Author : Young Writer Category : Tknovels
tukunna ma uwar me kukeyi da ku ka tsallake cikin masarauta kuka wuto nan? Da izinin wa kuka fito?".
"Sarki baya buqatar izini domin shiga faɗarsa, saboda nan ɗin nima fada tace"......... Ya faɗa yana sake ɗaure fuska dukda dama fuskar tasa shi ko da yaushe kamar an aiko masa da saqon mutuwa.
"Whatttt, waye kai? da har zaka sanyawa tosasshiyar ƙwaƙwalwar ka tunanin mallakar wata fada, ko fadar aljanu baka da matsayin mallaka ballatana ta mutane, matsiyaci bawa ɗan baiwa jikan bayi....."....... Ai kafin ta ƙarasa ya kaiwa maqoshin ta wani irin damƙa gabaɗaya ya fita hayyacin sa ya wani irin juyewa, "Wace ke da zaki shigo yankina kice zaki ɗaga min murya har ma ki zage ni, yau sai na kasheki, sai na kasheki naga uban da ya tsaya Miki, in kasheki in kashe banza dabba marar amfani". Ya ƙarashe yana huci.
Qaqari li'iliti Azal ta fara tare da ƙoƙarin ƙwace kanta ta hanyar Amfani da ƙarfin tsafin da suke dashi a jikinsu saboda irin haka amma ina ta ƙasa saboda riqo ne ya mata bana wasa ba, idanun ta duk sun firfito. Masu tsaron ta kuma dukkansu suna daga kan dutsen suna kallo dan basu da izinin gangarawa wannan wurin saboda iya kan dutsen nan iyanan ne iyakar masarautar su, kuma tsallaka shi zai zama taka dokar Masarauta ne, shahada ɗaya daga cikin su yayi zai sauka saidai taku ɗaya yayi Haisha'an ya wurga masa wani kallo ai ba shiri ya juya har yana kokarin suɓutowa .
Cikin shaƙaƙƙiiyar Muryarta dake neman daukewa ta ce, "Sim...Simba"....... wani tsalle Simba yayi ya dira har saida kura ya tashi a wurin tare da yin wani ƙara me sauti ya shiga zagaye su amma ya kasa matsawa kusa da Haisha'an ɗin da ya ɗau alwashin barwa Queen Hirut saqo akan ƴar ta Azal...........
TO FA MEKE FARUWA KUMA? GA FA HAISHA'AN YANA ƘOƘARIN KASHE UWAR MASU GIDA THE GREAT PRINCESS OF SWORD OF FIRE KINGDOM. ME HAISHA'AN KE TAƘAMA DA SHI NE WAI? IYAKAR DA MASARAUTA TA HANA ƘETARAWA SHI YA ƘETARA HAR YANA IKIRARIN FADAR SA CE , LALLE AKWAI TASHIN HANKALI. ANYA BASHI BANE SHADOW KUWA🤔 TO BA RUWANA KAR AJE A SANARWA AGENT AMJAD NACE KU DAI MU HAƊE A STEP 2
---------------------√
Dariya yake irin tasu ta manya kafin ya ce, "Ai ranka ya daɗe yanzu rabi da ƙwatan mutanen dake ƙasar Nifaz Hankalin su kaɗan ne daga mata har maza saboda ƙwayoyin da muka shigo musu dashi sunyi matuqar tasiri dan maganar da nake ma yanzu duk inda muka kaɗasu nan zasubi, babu wasu masu nutsuwar da wai in wani abu ya faru zasuyi zurfin tunani domin gano dalilin assasa shi instead ma sai kaga sun maida hankali kan wani abun da bashi da muhimmanci, kaga ɗalibai suna sha a matsayin maganin da zai sauqaqa musu karatu ta hanyar ɗauke musu gajiya da hana su bacci, ma'aikata ma haka, matasa masu zaman banza tare da yan matan dake cikin damuwa, a ganinsu hanya ce da zata sauqaqa musu basu san kuma mune suke sauqaqawa ba".
Girgiza kai babban mutumin dake zaune yayi kafin ya ce, "Munsa hannu a project ɗin nan na farin da za'a kawo domin a bi gonaki a sake su dan haka suna hanya ya kamata ku shirya da mutanan ku yadda abubuwan zai wakana akwai Budget me ƙarfi da za'a rarraba dan wannan ba irin wancan bane, saboda a yayin da duk amfanin gonakin su ya lalace dole ne zasu haqura su rungumi abincin waje da muhimmanci, dama kuma kaga noma da kiwo na ɗaya daga cikin abinda zai yi wahalar kawarwa amma yanzu da zarar an kawar dasu sauran abubuwan zasu zo da sauki".
"Yaushe kayan zasu iso ?"......... ɗayan ya tambaya. "Nan ba da jimawa ba dama suna jira ne amfanin gona ya gama tsiro wa, amma nasan zasu sake neman mu, so zamu zama cikin tsammanin su".
WANNAN SHI NE ANA WATA GA WATA, SU WAYE WA'ANNAN? DAGA INA SUKE ƘARƁAR WANNAN UMARNIN ? MEYE GOAL ƊIN SU NA YIN HAKAN? WANNAN AIKI NASU ZAI YIWU KO BA ZAI YIWU BA ? IN BAI YIWU BA WAYE ZAI DAKATAR DASU? DAGA INA ZAI FITO? MY PEOPLE HMMM CAKWAKIYAR TANA STEP 2, DAN ZAKU SHA RUWAN MAMAKI, TUNANIN KU ZAI JUYA FROM LEFT TO RIGHT, ABUBUWAN DA BAKUYI ZATO BA ZASU FARU, ZUKATA ZASU RAUNANA, AKWAI DISAPPOINTMENT SOSAI AMMA KUMA ZAKU NISHADANTU ZAKU MA KU ILMANTU KU DAI KU KASANCE TARE DANI.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
SAI MUN HAƊU A STEP 2.
INA ROQON ALLAH YA SADAMU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANNAN WATA NA RAMADANA, YA BAMU IKON AZUMTARSA GABADAYA. RAMADAN KAREEM.