BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   40 / 53

117K to 120K   out of 156.9K words

sai Ku ta Mata ban ruwa daga ta girma Ku fisge ta tun daga jijiyar".

"Hmmm!, a gsky bana daga cikin su Hushaima, dan ni duk kuɗaɗe na na halal ne ".

" Ba damuwa, zamuyi waya zuwa dare, zan koma bakin aiki na".......... Idon sa a kanta ya ce, "Aiki fa ba naki bane kwalisa, kamata yayi ace kina gida kina hutawa saidai kawai ki dinga jin alert, ke ai ba kalar wahala bace, ni duk abinda kike so zan baki kuma zan miki daga kan naira miliyan ɗai ɗai ɗai har ɗari ba matsala ta bace in dai zan samu haɗin kai daga gare ki".

Girgiza masa Kai tayi cikin halin ko in kula da jin maqudan kuɗaɗen da ya ambata ta ce, "Ba haka nake ba, aiki na shi ne dahir ɗi na, Kai naka na ɗan lokaci ne, daga Ka samu abinda kake so zaka ɗage a lokacin wa kake so na Nemo ya bani, ni bana matsawa komai zanyi amfani da nawa idan Ƙari ya samu in Ƙara, tunda ko teku bata ƙin ƙari amma dogaro da abun wani ba na Hushaima bane".......... Tana Kai nan ta fara ƙoƙarin fita, kuɗi ya zaro masu yawa ya sauke Mata Kan cinyarta, ɗauka kawai tayi ta zura a jaka ta fice ba tare data sake ce dashi uffan ba.


*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
            

_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._

⭐MALLAKIN⭐
               *SULTYWRITES*
                         A-K-A
               [YOUNG WRITER]✍️


___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._

  

@wattpadd sultywrites22


           STEP 1


PAGE _______54 & 55


Da Harara Jumayma ta bita a lokacin da ta shigo, wata yar budurwa ce ta fito daga manicure section baza ta haura 16 years ba, waya ce maqale a kunnenta sai sauri take, kallo ɗaya zaka mata ka san daga gidan Naira ta fito tun daga kan yanayin shigar ta zuwa takun da take, ba tare data lura da Hushaima dake tahowa ba suka mangaji juna, kafin Hushaiman ta gama tantance yarinyar data mangajeta taji saukar wani mari a kumatun ta kamar daga sama, a fusace yarinyar ta fara masifa, " Ke wace irin jaka ce dabba da bata ganin gabanta, kin shigo kina wani kalle kalle zaki goga min wannan ƙazamin jikin naki me warin talauci, are you insane nace are you insane ? Stop looking at me with those bastard eyes of yours, wawiya kawai".

Wani irin tafasa Hushaima take kamar zata kama da wuta tunda take a duniya ba wanda ya taɓa yi mata cin mutuncin da wannan yarinyar da ko Sahnish ya girme ta tayi ba. Ai bata san lokacin da hannunta yakai kan kwalbar wani hair oil dake Kan kanta ɗin reception ɗin ba sai ji kake tartsatsa ta rotsawa yarinyar nan a tsakiyar kai, wani irin ihu yarinyar ta kurma tare da zubewa ƙasa tana juyi hannayenta riqe da kanta, take jini ya fara malala dan kwalbar saida ta fashe a irin dukan da Hushaima ta Mata da ita, amma duk da haka bata haƙura ba sunkuyawa tayi kan yarinyar tare da faɗin, "Idan wannan shi ne tarbiyyar da aka baki, kuma kin saba yiwa mutane suna kyale ki saboda kina yar masu kuɗi, to ni baza ki min na kyale ba wannan iya marin fuska ne na rama amma ki kwana da sani duk maganganun da kika faɗa whl sai kinyi danasanin yin su, sai kin durqusa gaba na kina roqo n........" Kafaɗar ta da aka riqo ne ya katse ta, ba tare data san waye bane tana ɗagowa ta sauke mata mari. Riqe baki duk ma'aikatan da ihun yarinyar ya fito dasu sukayi ciki harda Hajiya data ɗaura hannunta aka dan tasan Hushaima ta jiqa mata aiki, ita kaɗai tasan wacece Hajiya sulaimiyya da ƴarta Huda amma gashi Hushaima ta fasawa yar kai kuma ta mari uwar.

Ai hajiya sulaimiyya batabi ta kan marin ba tsabar gigicewa da tayi, kan ƴar ta ta nufa tana kiran sunan ta ganin kamar ta suma ga jini na zuba kamar an yanka ƙaramar dabba.

Juyawa Hushaima tayi tana ƙoƙarin fita Hajiya sulaimiyya ta ce, "Karku barta ta fita, Ku taimaka ku kama min yarinya ta mu Kaita asibiti karta mutu, na shiga uku na"......... Ta faɗa cikin tsantsar tashin hankali. Su Jumayma ne suka taimaka aka kai Huda Mota sannan suka dawo ciki suka haɗa kofa suka kulle.

Ita kuwa Hushaima tunda taji furucin hajiya Sulaimiyya dama bata wahalar da kanta ba ta koma ta zauna tana huci wai yau itace wannan banzar figaggiyar yarinyar zata mara, to ai ko a namijin ma sai ya jira whl, Amjad ne kawai mutumin da ya ƙetara iyakar ta bata ɗau mataki a lokacin ba, amma zuciyarta ta hanata sukuni ta sanya take ta kai kawo ta ɓata lokacin ta da energy ɗin ta akan sa dan kawai ta samu hanyar ɗaukan fansa. Ƙwafa taja kawai, tana kallo suka ciccibeta sukayi waje, suka dawo suka tsare ƙofa, cikin tashin hankali Hajiya ta dawo ciki bayan su Hajiya sulaimaniya sun tafi, a rikice yake faɗin, "Hushaima ashe haka kake, da tana ɗaukan ka mutumiyar kirki me hankali, gaskiyan hausawa da suka ce tsintacciyar mage bata mage, amma nasan da kisan waye ne wannan matar da kika mara kika kuma fasawa ƴar ta kai da baka aikata ba, dan zata iya rufe wurin nan a cikin hour guda idan taga dama kuma whl ka shirya dan ta kira hukuma ni kuma ba ruwana". 

Wato yadda kukasan da dutse take dan idan bangon reception ɗin nan ya amsa to Hushaima ma tayi magana, ko ma ɗaga kai batayi ba ta kalle ta tunda ta zubawa wani wuri ido ko kiftawa batayi sai kaɗa ƙafa take kamar goɗiya. Haka Hajiya ta gama bambaminta taja gefe ta tsaya dan tasan idan har ta sake Hushaima ta bar wurin nan to kashin ta ya bushe wurin hajiya Sulaimiyya, dan ita zata rufe a matsayin Hushaiman har sai ta fito da ita alhalin ita yanzu ko lahira za'a Kaita batasan daga ina Hushaiman take ba.

Suna a tsaitsayen kamar sojojin haya har polisawan suka ƙaraso, ba musu Hushaima ta tashi ta bi su suka fita, saidai ganin inda suke neman sata ya sa taja baya da faɗin, "Whl bazan hau bayan mota ba"......... Katsa Mata tsawa ɗaya daga cikin su yayi da faɗin, "Kina me laifi har kina da zabin inda zaki shiga, common get in jare".

"Whl ba zan shiga nan ba kuma ai laifi bani kaɗai bace me laifi ita ta fara nema na da bala'i"........ Ɗan sandan ne ya kalli Wadda ta kasance mace a cikin su kana ya ce, "Monica get her in"........... Da sauri Wadda aka Kira da Monica ta riqo keyar Hushaima da nufin ta turata ciki aikuwa ta make hannunta da faɗin, "karki Ƙara taɓani karkiga kina yar doka whl sai na iya tsinka miki mari".

"Ohh really so are you threatening me ? Lalle baki san hukuma ba, ni zaki mara?"..........Tsaki Hushaima ta ja tare da tura mata keya ta ce, "ko titin ƙarshen duniya zamu muje ni dai kawai ba zan shiga baya ba Yauwa"........ Kan bindiga ɗaya dan sanda ya kafa mata da faɗin, "Zaki shiga ko sai na tarwatsa ƙwaƙwalwar ki anan"......... Kallon sama da ƙasa tai masa kafin ta ce, "Dan ALLAH karka fasa, dani da ku marabar mu uniform ne kawai dan yadda kuka saida ranku kunawa ƙasa aiki, nima haka na saida raina nakewa rayuwata aiki dan haka karka fasa harbawa, ga me fili ga me doki, ka harba mu gani in hukunci bai hau kanka ba kai ma".

Duk yadda aka Kaɗa aka raya Hushaima ta kafa ta tsare baza ta shiga baya ba, anyi ta barazanar anyi ta ƙarfin amma daga inda ta tsaya bata motsa ba, haka dole suka haƙura ta shiga cikin motar sannan suka wuce da ita.



---------------------√



           SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥



Masarauta ce ta jajirtattun Mata domin Kai tsaye zamu iyacewa feminist kingdom ce, Saboda Matan su suna da power da freedom fiye da mazan, domin su suna ɗaukan mazan su ne matsayin bayin su, kwata kwata maza basu da yan'ci a wannan masarautar suna rayuwa ne Matsayin bayi kuma ƙasƙantattu. Su ɗin sun kasance masu bautar rana ne, kuma a tsarin mulkin sarautar su ƙani ko ƙanwar sarauniya bazai iya gadar mulki ba dole sai dai ɗan wanna me mulkin, gashi duk masu mulkin sunfi haifar mata hakan yasa su suke ta hawa da sauka akan wanna kujera.

Sun ƙware sosai a fannin Archery, art da agriculture, sannan sun iya sword fighting sosai dan training me ƙarfi akewa kowani yaro ko yarinyar da ya taso a masarautar tun suna ƙanana sai sa duk ƙanƙantar yaro zakaga yana wasa da sword kamar me. Suna da arziki sosai amma fa basu ko taɓo ƙafar Aurellon ba amma kuma saboda ƙarfin zuciya irin tasu a haka suke ja da Aurellon ɗin. A bangaren tsarin gini kuwa qaton castle ne matuƙar girma da kyau, a cikinsa akwai ƙofofi da bangarori da dama dan har palace ɗin a cikinsa yake, haka ta bayan castle ɗin ma wasu parts parts ne da aka ware na ma'aikatan masarautar maza.

Abinda ya jawo rikici tsakanin su da Aurellon ba komai bane face yankin su da Aurellon ta kafa masarautar ta akai domin ainahin mahaifin Queen Alitash 1 wato Nujum Samrah shi ya zauna a wannan yanki da iyalansa mafarauci ne sosai, saidai dare ɗaya aka tashi aka samu gawarsu shi da matar sa, ƙanwarsa da kuma mahaifinsa, sai ƴar'su guda daya da ba'a ganta ba, bayan wucewar wanna al'amari ne aka kafa Aurellon, sai kuma aka samu labarin bayyanar Yar tasu mai suna Alitash saidai ko da ta dawo tayi ƙoƙarin amsar yankin mahaifin nata amma hakan ya gagara, wannan dalili yasa ta tafi ta kafa ta ta masarautar itama tun ba'a farga ba har sunan masarautar ta ta ya fara yaɗuwa a wannan lokacin ne ta fara qalubalantar Aurellon, wannan shine asalin rikicin su da har yanzu yaqi ƙarewa duk wani jinin Queen Alitash da ya hau ɗorawa yake daga inda aka tsaya.  WANNAN KENAN!.

Wani sassaqaqqen dutse ne da aka sassaqa a suffar mutane zaune akan wata sassaqaqqiyar kujera dake ƙofar wani kogon dutse riqe da wata sanda da suke kira da sandar doka sai wani qaton zobe da suke kira da zoben adalci. Babban fili ne a ta gabansa wanda ke cike da duk mutanan dake rayuwa a masarautar ciki harda Queen Hirut, dukkanin su sanye suke da fararen kaya qal idanunsu duk a rufe, kowannensu riqe da wani kasko da suke jefa wasu itatuwa a ciki hayaqi na tashi. Wata wadda ga dukkan alamu itace malamar tasu tana tsaye gaban wannan sassaqaqqen gunkin riqe da nata kaskon idanunta a rufe, gefenta kuma wani mutum ne durƙushe gaban wannan dutse, baqin ƙirin dashi gashi dan siriri kamar aljani, matar ce ta fara magana. " Ya kurangina, ya hasken duniya, ya babban Alkali ka bayyana mana adalci a yau, kamar yadda kake bayyana kowane lungu da sako na ƙasa (Astagfirullah)".......... tana yi tana baza hayaqin da hannunta, haka ta cigaba da yan surkullen su cikin harshen amharians, tsawon lokaci suna a haka har sai da rana ta daidaita a sararin samaniya sannan duk suka buɗe idanuwansu. Tashi wannan mutumin yayi ya ɗauki wani qoqo dake cike da wani ruwa a gefensa itama matar ajje nata kaskon tayi ta ɗauki qoqon dake gefenta sannan suka matsa wurin su Queen shi da ita,  ɗaya bayan ɗaya suka fara binsu suna yayyafa musu wannan ruwan har suka gama sannan duk suka durƙusawa kurangina, daga nan kuma suka tafi raka Queen Hirut faɗarta sannan kowa ya tafi yin ayyukan gabansa. Wannan shi ne bautar da sukeyi a kowacce safiya idan rana zata fito haka in zata faɗi zasu fito ne su tsaitsaya a gaban kurangina suna wasu surkullen su har sai rana ta faɗi.

_________Qaton yanki ne dake ƙarshen iyakar masarautar wanda aka ware domin yin noma kawai. Ɗaya daga cikin mutanan dake yin kunya ne ya taɓo ɗan uwansa yana nuna masa dawakan da suka tsaya daga bakin iyakar masarautar tasu. A daidai lokacin ɗaya daga cikin mutanan dake kan dokin ya ɗaga wani abun busa me matuƙar kyau da kyalli ya kai bakinsa tare da jan wata doguwar busa tsawon seconds 120 ba tare da yaja numfashi ba, kusan duk wanda ke cikin masarautar ba wanda bai saki abinda yakeyi ba domin hakan alama ce dake nuna anyi baqi daga Aurellon ko kuma sun kawo saqo. Sakin abinda sukeyi sukayi tare da nufar wurin mutanan dake kan dawakan, kafin ma suyi magana suka miqa musu takardar da suka zo da ita tare da juya akalar dawakan su suka tashi Ƙura sannan suka rufa a guje suka bar wurin.

Kallon Ɗan uwan nasa yayi da fadin, "Dawit wanna fa inaga saqon Queen Hirut ne".......... "Kuma kaga ya kamata muyi gaggawar isar dashi gareta dan bamu san me ya ƙunsa ba tunda daga Aurellon ne"........ Ya ƙarashe yana kallon tambarin eagle dake jikin takardar domin tambarin eagle shi ne alamar Aurellon a duk faɗin duniya . "Muje muyi sauri in mun dawo ma ƙarasa"....... Dawit ya faɗa yana cilla fartanyar sa a inda yake haqa kunyar sannan suka tafi da gudu dan isar wa da sarauniya saqon ta.

Ko da suka ƙarasa wani dogari ne ya tare su tun kafin suyi magana ya ce, "Ina saqon?"........ Miqa masa sukayi ya juya ya shige cikin fadar ba tare da yace dasu komai ba. Wow zo kuga qawa ta ainahin gargajiya da zamani domin fadar Queen Hirut ba wai an ƙawata ta bane da iyakacin abubuwan zamani ah ah harda na gargajiya, kama daga kan zane zanen dake bangon zuwa kan furnitures da sauransu.  Kaso 60 na mutanan fadar mata ne kaso 40 ne kawai suka kasance maza, ta kowani Angle kuwa dogare ne riqe da sword sai kyalli yake. Daga mazan har matan Babu Wanda zaka iya cewa ga kyallin hakoransa a waje gwara su mazan gasu nan ga kamar su ne, suna zaune a ƙasa kamar wasu almajira alamar ba jin dadin yanayin suke ba kawai dai a rashin zabi ne suke nan. Ga kuma wasu murtika murtikan Siberian tigers dake ta shawagin su cikin fadar kamar a daji.

A tsakiyar fadar wanna dogarin ya zube tare da fara zubawa Queen dake hakimce kan wata iriyar ƙayatacciya kujera dake a saman stage ɗin fadar, both sides ɗin ta ma Siberian tigers ɗin ne kwance sai lashe baki suke suna bin kowa da kallo. Tana sanye da cersei gold dress saidai ita tata an ƙerata ne da fatar dawisu, kanta ba komai sai silky golden yellow hair ɗin ta da ya zubo kan kafaɗunta ta ɗaura wata crown hat akai, ba fara bace can haka zalika ba baƙa bace za'a iya kiran skin dinta da golden yellow, ga dogon hanci kamar su suka zana kayansu haka dan bakin nan tsit kamar cokali ba zai shiga ba ga idanuwa tubarkalla, dattijuwa ce dan zata iya kai shekaru 52 - 53 haka, amma kyawun jiki da kuma daular mulki da arziki ya sanya sai kayi tunanin baza ta fi 40 ba.

Bayan ya gama mata kirari ya ce, "Saqo ne daga Aurellon"......... Ɗaya daga cikin mazan dake zaune ne, wani dattijo ya yunqura ya karɓa takardar sannan yace da dogarin yana iya tafiya, Saida yayi godia sannan ya tashi ya fita.

Wata matashiyar budurwa ce hakimce a wata ƙayatacciyar kujera da zan iya cewa daga ta Queen Hirut sai tata a kyawu, baza ta haura shekaru 28 ba a duniya, kalar skin ɗinta irin na Queen, tana sanye da Medieval Dress me Corset Belt da Wide Sleeves red and gold. "Me kake jira ne Abal (baba) karanta mana".........Ta faɗi hakan a tsaurare ba wani alamun tausasawa ga mahaifin nata .

Gyara zama yayi sannan ya warware Scrolls paper ɗin dake nannade. Da turanci suka rubuta letter ɗin saboda sun san su basajin yaren su na Arabic. " From his majesty sultan Abdulbasit Abdul Aziz. AURELLON SULTANATE. To honourable council of sword of fire kingdom, the Queen Hirut."

"We have received irrefutable reports that your daughter Anoosha and her agent conspired to murder crown prince Reeslan Maleekh, our heir and that the prince personal guard was brutally slaughtered in the act. Such treachery strikes at the very heart of our dynasty and cannot be tolerated. So you are here by warned to surrender all conspirators involved in the plot within ten days and offer a formal apology and suitable reparation for the loss of the prince's protectors failure to comply will compel us to take all necessary measures to avenge our blood and protect our succession and the peace between our realms will be irrevocably broken. We pray this matter can be resolved without further bloodshed and await your swift response."

" SULTAN ABDULBASIT ABDULAZIZ, the king of Aurellon sultanate"......... Sai stamp ɗin eagle da suka buga a kan sunan.

A fusace yarinyar ta miqe cikin yaren amharians ta ce, "What!!!!! Inati kinaji fa, kamar ma barazana

40 / 53