Author : Young Writer Category : Tknovels
dan al'umma inaga a cigaba da jan hankalin su wurin faɗin cewa ana cigaba da bincike kamar yadda sauran ƙasashen ma ke faɗar nasu, har zuwa lokacin da zan gama aiki na".
"In kuwa haka ne, dole a ƙara ma matakan tsaro saboda hukumar JISD ma ta buqaci hakan ɗan a duk cikin team ɗin naku sunan ka ke yawo".
"I'm sorry sir Amma bana bukatar abinda zai janyo hankalin mutane Kai na".
Director general na NIA ne ya ce, "Zasu kasance tare da Kai a matsayin ana tsaron ka ne dan Kar ka gudu, are you akay with that?".
"Thank you sir"........... Shi ne abinda ya faɗa wanda hakan ya nuna musu ya amince.
To wai yanzu kun gane IDs ɗin miye wa'annan securities ɗin jirgin suka samu a jikin Amjad da har ta dinga bashi hakuri, to special ID ɗin sa ne da hukumar JISD ta basu a lokacin da suka fara mission kan shadow, tare da ainahin ID ɗinsa na jami'in tsaron farin kaya. Sannan in baku manta ba a lokacin da su Hajj zawaad ke tattaunawa ai sun ambaci ƙasar Belgium ma ta buqaci a bata Amjad ta yanke masa hukunci idan har ƙasar Nifaz sun kasa saboda itama ta samu sunansa a cikin jerin masu laifi na ƙasarta to duk a cikin tsarin aikin su ne, dan acan babbar headquarter ɗin tasu take. Sannan abu na ƙarshe lokacin da aka sanar da wanzuwar criminals a cikin jirgin da zai tashi daga Belgium zuwa ƙasar Nifaz da gaske ne akwai criminals ɗin a ciki kuma duk an kasa ganosu sai widad, shi ya ganosu ya kuma kamasu ya miqawa securities na airport ɗin, a lokacin kuma kiara ta ƙaraso wurin daga nan ya mika mata sauran aikin ya koma cikin jirgin, ita kuma ta sanar da jami'an dake da alhaki a wannan bangaren. WANNAN KENAN.
Minister of communication ya sake amsawa da, "About the matter of rape, are you also accountable for the circular?".......... Shuru yayi dan bazai iya bayyana sirrin gidan su ba sai kawai ya ce, "No I'm not"............. Kallon director general of NIA minister of communication yayi tare da faɗin, " DG i think ya kamata ayi bincike akan wannan abun, cox people are taking it serious Kar saboda abinda ya faru yasa maqiya su samu damar yada tasu manufar anyhow, dama abun na zuciyata dan bamu samu zama bane saisa ma ban taso da zancen ba".
Ɗan jijjiga kansa yayi kafin ya ce, " Zan sanya ayi bincike akan hakan"........... shi dai Amjad baice komai ba dan yasan bashi da ikon hanasu amma kuma ba hakan yaso ba .
Minister of justice ya ce, "Gobe ne zasu tsaya a kotun ai dan ɗazu nayi waya da judge C. John".
"To ka shaida masa ya tabbatar ya tsaya kan case ɗin, ya kuma yi abinda ya dace". Daga haka suka sake tattaunawa kafin su fito gabaɗayan su, aka bashi sojoji mutum takwas matsayin Wanda zasu kasance tare dashi har zuwa lokacin da komai zai kammala.
JISD wato joint intelligence and security division tawagar bincike ce ta haɗin guiwa, tawaga ce da hukumomin tsaro na ƙasa da ƙasa ke amfani da ita musamman idan manyan laifuka suka shafi ƙasashe da dama a lokaci guda, kamar dai laifin safarar mutane na ƙasa ƙasa da ake tuhumar shi wannan Shadow da ba'asan ko waye shi ba. Saida suka tantance jami'ai masu ƙwaƙwalwa matuka tare da ƙwazo kan aikin su da jajircewa, in dai bincike ne daga nesa in ka taho kawai tsirara suke kallon ka saboda tsabar iya aiki irin nasu.
Amjad ba wanda yasan yana daga cikin su a duk family ɗinsa sai mutum ɗaya wanda bazan faɗa muku shi a yanzu ba sai nan gaba, zakuji kuma ku ga komai da kanku. Philip, Danny, jack da Nazbeer dukkansu jami'an sirri ne dake ƙarƙashin Amjad ɗin. Philip kam ma Amjad shi ne sanadiyyar sa na zama jami'in sirri.
Duk ƙarshen shekara Hukumar tasu na haɗa ayyukan dake gabansu sannan su rarrabawa jami'an su, kasancewar su jami'an JISD ba inda aikin su baya kai su in dai abinda ya shafi arewacin Atlantic slice ne. Ba aikin da yake ɗaukan su sama da wata biyu amma gabatar da aiki akan shadow ya ruguje wanna Fariya tasu domin da yawa daga jami'an su sun buga sun ƙaɗa amma babu wani labari kan shadow bare Kuma su yi nasara, sai dai a taron da sukayi na wannan ƙarshen shekara, Amjad ya zabi aiki akan shadow, a take Kuma Widad ma ya amsa cike da ƙarsashi, nan Ashley ma tace zata shiga cikinsu, take Kiara ma ta daga hannu, haka Ace da Kuma Akil. Nasan zakuyi mamaki idan kukaji waye Akil, to ba kowa bane face mutumin dasu BB LALO suka kashe gaban Amjad, sun turashi cikin su BB LALO da niyyar ya samo musu wani bayanai saidai fa duk tunanin su ya kunce dan duk wanda yake tare da SHADOW to fa takunsa daban yake. Ganin ba wani motsi ta bangaren Akil yasa Amjad shirya wannan plan nasa, sai gashi kuma tun farko farkon tafiya Akil ya rasa rayuwarsa akan hanyar binciken SHADOW. Hmmmm a tunanin ku su Amjad zasu iya binciko shadow kuwa? Kuna ganin gabaɗayan su zasuyi nasara a tare? Ko kuma dai za'a sake rasa wasu rayukan? To muje zuwa dai.
Ba karamin dadi hukumar tasu taji ba dan haka ta sake ƙarfafa musu guiwa tare da basu tabbacin duk wani taimakon da suke buqata a shirye take ta basu, sannan ta naɗa Amjad matsayin team commander na wannan tawagar. Widad da Amjad kwata kwata basa shiri ada akwai zazzafar gaba a tsakanin su wadda ta juye ta koma gasa a fagen aiki, Kwata kwata widad baya son Amjad ya fi shi kwazo da ƙoƙari, shi kuwa Amjad a lokacin duk abinda yasa a gaba sai yayi nasara gashi da kwarjini da farin jini a cikin jama'a, kaɗan kaɗan widad ya fara ɓata masa aiki tun baya fahimta har ya gano cewa Widad ke ɓata masa aiki, a lokacin ne zazzafar gasar ta fara a tsakanin su, in aka basu aiki saidai kowannen su ya rasa su barwa na ƙasa dasu, sosai Widad ya sake dagewa amma duk da haka fa Amjad na gabansa ya kuma canza sabon salo da Widad ya rasa ta yaya zai ɓullo masa, tuni Amjad ɗin ya sake shan gabansa amma duk da hakan bai yarda ya gaza ba sai ma salo da ya canza shi ma, Akwai wata jarrabawar qarin girma da suka shiga, sosai Widad ya shiga tashin hankali a lokacin da yaga questions ɗin dan har sauran sun gama sun fara fita, kawai yaga an sauke masa paper tare da zare tasa ko da ya ɗago bai ga kowa ba amma yana dubawa yaga an gama tsarge masa komai, cikin farin ciki ya je ya miqa tasa ya koma inda suke zama bayan sun gama har sai result ɗin ya fito, sai wani buɗawa yake, shi dai Amjad bai ɗaga ido ya kalle kowa daga cikinsu ba, har aka zo sanar musu da result, Amjad da widad kunnen mage sukayi domin score nasu ɗaya amma a haka Widad yake faɗin rage masa akayi, a cikin wanna set nasu su hamsin ne amma su goma sha biyar ne suka wuce.
Daga nan aka musu qarin girma suka cigaba da aiki, saidai kuma a yanzu Widad yana ƙoƙari sosai har ya zaman yanzu aikin sa shi ke zuwa na farko kafin na Amjad, shi kansa mamaki abun yake bashi har ya dasa ayar tambaya akan hakan, sai kawai ya shiga bincike, akwai wani aiki da aka basu na bincike akan expired magungunan da ake shigowa dasu amma sai a sauya musu kwali a dinga sayarwa mutane, ko da suka haɗa report suka kai sai aka yaɓawa Amjad matuƙa. Da mamaki Amjad ɗin ya ɗago dan yasan abinda yayi sai idonsa ya sauka cikin na Widad dake masa murmushi, baice komai ba ya ɗauke Kai . Sai da suka fito widad ya sameshi tare da masa godia dan ya gano cewa lalle Amjad ba irin mutanan da yake tunani bane, duk zazzafar gasar da suka dinga tafkawa ashe wai saboda ya sanya Widad ɗin ya jajirce ne, kuma shi ya sanyawa Widad answer na questions ɗin da aka basu lokacin jarabawar qarin girma, shi yake qin yin aiki ya barwa Widad, ba ƙaramin nadamar abubuwan da ya dinga wa Amjad ɗin yayi ba a lokacin daya gano wanna abubuwan. Dan ya tabbatar ko me ya zama da taimakon Amjad . Wannan shi ne silar ɗinkewar su, suka zama kamar wasu yan uwa, su kansu hukumar tasu ba karamin daɗi sukaji ba saboda ganin haɗin kan masu kwazo biyu, kamar yadda Amjad ya tabbatar sunan widad ya shiga cikin jerin masu ƙwazo, haka yasa shima widad ya saukar da Kai ya ke koyon wasu abubuwan bilhakki da gaskiya a wurin Amjad ɗin, dama shi Amjad bashi da matsala, sosai suke matuƙar ƙaunan Junan su dukda basa bayyanawa, dan Widad ba dai miskilanci ba ga jin kai da yanga kamar wata mace, amma duk da haka Amjad ya iya zama da kayansa, suyi faɗa su shirya, duk da faɗan baya wuce kan iya shegen Widad din da in ya motsa yake ƙular da Amjad ɗin. WANNA KENAN.
Game da Syrup da Amjad ya sha lokacin da zai je wurin su BB LALO wanda wasu suke tambayar shin yana shaye shaye ne ? Ko ɗaya Amjad jami'i ne da ya san illar da shaye shaye ke yi a ƙwaƙwalwa kuma yake yaqar ta'amali da hakan, abinda ya sha ba komai bane face biotin liquid, shi ɗin maganin dake causing inaccurate interpretation a blood test result Wanda shi ne abinda su BB LALO sukayi wato su basa tantance mutum ta fuska ko murya saboda sunsan akwai ta bogi dan haka suke ɗaukan sample na jinin mutum, shi kuma Amjad shi ne yayi amfani da biotin dan kauda Bara.
Cikin tsananin tashin hankali Juraysh ya miqe bayan ya gama waya da Amjad ɗin saboda shi bai taɓa tunanin abin zaiyi worst haka ba, amma kuma abinda zuciyar sa ta ƙasa aminta dashi shi ne Amjad criminal ne, duk da in har wannan abu ya tabbata na cewa hukuma na nemansa to fa dolensa ya yarda amma how comes, dan makullin mota ya zara ya fito cikin sauri, mahaifiyar su da suke kira da Aunty ya tarar tana yiwa ƙannensa magana kan suje su kwanta dare yayi, ganin fitowar sa a birkice kamar bai gansu ba yasa ta kiran sunan sa , "Kai!". Ta faɗa Kasancewar Juraysh ɗan fari yasa bata iya kiran sunan sa kai tsaye saidai tace kai ko kuma yaro.
Dakatawa yayi tare da juyowa ganinsu ya sashi faɗin, "Ahh Aunty baku kwanta ba?".........."ina zaka ka fito kana ta zabga uban sauri haka?"......... ɗan shafa goshinsa yayi tare da faɗin, "zanje wurin Anah ne".
"Anah? Lpy dai ?"........... Ta tambaya tana ƙureshi da ido, ɗauke kansa yayi tare da faɗin, "Amjad ne ya barmin saƙo a gidan shi ne nakeso in je in karɓa".
"Kuma shi saqon ba'a iya bari a karɓeshi da safe , dare fa yayi yanzu, inaji ma 11 ta gota, kuma kasan yadda gari yake"..........."karki damu Aunty yanzun zan karɓo na dawo".
"Shikenan, a dawo lpy, Karka daɗe".
_______________Tsaye suke dukkansu su ukun a parking lot suna tattaunawa kan Batun Amjad da suke da tabbacin zuwa yanzu an yi gaba dashi dan sun kira ɗaya daga cikin yaran Amjad ɗin ya shaida musu sunzo sun tafi dashi, tunda dama Awais din ne ya faɗa musu inda zasu sameshi. Awais ne ya ce , "Yanzu duk ba wanna ba tunda har anyi gaba dashi ina ga kawai a dawo da yarinyar nan da iyayen ta suce su kawai sun yafe"............ Julaybin da ya tafi wani tunani ya ce, "Kai Baka da hankali Awais wani lokacin sai Ka dinga abu kamar Ka manta hukuma ba wurin wasan yaro bane, ai kawai a boyesu in komai ya lafa a Kara musu wuta su bar kasar domin ni banason wani jeka ka dawo"........... Kafin Awais ya bashi amsa motar juraysh ta shigo ciki, dariya Nuhail yayi da faɗin, " kaga Hamana ba zama tunda an naɗe firauna".......... Dariya shi ma awais ya kwashe da ita suka tafa, shi dai Julaybin bai ce komai ba sai bin motar juraysh ɗin da yayi da kallo .
Juraysh kuwa hana fitowa ya wuce ciki ba tare da ya nuna ya gansu ba a zuciyar sa faɗi yake dole yayi wani abu dan shi whl bai yadda da duk wannan Abubuwan da ake faɗa ba, especially yanzu da ya shigo yadda yaga farin ciki fuskar su Nuhail ya tabbatar masa akwai wani Abu.
TO GA DAI SU AWAIS GA KUMA SU HAJJ ZAWAAD KOWA NA TUNANIN AIKIN SU NE YAYI NASARA BAYAN KUMA DUKKANSU ZAN IYA CEWA TAFIYA SUKE AKAN GADAR DA SHI UBAN GAYYAR NE YA SHIMFIDA DA KANSA. TAYA SUKE TAFIYA AKAN GADAR SA BA TARE DA SUN SANI BA ? KO YA WASAN ZAI KASANCE ? WAYE DAGA CIKIN YARAN AMJAD YAKE CIN DUNDUNIYAR SA? MUJE ZUWA DOMIN SAMO AMSOSHIN NAN TARE DAKU.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______39
Misalin ƙarfe 2 na dare fitsari ya tashe ta, leqawa bayin tayi taga ba ruwa hakan ya sata ɗaukan buta ta dauki wayarta ta kunna Flash light ta fita, tsakar gidan duhu ƙirin dan ba wuta, mutum ta hango tsaye ya ɗage Kansa sama, ƙurawa dan bakinsa ido tayi hakan ya sata fahimtar Magana yake, yana sanye da sweet pant black sai white vest, dukkan hannuwan sa riqe da waist ɗinsa, haske shi tayi da fitilar wayarta ta amma bai juyo ba, ba tare da wani ɗar ba ta nufeshi tana zuwa ta sake haske fuskar sa, ajiyar zuciya ta sauke ganin Jey ne. "Ashe ma Kai ne, har nace ko wani barawon ne ya shigo mana"............ Ido kawai ya zuba mata ba tare da yace komai ba sai dan bakinsa dake tauna chew gum kaɗan kaɗan cike da salo, juyawa tayi da nufin zuwa ta ɗaibo ruwan taji an figo ta, wani irin juyi yayi da ita tare da shigewa bayan wata ballalliyar kofar da aka jingine jikin bango, kallon sa take cikin ido dan gabaɗayanta rungume take a jikinsa, da hannu ɗaya yake riqe da ita dayan kuma ya saka ya rufe bakinta da hancinta, idonsa cikin nata yake mata alama da kar tayi wani yunquri.
Kawu Adamu ne ya fito da ƙatuwar sanda yana faɗin, "kaii su waye Anan? Yanzu kuma an fara biyo dare za'a mana ɗan hali saboda anji na saya machine, to whl ba ɓarowa ba ko aljani bai isa in ajje ya ɗauka ba in kuma da Wanda ya isa ya fito muyi gaba da gaba"............. Ya faɗa Yana daga sandar sa, Umma delu ce ta biyo bayansa tana faɗin, " Haba Malam wai miye haka? ta ya zaka fito tsakar dare Ka tara mana mutane, waye zai wani bi dare ya hana kansa bacci akan wata roba robar Ka".............. Nan fa ya juyo kanta, "To to yar hassada, ke Delu ki fita ido na, to ita dai roba robar da kike rainawa ita da yawa suke nema basu samu ba dan haka ki barni na yi takiya ".
"Wani karamin ɗan iska ko yar iskar ce ta hana mu bacci tsakar dare, ɗan baccin da bawa zaiyi ma ya kwantar da haƙarƙarin sa sai azo a dinga firgita shi, ni whl bana son irin haka".......... Faɗar Shamsy yana fitowa daga ɗakinsa kansa sanye da under skirt. Kallon banza kawu adamu ya masa tare da faɗin, "Harda su kaza a cin danƙo, Kai Ka Bari sai ƙashin Ka yayi kwari Ka zama namiji sai kazo kayi magana "..........."Ahayye cas, yo ni me zai haɗani da kwarin ƙashi ina mace me rauni, amma fa in ka kawo min ba gishiri whl sai in iya kwaɓewa mu daku a fidda raini, kai yanzu na tsaya ka tsaya ai sai a zaɓeni ba'a zaɓe ka ba, ahhh yoo saboda ALLAH fa"............ Ya ƙarashe yana wani lankwashe Kai, takaici ne ya kawo kawu Adamu wuya, tsaki ya buga tare da jan sandar sa ya koma ɗaki umma Delu ta rufa masa baya.
"Wuuu yaji tsoro".......... Shamsy ya faɗa yana ɗaura hannunsa a baki kamar me guɗa, sannan ya juya ya koma ɗakinsa.
Sai a lokacin suka saki numfashi a tare dan zakuyi mamaki in nace muku tsawon lokacin nan Jey da Hushaima basu shaqi ko fitar da numfashi ba, Wanda hakan ya sake sawa Jey shakkun Hushaima saboda ba kowa bane zai iya ɗauke numfashi na tsawon wanna mintunan ba Ka ganshi daram. Fitowa sukayi yana riqe da tsintsiyar hannun ta gam, ganin yana ƙoƙarin nufar ɗakinsa da ita yasa ta faɗin, "Malam ina zamu ne ni Ka sakeni".............." Shut up". Ya faɗa a ɗan zafafe yana ɗaura yatsansa akan ɗan bakinsa alamar ta rufe masa baki. "Anki ayi shattaf ɗin whl Ka sake ni ko na tara ma jama'a".......... bai saurare ta ba bai kuma tsaya ba har saida suka shige ɗakin nasa, wurgata ciki yayi tare da rufe ƙofar ya kunna solar touchlight ɗin dake ɗakin take ɗakin ya dau haske rauuuu. Dukda a zafafe ya wurgata cikin ɗakin bata yarda ta faɗi