Author : Young Writer Category : Tknovels
isa a faɗi aibun wannan ɗan gwal ɗin ba a gabanta".
"Muje kawai"......... Julaybin ya faɗa Yana miqewa tare da gyara zaman hannun babbar rigar sa suka yi waje.
---------------------√
Hushaima kuwa suna zuwa police station DPO ya bada umarni a wurgata cell sai anji halin da Huda take ciki a hospital tukunna. Su kuwa su Hajiya Sulaimiyya sai yamma sukazo itada Hajiya Yakura, iso aka musu zuwa office ɗin DPO, nan Hajiya sulaimiyya ta sake kora masa jawabi sannan aka ɗau statement ɗin su saboda Hajiya sulaimiyyar tace baza ta yarda ba sai anje kotu, bayan an gama komai ta cika DPO da kuɗaɗe masu nauyi sannan ta ƙara jaddada masa ko uban waye yazo kar a bada bailing Hushaima, daga cikin cell sai gaban Alkali. Sanin matsayin ta yasa DPO ya amince without second thought, gashi kuma an cika shi da yan canji.
READERS A TUNANIN KU WACECE WANNAN HAJIYA SULAIMIYYA ƊIN ?
Shi kuwa Sahnish dama lokacin ɗauko Shazeen daga makaranta na cika yaje ya ɗauko ta suka tsaya ya saya mata abinda zata ci suka wuce gida. Ko da suka koma gidan a rufe suka samu ɗakin Hushaiman, bai wani damu ba dan yasan wani lokacin suna riga ta dawowa dan haka yace Shazeen ta wuce ɗakin sa shi kuma yaja benci kusa da Barde dake zaune yana ta faman lissafe lissafe shi da Uday na kuɗin da zasu rarraba wa mutanen su wanda zasu fita rally tare kamar yadda su ma aka neme su aka ɗaura su akai dan su kasance ƴan daban siyasa.
Shi ma zaman sa yayi yana lissafin turarukan sa da wanda suka ƙare da wanda zai ƙara siyowa da kuma ribar sa, saidai har ya gama Hushaima bata shigo ba hakan yasa ya tashi ya wuce ɗaki ya rage kayansa ya ɗauko bokiti ya fito ya ɗibi ruwa ya shiga wanka, ko da ya fito ya koma ɗakin ya shirya ƙofar gida ya fita sai dai shuru shuru har akayi kiran sallar magriba ya koma cikin gidan yayi ya sake fitowa ya zauna, har lokacin sallar isha yayi ya sake tashi yaje yayi ya dawo ba Hushaima ba labarin ta, tun yana ɗaukan abun wasa har ya haqura ya tashi. Cikin gidan ya koma ya wuce ɗakin sa, wayarsa dake hannun Shazeen ya karɓa ya shiga contact ya lalubo number Hushaima yayi dialing dan da yaqi kira ne saboda fushin da yake da ita, missed call ɗaya, missed call biyu, missed call uku ba'a ɗaga ba duk da hankalin sa ya fi bashi yau ma wannan saurayin nata ne ya ɗauke ta daga wurin aiki amma Kuma yasan duk inda take bata qin ɗaukan wayar sa, saboda a duk inda take hankalin ta yana kansu indai zata ga wayar sa zata ɗauka taji lpy yake kira, wannan tunanin da yazo masa ya sanya hankalin sa tashi, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya tare da faɗin, "Shazeen saka hijab ɗin ki mu fita"......... Ɗaukan hijab ɗin nata na makaranta tayi ta saka dan dama kayan makarantar ne a jikinta har lokacin saboda duk kayanta na ɗakin Hushaima ne kuma key na wajenta.
Riqe hannunta yayi suka fita bai tsaya ko ina ba sai wurin aikin su Hushaima dukda yasan a irin wannan lokacin ba lalle ne ya samu kowa ba, hakan ne kuwa ya kasance dan a kulle ya samu wurin sai wani mutum tsaye da touchlight ɗin sa yana ta haske haske, ƙarasawa yayi wurin sa tare da masa sallama, amsawa yayi yana me haske su da touchlight ɗin. Hannu Sahnish yasa ya kare fuskar sa da faɗin, "Malam ka haske mana ido kuma ai"..........."Eh to ai dole na haska saboda tsaro rayuwar ta yanzu ba gaskiya ne, Daga ina haka?".
Gyara tsayuwar sa yayi kafin ya ce, "Da ALLAH nazo tambayar yar uwata dake aiki ne anan, munga lokacin tashi yayi kuma bata dawo gida ba shi ne nazo tambaya naji ko lpy"..........."To ai yaran dake aiki anan da yawa waccece daga ciki?".........."Bansan ko kasan sunan ta ba, Hushaima!".
"Au tooooo, wata yar fisgagga masifaffiya zakace, ai wata yar masu kuɗi ta fasawa kai ɗazu da rana, to shi ne matar ta kira police suka rakice ta can dai haka sukayi gabas maso yamma ban dai san wani station ɗin aka wuce da ita ba".
"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun³"........ shi ne abinda Sahnish yake ta nanatawa kafin yayi ƙarfin halin faɗin, " Da ALLAH Malam ko kasan station ɗin da suka je?"..........." Kaga nifa gadi kawai nake musu, saidai na baka lambar Hajiyar me wurin sai ka kirata kaji dan nasan ita baza ta kasa sani ba".......... Da sauri ya ce, "To Nagode, bani lambar"...........Ya ƙarashe yana zaro wayar da sauri hannun sa har rawa yake wurin loda number da me gadin ke faɗa masa cikin wayar.
Ita kuwa Hushaima ƴan sandan nan sunyi juyin duniya ta basu number wani nata su kira taqi, su dama dan su kira ne su faɗa musu halin da ake ciki ne ko suna da halin ɗaukar lawyer, sannan a samu wanda zai dinga kawo Mata ruwa da abinci har lokacin da za'a shiga kotu, amma Hushaima ko kallon su ma batayi ba ta bawa banza ajiyar su, da suka gaji suka fadawa DPO yace su barta da kanta zata bada in taji wuya, saurayen cell kaɗai in aka barta dasu sun isheta.
Sahnish na kiran Hajiya yakura ta shaida masa police station ɗin da Hushaiman take, ba ɓata lokaci yaja hannun Shazeen suka nufi police station ɗin, bayan sun shiga yayiwa yan sandan dake kan kanta ɗin sallama suka amsa, " Yauwa sannu"......... Wani daga cikin ɗan sandan dake rubuce rubuce bakin kantar ya faɗa yana bin Sahnish ɗin da kallo ganin yadda yayi wani iri kamar marar gaskiya saboda rashin sabo da irin wuraren, dan shi duk abin tashin hankali baya son sa, ganin uniform din ƴan sanda ma ko soja firgita shi yake ni kuwa nace lalle Hushaima tayi gsky, anya Sahnish ba maza ya rako duniya ba kuwa.
Daurewa yayi da faɗin, "Amm da ALLAH ranka ya daɗe tambaya nake ko nan aka kawo wata da sukayi faɗa a wani salon sunan ta Hushaima Sahnish Shazeen ".
"Nan ne!, Ya akayi ?".........." Qanin ta ne ni mun ji shuru ne har lokacin tashin su yayi bamu ganta ba, shi ne mukaje muka tambaya aka faɗa mana abin da ya faru da kuma inda aka kawo ta"......... Juyawa ɗan sandan yayi wurin sauran ya ce, "Constable Buhari DPO na nan kuwa?"......... Ɗan shiru Constable Buhari yayi kafin ya ce, "Anya kuwa saidai na duba banajin yana nan gsky".
"To da ALLAH je ka duba in yana nan kace masa ɗan uwar yarinyar nan ne da ke da case dasu Hajiya sulaimiyya"..........Tashi Constable yayi ya wuce ciki can sai gashi ya dawo yana faɗin, "Ya tashi saidai ya dawo gobe".
"To kaji baya nan saidai ka dawo gobe kamar ƙarfe goma haka".
"Yanzu officer ba za'a iya bamu bailing ta ba kenan?"........ Dariya yayi yana kallon Sahnish ɗin kafin ya ce, "Kai yaro baili fa kace? ai bama a fara wannan zancen ba tunda ba'a san halin da yarinyar data fasawa kai take ciki ba, dan har yanzu ance bata farfaɗo ba, kuma ma in zan Baka shawara tun wuri ka fara neman lawyer dan iyayen yarinyar sun buqaci a turasu kotu kuma har an ɗau statement dinsu ma zaa aika so batun baili duk babu shi a yanzu".
Wani irin faɗuwa gaban Sahnish yayi, cikin rawar murya ya shiga roqon su amma ko dubansa basuyi ba ƙarshe ma sai cewa ɗayan yayi, "To kai haka ma ake zuwa baili kamar zakaje karɓar sadakar kunu"......... Cikin rashin fahimta Sahnish ya ce, "Bangane ba ranka ya daɗe"..........." Shikenan tunda baka gane ba juya ka koma inda ka fito, ka dawo goben".
"To officer dan ALLAH ka min alfarma na ganta mana"........ Kallon baka da hankali suka masa kafin ya ce, "Kai baza ka ganta ba ka wuce ka bamu waje ka cika mu da surutu".......... Cikin rawar ƙafa Sahnish yaja hannun Shazeen sukayi waje hankalin sa in yayi million ya tashi, wurin wa zai nufa wa ya sani da zai masa alfarma, sun kusa minti talatin tsaye a bakin police station ɗin kafin ya yanke shawarar kiran baba ilerika. Ɗaga waya yayi ya kira shi........
Baba ilerika ne kishingiɗe a majalisar tasu shi da abokan sa sai tafka muhawara suke akan lamarin siyasar ƙasar Nifaz ɗin, Wani me suna Jarwai ya ce, " Kai ni fa Malam lawan ba zan taɓa yarda cewa ba izinin gomnati a duk wa'annan abubuwan dake faruwa ba, kai ai bani ba ma duk me hankali yasan da wata a ƙasa kawai so ake mu saki sana'ar mu, mu dogara da abubuwan da ake shigo mana dasu daga waje a Matsayin cigaba daga nan kuma mu koma ƙaraƙashin ikon su ya zama su zasu ɗinga juyamu yadda suke so, saboda bamu da ikon sarrafa komai daga ƙasarmu"............ Malam lawan ya ce, "Yanzu miye laifi dan an kawo abubuwan cigaba mun karɓa, ku bakwa ganin ƙasashen da basa ƙarɓar abubuwan cigaba ya suke? Ai basa gaba".
"Ai kuwa sunfi zaman lafiya Malam lawan, shin ka taɓa jin labarin irin wa'annan gurbattatun abubuwan dake faruwa a irin wa'annan ƙasashen? Ai babu. Saboda ta hanyar da ake shigo mana da abubuwan da ake cewa na ƙaruwa ne ta nan ake shigo mana dana cutuwa ma, Kaga ka yarda kawai jarwai ya fika gsky a wannan Maganar, taya ma to za'a ce mu saki kiwo mu saki noma za'a dinga shigo mana da komai ba sai mun wahala ba, in kuma munaso muyi da kan mu za'a shigo mana da Artificial intelligence ɗin da zasu sauqaqa mana kayi tunani fa".
Jarwai ya ce, "Ai qasimu ba dan komai bane kawai dan su rabamu da sana'o'in mu ne, kuma ba zai yiwu ba dan tunda suka fara motsa wannan Maganar to akwai shirin da sukeyi dan haka whl kowa ya nemi sana'ar hannun da ba wata shegiyar gunkin ko engine da za'a sawa battery ace zai iya yi, wannan shi ne kawai abinda zai cecemu".
Shi dai Baba ilerika yana daga kishingiɗen sa yana goga ashuwakin sa yana kallon masu wucewa ba tare da yace dasu uffan ba, wayar sa ce ta Fara ƙara, zarota yayi daga aljihun gaban rigar sa ganin Sahnish ya sashi yin picking tare da karawa a kunne. "Helo Sahnish ya akayi ne?".
"Baba akwai matsala whl".......... Yadda yaji Muryar Sahnish ɗin ya sashi tashi daga kishingiɗen da yake yana faɗin, "Subahanallahi ALLAH ka raba mana hanya da matsala, meke faruwa?".
"Baba Hushaima ce suka samu matsala da wata a wurin aikin su har ta fasa mata kai, to yanzu sun kawo ta police station nazo nayi duk iya bakin ƙoƙarina sun hana ma a ganta ".
"Tooo abinda ya faru kenan, yanzu kai kana ina ? Kuma wani police station ne?".
"Ni muna ƙofar police station ɗin yanzu......." Nan ya kwatanta masa police station ɗin.
"To ku jirani anan bari na ƙaraso, kaik jama'a daga wannan sai wannan Hushaimaaa"....... Ya ƙarashe yana kashe wayar tare da miqewa ya kalli sauran abokan nasa da suke ta faman tabka muhawara sannan ya ce, "To Jarwai mu wata yar camama ta taso, za kuma mu ƙara gaba"....... Dariya Jarwai yayi kafin ya ce, "Shege ilerika bakaso a zauna lpy in dai akwai ci a rigimar"......... Miqewa tsaye yayi yana karkaɗe rigar sa ya ce, "Ahhh to kuwa kaga laifi na ne duk inda ci yake kuma ai kowa yana so "......... "To ko nazo na raka ka ne". Faɗin Malam lawan.
"Makaho ne ni ko kuturu da bazan iya kai kaina ko ina ba har sai na nemi ɗan jagora, ko kuwa ah ah jariri ne ni da sai an ɗaukeni?"......... Girgiza Kai Malam lawan yayi yana Dariya ya ce, "kaga ni fa wasa nake mutumi na, jeka ka dawo".
Qasimu ya ce, "Kaga ilerika jeka abunka rabu da su, kar ma su ɓata ma lokaci harkar ta wuce ka".
-------------------------√
AURELLON SULTANATE💎
Ziyada ce ta shigo falon da Ummu ke zaune tare da hadiman ta, kowa da aikin da yake wasu kuma suna zaune a gabanta suna mata hira, wasu suna matsa mata ƙafafu, wata tana haɗa mata tea, suna ganin shigowar ziyadan suka fara risinawa suna mata Barka da shigowa duk da a zaune suke. Cikin takun da ke nuna eh ita ɗin jinin sarauta ce kuma sarautar ma ta Aurellon ta ƙaraso, wuri ta nema ta zauna ba tare da tayi magana ba, ganin yanayin fuskarta yasa Ummu faɗin, "Ku tashi kuje kawai sai na neme ku"............" A tashi lpy sarauniyar sarauniyoyi, ALLAH ya ƙara miki lpy"....... Suka haɗa baki wurin faɗa suna miqewa. Wadda take haɗa tea ce ta ce, "Ranki ya daɗe za'a miqo tea ɗin ne ko naje?"......... Hannu kawai ta miqa mata alamar ta bata, duqawa tayi kan guiwowin ta sannan ta miqa mata ɗan ƙaramin mug ɗin na gold dake haɗe da wani ɗan ficicin teaspoon da kuma saucer da aka ɗaurashi akai. Tana karɓa Khadimar ta juya ta bar wurin.
"Meke faruwa ne ziyada?"....... Ummu ta tambaya tana kurbar tea ɗin dake hannun ta .
Kafin ziyada tayi magana Reeslan ya shigo yana gyara zaman band ɗin kansa, sanye yake da wata Black Polo t shirt data fito da kyakkyawar surar jikinsa ta cikakken ɗa namiji sai caramel colour skinny jeans da ya sa, baiyi masauki ko ina ba sai gefen Ummu, ɗan tsukakken bakinsa ya kai bakin mug ɗin dake hannun Ummun ya kurɓi tean, sai kuma ya gyara zamansa tare da sanya dukkan hannayen sa biyu ya karɓe mug din da saucer yana faɗin, "Ummu saidai fa kisa a kawo miki wani, waye ne ya haɗa a cikin khadiman naki?"........... Sakin baki Ummu tayi tana kallon sa kafin ta kai hannu ta riqe kunnen sa ta murɗe, ɗan ɓata fuska yayi amma bai ce komai ba, dungure masa kai tayi tare da faɗin. " Ka nutsu ɗan ALLAH Reeslan, ka ajje duk wani rashin ji a gefe, ka sani kai ne fa magajin kujerar Aurellon, ni kwata kwata na rasa ya zanyi dakai whl".
"A'a Ummu ni fa nace saidai Habiby ya ƙarɓa ko shi ko Sahel dan gaskiya ni bazan iya wata sarauta ba, dan ALLAH ki daina faɗar hakan ma Ummu yana bata min rai whl"........ Ya faɗa yana tsuke fuska kamar bai taɓa sanin wani abu Murmushi ba a duniya. Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana kallon ɗan nata da a ko da yaushe su kayi ƙoƙarin kwatanta shi da sarautar tasu sai ya nuna bacin rai da fushi ko da kuwa Sultan da kansa ne zai masa maganar. "Tohm shikenan naji yanzu daga ina kake?"........ Ba tare da ya kalleta ba alamar ransa ya ɓace da maganar data masa ya ce, "Naje Horse ranch na duba Hirtik ba lpy, sai na biya fada wurin su Abbu ".
"To ka tashi kaje wurin Rouslan domin bayajin daɗi inajin tun fitar ka yake ta amai sai da aka kira Abyan ma yazo ya duba shi, amma Imam ya aiko da ruwan addu'a, kai ma in kaje Ka ganshi kazo ka karɓi naka kasha "..........Tunda ta ambaci Rouslan bashi da lpy ya juyo da mugun sauri, "Ummu bansani ba ai meysa ba'a kirani ba, how za'a kira wani Abyan bayan gani, wai meysa ake min haka ne, shikenan mutum baya kuskure ne, ko shi Abyan ɗin baifi ƙarfin kuskure ba. Ba dan alqawarin da nayi wa Rouhi ba whl da sai na koma kan aiki na saidai duk abinda zai faru ya faru"......... Kafin Ummu tace wani abu ziyada ta ce, "Yah Reeslan ka tarar da abinda ke faruwa da kaje fada".......... Ɗan kallon ta yayi hankalin sa akan Ummu da ita kuma ta juya wurin Ziyada tare da tambayar ta, " Meke faruwa ne ziyada? Tun ɗazu na lura da magana a bakin ki kuma kinzo kin zauna kinyi shuru".
"Ummu Ammu yassar ne akace ya yanke jiki ya faɗi yanzu a fada ".
"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun me ya sameshi haka?" .
Reeslan da ya tashi domin zuwa wurin Rouslan ya ce, "Sai dai haƙuri Ummu, amma Ammu yassar ba zaiyi ba, shi ma mutuwa zaiyi".......... Dafe ƙirji Ummu tayi idanunta na cikowa da hawaye cikin rawar murya ta ce, "Reeslannnn! Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un, Reeslan bana hanaka irin wannan maganganun ba meysa bakajin maganata? Meysa Reeslan so kake sai zuciyata ta buga ko?"..........Ta ƙarashe cikin Muryar dake bayyana tsananin tashin hankalin da take ciki, wannan shine karo na uku da irin haka ta faru kuma in Reeslan ya ambaci mutuwa mutum zai yi, to fa mutuwar yake amma Ummu bata taɓa yarda wani ya sani ba ciki harda mai martaba, sai addu'a kawai data dukufa dayi saboda bata so a canfa mata ɗa.
Ita kuwa Ziyada da bata san abinda ke faruwa ba sai cewa tayi, "yah Reeslan me Ammu ya ma da zaka masa fatan mutuwa?"......... Wucewa kawai yayi ba tare da ya bawa ɗayansu amsa ba , Ummu ce ta ce, "Ziyada karki sake naji wannan maganar a bakin wani, yadda akayi ta a nan a barta a nan whl ko da wasa naji ta sai ranki ya ɓaci".........Tana kaiwa nan ta miqe ta bar falon zuciyar ta cike da fargabar abinda zai biyo baya.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty,