BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   35 / 53

102K to 105K   out of 156.9K words

gyara daurin zaninta da kullum yake kan kirji. "A'a ku tsaya, wai meysa kuke haka ne? Ku yi ta abu gaban ya'yan ku ko kunya bakwa ji". Kandala Amaryar baba ilerika ta faɗa tana shiga tsakiyar su.

"Bani waje ki gani kandala, idan ba gyarawa Atine zama nayi a gidan nan ba baza ta daina min gani gani ba".......... Daƙyar da siɗin goshi aka raba mama Atine da umma Delu.

Shi kuwa Sahnish tuni ya taimakawa Hushaima ta tashi suka shiga ɗaki ya ɗauko mata kayan da zata canza sannan ya fito ya bata wuri ta sauya. Saida ta gama ya koma ɗakin ya taimaka mata suka fito daidai lokacin Baba ilerika ya shigo da saurin sa ko bi takan su Mama Atine baiyi ba yace da Sahnish su fito.

Da ragowar kuɗin da Jey ya basu sukayi amfani a asibitin yayinda Baba ilerika yayi uwa yayi makarɓiya ya tsaya akan komai saboda Sahnish na tare da Hushaiman hatta magungunan da aka basu shi yaje ya siyo ya dawo sannan suka nufo gida.

Sai da Hushaima tayi kwana biyu tana jinyar jikin ta kafin ta warware ta cigaba da harkokin ta.




----------------------√




AURELLON SULTANATE💎



AURELLON SULTANATE wata babbar masarauta ce me girman gari guda domin duk abinda za'a samu a gari to akwaishi a ciki kama daga Kan population na mutane wanda dama suke haɗuwa su zama gari to su ne matakin farko na kafa Aurellon sultanate, domin kuwa mutanen cikinta yawa ne dasu, kuma duk yaren su ɗaya al'adun su daya in kaga wanda ba nasu ba to daga cikin bayi, hadimai, fadawa ko kuma dakarun su ne.

Akwai makaranta, jami'a, asibitoci, court, police station, barrack na sojoji, fuel station, gidan television nasu, masana'antun su, ɗakin karatu na musamman (Library), Hotel, Shopping Malls, Airport, da dai sauran su, they are very creativity domin yan baiwa ne su, suna ƙirƙirar abubuwa da dama su fitar dashi ƙasashe, duk mutanan dake cikin Aurellon basa fita wajen ta yin aiki, a cikin masarautar su sukeyi, saidai su fita waje dan ra'ayin kan su amma ba dan neman wani abu da basu dashi a masarautar su ba, duk wasu abubuwan more rayuwa sun tanadarwa kansu in nace komai ina nufi komai. Suna da kwararrun masu busa sarewa da kuma gwanintar murza linzamin dawakai.

Sultan Abdulbasit Abdulaziz wato Sarkin garin ya kasance dattijo me adalci ga al'ummar sa, mutum ne mai kuma sauƙin Kai da son zaman lpy, yana da mata uku, Sheikha Barrah itace matar sa ta farko tana da ya'ya takwas duk mata, biyar sunyi aure sai uku ne a gabanta. Sai Sheikha Balqis tana da hudu mata ɗaya namiji, biyu sunyi aure saura yan mata biyu da namiji ɗaya. Sai Amarya wato Sheikha Mahra tana da shida huɗu mata biyu maza, ɗaya ce kawai tayi aure.

Ginin Aurellon sultanate ya fita daban a tarihin qawatattun gine ginen duniya, domin gini ne da aka narka dukiya akayi shi ba algus, wasu irin dogayen gini ne da sukayi matuƙar tsaruwa saboda haɗuwar su, kusan duk wani abun qawa da aka qawata ginin dashi diamond ne, ta yadda ko ba wuta hasken wannan diamond ɗin da kuma glasses ɗin nan kaɗai ya isheka ballatana ba'a dauke musu ko na second ɗaya.

A bangaren ƙarfin iko kuwa tana da ƙarfin iko fiye da tunanin me karatu, domin kuwa mulkin su absolute monarchy ne duk sarkin da za'a naɗa sai aurellon ta duba cancantar shi take Naɗashi kuma karkuyi tunanin su take zuwa ah ah, sarkin da za'a naɗa ɗin ne zasu zo Aurellon tare da mutanan sa, idan ta Naɗashi sunayin shagalin bikin tayashi murna sannan su haɗashi da yan rakiya har zuwa masarautar tasa, tana da ƙarfin ikon dakatar da shugaban ƙasa da zarar ta samu labarin wani batanci da yakewa al'ummar sa, duk duniya shakkar tinkarar ta suke, suna da tsaro sosai tare da dokoki da kuma qa'idoji ba wanda ya isa shiga cikinta kai tsaye haka zalika fita.


______________Wani ƙayataccen falo ne da yaji kayan qawa da more rayuwa, zagaye yake da wasu royal cushions set uku sai TV da kuma na'urorin sanyaya ɗaki , banda sassanyan ƙamshi me kwantar da zuciya tare da sanyi AC ba abinda ke tashi, wani kyakyawan dattijo na hango zaune kan kujera ya ɗaura ƙafarsa kan wani tumtum me laushi, fari ne tas ga dogon hanci kana ganinsa kaga irin larabawan asalin nan, Sanye yake da farar saudi thobe, lallausan gashin nan ya koma grey saboda furfurar data fito akan Black silky hair ɗin nasa, zai iya kaiwa shekaru 67 a duniya. Hannun sa riqe da wani ƙaramin mug Mai masifar kyau sai walwali yake, kallo na nakai gaban sa inda wata kyakkyawar mata da zatayi shekaru 45 zuwa 46 a duniya amma ba zaka taɓa zaton takai wannan shekarun ba dan in Ka kalleta zakayi tunanin baza ta haura 30yrs ba saboda kyawun jikinta da ya haɗu da jin dadi, sanye take da Mukhuwar kalar red and peach wuyanta da hannayenta kuwa duk ta ƙawata su da wasu danƙararrun gold na HD AURUM MINING, sai walwali take.

Cikin harshen larabci dattijon ya ce, "Mahra kin cika son wahalar da kanki da yawa, da kin bar Khadiman sun yayyanka ai"........... Kallo na Kai kan abinda take yi, grapes ne da apple take yankawa a cikin wata ƙaramar bowl. "Zan iya barin su suyi komai Sultan amma ba zan bari khadimai suyi hidimar mijina ba"........ Wani dan gajeren Murmushi yayi cike da izzar mulki ba tare da ya sake cewa komai ba, saidai yanayin fuskarsa ta nuna yaji dadin maganarta, wannan dalilin yasa duk cikin matan sa Mahra ta fita daban, saboda duk abinda ya shafe shi bata barwa khadimai ko bayi ita takeyi da kanta, shiyasa matsayinta yake na daban a wurin sa, har hakan yasa abokan zaman ta suke ganin kamar yana fifita ta tane akan su saboda itace mahaifiyar sarakee me jiran gado.

"Ya jikin Rouslan kuwa?".......... Sai da ta miqa masa bowl ɗin sannan ta gyara zamanta kusa dashi tare da faɗin, "Dama Ina ta so nayi ma maganar Sultan, Ni wai meysa ba za'a fitar da Rouslan waje ba, na rasa gane kan wannan rashin lpy tasa, daga wannan Dr yace ciwon zuciya sai wannan yace migraine sai wanna yace kaza gabaɗayansu sun kasa gano ainahin abinda ke damunsa".

Kafin Sultan yace wani abu wata budurwar yarinya da baza ta wuce 17 years ba ta shigo da gudu kamar zata kifa. "Haba Albee ya zaki shigo haka k........" Bata rufe bakin ta ba wani dogari ya shigo da sauri shi ma yana sanye da uniform dinsu red and dark brown, a murɗe yake kamar wani dan wrestling, zan iya ce muku duk dogaran Aurellon sultanate ba wanda zaka kalla sau ɗaya ka so sake kalla, zubewa yayi kan guiwowinsa kansa a ƙasa ya ce. " Tuba nake Sultan a mun afuwa, gimbiya Albeena ce tazo zata shigo na buqaci ta tsaya na nema mata izini tukunna amma bata saurare ni ba ta shigo, amma idan nayi laifi ai mun aikin gafara".......... Ya ƙarashe yana mai sake yin ƙasa da kansa.

" Zaka iya tafiya"........... Sheikha Mahra ta faɗa. "ALLAH ya ƙarawa Sheikha lpy "......... Ya faɗa cikin tsantsar girmamawa tare da tashi ya fita ya jawo musu ƙofar.

Rarrafawa tayi wurin mahaifin nata tana da faɗin, "Abbu Ya Reeslan...... "........ Numfashi da take saukewa da sauri sauri ya hanata ƙarasawa sai ƙofa da take nunawa, "Reeslan yana Ina?"......... Sheikha Mahra ta tambaya. Kuka Albeena ta fashe dashi tare da faɗin , "Ummu an kashe su".

Zakuɗowa ummu tayi daga cikin kujerar tare da faɗin, "Wace irin maganar banza ce wanna Albeena kanki ɗaya kuwa?"............ "Ummu an Kira wayoyin ku ba'a samu ba, yanzu aka sanar da an Kai musu hari Kuma ba wanda ya tsira duk sun mutu".

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, innalillahi wa inna ilaihir raju'un"......... Ummu da Abbu suka shiga maimaitawa a tare, miqewa Abbu yayi amma sai tsayuwar ta gagare shi saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga dukda yadda yake ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin nasa saboda Ummu, komawa yayi ya zauna yana kallon yadda falon ke juya masa. "Ummu tawaam miqomin wayata a ɗakina yanzu". Cikin ƙarfin hali Ummu ta miqe ta wuce ciki.

Bata jima ba ta dawo da wayoyi biyu a hannun ta, "Sayyid Iffan ne yake ta Kira fa Sultan".........." Kawo mu gani". Ya faɗa a Nutse kamar ba abinda ya dameshi, karɓar wayar da ta bashi yayi tare da answering call ɗin, bai tsaya bi ta kan gaisuwar Sayyid Iffan ɗin ba ya ce, "Iffan a wani hali Maleekh yake?"........... Shuru sayyid Iffan yayi cikin jimamin labarin da zai sanar da sarkin nasu. Shi ɗin ya kasance minister labarai ne na nan masarautar tasu, duk wani labarin da ya shafi masarautar tasu to kafin kowa ya samu labari shi yake fara samu sannan ya isar da Labarin cikin masarautar. Sanin cewa Sultan baya maimaita Magana sau biyu yasa shi daurewa ya ce, "A yanzu duk mutanan da Maleekh ya fita dasu an kashesu sai dokunan su kawai aka bari, amma shi babu wata masaniya akan halin da yake ciki dan ba'a ganshi ba".......... Allah sarki dattijo Mai tawakkali duk da girgizar da zuciyar sa tayi bai bari hakan ya bayyana a muryar sa ba, ya ce, "Iffan ka yiwa Babil magana a tabbatar an binciko halin da Maleekh yake nan da 1 hour". ( Babil shi ne minister bincike na masarautar, dan su fa basa haɗawa mutum ɗaya aiki biyu saboda aikin masarautar su girma ne dashi) .

"An gama Sultan ". Sayyid Iffan ya faɗa cike da girmamawa, kashe wayar Sultan yayi tare da kallon Ummu wadda kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da kukan zuci take, "Ummu tawaam karki damu, in Sha ALLAH ba abinda zai sami Reeslan, dan ni banji a jikina ya mutu ba in sha ALLAH yana raye kuma zai dawo gida cikin ƙoshin lafiya, dan haka kuje kawai ki kula da Rouslan, Kar ku bari labarin nan yaje masa har sai mun samu kira daga Babil "......... Da, "Okay". Ummu ta amsa a sanyaye tare da juyawa ta koma cikin ɗakin, jim kaɗan ta fito sanye da wata zazzafar alkyabba red me golden stones sai ɗaukan ido take. Tashi Albeena da har lokacin kuka take marar sauti tabi bayan mahaifiyarta ta, sai da suka wuce wani corridor sannan suka isa gaban wani transparent elevator suka shiga ya sauqo dasu qasa. A wani qaton falo da yafi na saman haɗuwa da qawatuwa suka ɓulla, bayi suka tarar tare da khadiman dake bangaren Sultan ɗin suna ta kai kawo, suna ganinsu duk suka zube suna mata Barka da fitowa haɗe da kirari irin wanda akewa matan sarakee, ɗaga musu hannu tayi kawai ta wuce Albee biye da ita, su ma duk rufa mata baya sukayi kamar yadda al'adan gidan take na raka duk wata gimbiya da zata shigo bangaren, haka suka dinga wuce tafka tafka falukan har suka fito zuwa shahararren compound ɗin gidan da ya gaji da haɗuwa, ta ko ina fitulu rau kamar rana.

Wata mercedes maybach series S ce Pake a ƙofar fitowar da alama dama su ake jira, dogaran dake tsaitsaye ne suka buɗe musu both side na ƙofar motar, Ummu ta shiga Albee kuma ta zagaya ta ɗaya side ɗin. A hankali motar ta fita daga ɓangaren na Sultan ta kewayo ta left side ɗin da a sama aka rubuta , S. MAHRA da manyan harrufa wato Sheikha Mahra da wasu irin sea blue gems. Tsayawa motar tayi yayinda dogaren dake gaba suka fito da zafa suka buɗe musu, suna fitowa dogaren dake bangaren suka tattaso suna jero musu kirari, Ummu batabi ta kan kowa ba ta shige Albee biye da ita kamar jela.

Nasan zakuyi tunanin shin babu hanyar shiga part ɗin ummu ne daga na Abbu? To akwai a taƙaice zaka iya zuwa kowani part na Matan Sultan ta cikin bangaren sa, dan bangaren nasa shi ne a tsakiyar nasu, saidai fa akwai yar tafiya, to wannan tafiyar ce Ummu baza ta iyayi ba a yanzu saboda zuciyarta data mata nauyi a dalilin tashin hankalin da take ciki, dan a lokacin da zata shigo bangaren ba ta gaba ta shigo ba ta cikin part ɗin nata ta isa.

Suna shiga falon farko suka hadu da Reeslan da ya fito, sanye yake da kananan kaya maroon ɗin t shirt da baƙin wando, wanda suka Ƙara haska farar fatarsa, gashin Kan nan kuwa ya raba shi biyu ya ɗaure na saman a tsakiya da band na ƙasan kuma ya zubar dashi akan dokin wuyansa. Riqo hannun sa ummu tayi da faɗin, "Ina zaka kuma Rouhi?".......... Sake kallon sa nayi da kyau cike da ɗimbin mamakin sunan data ambata, yoo ai ni na dauka Reeslan ɗin ne ya samu isowa sai da na ƙura ido sosai na lura wannan bai Kai Ruslan ɗin murdewan jiki sosai ba, Amma bacin haka komai nasu irin daya ne hatta da kallon su ɗin nan me isa har zuciyar bawa, to a hakan ma fa wai nayi ƙwaƙwa ne dan na samo abinda ya banbanta su.

"Ummu da gaske Habiby ya mutu? da gaske ba'a ganshi ba, ba'asan in da yake ba?".......... Duk da a cikin tsantsar tashin hankali yake amma magana yake cike da nutsuwa da kuma aji irin na ya'yan da jinin sarauta ke gudu a tsoka da jijiyoyinsu. Bata bashi amsa ba ta ja hannun sa suka wuce ciki. Suna shiga ɗakinta ta nufi wurin two seater sofa dake ciki ta zaunar dashi sannan ta zauna gefen sa wanda hakan yasa tsananin kamannin ta dashi ya bayyana a yanzu da suka jera, cikin tausasawa ta ce, "Kwantar da hankalin ka Rouhi, Habibyn ka yana lpy in Sha ALLAH, karka tada hankalin ka"........... Dan girgiza kansa yayi tare da faɗin, "Ummu ɗazun fa da yamma yace min yau so yake ya fita wajen gari ya sha iska tare da dokin sa Hirtik nazo muje nace masa ah ah ni bana jin fita yau yaje kawai, saboda bana jin ƙarfin jiki na nasan in ya sani zai tashi hankalin sa ne. Whl Ummu nayi dana sanin rashin binsa da maybe a Kai na hakan zai faru ba shi ba......"............ Katseshi tayi da faɗin, " Haba Rouhi kayi shuru mana haka, ai kowani bawa da tasa qaddarar, ko dan Kuna tare sai ace bari a goge qaddarar Reeslan a rubutuwa dan uwan tagwaicin sa Rouslan? Abinda nake so dakai karka sa damuwa a ranka Dan ALLAH, Abbunku yasa a bincika duk inda yake nan da 1 hour, Kuma kasan ƙasa da haka zamu samu labari dan haka Ka kwantar da hankalin ka kaji. Ka ma ci abinci tukunna?".......... Ta faɗa cikin sigar lallashi da Kuma tausayawa ɗan nata saboda shaƙuwar dake tsakanin sa da ɗan uwan nasa. Reeslan da Rouslan identical twins ne da basu da banbanci a komai dan ko mahaifan su ba a kowani lokaci suke iya banbance su ba, Dan ma dai Rislan yana da zafi sosai gashi mafaɗaci ba'a taɓa yin doguwar magana dashi a wanye lafiya in anja da nisa ma yana iya rufeka da duka. WANNAN KENAN.

"Sai Habiby ya dawo zamuci".......... Zazzafan numfashi Ummu ta furzar ba tare data iya sake cewa komai ba sai waya data ɗauka tayi kira ana dagaywa ta ce, "Ziyada ke da su waye?". A ɗan sanyaye ziyada ta ce, "Ni da su Albeena ne, sai su Nuaymin da suka shigo ɗazu"..........." Turomin su Nuaymin ɗin ɗaki na yanzu"........ Dan shiru tayi jin Ummu na shirin kashewa ya sata faɗin."Ummu ya ake ciki batun ya Reeslan?"......... "Albeena bata gaya miki bane?".

"Tace wai Abbu yasa a bincika ba?".........."Eh turo min yaran kawai"..........Ta yanke maganar saboda yadda Rouslan ya kafeta da ido.

Ba'a jima ba sai ga wasu yara sun shigo su uku babbar bata fi 10 years ba sai mai bin ta da bazai haura 8 years ba, sai kuma wani yaro da baifi 5 ba sai ta karshen da itama bata fi 4 ba. Suna hango Rouslan suka nufo wurin sa, Nuaymin ya ce, "Khali (uncle) Ina jigsaw puzzle ɗin nan da ɗazu kace mu ajje idan khali Reeslan ya dawo zamuyi wasa dashi to linda ta batar da sauran sai guda biyu ta bari".

"Khali whl karya yake min shi da Nuaymah ne suka watsa abinsu, Ummu ALLAH kicewa Nuaymin ya fita ido na yaran nan ya rainani, kullum sai ya ce nayi ƙarya". Faɗar babbar cikin nasu da aka Kira da Linda .

Murmushin ƙarfin hali Ummu tayi tare da biyewa yaran dan dama tace suzo ne saboda Kar su bar Rouslan ɗin yayi tunani sosai, kusan 30 minutes wayar Rouslan ɗin tayi Ƙara zarota yayi daga aljihu ai yana ganin me Kiran ya miqe tsaye da sauri. "Menene ? Waye?". Ummu ta tambaya a jere, inaaa bai tsaya bata amsa ba yayi answering call ɗin tare da faɗin, "Habiby where are you?"......... Miqewa itama Ummu tayi tana kallon sa da jiran amsar da zai faɗa. "Zamuzo yanzu mu taho dakai".........." No karku zo yanzu ku bari sai da safe I'm safe here, har sai safiyan kun iso".

"Ah ah Habiby ka bari muzo yanzu ka faɗa mana location ɗin da kake"............" Me sa kake da gardama Rouh nace ku bari sai da safe mana ". Ya faɗa cikin faɗa faɗa, miqawa Ummu wayar Rouslan yayi saidai itama duk yadda tayi dashi yaqi faɗar inda yake kawai dai yace musu yana lpy da safe suzo su ɗaukeshi anjima zai tura musu location ɗin. Ko da suka gama wayar Ummu Sultan ta kira ta sanar masa, Kiran sa yayi shi ma sukayi magana daga nan ya kira Ummu yace karsu damu su barshi sai da safen kawai, dole ba yadda suka iya da taurin kan Reeslan haka suka haƙura.

Ranar kwana sukayi suna waya da Rouslan ɗin wanda yaqi yarda ya koma ɗakin sa yace tunda Reeslan baya nan a ɗakin ummu zai kwana, itama daren bata samu kwanciya ba kwana tayi tana nafilfili har zuwa sallar asuba, sai Lokacin Rouslan ya tashi ya fita, ɗakinsu yaje yayi shirin masallaci ya fita

35 / 53