Author : Young Writer Category : Tknovels
3Gs supreme, kansa a ɗan sunkuye Wanda hakan ya bawa gashin kan nasa damar zubowa ya rufe fuskar sa, bokitin data shigo ɗauka ta ɗauka ta fita ba tare da tace dashi komai ba taje ta ɗaibo ruwa, suna tsaye a tsakar gidan suna maida zance harda su baba ilerika dasu kawu adamu kawai suka ga wasu murtika murtikan mutane sun shigo sanye suke da wasu irin kaya, bujen wando da riga red and dark brown sai wata hula Mai kamar ship dake a saman red hair ɗinsu, su biyar suka shigo sai zare ido suke su nufi wannan ɗakin su nufi wancan duk sun fito da kowa sai a ƙarshe suka nufi ɗakin Hushaima ita dai tana tsaye a wajen rijiya hannunta ɗaya akan kugunta ɗaya riqe da guga tana kallon ikon ALLAH, mutum biyu ne suka shiga ɗakin ba jimawa suka fito tare da bawa kowa umarnin yayi ƙasa, da sauri duk suka zube kan guiwowin su Banda Hushaima data harde hannuwanta a kirji.............
----------------------√
A falo ya samesu itada Nashwa dan tuni an sallami nurse tunda Nayrah ɗin ta warke, cikin sakin fuska ya amsa gaisuwar da Nashwa ke masa tare da kallon Nayrah dake ta kumbure kumbure tun shigowar sa ita a lalle tayi fushi, baice mata komai ba ya wuce . "Ya Amjad". Nashwa ta Kira sunan sa, dakatawa yayi tare da juyowa yana sauraren ta, "Yah Amjad daman Ina so naje gida ne in ba damuwa"........ A ɗarare tayi maganar kanta a ƙasa saboda bata san amsar da zai bata ba, dan tun ranar ya aiko musu da sabbin wayoyi amma fa duk Numbers ɗin yan gidan baya aiki bama ya shiga gabaɗaya.
Ba alamun damuwa ya ce, "Ai baki fadamin ba Nashwa, ki bari in na fito sai muje na kaiki da Kai na".......... Cikin Jin daɗi ta ce, "Nagode sosai ya Amjad, a fito lpy"......... Wucewa yayi ciki, yayin da cikin fushi Nayrah ta tashi tabi bayan sa, yana cikin rage kayan sa yaji shigowar ta dakatawa yayi da unbuttoning ɗin rigar ya juyo tare da buɗe mata hannu alamar ta taho, turo baki tayi tare da juya masa baya, "Ninie rigima". Ya faɗa yana takawa har inda take ya yi hugging dinta ta baya tare da zuro kansa ta wuyanta. Kuka ta fashe masa dashi tare da juyowa ta fara tureshi, faɗi take, "Ni ma whl nashwa zan bi na fasa zaman dakai, tunda gadin gida Ka ajjeni inyi". Dariya yayi wadda ta mance rabon da taga yayi irinta kana ya ce, "Haba yarinya ai ƙarya kike whl, zama daram Matar Amjad"......... Wani kukan shagwaɓar ta sake fashewa dashi, hannun ta yaja zuwa bakin gadon ya zaunar da ita sannan ya zauna, In a serious tone ya ce, "Miye matsalar ne Ninie, bana son ganinki cikin damuwa hakan yana ɗaga min hankali, a baya Ina cewa batun auren mu ne, yanzu kuma an yishi an wuce wurin, dama na fada Miki auren bashi bane wahala a wuri na........" Shuru yayi yayin da ta ƙarasa masa da faɗin, "Zaman auren ne matsalar ko ? To shikenan ai laifi na ne".
"Ninie Please ki fahimce ni mana, kinsan yanayin ayyukan dake gabana a yanzu kuwa, ina da abubuwan dake buqatar lokaci na Amma duk da haka Ninie dole zan raba Kai na biyu saboda na Miki abinda kike so ki daina tada hankalin ki dan ALLAH ". Ya ƙarashe yana jin kamar zai sa ihu, tafin hannuwansu ya haɗa tare da zura yatsunsa tsakiyar nata yana matsawa a hankali.
kallon sa tayi taga yadda ya cakuɗe fuska yana kallon ta kamar wani baby, goge fuskar tayi sannan ta ce, "Wani irin aiki ne kakeyi a yanzun, bayan duk wani aiki ka tsayar da yin sa". Ta sakaya da hakan dan baza ta iya faɗa masa kai tsaye cewa an tsayar dasu kowani aiki ba.
Dan girgiza kansa yayi kaɗan kafin ya ce, "In har Ninie ta yarda da mijinta to karta ƙara tuhumar sa kan aikin sa, in lokaci yayi da kai na zan sanar Miki"......... Wani kallo ta jefa masa kafin ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ka samu labarin su Mumu kuwa? Saboda mu dik mun ƙasa samunsu a waya, nasan yanzu haka hankalin dad ya tashi sosai ".......... Murmushi yayi da faɗin, "Yes dan har ma ya aika sammaci gida cewa na sace masa yayansa biyu".
Dafe kirjinta tayi da faɗin, "Again, Amour Dan ALLAH kayi hakuri da abubuwan dasu Dad suke ma, duk a dalilina ne dad ke wulakanta ka haka amma Kai kasan da ba haka suke ba, su Mumu suna son ka sosai "..........."Na sani Ninie saisa nake musu uzuri ai, na fahimci halin da suke ciki Kuma anjima zamuje mu Kai Nashwa gida tare, daga nan zamuje gida wurin su Anah". Ya ƙarashe yana sakinta ya nufi hanyar toilet sai Kuma ya tsaya tare da juyowa ya ce, "faɗa abinda ke bakin ki?"
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Da gaske da sa hannun ka a mutuwar farshad?"......... Haɗe girar sama data ƙasa yayi kafin ya ce, "Eh............
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd SultyWrites22
STEP 1
PAGE _______ 47 & 48
"Da gaske da sa hannun ka a mutuwar farshad?" ............ Haɗe girar sama data ƙasa yayi kafin ya ce, "Eh". Da baya baya ta tafi tare da faɗawa kan gadon, runtse idanunta tayi da ƙarfi saboda yadda zuciyarta tayi wani irin hantsilowa kamar zata faso ƙirjinta ta fito, ko ina na jikint ƙerma yake, kenan saboda ita yasa aka kashe Farshad, kenan saboda ta faɗa masa su dad sun dage sai ta auri Farshad shiyasa yayi tunanin kashe shi ne mafita. Maganar sa ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula tare da buɗe idanunta da sauri. "Haka Dad ɗinki ya ce, amma ni bansan komai ba, son samu suyi bincike ba wai maqalawa Wanda ransu ke so ba".......... Daga haka ya juya ya wuce toilet ya barta nan zaune tana binsa da kallo kamar wata doluwa.
_______________Dad ne zaune shi da Mumu suna magana faɗi yake, " Ai duk abinda ya samu ya'yana sai yayi bayani gaban hukuma saboda a gaban kowa ya fita dasu ".
"To wai Kai Alhaji duk binciken da akayi ba'a samo inda suke ba ko shi ɗin in da yake?"..........." To ke da kin ɗauka ƙaramin hatsabibi ne yaron nan ina gaya Miki kina ƙi, ni fa dama tun farko dan kun nuna k..........." Maganar sa ta katse sakamakon shigowar Nashwa da Nayrah ɗin, da sauri duk suka miqe yayinda Nashwa ta tafi da gudu ta rungume Dad tana faɗin, " I missed you dad".......... ita Kuwa Nayrah tsayawa tayi ta kasa gaba ta kasa baya saboda tsoron tarbar da su Mumu zasu Mata kasancewar tasan suna fishi da ita ne ko daren ranar da suka baro asibitin, tunaninta ya katse ne a lokacin da Mumu ta riqo ta tana faɗin, "Nayrah Nashwa ALLAH Alhamdulillah, ya akayi kuka zo nan ? A ina aka boye Ku ? Ba dai abinda ya same Ku ko?"......... Ta faɗa tana tattaba jikin Nayrah ɗin kamar me neman wani abu .
Komawa sukayi suka zauna, Dad ya ce, "Nashwa ALLAH yasa ba kwace muku wayoyi akayi ba, saboda kwata kwata ba'a samun ku?".......... ƙiftawa Nashwa ido Nayrah tayi hakan ya sata faɗin, "Dad wayoyin ne suka sami matsala tawa ta fashe ta Nayrah kuma ta faɗa ruwa sai yau ya Amjad ya kawo mana wasu, kuma muna lpy ba abinda ya same mu muna gidan Nayrah ɗin ne".
"Gidan Nayrah ?"........... Mumu ta maimaita tana wurgawa Nayrah ɗin wani kallon da ya sata sunkuyar da Kanta ƙasa. " ALLAH sarki Nayrah ban taɓa ganin Amarya marar galihu irin ki ba, kice haka aka kwashe Ku kamar awaki aka je aka zubaku a gida ko"............ Dad ne ya amsa da faɗin, " Duk fa abinda zaki faɗa a yanzu ihu ne bayan hari hajiya Lateefa, ni dai tunda suna lpy ai shikenan".
Da mamaki Mumu ta ce, "Shikenan kamar ya? kana nufin Ka hakura Ka yarda ta cigaba da zama dashi kenan ?"........ Shuru Dad yayi yana kallon Nayrah data sunkuyar da Kanta tana wasa da yatsun hannuwanta".........." Ki barta tunda haka ta zaba taje ALLAH ya bada Sa'a".
Mumu zata sake magana Amjad ya shigo da sallama, wuri ya nema gefen Nayrah ya zauna sannan ya gaishe da Dad ya juya zai gaishe da Mumu ta tareshi da faɗin, " Riqe gaisuwar Ka bama buqata, wato mu zaka nunawa iko ko? Ka ɗauke mana ya'ya tsawon sati wato ka zuba mana ido kaga iya gudun ruwan mu ko? to yayi muma yanzu zamu nuna ma ƙarfin namu ikon, Nayrah idan har kika sake kika bishi ban y........."
Dad ne ya tare ta da faɗin, "karki fara hajiya Lateefa, karki kuskura kiyiwa ya'ta baki ina cewa ita tace taji ta gani, to mu barta mana ai munyi namu ko, ke tashi ki fita ki barmin gida"............ Miqewa Amjad yayi da faɗin, "Muje"........... Jiki a sanyaye ta miqe, wani murmushin takaici Dad yayi tare da ɗauke Kai ya dubi Nashwa da jikinta duk yayi sanyi tana kallon yar uwarta ta , "Ke tashi ki wuce ciki". Dad ɗin ya faɗa cikin ɓacin rai.
Gaban Mumu Nayrah ta ƙaraso tare da zubewa Kan guiwowinta saidai kafin tace wani Abu taji saukar wasu tagwayen maruka Kan kuncinta, da sauri Amjad yayi waje dan bazai iya daurewa ba ganin ana dukanta a inda bazai iya rama mata ba, wasu zafafan hawaye ne suka sauko Mata, ɗago Kai tayi tana kallon Mumu cikin rawar murya ta ce, "Mumu na hakura na yafe auran whl na hakura Dan ALLAH kiyi hakuri "............" Ba fa zaki haƙura ba ki tashi ki bishi ai kin makaro, da lokacin kafin kije gidan sa kikace Kin haƙura zan yarda Amma yanzu whl Baki isa ba, tashi ki fita". Dad ya faɗa a fusace yana miqewa kamar zai kai mata duka, da gudu ta tashi tayi waje, tashi Mumu tayi da faɗin, "Wai Alhaji meke damunka ne? ya kake neman jefa min ƴa' a rami ne, ya ina ƙoƙarin shawo Kan lamarin gidana kana wargaza min, in kuma yayi amfani da wanna damar ya saida min ya' fa "............" Ke kaɗai kika haife ta ne?". Dad ya tambaya sharply.
"Alhaji!."......." Lateefa". A tsorace Mumu taja baya tana bin Dad da wani kallo me kama da tsoro tsoro. Kaɗai rigarsa yayi ya wuce sama ya bar Mumu sake da Baki, abinda ya daɗe bai faru ba tsawon shekaru kenan, Meke shirin faruwa da ni ne? Ta wa kanta tambayar da bata da amsar ta.
-----------------------√
"Ke baza ki durƙusa bane?"........... Wani me ƙiran adawan farko ya faɗa yana zarewa Hushaima ido. Ba tare da wani alamar firgici a tare da ita ba ta ce, "Kan wani dalilin zan durƙusa kenan?" ..........." Ke ba fa a mana rashin kunya ko gardama, Maleekh ne zai fito kuma dole ki durƙusa dan shi ɗin shugaba ne a gareki da duk wasu al ummar dake yankin nan da kuma wasu yanki na duniya".
Buɗe baki tayi cikin salon rainin wayo ta ce," Au da ALLAH fa? Shugaban ƙasa ne ko uban gida na ne ko kuma miji na ne shi da zai shugabance ni?".
"Shi din yarima ne mai jiran gado na AURELLON SULTANATE".......... take duk mutanan dake tsakar gidan suka sha jinin jikin su tare da yin ƙasa da kansu ko numfashin kirki daƙyar sukeyi, wani irin tsit gidan yayi kai kace mutuwa ce ta gifta.
Shuru tayi dan tabbas ta taɓajin tarihin wanna masarautar a wurin Amla, a yadda ta faɗa Mata masarautar tafi kujerar shuwagabanni da yawa iko da ƙasarsu.
Dawowa tayi daga gajeren tunanin data tafi amma bata jin akwai wata halittar da zata iya durƙusawa dan kawai ya wuce cabbb ta ma zama banza kenan "............." baza ki bi umarnin da ake baƙi bane sai fushin Maleekh ya hau kanki?".............." Whl sai dai ku kasheni Amma in dai sai na durƙusa sannan zai wuce to saidai yayi tsami a ɗakin". Ɗaga wata murɗaɗɗiyar dorina dake hannun sa yayi ya zabga mata ya sake ɗagawa zai Ƙara mata Sahnish yayi saurin shiga tsakiya wani ihu ya sa tare da buga tsalle ya zube a wurin saboda dorinar da mutumin ya sauke mai sai da ya jiyo ƙamshin lahira, cikin wani irin yanayi na fita hayyaci ta dyago tare da fizge dorinar, da hannu ya kai mata duka, ta tare lokaci guda idanunta suka sauya launi, da sauri Sahnish ya rarrafa gaban Maleekh kamar yadda suka ambata, wanda a lokacin ya fito daga ɗakin ya sanya wata sabuwar riga, take iskar gidan ta sauya zuwa ƙamshin turaren sa na bolt lightning.
Ƙafarsa Sahnish ya riqo ya shiga roqon sa, "Dan ALLAH ka taimaka Kar su ji mata ciwo, Dan ALLAH Kai ɗin babba ne Kuma shugaba ne ga Al'umma, bai kamata ka bari aci zalin Al'ummar ka a gabanka ka ba, ka taimake mu dan ALLAH, ko dan ƙanwar mu Bamu da kowa sai ita Dan girman ALLAH karsu kasheta ka taimake mu". Ya ƙarashe yana nuna Shazeen dake kuka sosai tana kokarin zuwa wurin Hushaima ɗaya mugun ya riqeta. Sai dai duk wannan magiyar da Sahnish yakeyi ko ɗagowa Maleekh bai yi ba ballantana ya san yanayi, tunda ya zube hannayen sa a aljihu kansa a ƙasa gashin kansa dake baje ya zubo ya rufe fuskar sa. Tashi Sahnish yayi dakyar saboda jikinsa dake masa wani irin azababben radaɗi tun da ya samu rabonsa, rarrafawa yayi ya riqe ƙafar wanda ke dukan Hushaiman yana bashi haƙuri, wata irin harbi ya kai masa da ƙafar sai ganin Sahnish sukayi ya wani tashi kamar tsuntsu bai sauka a ko ina ba sai ƙofar soro, amma duk da haka yana sauka ya sake miqewa ya nufi wurin sauran saidai ba wanda ya kalleshi ballantana ya tanka masa, saida mutumin nan ya tarawa Hushaima gajiya iya iyawarsa, ita kuwa har lokacin a tsaye take ƙiƙam bata da niyyar sunkuyawa, dan tun tana ƙoƙarin faɗa ta ƙwaci kanta har ta haƙura ta tsaya kawai .
A lokacin da ya dago kusan da yawa daga cikin mutanan gidan dake satar kallonsa ta ƙasan ido, ba dan a tsare suke ba da sai sun ara ana Kare saboda tozali da wannan kyakyawar halittar da sukayi, sosai kyawun sa tsorata su.
" Ya Isa gaɗɗo".......... Ya faɗa da daddaɗar muryar nan tasa, sannan ya fara tafiya da sauri sauri cike da ƙarsashi da kuma takun jarunta kamar wani saɗauki ya nufi hanyar fita daga gidan, da sauri duk suka rufa masa baya saidai taku daya biyu sukayi gaɗɗo ya zube a wurin. Rufowa kansa sukayi suna tambayar sa lpy, wani irin ihu ya ƙwalla da sai da gabaɗaya unguwar ta amsa faɗi ya ke, "Kuyi hakuri dan ALLAH Kar ku tabani".......... Da Mamaki mutanen gidan suke kallon sa ciki har da Maleekh daya dakata da tafiyar ya juyo yana kallon gaɗɗon dake zube a ƙasa yana ja da baya da baya yana faɗin karsu taɓashi.
Zamewa tayi a wurin tana ƙanƙame jikinta tare da faɗin, "Sahnish ruwa, ruwa".......... Da sauri ya matso wurinta yana kiran sunan ta. " Ka zuba min ruwa a jiki na, Sahnish kayi sauri zan mutu"......... Ta faɗa jikinta na wani irin kakkarwa, ai baisan lokacin daya ɗauki wani bokitin dake cike da ruwa ba ya juye mata a jiki wata irin doguwar ajiyar zuciya ta ja take haƙoran ta suka fara haɗuwa da juna kamar wadda masassara ta kama .
Hannu suka Kai da niyyar riqo gaɗɗo Amma Ina wani ihun ya sake kurmawa tare da tashi zaiyi waje a guje da sauri sauran yan uwan nasa suka riqeshi. " Karku sake shi ku kaishi mota"........... Maleekh ya faɗa a dake sannan ya juya ya fice. Daƙyar aka kakkama gaɗɗo aka fitar dashi zuwa mota sai fisge fisge yake.
Da sauri su Baba ilerika sukayi kan Hushaima data dora kanta kan kafaɗar Sahnish sai ajiyar zuciya take saukewa. Baba ilerika ne ya ce, "Sahnish ka samu kuje ciki ta canza kaya bari na samo mota a Kaita asibiti"............" Ga mashin ɗi na ma"......... Kawu adamu ya faɗa, tsaki Baba ilerika yaja tare da juyawa ya nufi hanyar waje. "Kaji ko kaji ba, kyakk wato yanzu hassada fa ba sai na waje ba Ɗan uwanka ma tsab wani lokacin zaiji kamar ya hadiye ka saboda ka shigar masa ido".
"Haba adamu, ya a na alhinin wani abu Kuma zaka taso da wata Maganar". Faɗin mama Atine.
"Ke da ALLAH rufemin baki, ai dake mijin ki ne dole zaki bi bayan sa, dama duk tare kuke ƙullawa to whl nasha tabara na sha Yasin duk abunku saida ku ganni ku banni".
"Kaiii Alhaji na ina yinka, sai sa kake burgeni, daɗi na da gobe saurin zuwa, haka zasu ganmu ayye haka zasu barmu ayye da gani da barmu daidai da fura da damu daidai.........." Umma delu ta faɗa tana tafi, a zuciye mama Atine ta kaiwa kafaɗar Umma delu duka da faɗin, "Ke delu karki ce zaki samun baki a magana ta, whl tsab zaki haɗiye harshen ki a wurin nan"......... Buge hannun Umma delu tayi tare da faɗin, "ke Atine bar ganin ki himmm, ƙashi ɗaya ne dani whl"..........." To ko za'a gwada ne". Mama Atine ta faɗa tana ja da baya tare da