Author : Young Writer Category : Tknovels
yayi kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru tare da sake juyawa yana kallon cikin masarautar tasu ta windown . Rouslan Bai sake cewa komai ba sai ma lumawa da yayi cikin wata duniyar tunanin .
Kamar wanda aka tsikara cikin faɗa ya ce, " Kai wai baza ka taka motar nan bane kana tuqa mota kamar wanda ke tuqa jaki"......... Ba sai na faɗa ba kunsan waye zai faɗi haka Reeslan Maleekh ne naku na gargajiya.
"Afuwan Maleekh, ALLAH ya huci zuciyar ka"......... Driver ya faɗa yana ƙara take motar a guje. Ƙwafa yaja baice komai ba har suka ƙarasa masallacin fada in da ya cika jingim da mutane bako masakar tsinke duk inda ka wulga mutane nen su ne, wai a lokacin ma ba'a fito da gawar yassar ɗin ba kenan. Can na hango Sultan kana kallon sa kasan yaji mutuwar ƙanin nasa .
Fadawan da suka rako su Rouslan ne suka shige gaba tare da fara tutture mutane suna faɗin, "Gyara gyara magada kujera aurellon zasu wuce, takawar ku lpy yayan sarki jikan sarki sarauta aurellon dole"......... Basu tsaya ko ina ba sai wurin mahaifin su Sultan, rungume shi sukayi wannan ta left wannan ta right ba sai na faɗa ba kunsan yadda gaisuwar larabawa take. Dan bubbuga bayan su yayi a hankali tsawon seconds kafin su ɗago da faɗin, " ALLAH yajikan Ammu, ALLAH ya bamu hakurin rashi yasa Mala'ikun Rahma su karɓi bakwancin sa".
A hankali Sultan ya motsa labbansa tare da amsawa da ameen, daga haka suka koma gefen sa suka tsaya suna jira a fito da gawar.
______________Tun da ya fito hadimai suke zubewa suna kwasar gaisuwa a wurin sa ko lura da ummie dake zaune a falon tare da masu mata hidima baiyi ba ya nufi waje yana wani buɗawa kamar wani nigga.
"Sahel!"...........Ummie ta kira sunan sa. Tsayawa yayi tare da juyowa sai kuma ya fara takowa zuwa inda take yana faɗin, "Ummie kina nan ashe ban lura ba ai, na fito ina sauri naje wurin rasuwar nan kar ki zo kina faɗa kuma"........Ya ƙarashe yana faɗawa cikin luntsumammun cushion ɗin dake cikin makeken falon.
Kallon khadiman nata tayi ba tare da tayi magana ba duk suka miqe suka bar wurin, dawo da kallon ta tayi kansa yana sanye da wani arnen crazy jean sage colour tare da wata oversized t shirt dark blue, ƙafarsa sanye da wani white canvas, haka wuyansa wasu dogayen sarqoqi ne kunnen sa ɗaya maqale da ɗan ƙaramin ɗan kunne me masifar kyau da tsada. " Yanzu Sahel a haka zaka fita? a haka zaka je gaban mahaifin ka da al ummar gari? a haka zaka je wurin da akayi rasuwa? Ba fa club bane ko joint ba kuma cikin abokai zaka ba. Kawun ka ne fa ya rasu, haba dan ALLAH wai kullum sai ka sani magana ne?".
Kallon jikinsa yayi da faɗin, "Ummie miye aibun kayan nan fisabilillahi, ko kinsan dollars nawa na ɓatar wurin sayen su kuwa?".
"Kai da ALLAH tafi can sha sha sha da baisan inda ke masa ciwo ba, ka tashi kaje ka canzo wannan kanbaltun kayan kamar ɗan bori ka kuma cire wa'annan sarqoqin banzan, kayi shiga ta mutunci kazo ka wuce"............ Miqewa yayi yana faɗin, "Gaskiya ni zan koma in da na fito wannan ai takura ne, ace mutum bazai sake yayi abinda yake so ba, to in banyi a gidan mahaifina ba a ina ake so nayi".
"La ilaha illallahu, oh ni balqis ALLAH nagode ma wannan yaro ya zanyi dashi ne, duk inda nayi sai yayi wani wurin"........... Ta faɗa cikin damuwa, tana nan zaune yazo ya fice har lokacin qunquni yake, ya dai sauyo kayan amma kuma still ƙana nan kaya ne saidai wannan da ɗan mutuncin su.
Ganin driver ya nufi bangaren Sultan ya sashi faɗin, "Bashshar ina muke zuwa ne ina cewa wajen rasuwar zamu je".
"Eh ranka ya daɗe ai a bangaren mai martaba ake zaman matan kuma a gidan marigayi suke".
"Okey"...........Ya faɗa yana zaro wayar sa ya shiga lallatsawa har suka ƙarasa, buɗe masa ƙofa akayi bayan sunyi parking amma sai da yaja kusan minti ishirin yana waya da wata budurwa sa mai suna Tina, Sannan ya sako ƙafafunsa waje ya fito, nan fadawa suka rufe shi suna masa kirari masu masa gaisuwa nayi, bundle ɗin 1k ya zaro a wata jaka dake rataye a ƙugunsa ya ɓalle wrappers ɗin tare da watsa kuɗin sama take suka shiga kokawar ɗiba, wata ya sake ballewa ya watsa saida yayi haka kusan sau huɗu sannan ya dauki hanyar shiga duk da kuwa a wajen ma akwai mutane sosai dake zama.
Yana shiga ya hango mahaifin nasa zaune kan wata one seater royal cushion daga gefen damarsa Rouslan ne da Reeslan zaune suna taya shi karɓar gaisuwa sai kuma su Ammu Fayzan wanda suke uba ɗaya da mai martaba da kuma su wazir da sauran hakimai, da kuma duk wasu masu matsayi a masarautar su ne cike a wannan falon, ƙarasawa yayi ta tsakiyar su ba tare da ya cire takalmin sa ba ballantana yayi sallama sai hannu kawai da ya ke ɗaga musu har ya Ƙarasa wuri su Sultan, gefen su Rouslan ya zauna tare da miqa musu hannu sannan ya ce , " Abbu ya qarin hakuri, a mun afuwa ban samu ƙarasowa da wuri ba whl, ashe Ammu ya wuce to ALLAH yasa anje a Sa'a"............ Sunkuyar da Kai su wazir sukayi yayin da Reeslan ya juyo ya zuba masa ido kawai, kallon Reeslan ɗin Rouslan yayi suka haɗa ido ya sunkuyar da kansa .
Wazir ne ya ɗan matsa kusa da Sultan da kallo ɗaya zaka masa kasan ransa a ɓace yake tun bayan shigowar Sahel ɗin, magana suka ɗanyi da wazir kafin ya tashi ya zo inda suke zaune ya kamo hannun Sahel ɗin da faɗin, " Muje nayi magana dakai".
Miqewa yayi yana faɗin, "To Abbu Ni daga can zan wuce ALLAH ya kara hakuri"......... Ya faɗa tare da bin wazir suka wuce ɗaya falon da ba mutane.
Gyaran murya wazir yayi da faɗin, "Sahel! Ran mai martaba ya yi masifar ɓaci da abinda kayi a matsayin ka na ɗansa, wannan shigar ba da ita ya dace a ganka ba a daidai wannan lokacin, sannan a lokacin da ake cikin alhinin mutuwa bai kamata kazo ka tada hayaniya ta hanyar watsa kuɗi ba, wannan ya saɓa dokar Masarauta domin watsa kuɗi Kamar almubazzaranci ne shi kuma almubazzari ALLAH da kansa ya faɗa a cikin Alqur'anin sa me girma innal mubazzarina kanu ikwanash shayaɗeen, in sadaka kayi niyya ka bayar hannu da hannu a mutunce sannan magan........"........... Katse wazir yayi da faɗin, "Ah Ah baba wazir Kar muyi haka dakai, ba wani dogon turanci kawai fito kace Abbu baya buqata ta a kusa da shi, dama can yafi son su Maleekh a wurin sa saisa su baya ganin laifin su"............ Yana kaiwa nan ya juya ya fita ya bar Wazir sake da baki.
Hotel ɗin da ya kasance na sauqar baki ne a cikin masarautar nan Sahel ya buqaci a wuce dashi sannan ya ɗaga waya ya kira wata number, ana ɗaga wa yace, "Hello Captain"......... Cike da girmamawa wanda ya kira da Captain ya ce, "Da girman kujerar ka yarima ƙarami"..........." Am kaga a shirya min tafiya yau zuwa Paris".
"An gama yarima Ƙarami amma saidai shirye shiryen zasu iya kai mu zuwa ƙarfe 12 am".........."Ba matsala da an gama ka kira ni".
"In ALLAH ya yarda ranka ya daɗe karka samu damuwa"........ Bai tare da ya bashi amsa ba ya kashe wayar yana ciza baki.
Suna Ƙarasawa hotel ɗin da baza ka taɓa tunanin wai a cikin masarautar yake ba saboda girman sa dan zai iya kai wa hawa ishirin ko sama, anan duk wani sarki ko shugaban ƙasa da ya kawo ziyara masarautar yake sauka, a samansa an rubuta "AURELLON GUEST IN" da wasu army green stones masu ɗaukan ido, karku manta komai na aurellon daga gold sai diamond sai kuma sauran precious stones.
Fadawan nasa na ƙoƙarin binsa domin rakiya ya dakatar dasu da faɗin, " kuje kawai kamar 11pm kwa dawo"......... Ya faɗa tare da shigewa da sauri securities ɗin suka fara zubewa suna miqa masa gaisuwa, hannu kawai yake ɗaga musu har ya Ƙarasa reception ya karɓi key ɗin ɗaya daga cikin vip rooms sannan ya wuce wurin elevator.
Su Rouslan kuwa ranar basu motsa ko ina ba sai dare bayan anyi sallar Isha tare dasu a masallacin fada suka musu sallama suka wuce. Sai da suka shiga mota Reeslan ya ce, "Rouh kaji abinda naji kuwa ɗazu?"........."A ina?". Rouslan ɗin ya tambaya ba tare da ya kalleshi ba.
Murya can ciki ya ce, "Warin wine naji a jikin Sahel".........Wani irin side look Rouslan ya bashi kafin cike da dimbin mamaki da ya gaza ɓoyuwa a muryarsa ya ce, "Warin me?"......... Shi ma ba tare da ya kalleshi ba ya ce, "Wine, kuma ba wai tabbas itace".......... Rouslan baya buqatar ya musawa Reeslan Saboda yasan duk abinda zai faɗa gsky ne , da ɗan alamun mamaki ya ce, "But taya aka samu wine a Aurellon?".......... Girgiza masa kai kawai Reeslan ɗin yayi Amma baice komai ba, shi ma bai sake ce masa komai ba sai Nazarin yadda akayi Sahel ya samu wine a cikin masarautar tasu.
A gajiye suka ƙarasa gida dan haka ko ɓangaren Ummu basu shiga ba suka shige nasu, zubewa Rouslan yayi kan gadon yana faɗin, "Wash whl nagaji yau mun zaunu ba ƙarya, Habiby massage please"......... Ya ƙarashe a shagwaɓe, harara Reeslan ɗin ya watsa masa yana rage kayan jikinsa ya ce, " kai dama ai baka da wuyar gajiyar, Dan abu kaɗan ka gaj........" Bai ƙarasa maganar dake bakin sa ba wata guguwa mai ƙarfi ta doko windows ɗin ɗakin har saida suka girgiza, zaune Rouslan ya tashi yana kallon windows ɗin kafin ya ce, "Dama akwai hadari a garin nan ne da muka shigo?".
Reeslan bai bashi amsa ba illa wurin window da ya nufa, fitulun ɗakin ne suka fara rawa hakan yasa Rouslan tashi da sauri ya Ƙarasa wurin Reeslan da ya ɗaga curtain ɗin ɗaya daga cikin windows ɗin, a tare suka kalli juna cikin firgici lokaci guda kuma Reeslan ya fara huci Kamar wani kumurcin zaki shi kuma Rouslan ya riqo damtsen hannun Reeslan ɗin yana jin wata irin juya na ɗibansa.
______________11:30pm daidai Sahel ya fito daga hotel ɗin, ya sake wanka ya sauya kayan sa, nan ya samu fadawan sa na jiran sa kamar yadda ya faɗa musu, shiga yayi sannan suka ɗauki hanyar airport ɗin dake cikin masarautar, nasan zuwa yanzu kun waye da irin girman da Aurellon sultanate take dashi.
Suna daf da shiga airport wasu mutane suka sha gabansu hakan ya sasu tsayawa ba shiri, dukkansu fuskokin su a rufe ne idanun su kawai kake gani , ƙofar motar da Sahel yake ciki suka buɗe tare da faɗin, "Fito "......... Da mamaki ya kalle su ɗan yasan basu taɓa fuskantar barazanar yan fashi ko yan ta'adda cikin masarautar tasu ba saboda tsaron da suke dashi. Fadawan ne suka fito gabaɗaya zasu rufar musu ai kuwa suka fito da bindigu tare da faɗin, "kuna motsawa sai mun harbeku, kuyi ƙasa, kai kuma ka fito"............ ɗaya daga cikinsu ne ya harzuqa ganin mutanen da basu kai su power ba suna ƙoƙarin kawo musu wargi, take murɗaɗɗun tsokokin dake kirjinsa suka fara motsawa, cikin rashin tsoro ya dunfaro su saidai kafin ya ƙaraso sun sakar masa bullet a ƙafa, take sauran suka sauka kan guiwowin su cikin firgici, shi kuwa Sahel ganin abinda ke faruwa ai bai ƙara minti guda ba ya sauko, mutum biyu suka sashi gaba zuwa wata mota sauran Kuma suna tsare da fadawan har saida wa'ancan suka shiga suka tada motar sannan suka bar wurin da gudu suka wuce motar tasu suka ɗale tare da tashinta suka bar wurin, suma fadawan basu tsaya ba suka sabi ɗan uwan nasu da aka harba suka sanyashi cikin mota suka rufa musu baya, saidai ko ƙurar motar su basu tarar ba.
TOH FA SU WAYE SUKA ƊAUKE SAHEL KUMA?
ME ROUSLAN DA REESLAN SUKA GANI HAKA?
MEYE DALILIN TSANAR DA MAAMA TA YIWA SULHAM? WAYE WANDA SUKAYI WAYA? MIYE TSAKANIN SU?
MU HAƊE A STEP 2 DOMIN SAMO DUKKA AMSOSHIN NAN.
------------------------√
Suna ƙarasawa asibiti Amjad bai jira an gama tsayawa ba ya buɗe ƙofar motar yayi cikin hospital ɗin, Bai jima ba ya dawo tare da wani Dr da nurses sai gadon tura marassa lpy. Nan aka ɗaura Ace akai sannan aka wuce dashi ciki, dukkansu rufa musu baya sukayi harda jami'an tsaron da aka bawa Amjad ɗin, a ƙofar ɗakin suka tsatsaya, Jey ya ce, "Wai me ya faru dashi ne?".......... Ash ce ta amsa masa da , "Tashi yayi kawai sai muka ga ya dafe kansa kafin kace wani abu ya faɗi" .......... Kiara na ƙoƙarin magana Dr ya fito. "Dr ya ake ciki?"......... Ash ta riga tambaya.
"I'm sorry ko da kuka zo dashi ma ya riga ya rasu"........... Amjad ƙasa ko da motsi yayi shi dai kawai ya zubawa bakin Dr ido ne, Ace ɗin da yanzu suke tare, yanzu suka gama magana sannan daga Faɗuwa ace ya rasu, gabaɗaya ya ɗauke wuta Amma a fuskar sa baza ka iya gane halin da yake ciki ba. Jey ne ya ce, "Kai Dr ka san aikin ka da kyau kuwa?"..........."Sai haƙuri Amma ya riga da ya rasu ranka ya daɗe".
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un"........... Jey ya faɗa yana cafkar gashin kansa da matukar ƙarfi .
"Dr what was the cause of his death?"........... Kiara ta faɗa a ruɗe. Girgiza Kai Dr yayi tare da faɗin, "We don't find any reason komai na jikin sa lpy ƙalau, kawai kwanan sa ne ya ƙare".
"No Dr ba yadda za'ayi mutum ya mutu ba dalili, ko dai baku da abubuwan gwaje gwaje yadda ya kamata ne?"............ Ash ta sake tambaya, abunka da ba musulma ba su a nasu sanin mutum baya mutuwa haka kawai dole sai da sanadi.
Daƙyar Amjad ya jawo magana daga ƙirjin sa dan tabbas yaji zafin mutuwar Akil amma Kuma ta Ace tafi tsaya masa a rai, "Dr ku shirya gawar, Ash kuyi duk cike ciken da ya kamata ku karɓo gawar".......... Yana faɗa ya matsa wurin Jey tare da dan bubbuga kafaɗar sa alamar ban haƙuri, ɗagowa Jey yayi idanuwan sa sunyi jajir kusan duk da basu kasance yan ƙasa ɗaya ba a wuri ɗaya aka basu horo kuma anan suka fara aiki kafin kowa ya koma aiki ƙarkashin hukumar ƙasarsa amma duk wani aiki na haɗin guiwa irin wannan tare suke yi. Ace abokin faɗansa ne dan akwai shi da son tsokana da wasanni, shi Kuma Jey baya san damuwa da surutu sai dai shi kuma Ace indai yana wuri to fa sai ya hana Jey sakat.
Girgiza masa Kai Amjad yayi tare da jan hannun sa sukayi waje jami'an tsaron suka rufa musu baya, a jikin motar su suka tsaya Jey ne ya ce, "Amjad na fara sarewa akan case ɗin nan, tun tafiya batayi nisa ba mun rasa mutum biyu, Anya kuwa kana ganin zamuyi nasara?".
"Haba Widad, meysa zaka nuna gazawa meysa zaka alaqanta mutuwar Akil da Ace da wanna case ɗin da muke "............Girgizawa Amjad Kai yayi da faɗin, "Ka tuna lokacin da aka harbi Akil kai da kanka ka shaida mana sunce wanna shi ne hatsarin dake tattare da neman sanin Shadow".
"To Widad yanzu wani ne ya harbi Ace ko Kuma munje binciken Shadow ne Ace ya mutu? Ka ajje wanan maganganun gefe, ka sani in mun jajirce mun samo shadow lada zamu samu ka tuna dubban rayukan al'umman da suka salwanta a hannun sa, kayi tunani ta wace hanyar ran su yake fita a jikin su, wace irin azaba ake gana musu?"......... Dakatawa yayi tare da jan zazzafan numfashi ya ce, "Ka kira ka sanar dasu sir Richard, nasan zasu buqaci a tura musu gawar can Kai sai ka bi su saboda su Kiara mata ne bai kamata ace su zata je ba, and moreover Ashley ma kasan dole zan buqace ta saboda baza ayi wasa da wannan damar ba"......... Gyada masa Kai Jey yayi kawai, a lokacin kuma su Ash suka fito da gawar tare da wasu nurses, bayan motar Amjad da yasa aka ciccire kujerun aka saka gawar. Har suka gama komai suna shirin tafiya Amjad ya lura da Jey dake tsaye kawai yana binsu da ido . Komawa yayi wurin sa a sanyaye ya ce, "Widad muje !".......... Binsa yayi a baya suka wuce.
Gida Amjad ɗin da suka baro suka nufa tun daga hanya Jey ya Kira ya sanar da sir Richard, take aka bada izinin kai gawar tasa Saboda su Kuma a can su sir Richard ɗin zasu Kira familyn sa su sanar dasu dan su je can ɗin su haɗu. Cikin minti goma Sha biyar aka gama musu komai na tafiya Kuma sunyi Sa'a a daren da misalin 4am akwai jirgin da zai tashi zuwa Belgium ɗin dan haka suka sake juyawa suka ɗauki hanyar airport ɗin gabaɗayan su, Nan ma saida aka gama duk wasu cike cike Dan ma dai duk inda suka nuna ID ɗinsu ba'a tsaurarawa, tuni aka wuce da gawar Ace, Jey ya kira mahaifiyar sa ya sanar mata saboda bai samu ya koma gida ba ta bishi da addu'a.
Side hug ya bawa Amjad sannan ya ɗagawa su Ash hannu ya wuce da ɗan sauri saboda har an fara sanarwa jirgi ya kusan tashi.
Jan hannun Ash dake share hawaye kiara tayi suka bar wurin, shi ma Amjad bin bayansu yayi kansa a ƙasa baza ka taɓa iya gane yanayin da yake ciki ba, Ace ya shigo ƙasar Nifaz da ƙafarsa yau an fita da gawarsa kamar yadda Akil ya shiga Denmark da ƙafarsa aka fitar da gawarsa, maganar Widad ta ɗazu ce ta dawo masa cikin kansa, saurin kawar da zancen yayi yana ƙarfafa kansa ya shiga motar da aka buɗe masa suka wuce gidan nasa. Suna shiga wayar Philip na shigo masa inda yake faɗa masa sun ɗau hanya da mutanan.
Tunda suka koma ba wanda ya rintsa a cikin su har gari ya waye, wanka kawai sukayi suka Sha tea Ash ta fita wurin Nazbeer da Philip ya bawa na'urorin ya kawo masu ta koma