BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   47 / 53

138K to 141K   out of 156.9K words

sai Ace dake dan danna waya ɗagowa yayi Yana kallon su har suka ƙaraso ciki Jey ya miqa masa hannu suka gaisa shi Kuma Philip ya wuce Dan sanar da zuwan Jey ɗin wa Boss ɗin sa.

"To ka saki fuskar mana irin wannan muzurai da kake sai kace zakayi karo da ɓauna"....... Ace ya faɗa cikin salon zolaya. Kallon sa yayi ya ɗauke kai, "In ma wata ce ta haɗama zafi to ka qone a can".......... Hararar sa Jey yayi amma bai ce komai ba, kuma daman yasan ba zaice ɗin ba haka ya cigaba da tsokanar sa har sai da ya sashi Magana, "Dan ALLAH ka barni in sha iska, kai bakinka baya ciwo ne?"........."Shaqe ka nayi ne ? Bakina kuma ai ina brush me zaisa yayi ciwo"......... Ƙwafa Jey ya ja tare da zaro wayar sa ya share Ace ɗin.

Ɗan serious yaci kafin ya ce, "Ɗazu na kiraka bakai picking ba dama inaso naji ya labari ta wajen ka"........ Ba tare da ya kalle sa ba ya ce, "Me kake sauri ka bari su ƙaraso mana ko Kuma in na faɗa ma Kai zaka isar musu ne ni nayi tafiyata?" ......... Ace bai Ƙara cewa komai ba yaja bakin sa yayi shuru tare da cigaba da daddana Wayarsa. Suna nan zaune har su kiara suka shigo kamar kullum Kiara na sanye da dogon wando da top Mai hannu ɗaya long sleeve, curly brown hair ɗin nan nata zube a gadon bayanta daga tsakiyar kan ta kame shi da pin, ita Kuma Ash tana sanye da white denim mini skirt da black top Wadda daƙer ta rufe cibiyarta, ƙafar Nan tasha high heel kamar zai karye, sai system ɗin ta data riqo, "Excuse".......... Suka faɗa tare da Neman wuri suka zauna , Ace da ba ya rabuwa da tsokana ya ce, "Wannan kwalliyar wa akayi wa?"......... ɗagowa sukayi suna kallonsa, da ido ya musu alama da Jey dake zaune hankalin sa akan Wayarsa yana mata dannar wulaqanci kamar bayaso, Ash ce ta ce, "Da ba ma wanka ne?"......... ita kuwa Kiara wata muguwar harara ta watsa masa ta ɗauke kai.

Bai daddara ba ya sake cewa, "Wanka yayi kyau kuma na yaba"........ ya Ƙarashe yana ɗagawa Ash gira ɗaya tare da sakar Mata wani italian killer smirk. Ɗauke kanta tayi kawai dan tasan in ta biyewa Ace zasu tayi ne. Ƙasa ƙasa suke sake tattaunawa kan case ɗin ita da kiara har su Amjad da Philip suka bayyana a falon, miqawa Jey hannu yayi sukayi musabaha sannan ya miqawa Ace ma wanda kasancewar sa cikin su Shi ma ya fara sabawa da hakan, su Ash suka gaishe shi ya amsa sannan ya zauna shi Kuma Philip ya tsaya daga gefen hannun kujerar da yake zaune.

"To ya ake ciki? Meye sakamakon da kuke tafe dashi?"..........Ya faɗa yana kallon su.

Kiara ce ta motsa da faɗin, "Ni a nawa binciken da nayi shi ne duk mutanan da ake bawa shadow babu cikakken wajen da ake kaisu kawai boarder garin ake kaisu a ajje........." Bayani ta musu kamar yadda tawa Ash da safe sannan Ash ta ɗaura da faɗin, "Ni inaga muyi amfani da trackers da na'urar ɗaukan sauti a jikin mutanan da zamu bashi saboda mu bibiyi inda ake kaisu da Kuma abinda yakeyi dasu, kaga zamu samu hint sosai"........... Ace ya ce, "Amma kuna ganin hakan ba zai bamu matsala ba kuwa?"......... Amjad ne ya amsa masa da. "Kai miye naka binciken ya baka toh?".

"Kamar yadda ka sani ne, ba wani haske da zamu iya samu akan Shadow domin tunda kaga kowani ƙasa sunyi bulayin nemen sa sun kasa kasan ba ƙaramin hatsabibi bane, abinda yake ɗaure min kai shi ne shi fa baya karɓar tsoffi sannan baya karɓar yara ƙananu, matasa yake karɓa sannan kuma baya bada fifiko a tsakanin maza da mata, ma'ana wai yace mata sufi yawa a mutanan da za'a bashi ko kuma maza Sufi yawa. Amma ni inaga kawai mu tattara bayanan representative ɗinsa na kowacce ƙasa sanan mu datsi bayanan wayoyin su ciki harda BB lalo, ƙasar da aka fi samun Kira nan zamu fi maida hankali akai".

Girgiza Kai Amjad yayi tare da faɗin, "ko Kuma ƙasar da ba'a fiya Kira daga can ba ko?"........ Ash ta ce, "Meysa kace haka?".

"Ohh Wai kina tunanin duk abinda zaija attention zai kasance a ciki ne, ai duk inda kikaga komai baya tafiya sosai to nan zamu fi bincikawa. Widad bakace komai ba?"..........Ya ƙarashe yana maida kallon sa kan Jey da yayi relaxing yana binsu da ido, sauke ƙafarsa dake kan ɗayar yayi kafin ya ce, "Kai banji naka bayanin binciken ba da Kuma abinda ka yanke".

"Ohh common widad be serious mana, magana ake ta aiki fa in dai har kayi binciken nan let us know what you found out".......... Ɗage kafaɗun sa yayi tare da faɗin, "Well shawarwarin ku sunyi Kuma hakan ya kamata a fara bi Amma idan wanna plan ɗin baiyi ba, Na samo plan B idea".

Cikin zaquwa Amjad ya ce, "Go ahead miye plan B ɗin?".......... Ɗan shuru yayi Yana binsu da kallo kafin ya maida kansa ƙasa . Qasa qasa Kiara taja tsaki, cikin yanayin dake nuna ranta ya fara ɓaci ta ce, "Bamu da lokaci Widad ba Wai hira ake ba ko Kuma an nemi wani labari da zaka jawa mutane aji"........... Ɗagowa yayi ya zubawa Kiara ido na tsawon wani lokaci har saida Amjad ɗin ya gaji ya ce, " Kai muke sauraro fa?"......... Hakan ne ya dawo dashi hayyacin sa waskewa yayi da faɗin, "Akwai wata yarinya........"

A fusace kiara ta sake cewa, "Me ya haɗamu da yarinya mu da muke kan aiki Kuma?"........ Ace ya ce, "To kin tsaya kinji me zaice ne ballantana ki hau dokin zuciya"........ kallon sa Ash tayi dan tasan da biyu yayi Maganar, wink ya mata yana wata yar munafukar dariya.

Jey ne ya cigaba da faɗin, "Akwai wata yarinya a ƙasar Bangkok da nayi bincike ya' ce ga shadow "........... Kusan duk haɗa baki sukayi wurin faɗin , "Yar Shadowww"......... Cikin mamaki Banda Amjad da baice komai ba kawai kallon Jey yake yana nadar bayanai tun ma kafin Jey ɗin ya Ƙarasa magana.

"Yes ya' ce ga shadow sai dai tun tana ƙarama ya ɗauketa daga gabansa ya haɗata da wani wanda zai dinga kula da ita ya Kaita can ƙasar tare da nunawa mutane cewa ƴar sa ce".

"Shin ita tasan waye uban nata na gaskiya?"....... Ash ta tambaya cikin kullewar Kai. Girgiza kansa yayi da faɗin, "Wannan shi ne iya abinda na samu, ta San Shadow ne mahaifin ta bata sani ba bani da masaniya akan hakan, miye dalilin da ya sa ya ɗauke ta daga gabansa ya Kaita can ban sani ba, kawai abinda na sani shi ne tunda ta shigo bata taɓa barin ƙasar Thailand ba kunga kenan hakan na nufin tabbas shadow yana zuwa ganin ta a sirrance saidai taya? Yaushe? Kuma a Ina? Ban sani ba".

Ajiyar zuciya Amjad ya sauke sosai ransa yayi sanyi Kuma yaji hankalin sa ya ɗan kwanta at least suna da second option, wanna shi ne dalilin da yasa yake haƙuri da halayyar Jey saboda kwakwalwar sa na masifar ja. "Ina so ka tura min duk bayanan da ka samu akan ta"........ Juyawa yayi wurin Philip da faɗin, "Kaje ayi duk abinda ya dace a sanya tracker a cikin jikin su da Kuma na'urar ɗaukan sauti da sauransu, ayi connecting ɗin komai yadda ya kamata karka bari a samu matsala, sannan a gama komai daga yanzu zuwa safiya, your time start now".

"Yes boss".........Ya faɗa tare da juyawa zai tafi ya dakatar dashi, "Idan an gama ka kawo mana mutumin da Widad ya kawo".

"Yess boss".........Ya sake amsawa sannan ya juya ya fita da sassarfa.

System ɗinsa da ya shigo da ita ya ɗauko ya kunna tare da janyo stool ɗin dake gefen kujerar sa ya ɗaura akai yadda kowannen su zai gani sannan ya ce, "Za'a Kira BB LALO a shaida masa aiki ya kammala Ina za'a Kai yaran"........ Nan duk suka amince a kirashi ɗin. Kiran sa yayi wannan PA ɗin nasa daya harɓe Akil ya ɗauka nan ya sanar masa shi ne Kuma yana son magana ne da BB LALO, cewa yayi su riqe waya zai Kai masa, bayan ya Kai masa Amjad ya ce, "Good evening sir"........."Evening ya akayi?"

"Dama aikin nan ne an kammala Ina za'a kaisu, sannan a Ina zamu ɗauki cikon kuɗin mu"........... Murmushi BB lalo yayi me sauti kafin ya ce, "Ka saurareni Ina zuwa?"..........Ya faɗa tare da kashe Kiran. Da sauri ya juyawa Ash system ɗin tare da faɗin, " Tabbas Kiran waya zaiyi yi sauri ki mana kutse cikin layin nasa"......... Da sauri Ash ta sauko ƙasa gaban system ɗin cikin kwarewa ta fara sarrafa laptop ɗin, cikin second 100 tayi hacking na wayar BB lalo duk da kuwa matakan tsaro masu karfi dake kan wayar tasa amma haka Ash tayi tambari dasu. Kamar yadda Amjad yayi hasashe hakan ne waya yake yi da wani mutum. "Henry ka shaidawa Oga yaran nan Amjad fa har ya kammala aikin sa dan haka suna buqatar a basu location da zasu Kai mutanan da Kuma cikon kuɗin su".

"BB LALO wanna yaron daga gani kwararre ne gsky, wato ana binciken sa amma yana cigaba da shuka tsiyarsa lalle za'aje dashi. Kasan Wanda muka bawa aiki tun kafin yaron nan har yanzu basu kammala ba, tabbas nasan shugaba zaiyi farin ciki, abinda za'a yi su kaisu kusa da iyakar ƙasar Nifaz ɗin, kamar yadda aka saba in sunje zasu tarar da kuɗin su a can, zamuyi magana da shugaba abinda ake ciki game dasu zan sanar ma".

"Aiit thank you Henry".......... Da haka sukayi sallama cikin sauri Amjad ya ce, "Maza samo mana bayanin wanna mutumin waye shi? Ga dukkan alamu ya na magana da Shadow kai tsaye, ki datsi layin sa shi ma"......... Cikin zafin nama Ash ta fara aikin da Amjad ɗin ya sata gabaɗayansu hankalin su ya dawo kan Ash ciki harda Jey da ya ɗan zakuɗo yana kallo shi ma, kusan mintuna 10 kafin ta juyo ta kalle su a sanyaye ta ce, "Boss baza mu iya datsar number ta sa ba, ga dai number mun ɗauka Amma nayi nayi ba zan iya hacking wayan nasa ba saboda Akwai matakan tsaro masu tsauri sosai akai, sannan ba wani bayani a Kansa kawai dai abinda muka samu shi ne yana Bangkok a yanzu haka"......... Ɗagowa Amjad yayi ya kalli Jey da Shi ma ɗin shi yake kallo kafin ya ce, "Tabbas wanna shi ne mutumin dake riqe da yar tasa"......... Ace ya amsa da, "Ba wai a maganarka, shi ne ma".

Dafe Kai Amjad yayi saboda takaicin rashin samun bayani a Kansa da basu yi ba. Yana cikin wanna tunanin Kira ya shigo daga BB LALO bayan ya ɗaga ya shaida masa abinda wancan mutumin ya faɗa kamar yadda sukaji. "Okay sir nan da zuwa safiya zasu isa"........ Amjad ya bawa BB LALO amsa . " Alright ". Ya faɗa tare da kashewa .

"Ya kamata mubi bayan Philip domin ganin komai ya kammala da wuri Kuma ba'a samu matsala ba"....... Ash da jikinta yayi sanyi kan case ɗin ta ce, "ka manta baka Kira Sir Richard ka faɗa masa abinda ake ciki ba. Miqewa yayi tare da faɗin, " kuzo muje wayar na ciki"......... ya ƙarashe yana wucewa a sanyaye saboda gabaɗaya kansa ciwo yake masa, baya so a samu matsala ne ko kaɗan saisa hankalin sa ya tashi. Jey ne ya tashi yabi bayansa sannan Kiara tabi bayan Jey, Ash ma miqewa tayi saidai kafin tayi wani taku Ace ya janyo rigarta ta baya, Kasancewar takalmin ƙafarta me tsini yasa tayi baya kamar zata faɗi, riqo waist ɗinta yayi da hannu ɗaya tare da faɗin, "Haka akeyi kuma zaki tashi baki jirani ba"........."Meysa zan jira ka to?". Ta Tambaya tana binsa da wani irin kallo, ɗage kafaɗar sa yayi tare da faɗin, "Saboda ki samu karsashin tafiya ba tsoro"......... kafin ta gama gane me yake nufi yaja hannunta sun nufi ciki.



------------------------√



SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥



Lokacin da Omaine da Haisha'an suka shiga gaishe da mahaifiyar sa sun same ta ne cikin shiga ta alfarma kamar ba baiwar ba, durƙusawa sukayi suka gaishe ta, a wulakance ta ce, "Har ka fito kenan".

"ALLAH yayi Inah"..........Ya faɗa cikin tausasa murya.

"To ni dai ba abinda zan ce ma sai jiki magayi in Kuma baka gaji da zaman can bane, to ka cigaba da nuna iyawa Kai ba komin komai ba dillalin kashi"......... Kansa a kasa ya ce, "in Sha ALLAH zan kiyaye Inah".

Wani banzan kallo ta masa kafin ta ɗauke kai ta ce, "Ya rage naka, kar ma ka kiyaye ɗin. Ka je ka gaida Queen Hirut?".......... Shuru yayi dan a duniya ba abinda ya tsana sama da jin sunanta, ya tsani abinda zai haɗashi da ita. Inah ta sake cewa, " To tun kafin taji labarin an sakeka bakaje ka gaishe ta ba ka zo ka shafa min kashin kaji ka ɗauki tsumman kafafuwan ka ka tafi, ka kuma dinga tunawa kai ba koman kowa bane face dan bawa da baiwa".

"To Inah"........Ya amsa da to ɗin ba Dan ya so ba sai dan bazai iya mata musu ba, kuma ba zai iya ja in ja da ita ba".

"Ku tashi ku bace min da gani".......... Tashi sukayi a sanyaye suka fito, Omaine ya kalleshi, shi dai ba abun yace dashi Kar yaje ba yasan baya kaucewa maganar Inah Kuma yasan in yaje palace ma wani aikin zai ɓaro Yana cikin wanna tunanin yaji maganar Haisha'an ɗin, "Omaine ka jirani anan bari naje na dawo yanzu mu shiga kasuwa muga ko da abinda zamu kama"......... Girgiza Kai Omaine yayi da faɗin, "Bazan barka Kai kaɗai ba Haisha'an duk inda zaka Ina tare dakai".......... "Omaine bana so kowa ya shiga matsala ta dalili na".

"Then saika kiyaye matsalar"......... Bai Ƙara cewa komai ba sai hular sa Mai kama da tashi ka fiya naci da ya zaro ya sanya akan lallausan golden hair ɗin sa wanda duk da ba wani samun gyara yake ba amma a kwance yake ya zuba masa ta ko ina kamar wani kwando, na gaban nan ya sauka har kusan kan girar sa, da ya ɗaura farar hular saita haska shi sosai sun yi tafiya kafin su iso main ƙofar castle ɗin, shiga sukayi sannan suka ɗauki hanyar palace suna zuwa masu tsaron ƙofar suka dakatar dasu ta hanyar tura su baya ɗayan ya ce, "Kai Ina zuwa?"........... Omaine ya amsa da, "Zamuje gaida Queen ne".

"Ku tsaya a sanar mata"........Ya faɗa tare da shigewa ciki, can yazo yace su shiga. Takalman su suka cire sannan suka shige. Daga tsayen da yake ya ɗan rusuna da faɗin, "Barkan ki da rana Queen" ......... Yayinda omaine ya yi flat a ƙasa kamar yadda gaisuwar fadar take. A fusace assistant din Queen wato Chief Benish ta ce, "Kai matsiyaci ɗan baiwa jikan bayi durƙusa tun kafin fushin sarauniya ya hau kan ka"........ Juyawa yayi ya kalle ta a dake ya ce, "Fushin sarauniya ba fushin ALLAH bane Babu inda akace idan zamu gaishe da wani bawa mu kwanta masa kamar zamuyi sujjada, ALLAH kaɗai akewa sujjada".

"Javed ku saukar dashi ƙasa"......... Chief Benish ta faɗa tana miqewa cikin fushi, wasu gardawa dake cikin palace ɗin ne suka nufo inda yake tare da rirriqe shi suka shiga kokawar sai sun kaishi ƙasa, su uku shi ɗaya Amma sun gagara kai shi ƙasan kamar yadda aka basu umarni iyakar sa kawai ya sauka kan guiwowin sa yana fuskantar Queen Hirut da ita ma shi take kallo. "Ni dai bazan gaji da faɗa Miki gaskiya ba ke da mutanan ki, hanyar da kuke bi ba Mai bullewa bace, Ina muku da'awa ne saboda Ina mu ku kwadayin samun rahamar ALLAH inason ku ɗanɗani ni'imar dake cikin addinin gaskiya, addinin ALLAH, abinda kuke bautawa itama baiwar ALLAH ce, Kuma ba ita ta halicce ku ba. Abu na ƙarshe shi ne ki sani ko kin sa an kaini prison in dai ba sawa kikayi a kasheni ba dole wata rana zan fito Kuma in na fito haka zan cigaba da faɗaɗa ayar ALLAH, Ni kuma nasan ke baki isa ki min abinda ALLAH bai min ba, in har kwana na bai ƙare ba baki isa ki kasheni ba ..........." Bai ƙarasa ba wa'annan gardawan suka haɗa masa wani duka sai jini, hannun yasa ya dangwalo jinin sai kuma ya kalli Queen Hirut da in ranta yayi dubu ya ɓaci sai huci take daga zaunen, Cheif Benish ce ta ce, "Javed a kai shi guardroom a bashi horo me tsanani"......... Haƙuri Omaine ya fara basu cikin rawar jiki tare da faɗin, "Haisha'an ka basu haƙuri mana, ranki ya daɗe ki gafarce mu ki masa afuwa".......... Amma ina taurin kai irin na Haisha'an ko motsa bakinsa baiyi ba haka suka ja suka fice dashi Omaine ya bisu yana roƙar su amma ko kallon sa basuyi ba ƙarshe ma ball ɗaya daga cikin su yayi dashi.

Guardroom wani ɗakin duhu ne a ƙarƙashin ƙasa da suke horar da masu laifi, ɗakin ko hannun ka baka iya gani gashi ba iska sosai sai zafin masifa, da yawan mutane in aka kaisu can basa fitowa da ƙafarsu saidai gawarsu hakan yasa hankalin Omaine mugun tashi, baiji bugun da suka masa ba ya sake tashi ya bisu yana sake roqon su idanun sa shaɓe shaɓe da hawaye, masu tsaron wajen suka sa su fitar musu da omaine sannan suka haɗu suka tura Haisha'an ciki.

Da gudu Omaine ya juya dan zuwa wurin Inah domin ya sanar da ita, dan yasan ita kaɗaice zata iya ceton Haisha'an, a ƙofar bangaren su ya tarar dasu suna kokarin fitowa itada wasu daga cikin bayin, zubewa yayi gabanta tare da faɗin , "Inah dan ALLAH ki taimaki rayuwar Haisha'an Queen Hirut ta sa a kaishi Guardroom, Please Inah"........ Ya ƙarashe hawaye na zubo masa .

"Kamar yadda ka faɗa Queen Hirut ni kaina ta isa ta zartar da hukunci a kai na ballantana kuma ɗa na, and dama na gaya masa ai tunda har baiji ba

47 / 53