Author : Young Writer Category : Tknovels
gizo, naga kin sake karɓo mana lambar yabo, ALLAH ya sanya alheri".
Murmushi tayi me ƙayatar wa kafin ta ce, "Ameen ƙawata, Ina su Shazeen ne naji gidan shuru ko tana makaranta?".
"Duk suna Nan, Shazeen!, Shazeen!".
"Naam".......... Ta amsa tana fitowa daga ɗakin ganin Amla yasa ta taho da gudu ta faɗa kanta tana dariya, itama rungume ta tayi daga zaunen da take tana murmushi ta ce, "Sweetheart ykk ya scul ?".
"Lpy kalau aunty Amla, kullum Ina tambayar Aunty Hushaima Ina kika tafi, tace min kin tafi New york, har mafarkin ki nayi jiya".
Kallon Hushaima tayi tana murmushi ta ce, "kinji ko, ni Anya bazan daina ƙawancen nan dake ba, oh sweetheart nima kullum sai na tambayeki, yayar nan taki ce baƙin hali ya mata yawa, taƙi haɗamu mu gaisa".
"Can ta matse muku kuma, sai ki ɗaga ta ai kije ki faɗawa Sahnish ga Amla ta zo ya fito su gaisa".
"Dama Sahnish Yana Nan?"........."Yana ciki, saidai in wani Abun yakeyi"..........Tashi Shazeen tayi ta wuce ɗakin Sahnish domin sanar masa saqon Hushaiman.
Gyara zama Amla tayi tare da zaro wani form a jakarta ta ce, " Nayi wani karambani, Amma karɓi dai ki gani".......... Karɓa Hushaima tayi ta zubawa takardar ido sai Kuma ta ɗago tana kallon Amlan da yanayin neman Ƙarin bayani. "Form ɗin neco ne da aka fara siyarwa shi ne na siya Miki, kinga in results ɗin ya fito sai a samu wata higher institution ki jo na".
Da wani irin yanayi take kallon Amlan har tagama maganar sannan ta furzar da zazzafar iska, "Amla naji dadin karamcin ki a gareni, Amma da kinyi shawara dani baza ki siya ba domin ni inaga asarar kuɗin ki kawai kikayi, dan bazan iya zama na rubuta komai ba".
"To in baza ki iya ba, ba sai asa a rubuta miki ba, ai ba abinda zai gagara".
Sunkuyar da kanta tayi kamar me jin kunyar abinda zatace, kafin ta buɗi baki ta ce, "Amla taya zan nuna shaidar gama secondry sannan na kasa kare Kai na".......Da fuskar tambaya Amla take kallon ta saidai kafin tayi magana su Sahnish suka iso. "Ahh yau kuce manyan baki ne a gidan namu".
Yar dariya tayi da faɗin, " Kaji Sahnish Kuma da wani batu, ni ai ba baquwa bace, ya kake ya gidan?".
"Ni dai karki canza min zance ba haka nake nufi ba, Alhamdulillah kin iso lpy?".........."Lpy kalau alhamdulillah, meya same ka? ciwo kaji ne ?"
Hushaima ce ta karɓa maganar da faɗin, "Me machine ne ya bugeshi"..........."Subahanallah, ALLAH ya kare gaba, sannu Sahnish".
"Yauwa amla nagode, Bari na koma daga ciki kafin Ku gama".
"Ah ah, kaga bama jimawa zanyi ba, tunda na dawo ban fita ba sai yau shi ne nace Nan zan fara zuwa".
Murmushi yayi da faɗin, "Mun gode sosai, ALLAH ya bar zuminci".........Tashi Hushaima tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko dan kwalin ta suka fita raka Amla ɗin gabadayan su, tana ƙarawa Hushaima bayani Kan maganar neco ɗin da Kuma amfanin ilimin, anan Sahnish yaji, sosai ya nuna jin dadin sa tare da mata godia. Har wurin motar ta suka rakota, buɗe bayan motar tayi ta ɗauko wasu shopping bags guda biyu masu kyau ta miqawa Shazeen ɗaya sannan ta miqawa Hushaima ɗaya da faɗin, "Tsarabar New York ce, ba yawa gashi Nan ke da Sahnish"......... "irin wanna dawainiya haka Amla, mun saki wahala da yawa ai".
"Kinga madam ba fa Dan ke na kawo ba, kawai dai dan karki sawa na kannen na ido ne saisa kawai na Dan Kara dake".
Sahnish ne ya amshe da. "Kinga Amla rabu da wanna baki ne da ita kamar aku"........ Duka ta Kai masa ya kauce Yana dariya, juyawa tayi wurin Shazeen da faɗin, "Shazeen kiyi wa aunty Amla Godia".
"Ina ruwanki, tun kafin ki faɗa tayi ai Madam"......... one side smile ta saki wanda ya sake fito da kyanta saboda ba ko yaushe takeyin murmushin ba saisa in tayi yake mata kyau. "Muna ƙara Godia Amla, ALLAH ya saka da khairan".
"To Ameen"........ Amla ta amsa tana shiga mota, daga nan sukayi sallama tare da dan matsawa gefe shi kuma Sahnish ya shiga duba mata hanya da zatayi reverse ta fita daga layin. Saida ta fita a layin sannan suka juya gida.
A tsakar gidan suka zube nan kan tabarmar suna duba kayan. Sahnish riga da wando ne masu kyau da turare sai Hushaima data sako mata dogayen riguna uku, ɗaya armless sai long sleeve ɗin da take tafe da ita a ciki, biyun kuma jacket suke tafe dashi wanda ta tsaya iya ciki, sai turare da veil ƙarami. Na Shazeen kuma English wears ne masu kyau na yara daidai shekarun ta tare da hair oils da ribbons sai su chocolates. Ita dai Hushaima tattare nata tayi ta wuce ɗaki ta ajje tare da form ɗin da Amlan ta bar Mata su cike zata dawo ta karɓa, sannan ta cire kayanta ta ɗaura zani ta fita ta shige wanka.
Har ta fito su Shazeen na tsakar gidan, sai gwada kayan take, tana ganin Hushaiman tayi saurin matsawa tana faɗin, "Aunty Hushaima kinga yadda kayan suka min kyau"........ Cikin Jin dadi ta ce, "Naga kayanki Shazeen, Kaya sunyi kyau sosai, ALLAH yasa a kashe lpy, mun godewa aunty Amla".......Tsallen murna tayi ta koma wajen Sahnish ita kuma ta shige ɗaki dan shiryawa, wata yaloluwar doguwar riga ta material marar nauyi ta saka tare da jan robar wandon data ke daure gashinta da ita, fatabarakar Rahman shi ne abinda baki na ya iya furtawa ganin yalwar gashin Kan Hushaima Wanda dama tun daga fuska zaka shaida akwaishi Amma baza Ka taba tunanin zai Kai haka ba, dogo ne sosai dan ya kusan wuce kugunta gashi da tsantsi saidai bashi da cika can can kuma ba baƙi bane, light brown ne. Masarci ta dauka ta taje sannan ta daure shi in a sleek bun style. Juyawa tayi da niyyar fita Shazeen ta shigo da jakar kayan ta ɗaya hannun kuma ledan sweets ɗin ne, karɓar jakar kayan tayi ta ajje sannan ta karɓa na sweet ɗin ma ta eba mata kaɗan daga ciki ta bata sannan ta boye sauran ta juya ta fice.
Yana zaune a inda Shazeen ɗin ta barshi, zama tayi kusa dashi sannan ta kira sunan sa , "Sahnish!"........... Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da ya amsa ba. "Kai za'a cikewa form ɗin nan bani ba".
"Kamar ya bangane ba?" .........Ya faɗa yana bata dukkan hankalin sa.
"Kai zaa zanawa bani ba, Kai zakafi buqatar ta"........ Dan shuru yayi kafin ya ce, "Dani dake fa duk Abu ɗaya ne, kinfi kowa sanin abinda baza ki iya ba to ni ko tunanin somawa ba zanyi ba, ni inaga kawai mu faɗawa Amla gsky".
"Ban gane a faɗawa Amla gsky ba, kana so ka kunyata mu ma kenan, nace mata iya jss muka tsaya sannan yanzu kuma muce mata bamu taba zaman aji ba ko me ?".......... Ta ƙarashe tana wurga masa wani kallon cikin ido, shi ma kallon nata yake, tsawon two minutes suka ɗauka kafin ya ɗauke kansa da faɗin, "Shikenan duk abinda kika yanke, amma ki tuna shi dai karatu ba abu bane dake ɓoyuwa ina gudun ranar da Amla zata gane muna mata ƙarya, saboda ta ɗauke mu kamar yan uwa".
Dan shiru tayi tana tunani kafin ta ce, "A tsawon lokacin da mukayi duk bata taɓa fahimta ba sai yanzu, kai dai ka bari ɗin a zana makan kawai"......... Bai sake cewa komai ba ya tattare kayan sa ya wuce ɗaki, ita kuwa gyara zama tayi tare da nutsawa cikin duniyar tunanin rayuwar su.
-------------------------√
Tsaye yake kunnen sa maqale da waya, kallo ɗaya zaka masa Ka tabbatar da ba'a cikin dukkan nutsuwar sa yake wayar ba. "So nake kawai Ka binciko min ta yadda akayi har ya samu visa ya fita wata ƙasar, kuma ma ya akayi ba wanda ya sani bayan kuma a yanzu bashi da ikon ƙetara ko da iyakar ƙasa ne bare kuma ya yi tafiya wata ƙasar a jirgi".........Daga daya bangaren akace. "Oga Awais duk iya binciken da zanyi nayi shi a dai bangare na amma babu wata shaida data bayyana mana cewa Amjad ya fita daga ƙasar Nifaz, domin ɗazu na aika yarana airport ɗin su min bincike kwata kwata bama sunan sa a list ɗin mutanan da suka tashi daga birnin Nifaz a ranar da kuma satin nan gabaɗaya".
"Amma an tabbatar min ya shiga WorldLink international airport a shekaran jiyan da yamma"......... Awais ɗin ya faɗa cikin yanayin dake nuna a qage yake da samun bayanan da yake so.
"Tabbas ya shiga airport Amma saidai wani abun yaje yi, dan gaskiya bincike na ba kuskure a ciki".........takaici yasa ya ƙasa bashi amsa sai kawai ya Kashe wayar tare da dafe Kai cikin takaici ya furta, "Oh sh**t yaron nan Yana son wargaza mana lissafi fa".........Wata number ya sake dialing ana ɗagawa ya ce, "Akwai wani labari ne ta wajen Ka?".
"Akwai matsala dai, dan ni whl kai na yana barazanar rabewa biyu, idan fa harta tabbata Amjad ya fita alkadarin mu ya karye, burikan mu sun watse, sannan sirrikan mu na barazanar bayyana, gashi ina ta neman number Julaybin bana samun sa na kirawo Atiq yace min shi tun safe ya fita, na kira Bisma kuma ta shaida min julaybin din ya dade da fita, nayi tunanin har kaina ya kama ciwo".
"Tsaka mai wuyar da kake ciki Nima ina cikin ta Nuhail ko nace muna cikin ta domin duk mu ukun nan shirin mu ne silar tarwatsewar farin cikin sa, aikin mu ne yayi sanadiyyar watsewar alqiblar rayuwar sa tare da sanyashi a tsaka me wuyar da yake ciki a yanzu, shin ya kake tunanin makomar mu wurin al'umma da kuma dada da zan iya cewa sanadiyyar abinda mukayi ne baqin ciki ya kwantar dashi saboda kasan yadda yake ƙulafuncin shegen Amjad ɗin nan".
"Haqiqa muna cikin tashin hankali ba wai, amma yanzu miye mafita?".
"Mafitar mu ɗaya ce shi ne muyi fatan Kar zancen tafiyar da aka faɗa ya fita wurin Al umma, ALLAH kuma ya rufa masa asiri ba'a samu wani dan media ya masa hoto ba a airport ɗin"..........."Kuma Awais da gasken yayi tafiyar?"........Nuhail ya tambaya.
"Ba zan iya ce ma komai ba Nuhail, bangare biyu sun tabbatar min da Amjad yayi tafiya bangare uku kuma sun tabbatar da babu jerin sunan sa a wa anda suka tashi ma".
"To yanzu a wace matsayar zamu tsaya, Nima bangare na na saka a bincika mi........" Bai ƙarasa maganar ba ƙira ya shigo, "To gama shi nan ana kirana".
"Karka kashe ɗaga nima inaso inji".......... Picking Nuhail ɗin yayi da faɗin, "kawule ya Ake ciki?".
"Ranka ya dade daga farkon titin airport ɗin zuwa cikin sa gabaɗaya ɗauɗauku 15 ne, a kowacce kuma result ɗaya ne an shiga dashi airport ɗin daidai karfe 4:40pm a mota kirar range rover silver colour tinted glass, saidai an samu ɗaukewar wasu daga cikin cameras ɗin daga shigar sa wa'anda sune suka wargaza mana lissafi a yanzu, kasancewar baza mu iya tantance ya shige cikin filin tashin jirgin bane ko kuma bai Shiga ba, saidai an auna nauyin tayar motar da suka shiga nauyin ya ragu akan yadda ta shiga hakan ya tabbatar da ya sauka daga motar kenan"......... Duka nuhail ya kaiwa bango cikin qunar rai ya ce, " Duk yadda za'ayi Ku gano cewa ya tashin ne ko kuma bai tashi ba ko nawa ne zamu biya kasan kuɗi ba matsalar mu bane".
"Haka ne yallabai Amma kasan dokar daka ce akan aikin, so munayin sa ne ta sirri idan har zamuyi da zafi zafi to tabbas zance zai iya fita"......... Awais ne ya tare maganar da faɗin, "kaga Kubi a hankali Ku dai kawai Ku gano mana ya fita ko kuma yana cikin birnin Nifaz ne har yanzu"..........."Shikenan ranka ya dade zamuyi iya kokarin mu".
"Zan tura ma na mai yanzu"........... Nuhail ya faɗa, shi kuma ya shiga zuba masa godia, katse kiran yayi, yayinda Awais ya ce, " Nuhail kana ganin baza mu gwada Kiran Amjad ɗin ba ".
"Mu kirashi mu masa uwar me, zamu bada Kan mu ne kawai, kuma hakan zaisa yayi zargin wani Abu tunda ba saba kiran sa mukayi ba, kasan shi da brain".
"Shikenan, Bari muga abinda hali zaiyi, in na gama abinda nike anjima maybe zan shiga gida wurin hajiya ".
"In Ka fito daga gida Ka kirani sai mu haɗu a can".......... Da haka sukayi sallama tare da katse wayar.
TO FA, MY PEOPLE NI KAINA ABUN NAN YA FARA ƊAURE MIN KAI FA🤔 TO WAI SHIN TSAKANIN SU AWAIS DA SU HAJJ ZAWAAD SU WAYE KE DA ALHAKIN DUSASHE TAURARIN AMJAD? GASHI DAI KOWANNE BANGARE SUNA IKIRARIN DA SA HANNUN SU A CIKI? TUKUNNA MA MIYE MATSAYAR DA SUKE SAN CIMMA A KANSA? MEYSA SU DUKA SUKE FARAUTAR ABU ƊAYA? WANI IRIN SIRRI NE KE LULLUBE DA AMJAD DIN? SHIN SU HAJJ ZAWAAD SUN SAN CEWA SUNA FARAUTAR ABU ƊAYA DASU AWAIS NE ? TO WAI AMJAD YA BAR ƘASAR DA GASKE KO KUMA DAI AKWAI WANI ABUN DA YA FARU DA MU BAMU SANI BA?🤔
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
___________________________________
@whatpadd pen_of_simplicity
STEP 1
PAGE _______14 & 15
Tana zaune duk abun duniya ya isheta tun ranar dasu Philip suka zo gidan da daddare take neman layin sa bata samu, ga dad da mumu sun hura Mata wuta da zancen Farshad ɗin da suke son haɗa su aure, tayi nitso cikin tunani taji wayar ta na ringing, ɗagowa tayi tabi wayar da harara dan tasan bazai wuce jarababben Farshad ɗin da ya takurawa rayuwar ta ba, ɗauke kanta tayi ba alamar zata dauki wayar har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa. A fusace ta warto wayar da niyyar ɗagawa ta gaggaya masa magana koma me zai faru ya daɗe bai faru ba amma ganin number da batayi zato ba ya sata zubawa screen ɗin wayar Ido, code number ɗin ƙasar denmark ce ɓaro ɓaro kafin tayi yunqurin ɗagawa Kiran ya katse wani ya sake shigowa, ɗagawa tayi ba tare da tayi magana ba, nutsatstsiyar muryar nan tasa ce ta daki kunnen ta, "In ba Nayrah ba waye Amjad zai wa Kira har uku bai yi picking ba".
Take ta manta da fushin da take dashi a shagwabe ta ce, " Amour....." Sai kuma ta fashe da kuka.
"Kin ga abinda bana so ko, in Kukan zakiyi Bari na kashe sai kin gama"........Da sauri ta haɗiye Kukan nata tana faɗin, " kayi hakuri Dan ALLAH karka kashe".
"To naji, faɗa min yanzu waya ɓata miki rai har yayi sanadiyyar zubar tsadaddun hawayen nan".......... Sake shagwaɓewa tayi kamar yarinyar goye cikin wata irin baby voice ta ce, "ba kai bane" ..............Saurin tashi yayi daga kishingiɗen da yake a wani makeken gado da zai iya cin mutum shida ko bakwai, ba wani tarkace a ɗakin sosai amma ɗakin ya tsaru iya tsaruwa, daga left side dinsa glass ne a maimakon wall zaka iya hango komai da kowa dake waje, amma shi kuma na waje bazai iya ganin ka ba, opposite da bed din kuwa wata TV ce manne kamar wata wallpaper dan kwata kwata bata da kaurin normal TV, sai kuma sofa guda biyu da karamin table a tsakiya, a right side ɗinsa kuma wardrobe ne haɗe da dressing mirror ɗinsa.
"Me nayi?"............ Itace tambayar da ya Mata Yana miqewa ya taka zuwa gaban glass ɗin yana kallon mutanan dake harkokin su a ƙasa hakan yasa na gane cewa shi a upstairs yake.
"Ka tsokano mana aiki fa, tun ranar daka turo yaranka ɗin nan nake neman wayarka bana samu gashi ko a online bana ganin ka" .
"Yanzun me ya faru?"..........."Dad ya ƙara ɗaukan zafi dakai domin aiken da kayi ba abinda ya magance sai ma ƙara taɓalɓala komai da yayi, da kayi shawara dani da baza kayi irin wannan aiken ba, Meysa ma kai baka zo da kanka ba ko kuma kayi magana da uncles ɗinka su samu dad da Maganar".
"Ninie!, I know what I'm doing fa, kuma kinsan a yanzu s......." Shiru ya danyi sai kuma ya canza zancen da faɗin, "ba zai yiwu na zo gidan ku a halin da ake ciki ba, amma kiyi hakuri".
"To yanzu me muke ciki, dan ni Whl wannan Farshad ɗin ya takura min ALLAH na gani".
"Kamar ya?"...........Ya tambaya yana gyara tsayuwar sa.
"Yazo gida ban saurare shi ba, shi ne yake takuramin a waya"..........dan lumshe idanun sa yayi tsawon mintuna dan har ta ɗauka ya sauka daga kan layin ma sai taji ya ce, "Bakomai!, Ni dai kawai abinda nake so dake shi ne ki daina tada hankalin ki, saboda in kika tada hankalin ki ni kuma bazan samu nutsuwar yin abinda ya kamata ba kinji am Mata na".
Murmushi tayi tana jin wani sanyi a ranta ta ce, "Shi ne kayi tafiya baka faɗamin ba, sannan kuma ka rufe duk wata hanyar da zan same ka dan kawai ka tada min da hankali ko"..........kwantar da murya yayi har lokacin kuma idanun sa a lumshe suke ya ce, " Ba haka bane Ninie, wayar ce ta samu Matsala ban kuma samu time na maida hankali na saya wata ba".
Cike da shiririta ta ce, "Ai baka damu dani bane saisa, da ace ka damu da jin murya ta ai da a lokacin zaka saya wata".......... murmushi yayi me sauti da faɗin, "kullum ƙorafin ki iri ɗaya, ya kamata ki caza style ko kuma ki bani gari na