye ke zarya akan kumatun ta, ta dau tsawon 3 minutes kafin ta share hawayenta ta nufi inda wayar ta take ta ɗauka tare da dannawa Amjad kira, har tayi ringing ta katse bai ɗaga ba , sake kira tayi a karo na biyu saida ta kusan katsewa ya ɗaga, a lokacin fitowar sa kenan daga wanka yaga wayarsa na ta haske alamar shiga da fitar kira, dauka yayi tare da picking call ɗin yasa a handsfree sannan ya matsa gaban mirror ya ɗaura wayar. "Ya Niniyous ɗi na ta tashi?"........ Ya faɗa yana goge gashin kansa da ƙaramin farin towel ɗin dake rataye a wuyansa.

"Amour kana ina?"........... Ta tambaya in a serious tone. Tsayawa yayi da abinda yake saboda yanayin yadda yaji Muryar ta, sa hannu yayi ya ɗauki wayar da faɗin, "Meke faruwa?"........ Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Da matsala Amour, Dad yace wai ya warware baikon mu sannan ya bada ni ga ɗan abokin sa wai Farshad".

A maimakon ta ji alamun damuwa a tattare dashi kamar yadda ita take ciki tunda wanna abun ya faru, sai taji saɓanin hakan dariya taji ya kwashe da ita, dariya yake cike da jan hankali wanda in kana sauraron sa baza ka so ya daina ba, haka in kana gabansa ne baza ka gaji da kallon sa ba, saboda yadda dariyar ta masa kyau da kuma salon da yake yin ta. Shiru tayi tana sauraron sa har ya tsagaita sannan ya ce, "To yanzu miye abun tashin hankali Ninie, ke fa Matsala ta dake kina da saurin rikicewa abu kaɗan ke firgita ki, ina kika taɓa ganin an warware baiko haka, in kin manta in tuna Miki harta sadakin ki fa na bayar kawai fatiha ce ba'a shafa ba, sannan daga sama ace Miki an warware baiko kuma ki tashi hankalin ki".

" Ka fahimceni Amour kar ka dauki abun nan wasa, whl su mumu sun watsar da duk wannan"...........ajje wayar yayi yana daukan Gris dior body creme ya ce, "Ki kwantar min da hankalin nan naki Niniyous, zanyi wani Abu a Kai Karki damu kinji "...........Shuru tayi dan hankalin ta ya rabu ne gida biyu kuma. "Baki yarda dani bane tawan?"......... Ya faɗa cikin wata irin murya me saukar da kasala.

"I tr..ust you "............Ta amsa tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya.

"Sai da dai kikayi kuka ko? To na dai na cewa karkiyi kuka duk lokacin ma da kikaji kina sha'awar yin sa ki kirani nazo da bucket na tari kayana".

"Dama ai Baka damu ba, tunda abar tsokana nake zama a wurin a a maimakon ka lallashe ni".........dariya ya kyalkyale da ita kafin ya ce, "Kina da katoton aiki a gabanki kuwa, ni dake wa zai lallashi wani?".

Murmushi kawai tayi da faɗin, "ALLAH ya yafe ma amour".........." Ameen tare da Niniyous". Haka suka cigaba da hira yana shiryawa har ya gama sannan suka sallama ya dauki abubuwan da zai buqata ya fita . Dinning ya fara zuwa yayi breakfast sannan ya wuce sama, a falon farko ya same su ita da Adla, ƙarasawa yayi ciki ya zauna tare da gaishe da Anah , shi kuma Adla ta gaishe shi.

Amsawa yayi tare faɗin, " ke yau baza ki makaranta bane?"..........."bani da lectures yau yaya"........ Jinjina kansa yayi sannan ya ce, "Anah ni zan fita, dama nace barin hawo naga ko kin fito".

"To yanzu da sassafen nan ina zaka Babban mutum"....... ɗan shafa fuskar sa yayi kana ya ce, " Anah na riga na saba da fitar, in na zauna gidan takura zanyi, amma ba nisa zanyi ba".

"Ba wai bana son ka fita bane, hankalina ne baya kwanciya in Ka fita har sai naga ka dawo".

"Karki damu Anah zan biya na ɗauki su Aram ai, ba abinda zai faru in sha ALLAH".

"Shikenan amma ka kula da kanka, ALLAH kuma ya kare min kai ya maka Albarka ya kuma baka Sa'a"..........."Anah Ni fa ?"....... Adla ta faɗa tana bata fuska. Miqewa yayi tare da dungure mata kai, "Uwar gasa, Anah ni na wuce".......Ya faɗa yana daukan hanyar barin falon. "To ALLAH ya dawo da kai lpy "........ Anah ta sake faɗa.

Saida ya biya ya duba Dada sannan ya fita in da ya tarar da kamal yana jiransa. "Ina kwana boss"......... "Ka tashi lpy?". Ya tambaya yana shiga motar da kamal ɗin ya bude masa. "Alhamdulillah". Kamal ya amsa yana rufe masa ƙofar sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar yaja suka fice. Gidan sa suka nufa, suna shiga su Aram suka zagaye motar tasa fitowa yayi yana amsa gaisuwar kowanne su sannan ya wuce ciki ɗaya daga cikin su ne yabi bayan sa sai da suka shiga falon can ciki sannan ya tsaya ba tare daya juyo ba ya ce, "Philip da wani abu ne?".

Da sauri Philip da dama jira yake a bashi umarnin magana ya ce, "Yes boss, wata gagarumar nasara ce domin mun samu request daga SHADOW yana so mu masa aiki ne, duk wasu sauran details na tura ma "..........Amjad da tun lokacin da aka ambaci SHADOW ya juyo cikin wani irin slow move, murmushi yayi yana tafa hannu kana ya ce, " Weldon Weldon Philip, lalle wannan ɗin nasara ce a gare mu, yanzu zan duba komai, kaje zan neme ka in na gama"..........."Okay Boss". Philip ya faɗa yana dan rusunawa alamar girmamawa sannan ya juya ya fita.

Ɗakin ya wuce gaban wani ƙayataccen curtain da ya ƙarasa dakin kyau ya tsaya, zaro wayarsa yayi tare da yin wani danne danne sannan ya ɗago ya yaye curtain ɗin, wata computer ce ta fara magana a jikin bangon ga wata danger dake kawowa da ɗaukewa, hannunsa ya ɗaura akan danger take computerta gabaɗaya ta kawo wata greenlight tare da shatin yatsun hannunsa saida ta gama scanning din tafin hannun nasa da fingers print sannan wata kofar sirri ta buɗe ta jikin bangon, wani madaidaicin ɗaki ne ya bayyana baza ka taba cewa rana bace dan dim light ne kawai a ciki, yana shiga kofar ta rufe kamar ba a tsaga ƙofa a wurin ba, gaban wani tsararren table ya nufa da kafa yaja kujerar ya zauna, tare da danna wani abu a wayarsa wuta ya kawo a socket socket ɗin, wayan ya sake latsawa take Ac ɗin dake ɗakin suka Kunnu su ma, wayar system ɗin dake kan table ɗin ya jona jikin socket, still hankalinsa akan wayarsa har system ɗin ya gama budewa sannan ya ɗaura wayar gefen system ɗin a kan table, ya gyara zama tare da maida hankalin sa akai gabaɗaya ya fara wani aiki, sai da ya ɗau good two hours sannan ya kashe komai ya tashi yana miqe hannuwansa da suka tara jini. Wayarsa ya ɗauka ya kashe AC da wutar ɗakin sannan ya buɗe ƙofar ya fita. Gaban gadonsa ya nufa yana zuwa ya faɗa akan gadon tare da janyo pillow ya ɗaura kansa akai ya lumshe idanunsa amma ba bacci yake ba saboda ƙafarsa da yake dan jujjuyawa kaɗan kaɗan, ya ɗau tsawon lokaci a hakan dan har sai da akayi kiran sallar azahar sannan ya tashi yayi sallah.

Fitowa yayi ya wuce dinning, ɗinbin mamaki ne ya kamani ganin yadda dinning ɗin ke shaqe da manyan warmers, komai cikin tsari. Plate ya dauka da spoon ya ɗaibi abinda zai iya ci sannan ya tsiyayi juice ya koma ya zauna.

Yana kai spoon bakinsa wayar sa ta fara haske ba tare da ya daina cin abincin da yake ba ya yi picking call ɗin daga ɗaya bangaren akace, " Whl kai ba ƙaramin Kwaro bane Amjad, ka iya ƙera mota me tafiya da kanta sannan ka bar mutum da faman wahalar tuqi".

Murmushi yayi me sauti sannan ya ce, "To ai shi ne wahalalle shi wanda yake ganin shi ne matuƙin".

"Baka da kyau Sam Sam Whl, Mu kan mu tsoro kake bamu"..........lemo ya kurɓa da faɗin, "Habaaa ranka ya dade ai banda ku".

"Kai dai a bar zancen, na gama karanta saqon ka har na ma reply amma nace sai na kiraka, dan haka kaga sai anjima mayi magana".......bai ce komai ba har ya kashe wayar. Ajje wayar yayi sannan ya cigaba da cin abincin sa har wani kaɗa ƙafa yake . Yana gamawa ya koma parlour tare da kiran Philip.

"Have a seat "......... ya faɗa a lokacin da Philip ya karaso. Zama yayi kamar yadda ya bashi umarni yayin da shi kuma hankalin sa na ga wayar dake hannun sa can kuma ya ce, "Philip who do you think you can take with you to former deputy governor house Alhaji nu'uman?".........Shuru Philip yayi kafin ya ce, " I think Nazbeer".

Dan girgiza kansa yayi da faɗin, "No you are not going with Nazbeer I have got something else for him"........."But boss, what's the issue?"

Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba yana cigaba da latsa wayar sa ya ce, "check your phone, I sent everything to you, Jan kunne ne kawai. Ina da Abubuwa da yawa a gaba na zan shiga ciki, fatan ba wata matsala ?".........."Then Danny will go with me, if that's the case".

Dan matsa yatsan hannun sa yayi har sai da yayi ƙara sannan ya ce, "Be careful, Ku San takun ku, karku bani matsala".

"Yes boss!"

"Alryt you can go".......... Ya faɗa yana kallon wani wuri kamar me tunani, har Philip ya tashi zai fice ya kira shi, "Philip!"

"Yes boss"...........Philip ya faɗa yana tsayawa tare da juyowa yana fuskantar sa.

" Call Baba Sufi and ask him to call Awaais and the rest. Tell him to tell them dada's seriously sick, he's looking for me but he couldn't reach me, and send doctor kinal. Then make sure you cut our resident's network after they arrive, and take care of the rest of the matters. karka bani matsala ka san dai komai, I've repeated myself"..........Yana gama faɗin haka ya tashi ya wuce ciki.

Bashi ya fito ba saida akayi sallar laasar, sanye yake da wani crazy blue jean da ash shirt, kafarsa sanye da sneakers na kamfanin Louis Vuitton, haka fuskarsa ya sanya wani makeken sunshades tare da noes mask sannan ya kawo wata arniyar P cap ya sanya tare da juya gaban ya koma ta bayan . Tafiya yake cikin nutsuwa har ya fito compound ɗin gidan, nan su Aram dake zazzaune suka taso suna masa Barka da fitowa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi mota, da sauri suka bude masa ƙofar ya shige, kamal ya shiga mazaunin driver. Janye wa sukayi gefe dan sun san tunda bai neme su ba baya buqatar su a fitar tasa. A hankali Kamal yayi reverse tare da juya kan motar ya harba ta kan titi ba tare da yasan in da zasu ba, saida sukaje kan roundabout sannan ya ce ,

6 / 53