BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   27 / 53

78K to 81K   out of 156.9K words

sai dai in zuciyar sa zaka buɗe ka shige, a hankali ya shafo gemunsa sannan ya ce, "Juraysh ga Anah ga Kuma Dada, da ALLAH ka kula dasu sosai".

"Me kenan Amjad, kana nufin da gaske kana aikata hakan? da gaske kai me safarar mutane ne? Ka samu a duhu Amjad ?". Ya tambaya a rikice.

"Ba zan iya ce dakai komai ba Juraysh"......... Cikin ɗaga muryar da kanaji kasan tashin hankali ne ya jawo ta ya ce, "kamar ya baza ka iya ce min komai ba kasan kuwa abinda ke faruwa, me sa ko ma ka aikata baza kayi ƙoƙarin Kare kanka ba. Anah fa Kai kaɗai take dashi ya kake tunanin zataji, ga dada ma dake kwance kasan sanadin ka yake kwance, wai wannan wani irin abu ne?". Kansa ya ɗage sama still wayar na maqale a kunnen sa ya ce, "Juraysh Ina so ka shaidawa su Anah cewar bana gari nayi tafiya dan haka ta kwantar da hankalin ta, zan dawo in komai ya lafa, ni kuma i know what to do".

" Ka gudu fa Kenan?"................




---------------------√



Ɗagowa tayi tare da ɗaura dukkan hannayen ta kan table ɗin ta tokare habar ta dashi tare da zuba masa eyes dinta, ɗauke kansa yayi dan bayaso ya sake ce mata ta dai na kallon sa, taji haushi ta fasa bashi Amsa, ɗan gajeren murmushi tayi sannan ta koma ta jingina da bangon kujerar idonta na kallan wani wuri ta ce, "Zan gaya ma wacece ni da sharadin ni ma zaka gaya min wanene Amjad Hashim Darwin"............ Da wani irin sauri ya ɗago da faɗin, "Me... M.. me kikace ?".

"Amjad Hashim Darwin"........... Ta nanata kai tsaye tana kallonsa. Ni kuwa nace eh kwarai to bari muga yadda za'a buga wasan nan, shi yana can yasa a masa bincike a kanki ko miye dalilinsa oho? Ke kuma kina nan da taki qudurin fansar, to mu saidai muce ALLAH ya bawa me rabo Sa'a.

"Meysa kike son sanin sa ?"............ Yarfa hannuwa tayi tare da faɗin, " Burgeni yake, na kamu da son sa, ina so naje gareshi domin na bayyana masa soyayya ta amma bansan taya zan fara ba, saisa nake son sanin waye shi "............ A boye ya sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tare da jan karamin tsaki, ciki ciki kamar me koyon magana ya ce, "Taya zaki fara son wanda baki sani ba? Tukunna ma a ina kika haɗu dashi da har kika fara sonsa".......... kai tsaye ta ce, "A TV".......... kafin yace wani abu waitress ta iso wurinsu tare da tambayar su abinda za'a kawo musu, Jey ne ya bata umarnin kawo musu fried stir spaghetti da shredded chicken sai ruwa da lemo.

Shuru shuru kamar ba zai sake magana ba, kowa da abinda yake tunani can ya ce, "Mahaifin sa Hashim Darwin sanannane ne, domin refinery da Kuma company na aurum mining dinsa na ɗaya daga cikin companies da ƙasashe ke ji dasu, shi ne ɗan auta a maza Kuma shi kaɗai ne namiji a wurin mahaifiyar sa"............ "yana da yan uba kenan?". Ta sake watsa masa wata tambayar. Shuru Jey yayi kamar bai ji ta ba.

Jin bai bata amsa ba ya sata girgiza kai tare da faɗin, " kenan dai shi bashi da wani labari sai na mahaifin sa?"........... Juyowa yayi yana mata kallon rashin fahimta kafin ya ce , "Ban fahimta ba?" .

"Kai ne mutum na biyu daka ban wanna amsar duk tambayar da nakeyi ba ita ake ban amsar ba, duk wanda nacewa waye shi sai ya fara bani tarihin mahaifin sa, hakan ya nuna min shi ɗin ba kowa bane face banza, soko, da bashi da ginin kansa sai wanda aka masa ashe duk wannan abun fanko ne kwalin ne kawai me kyau amma ciki ba komai, gwara da ALLAH yasa na sani tun yanzu kaga zan taƙaitawa kai na wahala dan ni nafison mutumin da ya ginu da kansa ba wai wanda aka gina wa ba ".......... ta ƙarashe tana jan fatar lips ɗin ta na kasa ta kama cirewa, sakwato Jey yayi sake da baki yana kallon ta maganganun ta na kai kawo a kwakwalwar sa. Kawo musu abincin da yayi order shi ya dawo dashi nutsuwar sa, abinci ne plate biyu sai lemo da ruwa da yace kowa ɗai ɗaya.

"ke kawo min leda ".......... Hushaima ta faɗa tana kallon waitress ɗin . "Okay ma let me check".

"Menene ?"........... Ta tambaya tana mata wani kallon banzar bazara. " Cewa tayi bari ta duba, ni karki tara mun mutane".......... Jey ya yi saurin faɗa rai a haɗe dan shi dama tun ranar farko ya gane Hushaima fa kan ba komai sai bala'i da tsiwa fal ciki. Hararar ta watsa masa da faɗin, "Sai akace ma banji bane, ai naji tace zata duba ɗin "............ Tsaki yaja tare da miqewa ya bar wurin, kallon sa tayi sannan ta kalli wayar sa dake wajen hakan na nuna ba tafiya yayi ba kenan .

Bai ɗaɗe ba ya dawo dan kusan a tare suka dawo shi da waitress ɗin da Hushaima ta aika ta kawo mata leda, zama yayi tare da ɗaukan mocktail Juice din ya fara sipping a hankali. Ita kuwa Hushaima ledar ta karɓa tare da fara ƙoƙarin juye abincin a ciki ta tsinto maganar Jey, "What a messy, ke wai miye haka, ke bakyajin kunya ne ?"............ Ya faɗa Yana jin kamar ya mangareta tsabar takaicin dake cinsa, shi ya ma rasa dalilin da yasa bai raba tafiya da ita ba ko dan baisan ɗanyan kan nata ya wuce yadda yake tunani bane.

"Kunya? Kai ka Santa "............ Ta faɗa tana ƙarasa juye abunta sannan ta ɗaure ta miqe . Cikin ɗinbin mamaki ya bita da kallo ganin tana ƙoƙarin tafiya yayi saurin tsaidata da faɗin, "Zauna please".......... Ko kallon sa batayi ba bare yasa ran zata tsaya da sauri ya ɗauki wayar sa ya bita, saurin shan gabanta yayi cikin ɓacin rai ya ce , "Wai wacece ke da ina miki magana zaki min banza".

Ita ma nuna masa hannu tayi da faɗin, "Kai waye da zaka ban umarni in bi, to ni ba Wanda ya isa ya ban umarni in bi in dai ba radin Kai na ba, matsa ka ban hanya na wuce "........... Ta faɗa tana yanke shi tayi wucewar ta, baki sake ya bita da kallo sai Kuma ya nuna kansa da faɗin, " Me? Oh no ".......... Ya faɗa tare da ficewa daga wurin shi ma.

Hushaima tana fita ta samu Abun hawa dan haka ta tsare shi tare da faɗa masa inda zai Kaita. Shi ma ko da ya fito bai bi ta kanta ba ya tsallaka titin wurin wasu masu container yaja ya tsaya ya zubawa titi ido, ni kuwa nace to ko dai neman wanda zai huce a kansa yake.

Ita kuwa Hushaima me tuktuk na direta ta bashi kuɗin sa ya bata canji ta shige ciki, faɗan nasu na gado ta samu sunayi a gidan sai ife ife suke sun tara mutane fal, batabi ta kan kowa ba ta wuce ɗakin Sahnish in da ta sameshi zaune yana kallon wani indian Film a wayarsa me suna Eagle, "Kai ina ɗan makullin daki na"........... daga jin yadda tayi magana bai nemi ƙarin bayani ba ya ɗauko makullin ya bata, fita tayi ta koma ɗakinta.

Ba ita ta fito ba saida lokacin ɗaukan Shazeen yayi daga makaranta taje ta ɗaukota ta dawo, abincin data ɗaibo shi ta zuba mata taci, tana cikin ci ne Sahnish ya shigo, abincin yabi da kallo dan yasan ba a saida irinsa a layin amma sai bai tambaya ba kawai ya nemi wuri ya zauna tare da faɗin, " kina nan kuwa aka sha rigima da kawu adamu da baba ilerika?".

"Na shigo na same su sunayi ɗazu ai, me ya haɗasu?" .

"Kawu adamu ne yaje ya kwaso mutane wai azo a raba gida a bawa kowa hakkinsa shi Kuma baba ilerika ya dire yace baiga uban da zai raba masa gida ba tunda fili nasa ne kawu Adamu kawai taimakon kuɗin gini ya kawo suka haɗa, dan haka ba mahaifin su bane ya bar gidan bare yaje ya ɗauko mutane yace a raba gado "...........Tsaki taja tare da faɗin, "Aikin kenan me ka tara me aka barma, kaci abincin ne kai?".

"Naci, ke ina kika samo wanna?"......... Ya ƙarashe Yana nuna abincin dake gabansu .

"Jawaad ne mukaje wani wurin abinci shine ya siya ".

"Jawaad? Waye hakan"..........." Mtweee Kai kana da matsala, Jey nake nufi to".

"Auuu dama sunan sa jawaad?". Yayi tambayar tsakanin sa da ALLAH dan shi bai taɓa sanin sunan sa jawaad ba, yasan dai ana ce masa Jey. "To Wai shi Kuma ɗan waye ne na ga dai shi ba ɗan su baba ilerika bane Kuma baiyi kama da matsiyaci ba ballatana nace talauci ne ya kawo shi haya wanna gafalallen gidan, dan ko suturun da yake sawa sun isa biyan kuɗin ɗakuna a gidan nan bama daki ɗaya ba".

"Wai bautar ƙasa yazo yi a garin nan".

"Shi ne Kuma duk ya rasa gidan da zai zauna sai wanna, duk gidajen haya da irin afatmen (Apartment) ɗin dake cikin garin nan ".

"To Sahnish kana iya zuwa ka tambaya in baka yarda ba, ni dai abinda naji kenan". Hushaima ta faɗa yayinda a zuciyar ta kuwa wani tunanin ne ya hauro.

Bari muji a Ina Hushaima ta samu wanna hodar ? In baku manta ba lokacin da su karafiya suka jiwa Sahnish ciwo bayan taje ta gaggaya musu magana ai taje wani kango wurin wasu yan daban to anan ne ta karɓi wanna hodar saboda tsaro, dan tayi tunanin ko su karafiya zasu biyo mata ta bayan gida. Kuu ma kunsan ta ya aka kama su karafiya da wa'annan mugayen kwayoyin bayan ku ma su ko haɗa ido da irin wannan ɗin basu taɓa yi ba, to da sa hannun wa'annan yan daban ne saboda tasan sun taɓa samun matsala a junansu, amma dake duk sallamammu ne sai suka sake dinkewa, to ashe ta ciki na ciki ne da taje ta nemi su sanya mutanan su su ramawa Sahnish sai suka bata wannan shawarar ta zuwa wurin yan sanda sannan suka shirya mata yadda za'a kame su karafiya cikin ruwan sanyi, to da wannan shawarar tayi amfani, kunji yadda akayi . Kar fa kuyi mamakin yadda akayi ta san irin wa'annan manyan yan daban, whl Hushaima duk wasu yan iska dake birnin Nifaz ta sani, yarinya ce fitinanniya fiye da yadda kuke tunani.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______37 & 38



" Ka gudu fa Kenan?" .

"Kamar haka"............. Yana kaiwa nan ya kashe tare da rufe sim ɗin gabaɗaya ya tashi ya zura jallabiya ya fita. Wasu Manyan manyan sojoji mutum shida ya tarar zaune a falon yana fitowa duk suka miqe suna masa Barka da fitowa, shi ma amsa musu yayi cikin natsuwa, wanda hakan yasa na Ƙara murza ido na dan tunani na bangani da kyau ba, takardar dake nannade a hannun ɗaya daga cikin sojojin ya miqa masa, karɓa yayi ya warware ya duba, sai da ya gama karantawa sannan ya ɗago da faɗin, " Wait for me a bit ".

Juyawa yayi ya koma ciki, bayan kamar minti talatin ya fito sanye da maroon suit yayinda ƴar cikin ta kasance white, sosai yayi kyau matuƙa hannunsa riqe da wrist watch ɗin sa yana ɗaurawa, Philip ya yafito da hannu, da sauri ya iso ba tare da ya bar abinda yake ba ya ce , "Philip ka kula da komai kafin na dawo, akwai wani meeting na gaggawa da zan halarta yanzun, duk wasu sauran abubuwa in na dawo ka gabatarmin dasu"............ Yana Kai nan ya fara tafiya duk suka rufa masa baya .

Daga gidan sa basu tsaya ko Ina ba sai wani babban secure conference hall dake cikin headquarter ɗin tasu, sunayin parking jibga jibgan sojojin dake tsaitsaye suka buɗe masa ƙofar ya fito, cikin takun nan nasa na nutsuwa ya nufi cikin conference hall ɗin, tare da jagorancin sojoji uku da Kuma wasu ukun dake take masa baya, already dama shi ake jira dan haka yana tsayawa ƙofar tayi scanning ɗinsa sannan ta buɗe ya shige, su Kuma sojojin sukaja suka tsaya daga waje saboda taro ne na manyan mutane.

Qaton ɗakin taro ne da ya matuƙar tsaruwa gwanin birgewa sai tashin sanyi da kamshi yake wanda ya haɗu da room fresheners da Kuma turarukan manyan mutanen dake zaune a wurin, gashi daga kallon wurin zaka tabbatar akwai tsaro sosai, babban round table ne a tsakiya sai kujerun da suka masa qawanya, kowani kujera da Mic a gabanta tare da tag na suna da kuma rank ɗin mutum.

Direct gaban kujerar da ba kowa ya nufa wadda aka rubuta Agent Amjad Hashim a jikin tag ɗin dake kan table ɗin saitin empty kujerar. Zama yayi sannan ya danyi gyaran murya, yayi sallama kafin ya fara da gaisuwa da Kuma ban haƙuri na ɓata lokutan da yayi. Wani babban mutum ne da a jikin tag ɗin sa naga an rubuta CDS, shi ya amsa da faɗin, " Ba damuwa, in akayi la'akari da rashin sanar ma da ba'ayi ba, sai mutane kawai da muka tura ma. To dama dai dalilin wannan zaman namu na gaggawa ya ta'allaqa ne kan batun wannan gawurtaccen mai safarar mutanan da mukaji shiru tun bayan daka dawo ka shaida mana yadda kukayi da kuma abinda kake shiryawa, baka sake cewa damu komai ba?".

Ɗan sunkuyar da kansa yayi tare da gyara mic ɗin dake gabansa ya ce, "Sir abinda yasa ban sake cewa daku komai ba, muna kan aiki ne, ba wai kai tsaye mukeson kamashi ba, Muna son mu san me ake yi da mutanan? Ina ake kaisu ? Sannan su waye suke sashi? Dan wanna ta'asar bata mutum ɗaya bace, in kukayi duba matsalar tafi shafar nahiyar mu in particular ƙasar Nifaz da ake kan fuskantar barazanar satar mutane. In da mata ne kawai sai a iya tunanin wani abu daban, amma haɗawa ake gabaɗaya harda maza, abu ne me sauƙi mu gano mutanan dake yin wannan aikin, amma fa in an kamasu gobe ma wasu za'a shigo dasu kuma zasu ɗora daga inda wa'ancan ɗin suka tsaya ".

Shuru ɗakin taron ya ɗauka na tsawon wani lokaci kafin IGP ya ce, "Munji dukkan bayanan ka Agent Amjad, kuma mun gamsu amma fa ka sani Al'umma yanzu gabaɗaya sun zuba mana ido kan ganin matakin da za'a ɗauka a kanka, mu dukkan mu mun haɗu munyi tunani kan abinda kayi wanda a lokacin daka aikata baka nemi shawarar kowa ba kayi gaban kanka sai daga baya kuma ka sanar mana, a tunani na hanyar da kabi tayi tsanani da yawa gsky. Taya zaka fara bayyanawa duniya Kanka matsayin international human trafficker dan kawai saboda wani mutum ɗaya, wanda nasan in kayi amfani da baiwar kwakwalwar da ALLAH ya baka zaka iya kama shi ba tare da ka sanya kanka a wannan tsananin ba"............ Saida ya tabbatar da IGP ya Ƙare maganar sa sannan cikin nutsatsiyar muryar sa me cike da confidence da Kuma calmness ya ce, " Amm Sir Al'ameen duk yadda kuke tunanin Shadow Whl ya wuce nan, idan da banyi amfani da sawa an yada wanna zancen ba, bazai nemi aiki dani ba, kuma a farko nayi tunanin idan zanyi aiki dashi zan ganshi ne face to face saidai Abun ba haka yake ba, domin duk cikin masu yin aikin dashi ma ba fa wanda ya taɓa ganin sa kawai aiki suke masa, mutum ne da ya dade yana cin dudduniyar ƙasashen duniya. A binciken da nayi a duk shekara yana sawa ana bashi mutane sama da dubu uku Kuma daga ƙasashe mabanbanta, hakan ya nuna yana da mutane a ko ina kenan ? A wace duniyar yake da har yake tara irin wanna mutanen Kuma gomnatin ƙasar bata ankare dashi ba? Taya ma ake shiga da mutane ba tare da an sani ba ? Har yanzu muna kan nemo wannan amsar ne, sannan matsalata yanzu ai da mutanen gari ne ba da hukuma ko gwamanti ƙasashe ba, dan already ai kunsan daga Babbar headquarter ta Brussel an aikawa kowace gomnatin ƙasa da takarda cewa akan aiki nake, kuma kowacce ƙasa ta sa hannu ta amince mana".

NSA ne ya ce, "Amma Agent Amjad kasan ba Kai bane mutum na farko da ya fara aiki akan shadow ba ko?".

"Yes Sir na sani, manya na da yawa sun sadaukar da rayuwar su wurin farautar shadow amma har sukayi nasu suka gama basu samu ba sai dai ni Kuma..........." Dakatawa yayi tare da sa hannu a aljihun suit ɗin sa ya ɗauko wani card me ɗauke da stamp ɗin kasashe da dama tare da sa hannun sa a kasa ya ɗaura kan table ɗin sannan ya ce, "Wannan shine alqawarin dana ɗauka wa qasashen da abun nan ya shafa cewa zan kawo ƙarshen shadow da duk wani wanda ke bayansa, Kuma ni ne zan miqashi ga hukuma domin a yanke masa hukunci "............ Girgiza Kai NSA yayi tare da faɗin, "Baza ka iya ba Amjad"............." Zan iya sir". Ya amsa yana wani guntun Murmushi cike da confidence.

"Shikenan amma batun jama'ar mu ya za'ayi dasu kenan "............IGP ya sake faɗa.

"Ni daku da Kuma duk wasu jami'ai na ƙasa da na ketare knows who I am, so

27 / 53