BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   7 / 53

18K to 21K   out of 156.9K words

"Airport muka nufa"............"okay boss"......... Kamal ya Amsa.




--------------------√




Ba tare da wani tsoro ko fargaba ba a tare da ita ta dumfari majalisar su karafiya inda ta hango su suna ta yan zuqe zuqen su. Tana zuwa ta fisge wiwin dake maqale a gefen kunnen jagwa tana ci da wuta, wurgarwa tayi a kasa tare da tula mata ƙasa da kafa ta mirtsiketa sannan ta ɗago tana huci a fusace ta ce, " Wani ƙaramin tataccen ɗan iska ne a cikin ku ya daki Sahnish?"............ Ta ƙarashe tana wani mutsitsike ido. Kana kallon ta kasan bata san wani abu wai shi tsoro ba.

"Hahaha". Suka kwashe da wata irin dariya irin ta basawa kafin ɗaya daga cikin su wanda ke sake naɗa musu rizla ya ce, "Dukkan mu ne amma ni na jagoranci tawagar, ya akwai Magana ne?".

"Maganganu ma, ashe ƙaryar iskanci kuke, ina cewa ni kuke bi kuɗi, to ku tare ni mana tunda dani ta haɗoku bada shi ba, meysa zaku sanya shi cikin faɗan da ba nasa ba, to whl zaku san kunyi da yar halak sai na baku mamaki".

"Keeee bar nan kafin na Miki ɓalli ɓalli anan wurin billahillazi ".......... Karafiya ya faɗa yana miqewa riqe da wuqa a hannun sa sai langi yake shi kaɗai kamar igiyar shanya. "In naki fa ko zaka matsar Dani ne".........Ta faɗa tana juya masa manyan idanuwan nan nata masu rikitarwa. Yunkorowa yayi da faɗin, "kwarankwatsa zan bazar dake a wurin nan in bi ta Kan ruwan cikin ki in wuce".

Gyara tsayuwa tayi da faɗin, " In Ka fasa Ka raina iyayen da suka haifeka banza wawa ragowar hayaki, kuma na rantse sai kunsan dani kuke wasan, kun sanni sarai ai kunsan hali na"......... Wata zaftareriyar wuqa jagwa ya ɗauko a can gefen su tare da sara ta akan ƙasa ya ce, "ware!".......... girgiza kanta tayi da faɗin, "ALLAH ya ragewa Aya zaqin ta ba'a shirye na fito ba, amma da kai kaii dai whl baka isa ɗaga min wuqa ba, amma ku jira juyowa ta"..........Ta ƙarashe tana nuna su da yatsa sannan ta juya ta bar wurin .

"Yihuuu wa yace damu bamu ba muma muce dashi bashi ba, har akwai mai ɗaga mana yatsa a garin nan bamu gille hannun ba gabaɗaya"..........Ya ƙarashe cike da kuri. Ɗaya abokin nasu ne ya taso shi ma kamar zai kifa ya dafa kirjin jagwa ɗin da faɗin, "kwanta kwanta naman kaji, a huce haka"......... ƙoƙarin wucewa ya fara yana faɗin, "ka barni in je in qaddamar Mata zandam, mu da mukeyin gaba da gaba da maza a dawa ma bare wannan ƙaramar kwaron".

"Huce haka, barta zamuyi maganin ta kai kasan ko yanzu mun zabure ta, dan ba ƙaramar illa mukayiwa wancan yaron ba, dan haka rabu da ita in kere na yawo zabo na yawo........" Ya ƙarashe yana jan fito. Ƙwafa jagwa kana ya ce, "Amma ba dan ka hanani binta ba ko, da sai an kasa gane kamannin ta"......... Ya ƙarashe yana komawa gefen karafiya ya zauna tare da zarar kara ɗaya ya bata wuta.

Hushaima kuwa daga wurin su karafiya ba gida ta koma ba wani wuri ta nufa, sai da tayi tafiya ta tsawon minti talatin da kafarta dukda uban ranar da akeyi amma sam bataji Saboda murɗaddiyar zuciya irinta ta. Tana zuwa ta faɗa wani uncompleted building kamar wadda aka jefo, mamaki ne ya kume ni ganin wasu irin riƙaƙƙun yan daba na gaske masu ji da tashen tsageranci da tashanci, tana zuwa ta wuce ta tsakiyar su ta ɗale kan wani bulo ta zauna tana goge gumin fuskarta da bakin gyalenta.

Sai da ta ɗau tsawon minti goma a ciki sannan ta fito ta wuce gida. Tana shiga Sahnish dake kwance yana dakon jiranta, ya fara kokarin miqewa, da sauri ta ƙarasa ta taimaka masa ya zauna, cikin damuwa da kuma takaici ta ce, " Tashi Ka daure muje asibiti ".

Wani yawu me zafi ya haɗiye saboda ciwon da maqogoron sa ke masa kafin ya ce, "Baza muje asibiti ba chemist ma yayi".

"Sahnish raunin dake jikin Ka yafi ƙarfin chemist, Ka daure Ka tashi mu tafi kaji".........ta sake faɗa tana kallon sa cike da tausayawa.

"Asibiti yanzu in munje ma zaman jiran layi zamuyi, zaifi kyautuwa muje chemist ɗin dai ".

"Kai daina min musu Sahnish muna Ƙara ɓata lokaci ne ni inada abunyi, Ka tashi muje mu dawo kuma ai ba asibitin gomnati zamuje ba".

Waro idanunsa yayi kana ya buɗe baki zaiyi magana ta ce, "kar fa ka ƙara ce min komai, a tafashe nake bana so na sauke haushi na a kanka".........Bai sake yunqurin cewa komai ba ya fara ƙoƙarin miqewa ta taimaka masa ya miqe, a haka suka fito, a soron ƙofar gidan ta barshi taje ta ɗauko abun hawa, sannan suka taimaka masa ita da me tuk tuk ɗin ya shiga suka tafi.

Kamar yadda ta fada private hospital suka nufa, da taimakon me tuk tuk suka shigar dashi ciki sannan ta sallameshi ya tafi, file taje ta Buɗe masa sannan aka musu iso zuwa ɗakin likitan, bayan ya duba shi ya rubuta masa magunguna da allurar tetanus, sannan akayi dressing raunikan, aka ɗaura kashin hannun nasa da ya goce. Kallon ta likitan yayi bayan an gama ya ce, "Hatsari ya samu ne ?".

"Yan iskan unguwa ne kawai"........Ta bashi amsa dukkan hankalin ta na Kan duk wani motsi na Sahnish ɗin.

"Ashsha haka suke whl duk sunbi sun addabi mutane, ka yi magana su bi dare su datsaka kamar rake, ALLAH dai ya kare gaba. Amma saisa ake so mutum ya guji abinda zai haɗashi dasu dan in suka bugun nan cinnaku ne basu san na gida ba, kallo wannan laifi yake zama a wurin su.

"An gama ne Dr zamu iya tafiya?"........Ta tambaya dan yanda takeji zuciyarta na Ƙara hauhawa a duk kallon da zatayiwa Sahnish ɗin, shi kansa Dr ɗin maganganunsa ƙara ɓata mata rai suke, kamar ta rufe shi da duka.

"Eh zaku iya tafiya, Amma zaki dinga kawo Shi ana dressing raunikan, ga wanna in kin fita pharmacy saiki biya kuɗin ki karbi magungunan".

Karɓar takardar tayi sannan ta ƙarasa ta taimaka masa ya tashi suka fito. A reception ta zaunar dashi sannan ta wuce pharmacy tayi payment, ta fita ta Nemo tuk tuk ta dawo ta taimaka masa suka fita, tsayawa sukayi suka dauki Shazeen daga makaranta sannan suka wuce gida gabaɗaya.

Ko da suka isa gida ɗaki ta kaishi ya kwanta domin ya samu yayi bacci ya huta.

Kitchen ta shiga ta ƙarasa abincin data fara kafin shigowar Sahnish sannan ta zubawa Shazeen ta gyara gidan, dan ita ko yunwar ma bataji abinda ya dame ta ma ya ishe ta, ga yan kuɗaɗen da suka rage musu ba yawa, ga kuma jinyar Sahnish, aikin data samu kuma ba wai daga zuwa za'a fara biyanta ba dole sai tayi aiki zuwa ƙarshen wata. Wunin ranar sukuku tayi Shi har dare saida Sahnish ya tashi ne ma ta ga jikin nasa sannan ta samu ta sawa cikin ta wani abu shi ma dan Sahnish ɗin ya dame ta ne.

Yana zaune shi da shazeen a ɗakin sa Hushaima ta shigo, wuri ta nema ta zauna tare da faɗin , "Shazeen zo ki cikemin takardar nan".........Ta ƙarashe tana miqa mata Form ɗin data taho dashi tare da pen.

"Takardar miye wannan ɗin ?".......... Sahnish ya tambaya yana binta da kallo.

"Form ne na aikin da na samu a wani wurin saloon starlight beauty co., To da sukace gobe ma nazo na fara amma kuma tunda naga baka da lpy zan bari ka ɗan ji sauqi tukunna ".

Cikin farin ciki ya ce, "Kai alhamdulillah ALLAH abun godia. Kina ji baza ki fasa zuwa gobe ba, kije aikin ki dan bana so azo a samu matsala daga farawa kuma suzo su canza shawara. Kinsan a yanzu aikin yana da matukar muhimmanci a yanayin da muke ciki".

Bata bashi amsa ba har sai da ta gama faɗawa Shazeen abubuwan da zata cike dasu sannan ta ce, "to wai taya ma zan tafi na Barka kai kaɗai a gida alhalin baka jin daɗi. Zan je ɗai na kai musu Form ɗin sai na faɗa musu uzuri na yaso ko jibi in jikin naka ya sake yin kwari sai na fara zuwa".

"Wai jikina yayi kwari sai kace wani jariri, dan ALLAH ki bar wanna zancen kawai da safe ki shirya ki tafi".

"ALLAH ya kai mu, Shazeen miqo min ledar magungunan sa da pure water can na bashi mu tashi muje mu kwanta dare yayi kema Karki kasa tashi makaranta ".........tashi Shazeen tayi ta ɗauko ruwan da magungunan ta bata. Sai da Hushaima ta tabbatar ya sha magungunan sa sannan suka masa saida safe suka fita.

Washe gari da sassafe ta tashi kamar yadda ta saba ta gama duk abinda zatayi ta shirya Shazeen, suka yi kalaci a tare sannan suka fita gabaɗayansu suka kullo gidan. Sai da suka fara sauke Shazeen a makaranta sannan suka wuce asibiti aka masa dressing ciwukan, bayan sun fito Sahnish ya ce, "Mu biya a saukeki sai a wuce dani gida"........."Ah ah muje dai naga ka shiga gidan sai ni a juyo dani".

"Ke fa kullum kike maidani kamar wani Yaro, sannan kuma kizo kina faɗan cewa in zama jajirtacce"..........."To ai baka nunamin kai ɗin jajirtaccen bane ballantana na sake ma ragamar komai".

"To ai ke kika hanani zama jajirtaccen"........ Shiru ta masa shi kuma ya cewa mai tuk tuk ɗin ya kaisu starlight beauty co.

Basu ƙara magana ba har mai tuktuk ya faka ƙofar wurin Sahnish ya ce, "To sauka kije ALLAH ya bada Sa'a, amma tsaya wa zai ɗauko Shazeen a makaranta"........ Dan jim tayi kafin ta ce, "zan cigaba da daukota zuwa lokacin da zakaji sauki sai Ka karba".

"To islamiyyar fa?"............"Eh to wannan dai gsky saidai ka kira malamin nasu ka sanar masa uzurinka saboda kaga bazai yiwu na bar wurin aikin har so biyu ba".

"Shikenan to ba damuwa zan kirashi. Sai kin dawo"........ɗaga masa hannu tayi tana faɗin, "ka kula da kanka ". Sannan ta juya ta shige, shi kuma ya bawa mai tuktuk ɗin umarnin tafiya.

Yau ma Jumayma ta tarar sai cleaners dake ta aikin tsaftace wurin, "barkan ki"........Hushaima ta faɗa tana zaro Form ɗin a jaka ta tura mata gabanta. Kallon tara saura kwata jumayma tai Mata sannan ta ɗauke Kai, taɓe baki Hushaima tayi sannan ta wuce ta nemi wuri ta zauna. Shuru shuru har 10 sai sauran ma'aikatan dake ta shigowa, tashi tayi ta koma wurinta tare da faɗin, "sannu"........."Yauwa"........ ta amsa tana yatsina kamar taga kashi. "Hajiya fa?"........."Bata zo ba"..........."Jiya bata Miki bayani bane ".........."Wani irin bayani?" ........."Na ɓangaren da zan dinga aikin mana".

Sake ƙyabe fuska tayi sannan ta ce, " ki koma ki zauna sai ta shigo".........Bata sake cewa komai ba dan bata so a ja zancen da zai Kai matsayin da matar nan zata Kai ta bango dan tsab zata iya kwaɓe musu tun ba'a yi nisa ba. Kusan minti talatin ta ƙara sannan ta kirata. Kamar baza taje ba saboda a wulaƙance tayi kiran amma ta taushi zuciyarta ta tashi ta ƙarasa wurin nata. "Muje a nuna Miki aikin da zaki dingayi"..........Binta tayi a baya suka shige ciki, suna shiga ta ce, "Bunayna ga sabuwar ma'aikaciya nan ku nuna mata yadda aikin yake".........Da " to". Bunayna ta amsa sannan Jumayma ta juya ta fita. "Bismillah ƙaraso".......Bunaynan ta faɗa tana Murmushi, dan ita sam bata da matsala haka ma sauran abokan aikin nata, hakan yasa Hushaima bata samu wata matsala ba wurin koyon abubuwan da suke nuna mata.

Zuwa rana suka fara attending customers, sosai wurin ke cika da manyan hajiyoyi da ya'yansu, hakan yasa ta zage suke ta jibgar aiki kamar jakai, har zuwa lokacin da hajiya ta iso nan tasa aka kirata bayan sun gaisa ta ce, "Ina fatan dai ka gane komai ai?"........" Eh hajiya ai ba wahala ma aikin".

"To yayi kyau , akwai kayan aiki in ka tashi yau zasu baka, shi Ake sawa, sannan albashin ka dubu Arba'in monthly, cox ni kaga ma bani da buqatar Ƙarin maaikata kawai dai dan na tausaya Maka ne".

"Ba damuwa hajiya a hakan ma nagode, saidai ina da ɗan uzuri anjima zanje ɗauko yarinya a makaranta, dama qanina ne zai dinga ɗauko ta to kuma baijin dadi yanzun"........."Ba damuwa, amma Karta shiga lokacin aiki da yawa".

"In sha allah ".......... Ta faɗa tana tashi ta koma wurin aikin su, wurin jakarta ta nufa ta sanya wayar ta a ciki sannan ta koma ta cigaba da aikin da takeyi kafin hajiya ta kirata ta bari ta fita.

"Kam burauban can, Ni za'a yashe, to whl ko sama da ƙasa zata haɗu bazan yadda ba sai an fito min da dukiya ta".

Da mamaki duk ma'aikatan dake wurin suka kalli juna da faɗin , " Ai kuwa hajiya wurin nan wani abu bai taɓa ɓata ba bare kuma sata ki dai duba ko kin barshi a mota, amma tabbas ba wanda zai dauka Miki wani abu a nan".

Wata budurwa ce ta ce," To wai me aka sace Mata ne ma?"

"Kudaɗe na gabaɗaya babu sannan akwai zobe da bangles ɗina na gold da na cire nasa a jaka yanzu saboda zaa yanke min farce, amma yanzu na duba babu su ba alamar su, ƙafa ne dasu da zasu fita da kansu in ba ɗauka akayi ba".

ɗaya daga cikin ma'aikatan ce taje ta sanar da hajiya abinda ke faruwa tana zuwa matar ta ce, " Gwara da ALLAH ya kawoki, sata suka min kuma whl tun muna shaida juna kisa yaranki su fitomin da abubuwana".

"Ya hakuri Hajiya mu bi a sannu, kaya basa ɓata anan wurin amma bincike bai bar komai ba"....... Ta ƙarashe tana kallon su tare da tambayar, "iya Ku kenan ko akwai Wadda ta fita kafin nazo?".

"Iya mu kenan sai wanna yarinyar data fita ta dawo, sai kuma ma'aikaciyar dataje ta sanar Miki yanzu"......... Ta karashe tana nuna Hushaima da kuma Elijah .

"Ita wannan ba wani wuri taje ba sabuwar ma'aikaciya ce ma ni nasa aka kirata Amma tunda abun yazo da haka bari ayi caje kawai, barin kira Jumayma "......... Ta faɗa tana dialing contact din Jumayma, sunkuyar da Kai Hushaima tayi tana cigaba da abinda take.

Jumayma ce tazo ta caje kowa, saida ta gama ta ce...............



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️


___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._


@wattpadd sultywrites22


STEP 1


PAGE _______9 & 10



Jumayma ce tazo ta caje kowa, saida ta gama ta ce, "Hajiya baa samu komai a jikin su ba".

"Kowa ya miqo jakunkunan su ki zazzage anan"......... Hajiya ta sake faɗa.

Ba musu kowa ya jeho jakar sa aka fara zazzagewa ana zuwa kan jakar wannan budurwa data tambayi me aka sata sai ga bangles da zobe sun faɗo, salati duk ma'aikatan suka sa banda Jumayma data so a jakar Hushaima aka samu.

Karɓa matar tayi sannan ta ce, "Akwai kuɗaɗen Ku sake dubawa ".........sake zazzagewa akayi Amma ba'a samu komai ba.

"Billahillazi tunda aka samu wa annan a jakar ta, to kuɗin nan yana wurin ta dan wuri ɗaya na sa su".

Rantsuwa ta fara ita bata san ya akayi wa'annan kayan suka shiga jakarta ba Amma ba wanda ya saurareta sai hajiya data tambayi matar, "kuɗin naki har nawa ne?".

"Zasu Kai dubu ɗari da saba'in, kuma whl naira ta baza tayi ciwon Kai ba dan ni da Ka min sata gwara Ka tambayeni na baka, dan haka ta fito min da kuɗi na ko na haɗata da Wanda zasu karɓar min"......... Ta karashe cikin daga murya .

Hushaima na gama aikin tsifar da takeyiwa wata mata ta ƙarasa ta dauki jakarta tare da gyalen ta sannan ta ce , " Hajiya zanje na dawo".

"To adawo lpy, Amma karki Daɗe fa na faɗa miki".

"Toh"........ Tace, tana ɗagowa idanunta ya shige cikin na wanna budurwar, kallon Kar ta san Kar sukawa juna kafin Hushaima ta juya ta fice.

Abinda ya faru kuwa shine a lokacin da Hushaima ta dawo daga kiran Hajiya idonta ya sauka kan budurwar nan dake zura mata wani abu a jaka ba tare da kowa ya lura ba, tsayawa tayi saida ta jira ta gama sakawa sannan ta shigo ɗauke Kai tayi kamar bata gani ba ta dauki jakar ta zura wayarta sannan ta koma bakin aikinta, saida ta fuskanci hankali baya kanta sannan ta ɗauki jakar ta buɗe kamar zata ɗauki wani abu, kuɗade ta gani tare da bangles da zobe tsananin mamaki ne ya kamata, bata tsaya dogon tunani ba kawai ta ɗebe kuɗaɗen ta ɗaga pillow kujerar da suke ajje kayayyakin su ta saka, sannan ta ɗauke bangles ɗin da zoben ta wuce kamar zata jefa abu a dustbin ta zura su jakar wanna budurwar, ta wuce ta koma kan aikinta da mamakin wannan budurwa na meysa tayi sata? Dan tana da tabbacin ba rashin kuɗi bane saboda tasan kafin ta shigo ma maybe saida ta biya kusan kuɗin data sata din. Kuma meysa bata zaɓi jakar kowa ba sai ta ta? WANNAN KENAN.

Tuk tuk ta tsare ta hau lokacin data fita titi, ta faɗa masa inda zai kaita, kuɗaɗen ta ɗauko ta haɗa su wuri guda ta sa a jaka dan da a aljihunta ta zuba su, " tsuntsu daga Sama gashashe"....... Ta faɗa tana murmshi tare da ɗage kafaɗunta sama alamar i don't care.

Ko da ta ɗauko Shazeen tsayawa sukayi a hanya ta musu takeaway ita da Sahnish sannan ta bata ta shigar musu da shi gidan, Dan ita daga tuk tuk ɗin ta juya bata tsaya

7 / 53