Author : Young Writer Category : Tknovels
shikenan shi ya jiwo in ya mutu ma bani da asara taurin kan sa ya ja masa"......... Tana kaiwa nan ta yi gaba, sake shan gaban su yayi yana riqo ƙafafunta, mari ta zubga masa sannan ta sake cewa, "Kai idan ka sake motsawa daga inda kake da niyyar bi na, na rantse da kurangina (Astagfirullah) sai na sa an maka abinda bakayi zato ba"......... Daga haka ta fisge ƙafarta ta wuce.
A can kuwa ko da suka shige da Haisha'an guardroom sarƙa suka sanya masa a kugu kowa ya ja ɗaya sannan suka shiga zabga masa wasu irin dorina na fatar kada, baya gani balle yasan ta inda dukan yake fitowa har ya kare kansa dan haka yayi surrender kawai, tun yana daurewa har ya kai ƙasa ga ba iska sosai, ga duka ta ko ina. Sosai ya fara fita hayyacin sa, jijiyoyin jikin sa suka fara saki.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______ 64 & 65
Ko da Amla tazo tare suka koma wurin DPO da Sahnish dan Baba ilerika ya wuce yin wani uzurin da yaji Abun yafi ƙarfin sa, bayanin da DPO yayiwa su Sahnish ɗin shi ya sakewa Amla, saidai Amla tayi ƙoƙarin aiki da dukiya Amma fa sam DPO yaqi sauraran ta dan haka suna fitowa ta nemi ganin Hushaima, bayan an fito da Hushaima suka kalli juna, dafa kafaɗar ta Amla tayi da faɗin, "Hushaima ashe tsautsayin da ya faru kenan?"......... Ɗan gajeren Murmushin gefen baki tayi da faɗin, "Ba tsautsayi bane tsayawa kai da kare mutunci ne"......... Jan hannun ta Amla ta ɗanyi da faɗin, "Haba ya ana ƙoƙarin kashe wata wutar kina ƙoƙarin kunna wata, karki Ƙara faɗar haka, na samu DPO Amma yaqi ma saurare na dan haka yanzu zamuje wurin CP Kuma zamu ɗauki lawyer Amma ki cire zancen wata tsayawa kai or whatsoever ɗin Nan ko da an tambayeki kice tsautsayi ne ba dagangan kikayi ba........" Kafin ta rufe bakinta Hushaima ta ce, "Saboda me zanyi ƙarya bayan ita ta ɗauki wani kuturun hannunta ta mare ni sannan ta gaggaya min maganganu. Mari fa ? ke kinga yarinyar ne wai ni ni zata kalli tsabagen idona ta dallawa mari, whl ko kaɗan banyi nadama ba Kuma wasan Bai tsaya iya nan ba, ni za'a wulakanta a jefa a cell ko?".......... Kwafa taja tare da yin murmushin da ita ta barwa kanta sanin ma'anar sa.
"Wai ke Hushaima me hakan fisabilillahi, ya sai ana gabas kina yamma wanna yarinyar ki sani ba ƴar kananan mutane ba.......".........."ALLAH yasa uban ta ne shugaban ƙasa Amma whl bazan canza kalamai na ba, in sunga dama su ɗaureni har igiya tayi saura".
Sahnish da yayi tagumi yana kallon su ya ce, "kin ganta nan dai Amla ni har na rasa ya zanyi whl".
"Kaga in zaka san yadda zakayi ka fitar dani daga nan wurin to, in Kuma baza ka iya ba ka sanar min nayi iya nawa".
Cikin ɓacin rai Amla ta ce, "To Wai ba fitar dake ɗin ake so ayi ba Amma kin kasa sauraron abinda ake faɗa miki, wai yaya ne Hushaima Anya ba wani abu kika sha ba kuwa. And kinsan yadda zakiyi ki fitar da kanki ne kika bari kika kwana anan ɗin?"...........Tana kaiwa nan ta juya ta kalli Sahnish da faɗin, "Ka sameni a mota"....... Ta ƙarashe tana barin wurin, tashi Sahnish ɗin yayi sannan ya ce, "Dan ALLAH Hushaima ki sassauta wanna nuqufarcin naki wanna zafin ran ba zai kaiki ko Ina ba ki barmu mu rayu cikin salama muji da Abu ɗaya mana ".
Wani banzan kallo ta watsa masa kafin ta ce, "Kai saurara min kaji ko, karka ce zaka min wasu surutai, dukda nasan ni ba kowa bace bazan karɓi raini da wulakanci a wurin kowa ba, ban shiga harkar kowa ba Amma duk wanda ya shiga tawa whl banqi mu Kai daga nan har kotun qoli ba".
"Allah ya kyauta "........ Shi ne abinda Sahnish ya sake faɗa tare da juyawa yabi bayan Amla .
Daga nan state police headquarter suka nufa inda Amla tayi amfani da matsayin mahaifin ta domin su samu ganin commissioner ɗin da wuri, bayan an musu iso suka gaishe shi. "Have a seat ku zauna mana ga guri".........Ya faɗa cikin fara'a yana nuna musu wurin zama. "Thank you sir "........ Amla ta faɗa tare da zama tanawa Sahnish alamar ya zauna shi ma.
"Fita ma zanyi ai naji ance daughter alhaji Zawaad ne nace to bari na tsaya na saurareki, ya wurin mahaifin naki kwana biyu ma bamuyi waya ba".
"Yana Nan lpy sir, yana gaishe ka ma abubuwa ne suka dan masa yauwa saisa "........."Ah to ba damuwa Ina amsawa, akwai wani matsala ne?" .
"Eh sir dama ........" Abinda ya faru ta fada masa, take ya fara faɗa, "Shi Wakili (DPO) wato abinda yakeyi kenan, how za'ace baza a bada bailing yarinya ba kisan Kai tayi ko me? bari na kirashi naji dama aikin da ya keyi kenan"......... Ya Ƙarashe yana ɗaukan wayarsa ya Kira DPO tare da rufe shi da faɗa. Saida ya gama sannan DPO ya masa bayani. "Shikenan bari zanyi magana dasu"........... CP ya fada a sanyaye sannan ya ajje wayar yana kallon Amla da Sahnish tare da zaro hanky ɗin dake gaban rigarsa ya goge fuskar sa da gumi ya fara karyo masa, Nisawa yayi kafin ya ce, " A gsky Amla case ɗin nan babba ne domin ance har yanzu yarinya na coma sannan Kuma........." Ɗan shuru yayi kafin ya cigaba, "Unfortunately ba zan iyayin komai akai ba, saboda yarinyar da aka raunata ɗin ya' ce ga Alhaji Awais Hashim masu HD REFINERIES da kuma AURUM MINING, Kuma kinsan fitattu ne shugaban ƙasa ma ba ya musu wahalar gani. Abinda zance da ku kawai shi ne kuje ku ɗauki kwararrun lawyers sannan ku tsaya da addu'a dan gsky a fahimta ta nema suke su maida abun babba, kuma suna amfani da connection ne"......... Take jikin Sahnish ya ɗau rawa dan da a tsaye yake ba abinda zai hanashi yanke jiki ya faɗi duk da baisan mutumin da aka ambata ba Amma yasa wanna HD ɗin da CP ya ambata dan ana yawan ambaton ta gidanjen TV da radio, wata juya juya ya fara gani ai baisan lokacin da ya sauko daga kan kujerar ba, "Ranka ya daɗe Dan girman ALLAH ka taimaka min whl ita kaɗai nake da ita a duniyar Na........".
"Kaga Sahnish tashi muje"......... Amla ta katseshi saboda tasan ba abinda magiyar zata amfana. Cikin mutuwar jiki ta miqe domin ta Ƙare musu gabaɗaya saidai suje su sake shawara Amma case da babban mutum kamar Alhaji Awais bata hango nasara ba. Gashi ba yadda zatayi ta sanarwa mahaifin ta ko zai iyayin wani abu akai, dan idan mahaifiyar ta taji zatayi mummunan Saɓa mata saboda yadda ta tsani su Hushaiman . "Shikenan sir mu zamu wuce mungode sosai"..........."You are welcome ki gaidamin Alhaji da kyau da ALLAH".
"Zaiji in Sha ALLAH"......... Ta faɗa tana fita, Sahnish ya rufa mata baya. Ko da suka shiga mota kuka Sahnish ya fashe mata dashi wiwi kamar wani ƙaramin yaro, kasa ce masa komai tayi dan bata da wata kalma da zatayi amfani da ita wurin tausarsa saboda itama abun ya fara ɗaga mata hankali, har suka koma police station ɗin, sannan ta kalleshi da faɗin, "Sahnish nasan halin da kake ciki Amma kayi hakuri ka sawa zuciyarka dauriya, zan ajje ka anan ne saboda inaso naje gida nayi tunanin mafita, in Sha ALLAH Hushaima zata fita ka kwantar da hankalinka".
Goge fuskar sa yayi ba dan ya yadda ba sai dan kawai ya jita ne dan maganar CP ta cire masa hope a zuciyar sa. "Mun gode sosai Amla, ALLAH ya kaiki gida lpy"........... Ya faɗa Yana buɗe ƙofar motar, har ya fita Amla ta ƙasa cewa komai saboda tsananin tausayin su da taji ya cikata, da haka taja motar ta bar wurin.
Shi Kuma Sahnish kan kwalbatin dake opposite da police station ɗin ya nema wuri ya zauna. Wuni yayi cur a wurin dan ya shiga ya nemi ganin Hushaima suka hanashi Wai ba'a zirga zirga haka ya haƙura ya miqa musu abincin da ya siyo mata ya koma ya zauna har lokacin ɗauko Shazeen yayi yaje ya ɗaukota, itama magana ɗaya ce a bakinta wato Ina aunty Hushaima, rasa amsar da zai bata yayi Dan haka yace bata dawo ba. Abinci ya tsaya ya siya mata sannan suka koma ƙofar police station ɗin suka kafa sabon zama har dare ya kai mata Abinci sannan suka wuce gida .
Washe gari ma daƙer da siɗin goshi ya samu ganin ta nan ya shaida mata abinda su CP suka ce. Fuskarta cike da dimbin mamaki ta maimaita, "Alhaji Awais, yanzu wanna yarinyar da na fasawa Kai yarinyar Alhaji Awais ce?" .
"Kin sanshi ne ?"........... Sahnish ya tambaya yana kallon ta, batace masa komai ba illa murmushin data saki kawai, sai miqewa da tayi da faɗin, "Sahnish Kaje kawai karka damu"........... "Bangane ba Ina zaki kuma kinsan da ya akayi na samu suka barni na ganki ne?".
"Kaje kawai Sahnish nace ma karka damu "....... Tana kaiwa nan ta wuce ta koma cell ɗin da kanta, shi kansa Sargeant da kallon mamaki ya bita dan shi bai taɓa ganin yarinya irin wanna ba . Haka Sahnish ya tashi ya koma wurin da ya zauna jiya ya zubawa titi ido.
Kwanan Hushaima shida a police station duk wani Kai kawo da Amla dasu Sahnish zasuyi sunyi Amma babu wata alamun nasara, dan haka Amla ta nema mata wani kwararren lawyer da zai tsaya mata dan gobe ne zaman kotun.
Da Misalin 3:06pm na ranar lahadi Hushaima na hango tare da barrister zaune yana mata tambayoyi game da case ɗin nasu, a waje Kuma Amla ce da Sahnish, Shazeen sai Baba ilerika tsaye suna jiran su.
DPO ne ya fito take su Sargeant suka shiga sara masa kwata kwata bai lura dasu Sahnish ba saboda kamar a rikice ya fito. "Amm Sargeant Sunusi, maza Kaje ka fito da yarinyar nan da suke case da su Alhaji Awais ayi gaggawar sallamar ta yanzu yanzu ta bar station ɗin nan karta Ƙara minti biyar a ciki, sannan zancen kotu kace mata babu shi an janye"..........." Yes sir". Sargeant sunusi ya faɗa tare da sara masa shi Kuma ya juya ya koma Office ɗin sa.
Kallon kallo aka shigayi tsakanin su Baba ilerika, Sahnish ne ya ce, "Amla naji daidai kuwa? an sallami Hushaima fa Kuma an janye Ƙara?".
Itama Amla cikin ɗaurewar Kai ta ce, "Abinda naji kenan nima to Amma........, Wait bari naje wurin DPO ɗin"......... ta faɗa tana wucewa yayin da Sargeant Sunusi Kuma ya fito dasu Hushaima da barrister tare da wucewa ya ɗauko mata kayayyakin ta ya bata jiki na rawa saboda cika umarnin DPO.
A ciki kuwa Amla tana shiga ta samu DPO yana waya, "Yes sir ai an sallame su ma tuntuni".......... Shuru yayi can Kuma ya ce , "Okay sir godia nake".......... Kashewa yayi tare da kallon Amla ya ce, "Ah Ah dama kina Nan?".
"Eh DPO naji ka fito kace mu tafi sannan Kuma an Kori Ƙara shine nazo naji cikakken bayani".
"Ba wani cikakken bayani da zaki samu Amla abinda na sani kawai muma umarni aka bamu daga sama kan mu saketa dan haka kuje kawai, case closed".
" Shikenan ranka ya daɗe mun gode ".........Daga haka ta juya ta fita. A compound ta tarar dasu, remote ɗin motarta ta matsa motar ta buɗe ba tare data tsaya ba ta ce, "Ku shigo muje".
-------------------------√
AURELLON SULTANATE 💎
Ko da Mutallab ya aika da Yaran sa karɓo saqon Queen Hirut daga bakin gate ɗin su suka tsaya, Wata mata ce ta sauko daga kan giwar ta miqa musu sannan ta juya ta koma ta kama giwar ta ɗale suka juya suka bar wurin, sai lokacin suma masu karɓar suka juya ciki. Mutallab suka kaiwa shi Kuma ya koma fada yana zuwa ya zauna a tsakiyar fadar tare da faɗin, "An karbo saqon ya Sultan"......... Wazir ne ya ce, "Karanta a fili muji".
Karbar Mic ɗin da wani bafade ya bashi yayi ya maqala a gaban rigarsa sannan ya warware takardar ya fara karantawa kamar haka .
From: The Honorable Queen Hirut the queen of sword of fire kingdom.
To : His Majesty King sultan abdulbasit Abdul Aziz Theron of the aurellon sultanate.
"Your accusations are as outrageous as they are unfounded. The sword of fire kingdom has neither the interest nor the need to conspire against your fragile dynasty. Crown Prince Rislan, while tragic, is no fault of ours, and we will not be scapegoated for the shortcomings of your own court’s security. Your demand for conspirators is laughable and As for your request for reparations, we suggest you direct your grievances inward, for the incompetence of your own kingdom is not our financial responsibility. Should you persist in these baseless accusations or threaten the peace with your bluster, know that the sword of fire kingdom will not hesitate to defend its honor and sovereignty. We advise you to temper your paranoia and reconsider your position, lest you find yourself embroiled in a conflict you are ill-prepared to win.
_Signed_
The Honorable queen of the sword of fire kingdom. Sai stamp ɗinsu da aka buga me hoton wuta sai sword guda biyu da sukayi crossing a tsakiyar ta.
Duk shuru mutanan fadar sukayi ana jiran jin hukuncin da Sultan zai yanke. Gyaran murya yayi tare da faɗin, "Suna sukan masarauta Kai tsaye, sannan sun nuna a shirye suke Dan haka ramuwa ta tabbata a kansu, saboda haka na bada izinin a tura mutane domin ɗaukan fansa. Iya adadin mutanen da suka kashe mana kawai za'a kashe".
Da sauri Badram ( sarkin yaqi) ya miqe tare da faɗin, "Angama ya Sultan"......... Ya faɗa yana me jinjina masa da hannu tare da sauke kansa ƙasa kaɗan sannan ya juya ya fice daga fadar dan zuwa shirya mutanan da zasuje sword of fire kingdom. Babu wanda wanna hukunci na me martaba bai wa daɗi ba saboda wannan cin kashi nasu Queen Hirut akwai rainin wayo a ciki.
_______________Sheikha Barrah ce tsaye a ƙuryar ɗakin ta tana cizon yatsa, gabanta wata kyakkyawar yarinya ce da baza ta wuce 19 years ba tana sanye da wata golden dress me matuqar kyau da ɗaukan hankali, siririn mayafin data yafa ya zame ya koma kan wuyanta hakan ya bawa lallausan baqin gashinta na larabawan asali bayyana kasancewar ribbon ɗin data sa ya cire yana jefe a bayanta, gashin kuwa baqi sidik dashi ya kai har ƙarshen bayanta dan har taɓa ƙasa yake daga durqushen da take. Dukda sanyin Ac dake ɗakin ita gumi take ga hawayen da ya gama wanke fuskarta, cikin shesheqar kuka take magana Muryarta harta dashe. "Maama dan girman ALLAH ki barni na tafi, ki amince nayi nesa da masarautar nan, nayi nesa da kowa maama ki taimaki rayuwata, zuciyata zata iya bugawa idan na cigaba da zama".......... Ganin mahaifiyarta ta batace komai ba har lokacin yasa ta matso ta sake riqo ƙafafunta cikin raunin murya ta ce, "Maama ki qaddara bansan komai ba, na rantse Miki ko zan mutu bazan fidda sirrin ki ba domin ke uwata ce, kawai inason nayi nesa daku ne saboda.........." Shiru tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta, wani irin yawu Maama ta haɗiya kwat kafin ta ce, "Tashi ki je sai na nemeki".
Ba yadda zatayi domin ta san in har ta sake ran mahaifiyarta ta yafi haka ɓaci to fa komai zai iya biyo baya. Share hawayen ta tayi kafin ta ja gyalenta ta rufa akanta ta tashi ta fita tana layi kamar wadda ta bugu saboda kukan da ta sha ya mata over. Sulham kenan autar uwargida Sheikha Barrah, a maimakon ta fuskanci soyayya da tarairaya na kasancewarta auta sai take fuskantar kyara, tsangwama da hantara a wurin mahaifiyarta ta, gata da farin jini kowa son ta yake amma banda mahaifiyarta domin in a gaban yan uwan ta ne ko mahaifinta Sultan tsantsar soyayya da tausasawa ne tsakaninta da mahaifiyarta ta amma yayin da bata ganin idonsu to fa a nan ne zata shiga cusguna mata, tun da ta taso a haka take ba tare da tasan laifin data aikatawa mahaifiyarta ta ba. WANNAN KENAN.
A ɗan tsorace ta bi bayanta da kallo har ta fice ta rufo ƙofar, sai a lokacin ta saki ajiyar zuciya tare da ƙarasawa gaban mirror ta ɗauki wayarta ta sanya wata number tayi dialing, saidai har ta katse ba'a ɗaga ba, bata haƙura ba ta sake kira, saida tayi missed