Author : Young Writer Category : Tknovels
whl Amjad ba annoba bane, shin mumu kin ganshi da idanun ki ko kin tabbatar da abinda akace ya aikata, mumu dan ALLAH ki sauqo haka, ya kamata ace ko da kowa zai yarda ke da daddy zaku kasance mutane na farko bayan iyayen sa da zaku ƙaryata ku Kuma kareshi a wurin al'umma, mumu ki tuna alherin Amjad a gare mu bakiɗaya mana, mutumin kirki ne shi whl na rantse miki"........Ta ƙarashe kwallar dake maqale a idanunta na gangarowa.
"Ba shakka, to sannu uwata ahh nace sannu uwata, ko shi bai mana gori ba sai ke uwar iya Mai dogon baki, ke dai kinsan ko da can ubanki ai ba talaka bane, tunda sai da ya riqe muqamin Deputy governor ya kuma riqe muqamin house of rep jarrabawa ce kawai ta rayuwa ta bada ƙofar da har shi Amjad ɗin ya taimaka mana. Ina so na Kara tabbatar Miki bake ba auran wanna yaron dan baza ki janyo mana abun kunya cikin zurriya ba, gwara tun wuri ki nesanta kanki dashi tun kafin mahaifin ki ya samu labarin cewa har yanzu kuna tare, dan ba hannun na a ciki wawiya wadda bata san ciwon kanta ba"........ Ta faɗa sannan ta juya ta fice a dakin. Kuka Mai sauti Nayrah ta fashe dashi bayan fitar mahaifiyarta ta tare da kifa kanta cikin pillow ta cigaba da raira shi kamar danshi aka aikota.
-----------------√
"Yauwa tun da dai har ba ku da gado a gidan Nan to ku tashi ku barmin gida na, na baku yau zuwa gobe."
Cikin tausasa harshe Sahnish ya ce, "haba malam ado ina dai cewa kuɗin haya ne matsalar, Kuma ga kuɗin ka nan an baka to kuma miye na tashin hankalin".
Cikin daga murya ya ce, "Bana buqatar kuɗin hayar ku dan sayar da gidana zanyi, in kuma Kuna da kudin biya ne to sai ku fito dashi ".
Cikin gajiya Sahnish da tun dazu shi ke ta faman bawa malam ado baki ya juyo ya kalli Hushaima dakewa Shazeen kalaba ya ce , "Hushaima ki sa baki mana, kina jin fa abinda yake cewa".
Ba tare data kalle su ba ta ce, " Har nawa ne kuɗin gidan naka".
"Miliyan uku ne Kuma nasan kaf dangin ku basu da miliyan uku, in ma Kuna da dangin kenan ".
"Kai malam ado ya fa ishe ka, tun dazu kake ta faɗawa mutane maganganu, ana lallabaka kana wani boƙarewa wanna gidan naka ma har wani gida ne, ai baya daga cikin Sahun gidaje". Faɗar Hushaima daga inda take zaune.
"A haka dai a haka ya muku alfarma kuka samu matsugunni har kuka rufawa junan naku asiri, ke kinsan ko banza na muku rana, dan lokacin da kuke gallafiri a titi, ba dan ni ɗin ba ai da ba Mai baku gida ku kaɗai a wanna lokacin".
Miqewa tayi daga zaunen da take ta ƙarasa wurin su, karɓe kuɗin tayi daga hannun Sahnish ta zura a aljihun doguwar rigar dake jikinta sannan ta ce, "kai ado kake ko wa, in ga uban da ya isa yazo ya fitar damu gidan nan daga yau zuwa gobe, dan ma kaga ana lallabaka to bari na ma da Yaren daka fi ganewa".
"Um um Hushaima, ki tsaya mu bi abun Nan a hankali fa".
"An fasa binsa a hankali, yayi duk uban da yaga zai iya".
"Haka kikace ?". Malam ado ya faɗa a fusace.
"Eh Haka nace ko zanji duka ne"......... Ta faɗa tana zare masa idanu tare da ƙara taku ɗaya zuwa gabansa.
"Au to ni dukan nawa zakiyi kenan kike fiffiqa "...........Sahnish ne ya shige tsakiya tare da faɗin, "Dan Allah ku bar wannan abun, malam ado muje waje muyi magana, kayi hakuri".
"In dukan ne ma zaka gaza dakuwa ne, Amma ni kayi kaɗan na ɗaura hannu na a wanna ƙazamin jikin naka saidai nasa a lallasa min Kai, in kaga dama Kar kayi hakurin gida Kuma baza a tashi ba in ga isasshen daya isa ya fitar damu".
Cikin hayyaqowa ya ce, "in ban tozartaki na kunyata ki a bainan nasi ba kice ni ba ado danga nake ba"..........Biyo su tayi dan lokacin har sun Kai soron kofar gidan dalilin Sahnish daya ke binsa Yana turashi tare da kalaman ban hakuri.
Itama daga murya tayi wurin faɗin, "Kai da ka san su kenan ni nan da kake ganina bana gudun wani abun kunya tijararriyar Kai na ce, bana gudu bare tsoron wani tozarci, ka dade bakayi ba, shege ka fasa".
"Haba Dan ALLAH Hushaima wai miye hakan ne , na samu na turashi waje Kuma kin sake biyo mu sai kun tara mana mutane".
"Kai dallah banza rufemin baki, au Kai yanzu har gudun a tara mutane kake, rigima wa ta kashe , sai me dan an tara mutanen ko akwai ɗan iskan da ke ciyar da mu ko ya shayar damu ko Kuma shi zaman da muke a gidan sa kyauta yake mana? Tambayar ka nake a fadin unguwar nan in zaka kwana da yunwa ka tashi da ita akwai Wanda zai kankaro ƙanzo yace ai gidan nan basu ci ba ko Sahnish ya kwana da yunwa?".
"Whl ki daina irin hakan ba kyau ke macece"......... Yana kaiwa nan ya juya ya fita tare da gabzo kofar ya barta sake da baki, "ahhhh lalle Sahnish ka girma"......... Ɗaga kanta tayi sama tare da sanya hannunta tana gwada tsayinta, "well is allowed, zaka dawo gidan ka sameni ne dan jar qaniya". Ta faɗa tana me juyawa ta koma ciki.
"Aunty Hushaima kizo ki karasa min kitson ni kam". Faɗin Shazeen dake zaune rabin kai da kitso rabi babu.
"Daure kan haka Shazeen da daddare na karasa Miki".........Ta ƙarashe tana zagaye tsakar gidan hannunta ɗaya ta dunƙule tana nausawa cikin ɗaya tafin hannun.
Can Kuma ta wuce daki bata jima ba ta fito dauke da mayafin ta kallon Shazeen dake danne danne a wayarta tayi kafin ta ce, " zan fita Shazeen Amma ba zan dade ba, ga wayar nan zan barmiki kiyi game".
"To, amma karki daɗe ". Shazeen ta faɗa ba tare da damuwa ba da alama dama ta riga ta saba da zaman gidan ita kaɗai, yayinda ita Kuma Hushaima ta nufi soron gidan tana faɗin," kizo ki kulle, Kar Kuma ki bude sai kinji muryar dayan mu".
Ko da ta fita bakin titi ta nufa ta tsayar da abun hawa. "Hajiya Ina zuwa?". Mai tuk tuk din ya tambaya.
Shuru tayi tana taunar lips dinta kafin ta ce, "wurin dillalai".........."Wurin dillalai Kuma hajiya wace unguwa kenan?"
Cikin masifa ta ce, " Wace unguwa zan faɗa ma? Kai duk gararambar da kake a titi baka san in da dillalai suke zama ba ne kake sake min tambaya, nace ma ka Kai ni majalisar dillalai, in ka sani Bismillah in Kuma baka sani ba wuce ga hanyar nan har darus Salam".
"ALLAH ya huci zuciyar ki, hau muje". Sai da ta galla masa harara Sannan ta shiga yaja suka wuce.
Tafiyar minti bakwai sukayi ya tsaya gaban wata rumfa tare da faɗin, "yauwa munzo, a wanna rumfar ba irin dilallan da Babu".
Kallon yanayin wurin tayi kasancewar yamma ce yasa da yawan dattijai da kuma matasa masu zaman kashe wando sun fito shan iska majalisa wanda hakan ya haifar da yawaitar hada hadar masu kasuwanci a wurin daga kan masu pure water, gyada, rake da sauransu. Sauka tayi tare da zaro Naira ɗari ta miqa masa, karɓa yayi ya jefa a ma'adanar kuɗin kasuwancin sa sannan ya karawa machine ɗinsa wuta.
Wurin ta karasa tare da yin sallama, mutane huɗu ne zaune a runfar sai cikon na biyar dake zuzzuba musu shayi a kananun cups suka amsa. "Da Allah tambaya nake?"
"Allah yasa mun sani " daya daga cikin su ya amsa.
"Da Allah dillalin gidaje irin na haya nake nema".
Washe baki yayi da faɗin, "kinzo gidan, Nan da kika gan mu duk dillalai ne Amma kowa da irin gidajen da yake dillanci, gidan haya kike so, wani irin hajiya".
"Ƙarami kamar me daki biyu da bayi, sai madafa".
"Apartment ko zaman mutum daya?"
"Zaman mutum daya ".
"An gama ki bani number ki, duk abinda ake ciki sai na kiraki na sanar dake ko?".
"Ba damuwa Amma na bar tawa wayar a gida saidai na baka tawa sai ka kirani ya so sai nayi saving taka".
"To shikenan, ga wayar saka a ciki"......... Karɓar wayar tasa kirar baby Nokia tayi tare da loda number ta a ciki ta yi flashing sannan ta miqa masa, ta musu sallama ta baro wurin, da ƙafa ta tako har zuwa gida, lokacin data shiga gida har an Kira sallar magriba, alwala sukayi itada Shazeen sukayi sallah, bayan sun idar Shazeen ta dauko littafanta ta fara yin homework din da aka basu a makaranta, ita kuma Hushaima ta tashi ta wuce kitchen domin sama musu abinda zasuci.
A haka Sahnish ya shigo da sallama hannunsa ɗaya riqe da leda gefen dardumar ya zauna tare da ajje ledar a gefen sa ya ce, " Shazeen karatu ake haka ne ?".
"Homework nakeyi yaya , sannu da zuwa".
"Yauwa Shazeen". Ya faɗa yana Kallon Hushaima data fito daga kitchen dauke da hancin su tumatir da tattasai data ciccire ta wuce bola ta zubar.
" Yameer na waje yace yayi ta Kiran wayarki ɗazu bata shiga".
"Kaje kace masa bana Nan".
"Kayya Hushaima Wai miyesa kike son yiwa mutane wulakanci ne, ke wai bakya so kiyi aure ne, kinfi so mu dauwama daga wanna gidan hayar zuwa wanna ana mana wulakanci, kinga in kinyi aure ai zaki tafi da Shazeen abubuwa da yawa zasu ragar mana daga nan zamu san inda rayuwar mu ta dosa, Amma yanzu fa kwata kwata bamu da alqibla kawai dai muna rayuwa ne kamar wasu sakakkun shanu".
Daga inda take ta girgiza kai tare da faɗin, "Sahnish"..........Sai Kuma tayi shuru tare da yin ɗan murmushin fatar baki ta ce, "Zanso hakan Amma bamu da wannan gatan, wa kake tunanin zai auri yarinyar da suke zaman kansu, ka riga ka san irin aladar mutanan mu baza su taɓa aurawa ya'yansu yarinyar da basu kama wani nata ba, ba iyaye ba dangi, Dan haka Kar mu yaudari kan mu Sahnish, muyi kokarin ganin kawai mun gina kan mu, duk Wanda kaga yazo wuri na na koreshi to na ga da gaske yake ne kuma kai ma ka sani".
Tagumi Sahnish yayi kawai yayinda ita Kuma ta nufi waje saboda kwankwasa kofar da ake. Tana buɗe kofar ta tarar dashi tsaye kan dakalin gidan, Yana ganin ta ya ce, "kina ban wahala Hushaima, na fa kusan minti talatin kofar gidan Nan".
"Ayyah sannu ya kake ?".
"Lpy kalau, to ki saki fuskar mana, ko dai Sahnish ne ya fito dake ba shiri ko kuma dai ni ɗin ne ba'a shirya gani ba".......... Ya ƙarashe yana karkace kai kamar wani Maraya, dan gyara tsayuwar ta tayi tana daga cikin soron gidan dan kafarta ko takalmi babu gwara ma kanta akwai dankwali. Murmushin da bai kai zuci ba tayi tare da faɗin, "Ni kawai mamakin ganin ka nake".
"Miye Abun mamakin? Dama munyi dake na dai na zuwa ne? kece ma fa kika min laifi".
"Yameer kenan abinda na gaya ma ba laifi bane gaskiya ce wadda ni da Kai duk mun San ta, to meysa zamu bari mu yaudari kan mu, na riga na fada ma ni bani da lokacin soyayya saboda ko na bata ruwa bazan girbi amfanon ba".
"To ni Kuma ya za'ayi da zuciya ta". Ɗauke kai tayo daga kallonsa kafin ta ce, " Ka bata hakuri ka Kuma nisanceni hakan shi ma zai taimaka ma".
"Ni ban taba ganin yarinyar da take cewa a nisanceta ba sai ke Hushaima, wai meysa ? Ni fa da arziki nake son ki kuma ba wasa ya kawo ni ba, a gobe in kin amince min zan turo iyayena a nema min auranki".
Sautin "hmmmm". Ta ja tare da kaɗa kanta kadan ta ce...........
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______4
Sautin "hmmmm". Ta ja tare da kaɗa kanta kadan ta ce, "Bansan meysa kake da son ai ta maimaita abu ɗaya ba yameer, Dan ALLAH mu hakura kawai, nagode da soyayyar ka gareni Ina roqon ALLAH ya baka Wadda ta fini, Ina Maka fatan alheri, dan ALLAH karka ƙara zuwa in da nake"........ Tana kaiwa nan ta juya ta shige tare da rufo kofar gidan harda saka sakata.
"Hushaima! Hushaima! Ki tsaya kiji Dan ALLAH". Shuru yayi ganin da gaske fa baza ta saurare shi ba, komawa yayi ya jingina jikin motar sa tsawon wasu minutes kafin ya shiga ya tada ta ya bata wuta ya bar layin zuciyar sa a cinkushe, dan ALLAH ya gani yana matuƙar son Hushaima.
Ita kuwa Hushaima ba alamun wani damuwa a tattare da ita ta koma ciki, samun Sahnish da Shazeen tayi suna faman yanka kankana. "To iyayen ciye ciye kun yi sallah tukunna kuka zauna yanke yanke?"
Sahnish ne ya ce, "Eh ai kinsan dake mu ɗin rainon Pope leo ne"....... Shazeen ce ta ce, " yanzu fa muka idar Aunty Hushaima".
A fusace ta ce, "Whl Sahnish ka fita ido na, Kai na tambaya ne Dan iya, dama ɗazu Ina cike dakai ".
Ba tare da ya dago ba ya ce, "to Kuma ba sai ki rage ni ba. Yameer din ya tafi ne?"........... Ya ƙarashe Yana ɗagowa, wucewa tayi ta dau buta kana ta ce, "Eh."
Bai sake cewa komai ba ya maida kansa suka cigaba da abinda sukeyi shi da Shazeen ɗin, har Hushaima ta dauro alwala tazo zata tada sallah. turo mata tray ɗin yayi da faɗin, "Duba yanka Hajiya ba irin naki ba me kamar haƙorin giwa".
Tsaki taja da faɗin, "Kai ka sani Kuma in ka tashi ka duba min girkin dake kan wuta"........ Ta ƙarashe tana kabbara sallar Isha da aka Kira tun shigowar Sahnish ɗin.
"Zo muje mu Duba girkin kafin ta idar" ..........Ya faɗa yana ɗaukan slice ɗin kankanar da suka yanka guda ɗaya ya sa a baki sannan ya miqe, tashi Shazeen tayi itama dan dama ita tun suna yankawa ta shanye kusan rabi, kitchen ɗin ta bishi suka shiga.
Ita kuwa Hushaima ko da ta idar hijabin ta cire tare da komawa ta kwanta akan dardumar tana kallon sararin samaniya da wata ya haska zagaye da taurari masu haske, kaɗan kaɗan iska ke kaɗawa, sosai tayi nisa cikin duniyar tunani har bata san tsawon lokacin data ɗauka ba sai muryar Shazeen dake mata ihu a kunne ne ta dawo da ita hankalinta, da mamaki ta bisu da kallo ganin har dafadukar macaroni ɗin data hada ta dahu har sun zubo shi.
Kallon Sahnish tayi taga shi ma ita yake kallo, maida kanta tayi kan Shazeen da faɗin, "Wai har kun gama?".
"Akwai wani zahirin da kike nema bayan wanda ke gabanki"........ Sahnish ya faɗa cikin sigar tsokana, harara ta watsa masa shi Kuma yayi dariya kana ya ce, "sako hannu kiga Kar yayi sanyi ".
Bismillah sukayi dukkan su tare da sa hannu suka fara cin abincin a tare cikin mazubi ɗaya kamar yadda suka saba, Sai da suka gama Sahnish ya dauka tray ya wuce dashi kitchen ita Kuma Shazeen ta dauko tsintsiya ta fara kokarin tattare wurin, ganin haka yasa Hushaima nade dardumar tare da hijab ɗin sannan ta dauki tray kankanar tayi ɗaki.
Saida suka gama tsaftace gidan suka wanke kayayyakin da sukayi amfani dashi sannan Sahnish yabi bayan Hushaima inda ya bar Shazeen bakin rariya tana wanke hannayenta da kafafunta.
Shiga yayi tare da neman wuri ya zauna bakin yagalgalalliyar katifar tasu irin ta yam makaranta duk ta gama siɗewa. Kayan data gama linkewa ta haɗa ta ajje tare da dawowa kusa dashi ta zauna tana tambayar. " Ya akayi
Sahnish? Ina ka baro Shazeen din Kuma".
"Kai ke kina da matsala Shazeen gida a rufe zata fita ta sama ne. Ina kudin hayar Malam Ado ?".
"Me zakayi dashi?". Ta tambaya tana me tsareshi da fisgaggun idanun nan nata masu matukar rikitarwa.
"Mun daidaita dashi ne dama, yace gobe zaizo ya karɓa"........Shuru tayi can kuma ta ce, "Dan hau, ni da ai har na bazama na sa a nemo mana gida mu tashi mu bar masa tsiyar sa".
"Yadda gida je ke wahala har kina tunanin zamu samu gida a dan wanna tsakanin ne, ki bari dai kawai tunda na lallabashi zai karɓa na yanzun, kafin lokacin wani biyan yayi sai mu haɗa kuɗi mu nemi wani gidan mu tashi, ba shikenan ba an rabu lpy ba".
"Zancen banza ma kenan, zan tashi a gidan nasa sannan mu rabu lpy, ai whl duk wulakancin da ya mana sai na rama sai na ci masa uwa na huce haushi na".........."Hushaimaaaaa"...... Shuru yayi saboda Shazeen data shigo, canza zancen yayi da faɗin, "ban kankanar na ibi tawa na wuce daki".
Tray ta jawo masa. "Miqomin cup din can Shazeen"....... Ya faɗa Yana nuna mata cup ɗin dake gefen Hushaima dan yasan yanzu yana cewa Hushaima miqo min wata sabuwar paragraph ɗin zata bude. Kankanar ya ɗiba bayan Shazeen ta miqo masa cup ɗin sannan ya miqe da faɗin, " Sai da safen ku"........"Allah ya tashe mu lpy". Hushaiman ta amsa.
"Yaya sai da safe"........." Sai da safe Shazeen." Ya amsa yana ficewa daga ɗakin.
----------------√
Amjad kuwa daga gidan mommy gidan sa suka wuce, ba shi ya fito ba sai karfe 8:30pm, yana sanye da wasu lightwears, ash comfy long pant da tee na Lululemon brand sai baza kamshi yake kamar wani ango. Shi da Kamal kaɗai suka fita, ya hana sauran binsu.
Gaban wani ratsatstsen gida suka tsaya iya gate ɗin gidan kaɗai Abun