BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   29 / 53

84K to 87K   out of 156.9K words

ba, tsaye take tana kallon sa don ganin iya gudun ruwan sa. Wata karamar kujerar roba dake gaban wani table ya nuna Mata tare da faɗin, "zauna"........... ba musu ta zauna, laptop din sa dake buɗe ya rufe tare da tattare duk wasu tarkace sannan ya zauna bakin table ɗin kana ya ce, "Ina so in tambaye ki a karo na biyu, wacece ke?"

Dariya tayi cike da gaɓunta ta ce. "Ikon ALLAH yau ni ake tambaya wacece ni, gsky daɗi na da gobe saurin zuwa, ban taɓa tunanin wanna ranar zatazo kwana kusa ba ai"........... Shi dai Jey kallon ta yake ko kiftawa babu, gyara zama tayi tare da gyara murya ta fara magana, "Da farko suna naaa Hushaima Sahnish Shazeen, sannan ni mutum ce kamar Ka ina aiki a Starlight beauty Co. kuma nayi aiki a wurare daban daban, nayi cleaner a wata ma'aikata, nayi aikin gyaran su zobo a wani kamfani, nayi aikin raino a wani gida, nayi aikin girka abinci a otel(hotel), haka a wata moll (Mall) ma ina ɗan zagaya musu wurin ko da wasu zasu zo su nemi a zaɓa musu irin su man gashi ko na jiki masu kyau, daga ƙarshe kuma yanzu ina aiki a wajen gyaran jiki da sauransu"......... Kallon yadda take magana cike da confidence da kuma bakin gskyr ta da ya hango cikin idonta yayi, Amma duk da haka sai ya ce, " In kin gama shirya tatsuniyar taki saiki faɗamin ta asalin".

"Me sa to zan ma karya, tukunna ma in kasan bazan faɗa gsky bane me sa Ka tambaye ni, to kaje Ka tambaya kowa wacece Hushaima tunda ni ba Ka yarda da abinda na faɗa ma ba, Ni bana ƙarya kuma bana munafurci".

"Ai nasan hanyar tambayar kuma zan iya sanin waccece ke ba tare da naji daga gareki ba, kawai na zaɓi na tambaye kin ne. Ki fadamin wace ke, daga ina kuke? Su waye mahaifanku?"............ Cikin wata irin fusatar data bashi tsoro ta miqe tana faɗin, "Shin baza a iya sanin mutum dan kansa ba sai an jingina shi da wani, dole dole sai kana da iyaye ko kuma sai ansan matsayin iyayen Ka tukunna za'a ce Kai wani ne, tukunna ma miye haɗi na da kai "........... Cikin wanna munafukar muryar tasa ya ce, "lower your voice madam, karki tarawa kanki jama'a".

"Whl karka ƙaramin magana, kuma bazan rage muryar ba Kai kana tunanin akwai Wanda nakejin kunya ne, wai ko dan an same ni a ɗakin ka zanji wani abu ne, ban ajje uban kowa da zaice na jawo masa abun kunya ko abun magana ba dan haka ban damu da duk wasu maganganu ba, mu kaɗai muke rayuwar mu kuma mu kaɗai zamu rayu bamu buqatar kowa da komai ko kuma sauya tunanin kowa a kan mu, duk ma yadda kuka ɗauka hakan ne"........... tana kai wa nan ta nufi kofa a fusace, saurin shan gabanta yayi. Cikin wani irin fushi ta ce, "Whl in baka kauce Ka ban hanya ba sai na sharara ma Mari"........... Zaro ido yayi cike da ɗinbin mamaki kafin ya haɗiye wani yawu daƙyar ya ce , "Okay naji but zauna na yarda da abinda kikace kawai tsokanar ki nake, ke ɗin wata ce kuma jajirtacciya da bakya buqatar bango domin jingina bakya buqatar dakalin dafawa, haka kuma bakya buqatar taki domin tsirowa, irin Ku abun so ne da alfahri a ko ina, ke din wata ce Hushaima plz have a seat". Ya ƙarashe da wani irin sauti yana nuna mata wurin data tashi, ɗagowa tayi ta zuba masa idanunta da suka rikiɗe zuwa ja a lokaci guda, ɗan ja baya yayi tare da harɗe hannuwansa a ƙirji yana jifanta da wani irin kallo, "Bazan iya zama ba ina son kaɗaicewa a yanzun, ka bani hanya"........... Ba musu ya matsa Mata ta wuce, neman wuri yayi ya zauna zuciyar sa fal da tunani iri iri.

Ko da ta dibi ruwan daga rijiya direct a kanta ta shiga watsawa saida tayi wurin sau uku ko sanyin ruwan bataji sannan ta sake ɗaibo wani ta zuba a butar dake wurge anan ta wuce ɗaki, fitsarin ta shiga tayi sannan ta dawo ta sauya kayanta dake ɗigar ruwa ta kwanta tana sauke numfashi.

Ranar kusan makara tayi sallah dan har saida Sahnish ya shigo, sosai ya sha mamaki ganin Ƙofar ɗakin su a buɗe. Dan ta saba in dai lokacin sallah yayi saita shiga ta tabbatar ya tashi saisa da bai ganta ba ya biyo sawu, tana kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba amma ta kasa tashi. Hannunta Sahnish ya shiga bubbugawa yana Kiran sunan ta saidai har Shazeen ta buɗe ido ta tashi ita bata motsa ba, a firgice ya Kira sunan ta da ɗan ƙarfi, wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanun ta da har yanzu basu washe ba . "Hushaima lpy? Ko baki da lpy ne?"

"Sahnish har kun tashi mie?"......... Ta faɗa tana tashi zaune. "Har ma anyi Sallah ai, nayi mamaki da banji yau kin shigo wuri na ba kamar yadda kika saba saisa ma na shigo na duba".......... da sauri ta miqe tana faɗin, "Miyesa baka tasheni da wuri ba, ni ai kafin ayi Sallah nake shiga na dubaka".

A gurguje taje tayi alwala ta dawo Shazeen ma data buɗe ido ta shiga tayi, shi dai da kallo ya bisu har sukazo suka tada sallar suka idar, sai lokacin ya ce, "Hushaima meya faru dake ?" .

"Meka gani?".......... Ta tambaya ba tare data kalleshi ba. "Fuskarki ta nuna kamar akwai damuwa".

"Na danyi ciwon Kai ne amma na sha paracitamol (paracetamol)".

"Dama na sani za'ayi haka, ko in ɗauko miki ragowar maganin maleria nan ki Sha?"........... Tashi tayi ta cire hijab ɗin ta wuce toilet ta ɗauko bucket a toilet tana faɗin, "Ni fa naji sauki ba abinda zan sha kaji". Daga haka tayi waje samu tayi already mutanan gidan sun hau layi dan yau ta makara, Bonbon dake sawun farko cikin makirci ta ce, "Aunty Hushaima zo ki ɗiba mana ni bari na dawo kan layin naki"..........." Kar na takura Miki bonbon ban sani ba ko uzurinki yafi nawa, karki damu zan jira ".

"Ah ah gsky". Ta faɗa tana barin in da take tazo ta ɗauki bokitin Hushaima ta sa akan layin ta sannan ta ɗauke nata ta dawo dashi layin Hushaiman, godia ta mata sannan ta koma kan layin nata. Tsaki Jamcy taja tare da faɗin, "Shiga sharaf ba shanu, a dai rage shishigi".

"In ba tsoro ba mutum ya ambaci suna mana tarihi ya maimaita kansa yanzu sai na sake rage yawan hakoran mutum"........... Dariya duk suka kwashe da ita wadda ta Ƙara tunzira Jamcy amma batace komai ba sai kwafa da taja dan har yanzu tana jinyar bakinta ne. Haka Hushaima ta ɗiba ruwan ta wuce ba tare da tace da su ci kanka ba, bata samu Sahnish a ɗakin ba sai Shazeen dake ƙarasa assignment ɗinta dan haka ta shigewarta wanka Saboda yau zata aiki.




-----------------√




Cikin kuka take faɗin, "Dad Dan ALLAH ka ban wayata, mumu ki sa baki mana" .

Zaburowa mumu tayi da faɗin, "Ni sai dai in sa miki duka wawiyar banza wawiyar wofi ".

"Mumu Amma naga ai mijina ne Kuma ........" Dad ne ya tare da faɗin, " To tattabara sarkin aure, tun wuri ina shaida Miki ki cire zancen auran nan a ranki dan sunan sa warwararrre, tukunna ma a prison zakuyi zaman auren ne? mutumin dake hannun hukuma a yanzu"............ Wani sabon kukan Nayrah ta fashe dashi, a lokacin ne Kuma doctor ya shigo ɗan kallon su yayi tare da yin sallama ya ƙarasa shigowa, amsawa sukayi dad ya masa ya aiki, sake dudduba jikin Nayrah ɗin yayi kafin ya ce, "Ranka ya daɗe in baza ka damu ba ku ɗan bamu waje ina so nayi magana da ita".

"Ba dai wata matsala ko Dr?"........... Mumu ta tambaya. Girgiza mata Kai yayi kana ya ce, "Nop babu, kawai Ina so na mata wasu yan tambayoyi ne". Ba musu suka juya suka fita Saida suka rufe ƙofar doctor ya ce, "Sorry to interfere but wanna biological parents dinki ne?".......... Nayrah da har lokacin kuka take me cin rai na jin cewa an kama Amjad ɗin ta, ɗaga masa Kai kawai tayi alamar eh.

Ɗan shuru yayi kafin ya ce, " Ya kamata ki rage Kukan nan ko ki daina shi gabaɗaya for your health, a yanzu hutu kike buqata ba wai ki dinga tafasa jinin ki ba ".........." Dr ka aramin wayar ka Dan ALLAH ". Ta faɗa da dasasshiyar muryarta.

"Me zakiyi da ita?" ............ "An kwace tawa ne Kuma inaso na kira mijina"........." So you are married?". Dr ya tambaya da mamaki. Sake gyada masa Kai tayi alamar eh, dan shuru yayi can Kuma ya zaro wayar ya cire password sannan ya bata. Hannun ta har rawa yake wurin karɓa da sauri ta loda number Amjad a wayar sannan ta kira saidai baya shiga haka taita gwadawa amma amsar ɗaya ce wayar a kashe, dan dole ta haƙura ta bawa Dr wayar tare da komawa ta kwanta. Bai ce mata komai ba ya ɗauki kayan aikin sa yayi waje anan ya samu Dad Mumu ta sashi gaba tana ta masa zazzage zazzage, "Emm inaga ba damuwa zaku iya tafiya, ya kamata a barta ta huta dan tana buqatar sa Kuma bama san ana hayaniya sosai"........... Ya faɗa saboda ganin zaman nasu ba abinda yake haifar wa sai ƙarin tashin hankali wa marar lpyn.

Mumu ce ta ce, "Dr ai ni nake kwana a wajen ta"........... Girgiza mata Kai yayi, "Hajiya ko bakya nan mu nan hospital ɗin muna da kwararrun ma'aikata dake kula da majinyata, ba laifi idan kunje kun dawo da safe "........... Dad ya ce, "Shikenan ba damuwa duk abinda ake ciki in da wani abu ka kirani ka faɗamin"..........."karka damu Alhaji, ba wata matsala in sha ALLAH ".

Daga haka suka shiga yiwa Nayrah ɗin sallama hankalin su kwance cewa an kama Amjad basu da wata sauran fargaba. Ko da suka shiga samun ta sukayi kwance ta bawa ƙofar baya, Mumu ta ce, " Inajin ma tayi bacci ai muje kawai". Juyawa sukayi Dad a gaba Mumu a bayansa kamar wata uwar sa suka fice tare da jawo mata ƙofa, duk tana jinsu amma taƙi motsawa.

Juraysh kuwa daƙyar ya lallaba Anah sannan ya baro gidan Misalin 12:30am.

Shi kuwa Amjad suna dawowa gidan nasa, ɗakin sirrin sa ya shige ya Kira su Ash conference call, tattaunawa suke Kan aikin da suke na shadow Amjad ya ce, "Widad a wurin Ka ne fa har yanzu ba wani labari, har yanzu baka samo mutumin da suka bada detail a Kansa ba ne?". Shuru yayi har saida Amjad ya ɗan buga hannun sa a goshi dan ya sallama widad shiririta kawai yakeyi dan yasan halinsa wani sa'in, ya tsinto yar muryar nan tasa kamar ɓarawon da aka ritsa, " Na samo komai, kawai Ku gama naku aikin sai Ku min magana"......... Cikin rashin yarda Amjad ya sake faɗin, "In da akwai wani taimako da kake buqata Ka faɗa tun wuri?" .

"Babu"........... Ya faɗa daga nan suka cigaba da tattaunawa shi dai widad sai in ta kama yake sanya baki amma yana sauraran su, Ace ya ce, "But widad what's special game da mutumin?". Shuru sukaji suna dubawa suka ga ya sauka daga Kan layi, Amjad ya ce, "Don't worry dukda akwai abubuwa a gabana zan bibiyi abun".......... Daga haka sukayi sallama kowa ya kashe.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______40 & 41


Washe gari da wurwuri ya tashi ya shirya dan dama baiyi wani baccin kirki ba, sanye yake da milk silver dust yard ɗinkin yayi fitting ɗin jikinsa sai tashin kamshi yake, ga gemun nan da gashin baki ya sha gyara sai ɗaukan ido yake, haka gashin kansa ma duk ya kwanta luf kamar na ɗan jariri nan kuwa tsabar kuɗin da yake ci wurin gyara ne, kunnen sa kamar ko da yaushe maqale da wani ɗan white bud. Yana fitowa ya tarar da Philip yana jiran sa gaishe shi yayi sannan ya ce, "Boss your breakfast is ready"............ Dan akwai cooks maza dake wa yaran gidan abinci in kuma yana nan gidan ne sai su masa nasa daban, zaku sha ɗinbin mamaki in nace zan fada muku yawan mutanen da suke aiki ƙarƙashin Amjad kuma duk shi ke ɗauke da duk wata dawainiyar su ba ruwansa da banbancin Addini, saisa suke jin akan sa zasu iya bada rayuwar su, saidai kuma a yanzu an samu zakka wato dan qunar bakin waken dake sanar dasu Awais duk motsin Amjad ɗin.

Ɗan kallon saitin dinning ɗin yayi kafin ya ce, "Anya zan iya cin wani abu kuwa Philip, kasan aikin dake gaban na kuwa but let me just have a tea, jiya ka sanar da Wali (ɗaya daga cikin cook ɗin) batun ƙaruwar sojojin da muka samu?".

"Eh boss tun a jiyan ai, yanzu ma inajin sun gama yin breakfast ɗinsu".

"Okay ". Daga nan bai Ƙara magana ba suka nufi dinning ɗin Philip yaja masa kujera ya zauna ya yi serving ɗinsa black tea da snacks sannan ya koma falo ya zauna jiran sa har ya gama ya fito, tashi yayi ya bi bayansa sukayi waje suna magana ƙasa ƙasa, tasowa su Aram sukayi lokacin da suka ga fitowar sa bayan sun gaisa ya ce, "Daga yanzu Ku zauna a gida kawai idan da wani aiki zan muku magana, amma yanzu ga wa'anda zamu fara fita tare na wani lokaci ".

Cikin Rashin jin dadi su Aram suka amsa da to dan sun riga sun saba da kasancewa dashi in dai yana ƙasar. " Muje kamal". Ya faɗa yana wucewa, da sauri ɗaya daga cikin sojojin ya wuce da niyyar buɗe masa, Philip yayi saurin yi masa magana ƙasa ƙasa, waskewa yayi yaja ya tsaya jikin motar shi kuma ya buɗe masa ya shige sannan kamal ya shiga driver seat, ɗaya daga cikin sojojin ya shiga passenger front seat sauran kuma suka shiga sauran motocin su tare da sa motar sa a tsakiya suka fice daga gidan Philip kuma ya juya ya koma ciki.

Direct asibitin da aka canzawa Nayrah suka nufa, sosai aka dinga kaucewa ana basu waje saboda kallonsu kawai zai sanya ka saki fitsari a wando, already yasa anyi magana da Dr ɗin daman tun dare dan haka office ɗinsa suka tambaya aka nuna musu. Wasu mutane dake zaune a reception na hospital din, ɗaya ya ce, " Wai wancan ba Amjad din nan bane?"........... ɗayan ya amsa da, " Shi ne mana, baka ga har wasu jami'ai na masamman masu take masa baya aka bashi ba"..........."to wai har yanzu ba'a gama binciken bane?"............. "Kash kana da maida zance baya, to wai dama ba da haka ake so a raina mana hankali bane, su dama ai tunda manya ne ba'a musu hukunci kawai za'a ɗauke mana hankali ne daga nan a samu fitar dashi daga ƙasar sai an manta da batun sannan a dawo dashi, nawa akayi irin haka, kai yanzu fa in kana da connection kayi duk abinda kake so kawai".........." To in dai hakane ai akwai alkalin Alkalai, shi zai sakawa rayukan da aka salwantar"..........." Barsu kawai da halin su Rabiu, je ka duba mana result din test din ya fito ne ?".

__________Suna shiga likitan ya miqe cikin girmamawa ya ce, "barka da zuwa ranka ya dade".......... Hannu ya miqa masa sukayi musabaha sannan ya ce, " Ina ne room din ?"............. Da sauri Dr ya ce, "Ahhh to muje kawai in nuna muku mana". Ya ƙarashe yana zagayowa ya fito daga gaban table ɗin nasa ya nufi ƙofa cikin hanzari, ilahirin jikinsa rawa yake saboda wa'annan firgitattun sojojin da bai taɓa zaton akwai irinsu a ƙasar Nifaz ba, binsa sukayi zuwa ɗakin da Nayrah ɗin take, tana zaune akan kujera hannun ta riqe da mug ɗin tea da Nashwa ta zuba mata, sai wata cleaner dake canza bedsheet. Sallama Dr yayi ya shiga sai wani soja sannan Amjad da kamal dake bayansa sauran kuma sukaja suka tsaya a bakin Ƙofar.

Nayrah ta Kai spoon ɗin tea bakinta bata san lokacin da tayi masa wata wawiyar kurɓa ba saboda ɗagowar da tayi idanunta ya sauka kan Amjad, tari ta fara ba ƙaƙƙautawa da sauri Nashwa ta karɓi mug ɗin ganin yadda hannunta yake rawa sannan ta shiga jera mata sannu. Ɗagowa ta sakeyi a lokacin da tarin ya lafa tun daga kan kafarsa dake sanye da kyakkyawan brown loafers har zuwa kan kyakyawar fuskar sa dake fitar da wani sirrin kyau . "Ina kwana ya Amjad"........... Nashwa ta faɗa tana tashi daga gefen kujerar. " kin tashi lpy?". Ya maida mata da tambaya a maimakon amsa gaisuwar, ɗan ɗago Kai yayi ya kalli Kamal, da sauri Kamal ya juya wurin su Dr tare da faɗin, "In ba damuwa mu ɗan je daga waje Dr".......... Ba musu Dr ya fita yana faɗin a fito lpy, Nashwa ma gyalenta ta ɗauka ta fita, cleaner kuwa dama tunda suka shigo Dr ya korata, dukkansu ficewa sukayi suka ja musu ƙofa ya rage daga shi sai ita, gefen ta ya Ƙarasa ya zauna tare da riqo hannayenta gabaɗaya cikin nasa ya Kai baki yayi kissing yana murmushi, sai lokacin ta dawo

29 / 53