Author : Young Writer Category : Tknovels
call uku ana huɗun aka ɗaga, a hasale ta ce, "Wai ina ka Ajje waya inata neman ka? To ka sani akwai gagarumar matsala, kwan nan yana ƙoƙarin zame mini baragurbin da zai iya hanani rayuwa lpy wanda a ƙarshe in nayi wasa zai iya zama silar ajali na".
"Subahanallahi me kike shirin gayamin ne ya Sheikha ?".......... Saida ta Ƙara taku biyu sannan ta ce, "Shi dai wanna kwan da muka taɓa killacewa da hope ɗin mu kyankyashe abin cikin sa to shi ne kafin mu farga ya zama baragurbi, kuma an samu ƙaramar ƙofa ta ɓule, lalle kuma idan mukayi sake ta zama babba to tabbas warin sa zai iya bugar hancin kowa, wanda hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba kai Ka sani".......... Ajiyar zuciya aka sauqe daga ɗaya bangaren kafin ya ce, "Yanzu me ye kike ganin abun yi?".........."Zan zuba masa kasa".
Da sauri ya ce, "Kul Sheikha karki soma zuba wa baragurbin nan ƙasa, ba shi bane masalaha domin hakan zai janyo zargin dalilin da wanna kwan ya fito baragurbi".
Shuru tayi yayin da ya cigaba da faɗin, "Ki bani lokaci zan san abunyi, Amma karki bari ruwan ya tsiyaye gabaɗaya. Saboda yanzu muna cikin wani tashin hankali ne da alhinin rashin Sheikha Yassar saisa kikaga kin min missed calls ban ansa ba ina cikin mutane ne".
Cikin wani sabon tashin hankalin da ya gaza ɓoyuwa akan fuskarta ta ce, "Kace Sheikh yassar ya mutu?".
"Kin dai san ba zan Miki ƙarya ba ko, na ma ɗauka kin samu labari ai shiyasa kike kirana, domin ko karɓo gawar ba'ayi ba yanzu daga asibiti, dan baifi mintuna ba da rasuwar"......... Sauke wayar tayi daga kunnen ta ba tare data kashe ba, "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un yassar ya mutu hakan na nufin ba wani shaqiqin me martaba kenan da zai iya gadar sa face ɗaya daga cikin yayansa ukun Nan. Inaa tunda har ni dana kasance mace ta farko ban bawa Sultan magaji ba to suma ba mai gada a cikin ya'yan su whl"..........Ta ƙarashe tana wucewa ta buɗe sip ta ɗauko ƙayatacciyar alkyabbarta sannan ta kira khadimarta ta sanar mata zasu fita a shirya mata mota zuwa bangaren Anjani (Mahaifiyar su Sultan).
Gyara fuskarta tayi sannan ta sanya Alkyabbarta ta zura takalminta ta fita, mutum huɗu khadimai ta samu suna jiran ta tana fitowa suka fara mata kirari ba tare data saurare su ba ta wuce suka rufa mata baya suna cigaba da mata kirarin har waje inda aka shirya mata mota uku, ta tsakiyar aka buɗe mata ta shige saura khadiman suka shiga sauran motoci biyun, a hankali motocin suka fice daga part ɗin. Tafiyar minti goma ya kaisu bangaren Anjani dake cike da jama'a alamar mutuwar Sheikh yassar ɗin ta fara zagaya masarautar, ta ko Ina ka kalla dogaran su ne tare da khadimai suke ta Kai kawo.
_____________Ita kuwa ummu lokacin da labarin mutuwar yassar ya risketa kuka ta fashe dashi sosai na tausayin kanta, Albeena ce ta shigo ɗakin ganin ummu na kuka yasa ta ƙarasa jiki a sanyaye ta zauna wurin ƙafarta tana kallon ta ba tare da tace komai ba, tissue ummu taja ta goge fuskarta tare da faɗin, "Albee tashi kije ki Duba min in su Rouslan basu Kai ga fita ba ki turomin su"......... da "To". ta amsa sannan ta tashi ta fita dan zuwa aikar ummu.
Tana zuwa ƙofar ɗakin suna fitowa cikin shiga iri ɗaya fitted white Thobe da royal Arab ghutra da suka ɗaura a kansu. Ɗan rikicewa Albeena tayi ta zuba musu ido saboda ta ƙasa banbance Rouslan da Reeslan ɗin. "Kee miye kika wani zuba mana ido, Me ma ya kawoki nan?" .......... Sai lokacin ta gane Reeslan ɗin, tunda dama shi masifar sa ce take sa a gane shi, ɗan ja baya tayi a tsorace ta ce, "Ummu ce tace a kira ku dama".
"To tafi mana ko sai kin samu gaba ne uwar mu"......... Da sauri sauri gudu gudu ta juya ta bar wurin, Rouslan ne ya kalleshi da faɗin, "Bakyau fa, duk kabi ka firgita yara kasa sai tsoron ka suke ji".
"Rabu dasu, na munafurci ne ai jiya ina jinsu suna gulmata itada ƙawayenta kawai dai dan Ina sauri ne da sai na zane musu uwar jiki"......... Rouslan bai sake bi ta kan zancen ba sai cewa da yayi, "Ba fa tashi sama zamuyi ba".
"To tsaya kana lakwai lakwai tu kasan dai in Akazo sallar gawar, Abbu bai gan mu ba ransa zai ɓace"........... Ɗan sauri Rouslan ɗin ya Ƙara Amma duk da haka ya kasa kamo Reeslan Saboda shi takun jinin saraki yakeyi cike da nuna isa da mulki shi kuma Ruslan takun zakuna yakeyi cike da ƙarsashi da kuma zafin nama. A haka suka ƙarasa ɗakin Ummu, knocking sukayi sannan suka jira ta basu izinin shiga. Bakinsu ɗauke da sallama suka sa kai. "Ummu barka da rana "......... Rouslan ya faɗa yana zama . "Wurin janaizar zaku?"......... ta tambaya tana kallon Reeslan da yayi ƙasa da Kai kamar yasan shi take kallo.
Rouslan ya amsa da , "Eh ummu, whl Ummu jikina yayi sanyi da mutuwar Ammu, mutumin kirki ni whl Abbu nake tausayawa nasan sai yaji mutuwar fiye da kowa saboda duk cikin yan uwan da suke uwa ɗaya uba ɗaya su biyu suka rage maza".
"Ya za'ayi Rouslan, ɗai ɗaya mukazo Kuma ɗai ɗaya zamu koma sai dai muce ALLAH yasa mu cika da kyau da Imani wanda suka rigamu Kuma ALLAH yaji ƙansu".
"Ummu kuka kikayi ne sosai haka".......... Reeslan da ya saci kallon Ummu ya faɗa da mamaki dan yasan Ummu akwai dakiya da ƙarfin zuciya. Shi ma Rouslan Saida Reeslan ya faɗa ya lura da idanun ta da suka ɗan tasa yana jiran jin amsar da zata bawa Reeslan ɗin .
"Reeslan! Ka faɗamin gsky dan ALLAH meke faruwa dakai?".......... Kallon juna sukayi shi da Rouslan kafin Rouslan ɗin ya ce, " Ummu lpy Lau yake me kika gani?"......... "Kai rufe min baki Kai na tambaya ne?".......... Sunkuyar da Kai Rouslan yayi yana satar kallon Reeslan ɗin Wanda yayi shuru sai murza yatsun hannuwansa yake. " Kai nake tambaya ka min shuru?".
Ɗagowa yayi kamar zaiyi magana sai Kuma ya sake juyawa ya kalli Rouslan, tashi yayi da sauri ya fita, shi ma Rouslan ɗin tashi yayi ya mara masa baya suka bar Ummu sake da baki cikin ɗaurewar kai.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
___________________________________
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______ 66 & 67
Ɗakin sirrinsa suka shige gabaɗayansu ya kukkuna komai sannan ya ɗauko Sectra tiger ɗinsu da suke communicating da headquarter ɗinsu dake can Brussel ɗin ta ciki, yayi connecting da VPN ɗinsu wato virtual private network, sannan ya danna kiran kai tsaye. Bayan sir Richard ya ɗaga Amjad ya saita muryarsa da faɗin. "Hello good evening sir".......... " Evening Agent Amjad, how are you?".
"Good sir, dama na kiraka ne Kan batun aikin da muke yi akan Shadow.........." Kwashe komai yayi ya faɗa masa duk yadda ake ciki. Cike da ƙarfin guiwa Sir Richard ya ce, "Banajin duk wani aiki da za'a danqa shi a hannun ka Agent Amjad, Dan haka kayi ko ma miye, kawai dai in kuna da buqatar taimakon mu to akoda yaushe kuyi gaggawar sanar damu, dan haka all the best".
"Thank you sir".........Ya faɗa a sanyaye, tabbas dole su dage wurin ganin sun gano mutumin nan. Sir Richard na kashe waya ya kalle su da faɗin, "Bamu da time, muje kawai"....... Ya ƙarashe yana fita suka biyoshi a baya shi kuma yayi latse latsen sa ƙofar ta rufe.
Motar sa Jey ya shiga, shi ma Amjad ya shiga tasa shi da Ace, Kiara da ashley suka shiga mota ɗaya tare da Nazbeer da yace yayi driving ɗinsu, sauran masu tsaron da aka bawa Amjad ɗin suka shiga sauran motocin sannan suka fice daga gidan suka nufi state headquarter ɗin tasu da aka killace mutanan acan, suna zuwa suka samu Philip da sauran jami'ai suna ta aikin. A wani babban ɗaki me kama da office suka yada zango sannan ya ce da Philip da ya taryosu. "Philip kawo mutumin da Jey ya kawo, i can't wait kuzo saisa muka biyo sawu".........."Okay boss"....... Philip ya faɗa tare da juyawa ya fita, wayar Kiara ce tayi Ƙara hakan yasa ta ɗaga Kai taga duk sun zubo mata ido sai ta kashe kiran, sake Kira akayi ganin tana ƙoƙarin sake kashewa yasa Amjad faɗin, "Pick your call mana"......... Tashi tayi da faɗin, "Excuse please". Ta ƙarashe tana fita daga office ɗin, ƙasa ƙasa Ace ya ce da Ashley, "Kufa me da hankali ba soyayya mukazo yi ba"........"To ina ruwanka?"....... ta faɗa tana Hararar sa. "ALLAH yasa wani ya kiraki kiga yadda za'ayi"....... zata ƙara magana Philip ya shigo da mutumin sai raba ido yake, Tsakiyar office ɗin suka durƙusar dashi, daga shi sai three quarter, wasu yan na'urori Philip ya miqawa Amjad da faɗin, " Wa'annan sun kammala, sune Wanda za'a dinga jin motsin su wanna Kuma a system za'a sanya dan a dinga ganin inda suka nufa".
"Yanzu wanna an saka masa tracker da soundtrack ɗin?".......... Ace ya tambaya. Kafin Philip ya bada amsa Amjad ya ce, "Yes ".
" How?"........."Ohh Ace karka ban kunya mana kaifa kwararren jami'i ne "......... Shuru Ace yayi ya zubawa mutumin ido can Kuma ya ce, "Yes yes gasu nan a fatar kansa"......... Ya faɗa Yana nuna kan mutumin dake nan tankwal kamar ba'a taɓa halittar gashi a fatar kan ba dan har wani kyalli take, sai dai komin Ƙura idonka baka isa kace akwai wani abu a gun ba bayan halittar kan mutum saisu da suka haddace sa ido.
"Jey ɗauki system ɗin nan ka je ka yi connecting a waje tare da Bluetooth ɗin, sannan ka sanarmin results in komai yayi"........ Amjad ya faɗa Yana maqala kunne ɗaya sannan ya miqa masa system ɗin dake gaban sa, karɓa Jey yayi ya fita, can kan motar sa yaje ya ɗaura system ɗin tare da sanya wani abu kamar memory sannan ya maqala ɗayan abun a kunnensa me kamar Bluetooth, sai ga su Amjad sun bayyana a cikin system ɗin tar haka Kuma yana jin muryoyin su da abinda suke faɗa dan haka ya ce, "komai yayi"......... Murmushin jin daɗi Amjad yayi kafin ya kalli Philip ya ce, "Aiki yayi kyau, ka kawo mana sauran na'urorin, ya kamata each and everyone of us ya samu na'urar sauraron sauti da kuma ta GPS da video feed, sannan in Kun gama a cikin daren ku shirya ku nufi iyakar ƙasar nan karku bari aga fuskar ku kaji ko".
"Yes boss"....... Philip ya amsa, miqewa Ace yayi da nufin ƙarasawa gaban table ɗin Amjad saidai taku ɗaya yayi ya riqe kansa kafin su ankara sai ganin sa sukayi a ƙasa . " Ace!, ace!"...... Ash ta fara Kiran sunan sa, da hanzari duk sukayi kansa ita da Philip shi ma Amjad tasowa yayi yana faɗin, "Ace ya baka da lpy ne?"........ Tari ya fara tare da qaqarin amai kamar zai fitar da abinda ke cikinsa Amma ko yawu baya fita a bakin nasa, a hankali idanun sa ke juyewa bakin na barin cikin su, jijjiga shi Amjad ya farayi Yana Kiran sunan sa, dip sukaji yayi da sauri ya ce, "Philip get the cars, kiramun Widad" .......... Kafin ya rufe bakinsa Jey ya shigo, da sauri ya ƙaraso wurin su ganin abinda ke faruwa, yayinda Philip ya fita domin ya sanar da su Kamal su matso da mota.
Da taimakon su akasa Ace dake sanqame kamar gawa a mota. "Philip kayi handling sauran abubuwan karka fasa komai Kuma ka tabbatar komai ya tafi daidai kar a samu matsala".......... Ya faɗa yana zagayawa ya shiga motar da akasa Ace ɗin a ciki yayinda Jey ya shiga gaba ya bar motar sa a can, su Ash Kuma suka shiga motar da suka zo a ciki dan already ta samu Kiara ne a zaune ciki tana waya Kuma da alama da gida take wayar saidai kamar a tsorace take wayar.
Da mahaukacin gudu motocin suka fita daga harabar State headquarter ɗin.
-----------------√
SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥
Jin shurun yayi yawa yasa masu gadin shiga guardroom ɗin tare da amfani da touch light ɗin su me haske sosai, a nan suka gansu yashe a ƙasa kamar gawa ga Haisha'an zaune ya kunce daga sarkar da suka masa, duk ya jigata sosai dan jikinsa ko ina jini ne, basu bi ta kansa ba suka shiga ciccibar waɗanda suka shigo dashi a rikice suka fita dasu, tsabar rikicewa ko rufe guardroom ɗin ba suyi ba, tashi yayi tare da goge jinin dake sauqa gefen idon sa zuwa gefen bakin sa, rarrafawa yayi ya fita daƙyar, Yana fitowa ya zube a bakin wurin yana fitar da numfashin wahala.
Omaine dake ta Kai kawo a ƙofar wurin kamar zai yi ihu Ba abinda yake in banda addu'a a zuciyar sa na ALLAH ya kuɓutar da Haisha'an. Gani yayi masu gadin sunzo sun wuce da wanna fadawan akan kafaɗar su, da gudu ya shige wurin, nan ya hango Haisha'an ɗin zube a ƙasa rigar jikinsa duk ta farfashe ga jini dake zuba ta inda suka jijji masa ciwo, "Haisha'an!, Haisha'an! "........ Ɗagowa yayi ya kalleshi garara sai Kuma ya maida idon sa ya rufe, kama shi yayi da kyar ya miqar dashi tare da ratayo da hannunsa ɗaya a kafaɗar sa suka fara tafiya zuwa ɓangaren su.
Suna shiga ɗakin su ya zube a bakin ƙofar, da hanzari Omaine ya wuce toilet ya samo ruwan ɗumi da towel ya dawo inda Haisha'an ɗin yake zube kamar kayan wanki, yagargiyar rigar ya zare masa sannan ya shiga goge masa jikin nasa, dukda irin tsananin azabar dake ratsa kwakwalwar sa baiko motsa ba har Omaine ya gama da bayan ya mirgina shi ya fara goge masa kan kirjin sa zuwa ciki idanun sa fall da hawaye sai sannu da yake ta faman jera masa, Dan yasan akwai azaba kawai dauriya yake, haka ya gama sannan ya maida komai toilet ɗin ya zo ya taimaka ya ɗaurashi kan tsohon gadon nasu. Duk shekara Queen Hirut take canza kayayyakin masarautar Amma banda bangaren mazan, wa'annan su saidai a basu kuncen da aka fidda daga bangaren Matan.
Buɗe idanunsa da suka ɗan tasa yayi ya kalli omaine ɗin da ya miqe da faɗin, "Zanje na samo ma magani ba zan daɗe ba yanzu zan dawo"....... Yana kaiwa nan ya juya ya fice da sauri.
Har ya fara bacci lokacin da omaine ya shigo hannunsa riqe da wani dan qoqo, wurin sa ya nufa ya hau kan gadon sannan ya fara shafa masa wani koren magani dake cikin qoqon, yatsina fuska yayi amma bai ce komi ba.
"Sorry ɗan uwa in Sha ALLAH zai daina zafi"........ Haka ya dinga bi yana shafa masa a duk inda yaji ciwo har ya gama shafe masa a fuska, kirji da ciki sannan ya ce, "Taimaka ka zauna in shafa ma a bayan"....... Ba musu ya tashi ya zauna yana yatsina fuska alamar jikin ya masa tsami sosai, cikin tausayawa omaine ya sake cewa, "Sannu. Dan ALLAH Bros, ka haƙura ka bar mutanen nan da abinda suka zaɓawa kansu, kowa ai kabarin sa daban ba dole bane saisun yarda da gaskiyar da kake ƙoƙarin fahimtar dasu".
A Ɗan jigace ya ce, "Ba fa ina so su yarda bane Omaine wannan ya rage nasu amma Ni dai gsky ce bazan fasa faɗarta ba, Ka sani tunda har suka kashe mahaifi na saboda kawai yana addinin Musulunci a ɓoye to whl Ni ba zan ɓoye ba kuma Bazan fasa faɗa mata Gsky ba da ita da mutanan nata, kuma a gaban kowa zanyi sallah zanyi azumi in tana da iko a hannun ta Nima ta kasheni"......... Ɗan shiru yayi kafin ya cigaba, "Ka sani Omaine a duk randa Queen Hirut tasan da yawa daga cikin mazan masarautar ta sun musulunta ciki harda mijin ta toh fa kisan gilla zata musu kamar yadda suka wa mahaifi na, shin a haka kake so mu cigaba da rayuwa? to ba zai yiwu ba ".
Shuru omaine yayi cikin jimami dan yasan tabbas abinda Haisha'an ɗin ya faɗa gsky ne, dan sun karɓi shahada a wurin Haisha'an a ɓoye ne kuma duk ranar da Queen Hirut ta sani lalle yasan kashe su zatayi. Shuru yayi yana cigaba da tunani har ya gama shafa masa a bayan sannan ya ce, "Haisha'an kasan miye tunani na?"........ Girgiza masa Kai yayi alamar a'a sai ka fada. "Ka ajje batun yin gaba da gaba da Queen Hirut har sai munyi yawan