BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   25 / 53

72K to 75K   out of 156.9K words

ba kowa zaka kama ba Yan uwan ka ne tunda su suka daura auren s ........" Maganarta ta yanke a lokacin da aka buɗe kofar ɗakin.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22




STEP 1


PAGE _______33 & 34


Maganarta ta yanke a lokacin da aka buɗe ƙofar ɗakin ne.

Shi kuwa Amjad yana fita ya haɗu dasu yaya Adam na shigowa, Yaya Najib ne ya tsaida shi tare da faɗin, "Yauwa Amjad gwara da ALLAH ya haɗamu, dama muna neman ka Kuma ko bamu sameka anan ba daman zamu sa a kiraka".

"ALLAH yasa ba damuwa bace". Ya faɗa cikin ƙoƙarin sa na saita muryar sa gudun bayyana ɓacin ransa.

"Amjad so muke ka faɗa mana gsky shin Kai ne Mijin Nayrah da gaske ko kuwa yaya abin yake ne?"............" Ni ne". Ya amsa musu kai tsaye.

Kallon yaya Adam yaya Najib yayi kafin ya ce, "To kuma meysa zaka ɓoye kaƙi bayyana kanka har saida aka ɗaura auran, kuma me sa ka turo dan uwanka matsayin shi ne mijin".

Ɗan gyara tsayuwar sa yayi da faɗin, " In da ace ni ne da kai na nazo a jiyan da a yanzu ba'a ɗaura auren ba, saboda ku ma bana yanke zaton irin abinda mahaifin ta yayi shi zakuyi, amma da na tura Hunaiz a matsayin ni ne, gashi a yanzu ai an ɗaura auren ".

Yaya Najib ya ce, "Amma daka bayyana mana kanka da sai yafi ai, saboda aure ba'a yin sa da ɓoye ɓoye, Kuma bincike a aure ai ba laifi bane".

"A yanzu ma Kuna iyayin binciken ai Uncle, dan amsar da zaku samu kafin auran da yanzun duk ɗaya ce Kuma nasan kun santa".

"To wai hakan ne ko Kuma ah ah magana ne ta mutane?"...........Faɗin yaya Adam ɗin cike da tararrabin wannan lamari.

Hannayen sa ya zube cikin aljihu tare da ɗan girgiza kansa ya ce, "Lokaci alkali, Mai laifi Yana iya cewa bashi bane dan Kare kansa, haka Kuma ko da marar laifi ne cewa zaiyi ba haka bane, ba wai zai amsa da gaskiya bane saidai yace bashi bane, domin tabbatar da ni ɗin ne wanda ƴar ku ta aminta dashi kuna iya ƙarasawa ciki"............Yana kaiwa nan ya raba ta tsakiyar su ya wuce Yana Ƙara jawo p cap ɗinsa yadda zata rufe fuskar tasa da kyau, Kamal da yaja gefe ganin yana magana dasu yaya Adam yayi saurin rufa masa baya.

Barin faɗa muku wani abu ada ba abinda Amjad ya tsana irin P cap amma tunda wanna maganar ta fito sai ya zaman ko Ina yaje mutane na nuna shi da baki wasu da hannu a ɓoye ko a fili, kowa da irin abinda yake faɗa a Kansa, hakan yasa ya qulla abota da ita saboda ɗauke idanu a Kansa. WANNAN KENAN.


"Me ka fahimta a zancen nan nasa Najib?"............ Hannu yaya Najib ya watsa alamar ALLAH masani, sannan ya fara tafiya ganin haka yasa yaya Adam rufa masa baya, sai da suka tsaya sukayi tambaya aka nuna musu ɗakin da Nayrah ɗin ke jinya.

A buɗe suka samu Ƙofar ɗakin dan haka suka sa Kai kawai tare da yin sallama, duk cikin su rasa me amsawa akayi sai su Nashwa da suka amsa tare da gaishesu.

"To bayan wancan cutar da kuka mana sai da kuka sake biyo baya kuyi mana wata kuma? Dan daga ganin ku ba alheri bane ya kawo ku"......... Faɗar Mumu cikin ɗaga murya.

"Eh eh me ya kawo ku nan, Kuma me kuka biyoni ku min?".............Dad ya faɗa yana muzurai.

Yaya Najib ne ya ce, "Kabi a sannu Nu'uman duniya wanda bai zo bama jiransa take ballatana mu da muke cikin ta, mu dama mun daɗe da barin ka da matarka da Kuma iyawar ka dan haka yanzu ba wurin ku muka zo ba. Sai ku jira har sai lokacin da muka zo dan ku sai kuyi abinda ke ranku".......... Yunkurawa Nayrah tayi da niyyar zama yaya Adam ya tare ta ta hanyar faɗin, "koma ki kwanta Nayrah, ALLAH ya baki lpy ya tsare gaba"............. Komawa tayi ta kwanta tana amsawa da Ameen, yaya Adam ya sake cewa, "Nayrah shin kinsan Wanda kika amincewa jiya a waya cewa a ɗaura muku aure?"............ "Eh Uncle Adam na sani".

"Waye?"............ Yaya Adam ya sake tambaya. "Amjad Hashim Darwin".

"Au da sanin ki ma kenan munafuka kina gadon asibitin kina shirya wata ƙulleleniyar". Faɗin Dad a fusace .

Yaya Adam ya ce, "To alhamdulillah Nayrah mu zamu koma, ALLAH ya baki lpy dama abinda mukazo mu tabbatar kenan saboda yadda abun yazo yasa muka shiga shakku, Amma tunda da sanin ki da Kuma amincewar ki ALLAH ya bada zaman lpy ya kauda fitina a tsakanin ku" .

"Ameen Uncle Adam nagode sosai. Uncle Najib nagode a gaida min iyani ".......... "Zataji in sha ALLAH ". yaya Najib ya faɗa daga nan suka juya sukayi waje ba tare da sun sake kallan ko inda su Mumu suke ba, a fusace dad ya ce, "Banga amfanin zaman ki ba latifa, dama duk abinda yake faruwa dani har mutane ke jin haushi na kece sila".......... Da mamaki Mumu ta ce, "Alhaji ni?". Tare da nuna kanta da yatsa.

"Kwarai kuwa kece nan, gabaɗaya kin hana rayuwata zaman lpy, haba da ALLAH wanna wani irin abu ne "........... Ya faɗa yana juyawa ya fice cikin ɓacin rai shi ma.

Cike da fargaba Mumu ta ja kujera ta zauna tana bin bayan Dad da kallo cike da son gasgata abinda Dad ɗin ya faɗa. "Mumu kiyi hakuri dan ALLAH".......... faɗin Nayrah idanunta na cikowa da kwalla. "Whl idan kika ƙaramin magana Nayrah sai na rufe ki da duka, ba a gadon asibiti ba ko a makara kike ba abinda zai hanani cin ubanki yau"............. Wani abu me ɗaci Nayrah ta haɗiye tare da juyar da kallon ta wani wuri, tashi su Nashwa sukayi suka fice daga ɗakin dan karma suyi wani dan kuskure faɗan ya dawo kansu, tunda suka ga ta gadon asibiti ma ba'a barta ba ballatana su da ƙafafunsu.



----------------------√



Shuru Sahnish yayi bayan ta fita Yana tunanin maganar ta can kuma ya maida kuɗin aljihun wandon sa ya ɗauki ɗan makullin ɗakin data bar masa ya fice ya kulle mata ɗakin ya wuce nasa.

Tana fita bakin titi ta nufa tare da tsayawa ba tare da tasan inda zata ba kawai dai taji gidan na Mata zafi ne ita kuma ta riga ta kira hajiya tace Mata baza ta samu damar zuwa aiki ba ballatana yanzu ta shirya ta tafi. Mai tuktuk ne ya tsaya a gabanta tare da faɗin, "Hajiya tafiya me?".........."Eh". Ta faɗa ba tare data duba ko waye ciki ba ta hau . "Ina kikayi hajiya?"

"Duk inda Ka nufa ".......... Ɗagowar da zatayi idonta ya shiga cikin nasa kamar kullum yau ma ƙananun Kaya ne a jikinsa da sukayi matuƙar amsar sa, hannun sa riqe da wayar sa idonsa a kanta ganin ta juyo gareshi ya sashi ɗauke idanunsa tare da faɗin, "ki daina kallo na"............. Kwata kwata baisan meysa ba a duk lokacin da Hushaima ta zuba masa ido sai ya dinga jin jikinsa na amsa wa gabaɗaya, tun ranar da ya fara ganin ta a gidan, saboda Hushaima ALLAH ya bata ƙarfin ido Wanda ko yaya ta zuba ma su sai kaji su har cikin ɓargon Ka .

A nata bangaren kuwa ɗauke kanta tayi tana mamakin yadda akayi har yake kamata tana kallon sa, dan ita kwata kwata kallo ba dabi'ar ta bace dan ko a hanya zaku haɗu to fa zaka iya zuwa ta gabanta Ka wuce bata sani ba don gabanta kawai take kallo, Amma sai gashi takan samun kanta da yiwa Jey dogon kallo. Maganar Mai tuktuk ya dawo da ita daga duniyar data tafi, "Hajiya nace ni fa Crimson bites na nufa, nan zan sauke bawan ALLAH nan"............" Ba damuwa nima sauke ni a can ɗin"............. Kallon ta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juyar da kansa yana kallon titi.

Suna hawa wani titi kawai wasu yan zauna gari banza suka kama tuktuk ɗin suka ɗale ba alamar imani a tare dasu suka zaro wuqaqe tare da faɗin, "Wayar Ku ko ranku?".......... Me tuktuk cikin rawar jiki ya ɗauko yar rakani kashin sa ya miqa musu, shi kuwa Jey dama ba musu ya ce, " Dan ALLAH to ku tsaya na cire SIM ɗi na". Hushaima kuwa kallon su tayi ta watsar, "ke ina wayarki"........... Ɗayan ya faɗa da buɗaɗɗiyar muryarsa.

Fuska a haɗe ba alamar tsoro ta ce, "Na barta a gida mana, da irin ku a gari mutum zai dinga yawo da waya ne, ai saidai in binmu zakuyi sai na ɗauko na baku tunda ina tsoron ku". Ta faɗa tana watsa musu Hararar ƙasan ido.

"Haba baiwar ALLAH ke kuwa bakya San rayuwar ki ne, me akayi akayi waya, wayar banza Dan ALLAH ki basu". Me tuktuk ya faɗa jikinsa na rawa.

A faɗace ta ce, "Sai kazo Ka ɗauko musu ai, in kuma rai na a hannun su yake to karsu barni na Ƙara minti ɗaya, tana kaiwa nan ta sauka daga tuktuk ɗin tare da faɗin, " Waye me karɓar wayar a cikin ku ".

Kunna babur ɗin me tuktuk yayi Yana faɗin, " Ni Kam tafiya zanyi whl kije can Ku ƙarata, maybe ma tare suke ".......... Saurin dakatar dashi Jey yayi da faɗin, "Haba mana Malam sai kace ba musulmi ba, ai bai kamata a barta anan ba, kuma ku daina ɗaurawa mutane abinda baku da cikakken sani a kansa"............ Yana kaiwa nan shima ya dira daga tuktuk ɗin daidai lokacin da Hushaima ta juya tana magana dasu da alama tsiwar nan tata ta ƙarfin hali take musu, ɗaya daga cikin su ne ya daga wuqar zai burma Mata a wuya, kallon titin Jey yayi kwata kwata irin titin nan ne da babu mutane sosai da sauri ya nufesu domin taimaka mata saidai kafin ya ƙarasa kawai yaga tayi wata irin juyowa kamar walkiya sai gani yayi sunja da baya suna layi kafin lokaci guda su zube a ƙasa. Wani irin birki yaja tare da saurin toshe hancin sa da hannun saboda ganin abinda Hushaima tayi amfani dashi, hoda ce wadda ake amfani da ita wurin bugar da mutum tare da sanyawa ya tafi bacci ko dogon suma.

Sunkuyawa tayi tasa hannu ta zaro wayar Jey da ta me tuktuk ɗin ta nufo wurinsa, tana ƙarasowa ta zira masa wayar a aljihun gaban rigar sa sannan tayi wajen tuktuk ɗin.

Jey da ya daskare a wajen yabi bayanta da kallo kafin ya juya ya bita shi ma cike da ɗinbin mamaki tare da tunanin wacece wannan yarinyar wai. Yana shiga me tuktuk da ya danqi wayarsa ya bawa machine ɗin wuta suka bar wurin, dan shi ma akan idon sa akayi komai saida suka fito idon mutane ya ce, " ke kuwa baiwar ALLAH me ya haɗaki da irin wanna hodar?".

"Saboda tsaro mana, ko kai yanzu baka ga amfanin ta bane, yanzu fa rayuwar ta zama iya ruwa fidda kai, in ka iya allon ka ka wanke".

"Amma fa hakan na da hatsari Hajiya, dan kaman kina bawa mutane ƙarfin guiwa ne cewa su ɗauki makamai da kuma doka a hannun su".

"Au sai yanzu ka sani, baka san cewa doka ta bawa dan ƙasa damar amfani da ƙarfin da ya dace ba don kare kansa ko dukiyarsa daga wasu masu hari. Ballantana kuma a yanzu da bamu da tsaro. To saman ma a gurɓace take ballantana yan ƙasa, in har da sama a gyare take to fa dole yan ƙasa ma zasu zama gyararru. Yanzu ire iren mutanan can kana hanasu abinda suka nema zasu sokeka kamar raqumi kuma sun soke banza ba abinda za a musu, to wa ke da asara? Yan uwanka ne da abokan arziki, dan haka in ka samu kanka a irin wannan halin kayi iya naka ƙoƙarin ka fara tsira da rayuwar ka tukunna sai ka sako jami'an".

Shi dai Jey kallon ta kawai yake yama kasa cewa komai sai tunane tunane ne ke kawowa ƙwaƙwalwar sa farmaki, dukda tanajin idanunsa na yawo a jikinta bata ko nuna ta sani ba bare ta kalla inda yake ba.

A ƙofar gate din Crimson bites Mai tuktuk ɗin ya sauke su, juyawa tayi zata tafi ya ce, " Hajiya kudin fa ?".......... Da hannu ta nuna Jey da har lokacin bai sauko ba ta ce, " Zai biyaka ".

"Bangane zan biya ba kin bani ajiyar kuɗi ne?". Ya tambaya kai tsaye.

"Eh?".......... Me tuktuk ɗin ya tambaya yana juyowa ɗan shi bai ji abinda Jey ɗin ya faɗa ba kawai dai yaji sautin Magana ƙasa ƙasa.

"Na baka mana, ai ba nawa kaɗai bama har da naka da zaka biya duk na haɗa na baka ".

"Ikon Allah". Me tuktuk ya faɗa Yana kallon Hushaima da mamakin yadda akayi taji maganar da ko shi da yake kusa dashi baiji ba bare ita da take da dan tazara dasu dan ita tana daga wajen tuktuk ɗin ne.

Jey bai Ƙara cewa komai ba yasa hannu a aljihu ya ɗaukowa mai tuktuk ɗin iya nasa kuɗin, Dan da yayi niyyar biya mata amma yanzu ya fasa, sai dai me dubu biyu ya ci Karo dasu wanda baisan ya akayi suka zo jikin sa ba, da mugun mamaki ya ɗago suka haɗa ido harara ta watsa masa tare da yin gaba ta shige wurin . "Malam za dai ka biya kuɗin ko dan kaga ta tafi".

"Nawa ne ?"........... Ya tambaya daƙer dan ji yake kamar ya zura a guje anya yarinyar nan mutum ce kuwa . "Ɗari takwas"............ Ya bashi amsa, A maimakon ya bashi dubu ɗayar ya canza ya bashi ɗari biyu sai ya haɗa duka dubu biyun ya bashi, sannan ya sauka da sauri yabi bayan ta ba tare da ya kula me tuktuk ɗin dake ce masa dubu biyu fa ya bashi.

Samun ta yayi har ta nemi wuri ta zauna a wani table dake can ƙarshe, saurin tsayawa yayi tare da saita nutsuwar sa sannan ya cigaba da tafiya, sai da yazo table ɗin da take zaune yaja kujera ya zauna, "Ya akayi kuɗin ki yazo jiki na?". Shine tambayar da ya fara mata .

"Kuɗin wa'ancan yan hau ɗin ne, harajin wayar ku da suka so awon gaba da ita ne na karɓa muku".

"Ya akayi kika samu wancan hodar ?"........... Ya sake ɗaura mata wata tambayar. "Bai shafe ka ba ". Ta faɗa tana bin wurin da kallo.

"Wacece ke?"............ Ɗagowa tayi tare da ɗaura dukkan hannayen ta kan table ɗin ta tokare habar ta dashi sannan ta zuba masa eyes ɗin ta, ɗauke kansa yayi dan bayaso ya sake ce mata ta dai na kallon sa, taji haushi ta fasa bashi Amsa, ɗan gajeren murmushi tayi sannan ta koma ta jingina da bangon kujerar tana me janye idanunta a kansa ta ce, "Zan gaya ma wacece ni da sharadin ni ma zaka gaya min wanene Amjad Hashim Darwin"............ Da wani irin sauri ya ɗago da faɗin, "Me... M.. me kikace ?".



-----------------------√



Tsaye yake gaban wardrobe ɗinsa yana ciro PJ's ɗin da zai sanya wayarsa dake kan bedside drawer ta fara ƙara, matsawa yayi ya ɗauka ganin sunan dake yawo akan screen ɗin ya sashi saurin picking tare da faɗin, "Barka da dare sir"........... daga ɗaya bangaren akace, "Yauwa barkan ka dai Rear admiral Juraysh, ya aikin?".........cike da girmamawa ya ce, "Aiki da godia Alhamdulillah ".

"To Masha ALLAH, dama na kira ne na sanar ma kaya na zasu shigo yau da daddare kamar yadda aka saba, da tun ɗazu naso sanar ma to ina dan wani aiki ne, ka sanar da mutanan ku dake iyakar ruwan, banaso a samu Matsala da ALLAH ".

"In sha ALLAH baza a samu ba sir, yanzu nan zan sanar dasu "..........."To Shikenan Juraysh, Nagode sai ka jini".

"You are welcome sir"............ Ya faɗa cike da jin daɗin da muryarsa ta gaza ɓoyewa.

Yana katse kiran Juraysh ya lalubo wata number ya danna mata kira ana ɗagawa ya ce, "Na gama da wancan matsalar, yanzu kawai idan kaya sun iso dama kasan yadda mukeyi ai, Saidai wa'annan fa daban suke da wa'ancan dan sun gayamin akwai excessive nitrates and nitrites, ko yaya akayi amfani dashi amfani da wannan takin amfanin gona zai yi tsiro yayi kyau amma daga baya kaɗan komai zai lalace, in kuwa an samu wanda suka tsira to fa in al'umma sukaci wannan kayan gonar zasu illatu. Sannan Ku tabbatar kaso casa'in na kasuwannin taki an musu juye da wannan sabon takin, ku basu shi a farashi me sauƙi ƙasa da farashin da su suke saro nasu sannan kuyi amfani da dabarun ku wurin zayyana musu irin kyawun shi wannan takin. And batun su Alhaji Abid su ma, akwai kayan da muke basu a ciki a cire a basu".

"ALLAH ya taimaki HE, A daɗe anayi sai gaskiya"......... wani ƙayataccen murmushi Alhajin birnin yayi tare da faɗin, "Ba damuwa ka sanar dasu Abid ɗin dai da ALLAH".

"Yanzu kuwa ranka ya daɗe, na Barka lpy"......... bai ce komai ba sai girgiza kansa da yayi kamar na cikin wayar na gabansa sannan ya tsinke kiran, ya danyi wasu latse latse kafin ya rufe wayar, ya miqa hannu kan stool ɗin dake gabansa ya dauki tumbler dake ɗauke da sassanyar grapes juice har raɓa take.



_______________shi kuwa Juraysh cike da farin ciki ya shiga neman number mutanan su

25 / 53