BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   10 / 53

27K to 30K   out of 156.9K words

ɓata anan, saqon da ya bamu shi ne Kar kayi gangancin saka wani a matsala ta hanyar jingina shi da madam Nayrah domin hakan zai I........."

Tarar numfashin sa dad yayi, "iyaka yace zai sa a ɓatar dashi ko? to Kar ya fasa ya'ta sai na aurar da ita ga mutumin kirki wanda nakeso, ni za'ayi wa barazanar banza da wofi".

"With due respect sir ina baka shawara daka janye wannan zancen naka, dan babu halittar data isa Boss yayi takara da ita".

"Duk uban daya fasa......"..... Mumu ce ta toshe masa baki. "Dan ALLAH alhaji kabar abun haka".

Cikin ɗaga murya ya ce, "bazan bari ba whl bazan bari ba, yar tana matsayin ya'ta ace za'a min iko da ita, wato ma fin ƙarfi zai nuna min, Kai ku fice min a gida ko na haɗaku da hukuma dama neman Ku suke ido rufe, yanzu zasu ɗaure ku daga Ku har shi tantirin shugaban naku har igiya tayi saura, shi ma ai baifi ƙarfin hukumar ba kuma tana nan tana jiran sa".

Murmushi Philip yayi tare da bubbuga bayan Danny sannan ya juya ya fice Yana maida hular kansa, shi ma Danny ya rufa masa baya.

"Da Kar Ku fita mana, ƙaryar banza ƙarya wofi".

Nayrah ce ta fito daga kitchen hawaye jage jage a fuskarta ɗan tunda taji abinda ke faruwa tsakanin su dad da su Philip hankalin ta ya tashi ta shiga kiran sa amma bata shiga, sam bata san cewa matakin da ya ce zai ɗauka kenan ba, kuma tashin ta kenan daga bacci a firgice taga text ɗinsa cewa ta buɗe Ƙofa saisa batayi wani tunani ba ta buɗe, ashe ƴan daba ya turo musu yanzu in da sun yiwa dad wani abu fa?.

A gaban dad ta durƙushe kafin tayi magana ya rigata da faɗin, "Au to dama kina ciki kenan, tsohuwar munafuka wato baki rabu da mutumin nan ba ko? in ba haka ba taya zai san Maganar da nayi dake har ya turomin ɓarayi cikin gidana da tsakar dare , keee wato bakyaji ko, ni wai me kuke nema dani ne da kuke neman janyo min magana ku tozarta ni cikin alumma".

"Dad dan ALLAH kayi haƙuri da ab........."

Bai bari ta ƙarasa ba ya ce, "Ke ALLAH ina iya ɗaukeki da Mari idan baki kauce kin ban wuri ba, aure kuma dake da Farshad babu fashi ko zaki mutu na shaida Miki".........ganin dad ya hau dokin zuciya ba kuma zai saurare ta ba ya sa ta tashi ta wuce sama tana zubar da hawayen rashin madafa. Meysa Amjad zai yanke hukunci ba tare da ya nemi shawarar ta ba, gashi yanzu komai ya sake tabalɓalewa.

"Haba Alhaji Dan ALLAH mu bi komai a sannu, kayi hakuri, ka zauna in kawo ma ruwa ka sha sai muyi magana".

"Bani shan ruwan, ba abinda zan sha kema ai da haɗin bakin ki, kina sane da duk abinda yarki takeyi kika boye, burin ku dama ni ku hana rayuwata zaman lpy da kwanciyar hankali. To karki yi kuka dani in ya'yan ki suka salwanta".

"Haba Alhaji Ka dinga min adalci mana , Ka tuna da ni na baka shawarar aurar da Nayrah ga Farshad, duk saboda miye? Ba saboda mu tsira daga sharrin yaron nan bane".

Cikin fushi ya sake cewa, "Amma kina sane ai tana tare dashi har yanzu".........."Alhaji! "........ Ta kira sunan sa cikin wani salo, juyowa yayi ya zuba mata ido na ɗan seconds sai kuma ya dauke kai . "Zauna!". Ta faɗa cikin salon bada umarni. Zaman yayi ba tare da ya kalle ta ba, ita kuma ta tashi ta je kitchen ta ɗauko masa ruwan ta miqa masa ba musu ya ƙarba ya sha sannan ta ce, "Tashi mu tafi sama muyi magana a nutse"........ Ba musu ya tashi ya wuce tabi bayansa.




------------------------√




Washe gari ranta fes ta tashi, saida suka gama komai kamar yadda suka Saba ita da Shazeen sannan ta tashi Sahnish shi ma ya shirya, tare sukayi kalaci sannan suka fice gabaɗayan su, Shazeen suka fara saukewa a makaranta sannan suka wuce asibiti domin ayi wa Sahnish dressing ciwukan sa, daga nan suka wuce ta sauka wurin aikin ta sannan shi Kuma aka wuce dashi gida.

Lokacin ɗaukan Shazeen nayi taje ta daukota ta maidata gida sannan ta koma wurin aiki sai lokacin tashin su. Yau ma tare suka fito kamar jiya dan su bunayna basu da matsala sam gasu da saurin sabo. Yau ma kamar jiya a bakin titi suka rabo kowa ta wuce gida, ita dai Hushaima kasuwa ta wuce duk da gajiyar dake tattare da ita ga wani bacci da take ji dan daren jiya bata samu bacci da wuri ba, haka dai ta daure ta shiga.

Shigar ta kenan wayarta ta fara ringing ɗauko ta tayi a jaka, ganin Sahnish yasa tayi saurin ɗauka tana faɗin, "Sahnish lpy kuke?".

"Kash, in anyi magana kuma kice ke jaruma ce gashi yanzu daga waya har kin tsorata, to Me kike tunani?".

Tsaki taja, "Mtwee kana da matsala, miye ne ni?"........."Munga kin dade ne."

"Na shiga kasuwa ne akwai abinda Nike son siya"..........."To muma a siyo damu".

"Tunda ka ban ajiya ba"........ ta faɗa tare da kashe wayar ta maida jaka, daga bayan ta taji ance..........



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______12 & 13



Daga bayan ta taji ance, "sannu ƙaramar ɓarauniya"..........Juyawa tayi idonta ya shige cikin na yarinyar nan da tayi sata a starlight beauty co. sannan ta nemi ta ɗaura mata, Saida ta ƙare mata kallo sannan ta ce, "Yauwa sannu babbar barauniya".........."Ina kudi na ?"........ Yarinyar ta tambaya.

"Dama kin bani ajiya ne?"............ Itama Hushaiman ta maida mata tambayar tana binta da wani kallon banza. "Kuɗin da kika sata jiya, suna Ina?".

"Haa ikon ALLAH, au da kika sata kin bani ne kince na ajje Miki?".

"Amma dai kinsan ba naki bane meysa kika ɗauka, meysa baki maida su jakar tawa tare da Abun hannun da zoben ba, kika sani ramakon kuɗin da banci ba".

Wani gafalallen murmushi Hushaima tayi tare da faɗin, "Ke kina da kuɗi makamancin wancan ɗin kikayi sata".

"Amma dai kinsan ko kogi baiki daɗi ba, kuma abinda na sata ɗin da nayi a Sa'a ai kinga yafi abinda nake dashi ɗin, kawai ki ragemin zafi mu raba asara".

"Zancen banza ma kenan, kinga ni shawarar da zan baki shi ne ki nemi Abun yi domin sata ba sana'a bace dan sai wani ya ajje kin gani zaki ɗauka, in Bai ajje ba Kuma rayuwar ki tana cikin gararin babu, Dan haka ki maida hankalin ki tun da sauran mutuncin ki kafin a samu wasu su ankare dake su Miki dukan da baza ki moru ba"........ Tana kaiwa Nan ta juya da niyyar Ƙara gaba yarinyar nan ta riqo kafaɗarta tare da juyo da ita da ƙarfi tana faɗin, "Whl baki Isa ba ɓarauniyar banza ke har kina da bakin bawa wani shawara, ko kema ba satar kikayi bane?".

Hushaima na juyowa ta buge hannun da ƙarfi tare da nuna ta da yatsa ta ce, "kinga karki ɓatamin rai whl zan iya janyo miki Abun kunyar da har ki mutu baza ki manta ba, sannan ni ban taɓa sata ba, kyauta ce kika ɗauka kika ban tunda ke kika sakamin a jaka Kuma kika biya a asusun ki. Sannan Kuma gargadi na ƙarshe ko a titi kika ganni kika nuna kin sanni sai kin gwammace mutuwar ki kafin wanna ranar, banza Mai matacciyar zuciya, ki rufawa kanki asiri ki wuce ki bar kasuwar Nan tun kafin masu kaya su fara nemanki"............Ta Ƙarashe tana wucewarta ta bar yarinyar tsaye sake da baki cike da mamakin yadda akayi Hushaiman ta san tayi sata a kasuwar, jijjiga Kai tayi cike da borin kunya ta ce, "Zaki San sata gidan barawo rance ce"........... Ta ƙarashe tana saka hannu cikin hijab ɗin ta ta gyara zaman jakar dake kugunta Wadda take cike da hakkin mutane data sanfe.

Ita kuwa Hushaima tana gama sayan abinda zata saya ta tari abun hawa ta wuce gida, tama manta da batun wata ɓarauniya. Ganin me tuktuk ɗin na ƙoƙarin ɗaukan wata hanya daban ya sata faɗin, "Miqewa fa zamuyi"............ "Eh hajiya ai na sani zan biya ne na karɓi saqo sai mu wuce".

"Kaga Malam tunda mun kusa kawai mu ƙarasa ka saukeni sai ka wuce".........Hushaima ta faɗa.

"To Hajiya ai nan gaban mu ne zan karɓi saqon duk kan hanyar ne "............wata wadda Hushaima ta tarar a cikin tuk tuk ɗin ta ce, "Ni mun ma iso, sauke Ni anan" ..............."Gsky bazan tsaya ba ai ba nan mukayi dake ba".

"Kamar ya baza ka tsaya ba tace ma ta iso haa"........ Hushaima ta faɗa a fusace.

"Whl ko me zakuyi bazan tsaya ba sai na kaiku in da zaku".......... hankali tashe matar ta ce, "Malam nace ma na iso ka tsaya na sauka ko na ma ihun ɓarawo Whl" .

"Whl bazan tsaya ba"............ screwdriver Hushaima ta kafa masa gefen wuya da faɗin, " ko ka tsaida mashin ɗin nan ko na burma ma ita whl"........... Gefe guda kuwa matar nan leqowa tayi tana ihun faɗin ɓarawo jama'a ɓarawo ku taimaka. Jin haka ya sashi ƙara gudun mashin ɗinsa ɗan yasan yana tsayawa in mutane suka rafke shi sai sun halaka shi saisa kawai ya gommaci in ma caka masa Hushaiman zatayi saidai ta caka masa. Wani irin bugu Hushaima ta daddage ta kai masa a gefen wuya, rawa kan tuk tuk ɗin ya fara masa a hannu saboda a bazata yaji bugun, take jijiyar muqamikin sa ta riqe yayinda gudun tuk tuk ɗin ya sassauta, kafin ya gama dawowa hayyacin sa Hushaima ta kudunduni kayanta tayi tsalle ta dira a waje ganin haka yasa ɗaya matar ma bin bayanta. Nan mutane suka rufarwa tuktuk ɗin saidai ko da sukayi nasarar isa gareta me tuk tuk ɗin ya suma, ita kuwa Hushaima ba tare data damu da yan raunikan data ji ba ta tsari wani me tuk tuk ɗin ta wuce gida tana godewa ALLAH da ya taimake su.

Tana shiga ta samu Sahnish tsaye a tsakar gidan yanayin fuskar sa ne ya shaida Mata kamar yana cikin damuwa, ƙarasa shigowa tayi kallon furkarsa ta ce, "Sahnish lpy meke faruwa?"

"Meysa kike da taurin Kai ne Hushaima? Meysa duk abinda kika sa kanki sai kin yi ? Meysa in kina Abu bakya tunanin abinda zaije yazo"...........Cikin Rashin gane Kan zancen sa ta ce, "me.. me kuma ya faru?"

"Meysa zakiwa su karafiya shu ne idan kuma suka gane da sa hannun ki ciki fa? Whl baza su barmu ba kuma kin sani ".

"Shu ne kuma? Ni ? To ina ruwana dasu, ni ai tun ranar da suka ma wannan dukan naje mukayi cacar baki ko kallon inda suke zama ban sake yi ba, to uban wa ma yace ni na musu Shu ne?".

"Ba uban daya gayamin Sarkin masifa, kawai naje shagon Juma ne zan saya katin waya, sai naji wani yana faɗin wai hukumar yaqi da miyagun kwayoyi ta ƙasa ta kama su karafiya, kotu ma ake shirin kaisu saboda an same su da kwayoyi masu hatsari".

"Eh shikenan kuma sai zuciyar Ka tace ma ni nasa a kama su ko, saboda nice kullum cikin rigima ko Sahnish? Wai meysa Baka kyautata min zato ne? kullum a cikin zargi na kake nayi kaza nayi kaza".

A sanyaye ya ce, " kiyi hakuri, yadda kika fita ranar da qudurin fansa yasa nayi zaton haka".........bata ce masa komai ba ta ajje jakarta tana kokarin cire gyalenta suka ji ana kwankwasa ƙofar gida, kallon ta yayi da faɗin, " waye ne?".

Wucewa tayi ciki tana Kiran Shazeen ta ce, "Ina cewa tare dakai muke tsaye, kaje Ka duba mana".

Juyawa yayi ya fita zuwa ƙofar gidan dan ganin waye ita kuma ta shige ɗakin su. Yana fita ya tarar da wasu maza biyu tsaye sai wata makociyar su. "Lpy dai?".......... Ya tambaya yana binsu da kallo. Matar ta ce, "Gashi nan tun ɗazu ya Kafa min a ƙofar gida yana neman haɗani rigima da mijina, wai sai na fito masa da Hushaima nace masa ba nan bane yaqi yarda, to kai kaga gidan nata karka ƙara dawowa ƙofar gida na".

Kallon sa Sahnish yayi da faɗin, "To lpy dai?"..........."Eh lpy ba lau ba nayi mata kayan ɗaki ne sai ta bani rabin kuɗin tace zata cikamin rabin daga baya na bata kayan, to kusan sati kenan dana haɗota da yara na suka kawo Mata kayan, dake Babbar mota bata shigowa sai suka ajje daga bakin layi ita kuma tasa aka ɗauko mata kayan aka shigo dashi nan layin, to naji shiru kuma bana samun layin ta shi ne na ɗauko yaron da suka zo tare ya nuna min gidan wannan matar, ita kuma tace ba nan bane".

"Kayan ɗaki ? Kuma anan gidan? Sannan kace Hushaima?"........... Ya tambaya cike da mamaki.

"Eh, kaga ka shiga ka kirata kawai"..........Jijjga kansa yayi da faɗin, "kwantar da hankalin ka, zan kirama ita mana"...........Ya faɗa yana juyawa ya wuce ciki har lokacin mamaki yake. "Hushaima!, Hushaima!".

"Wai Sahnish lpy kake ta ƙwalamin Kira haka, wanka fa nake son shiga".........Ta ƙarashe tana leqowa.

"Eh wasu mutane ne suka zo neman ki, suna ƙofar gida "..........."Wasu mutane kuma? To uwar me zan musu?".

"Ah waqa a bakin me ita ai tafi daɗi, ki leqa dai ki gansu tukunna".

"Kai dallah in zaka faɗamin su waye ka faɗamin bana ciki da iskanci".

"Ya hakuri bani na kar zomon ba, wai wani kafinta ne da ya haɗa Miki kayan ɗaki, kika karɓi kaya kuma kika gudu baki cika masa kuɗi ba".........ya ƙarashe yana dariya ƙasa ƙasa.

"Kai kaga inda aka shigo da kayan ɗaki a gidan nan ne?"...........ƴarfa hannu yayi da faɗin, "To ni na san muku ne, yanzu dai kije ki sallamesu".

Ƙwafa taja ta nufi ƙofar gidan, tana fitowa matar ta ce, "Gsky zan gaya Miki karki Ƙara taro rigima ki turomin gidana wannan ai sai ki kashe min aure"........... Matar ta faɗa cikin ɓacin rai.

Saqale Hushaima tayi baki buɗe tana kallon ta kafin cikin ɓacin rai ta ce, "Ke da ALLAH malama dakata ni na nuna masa gidan ki ne, ke kinsan ba gudun rigima nake ba bare kice tsoron hakan yasa na turoshi gidan ki. Ki kama kanki Bana shiga harkar kowa a unguwar nan duk kuma wanda ya shiga tawa to whl rashin mutuncin da zan keta masa ko karai bazai shishina ba , Kai kuma uwar wa kayi wa kayan ɗaki?"......... Ta ƙarashe tana zaro masu rikitattun idanun ta. Duk wanda ya kalle ta a wannan lokacin yasan tabbas ba karamar yar rigima bace ba kuma tsoro a tattare da ita daidai da misqala zarratin.

"Dan ALLAH kiyi hakuri"...........Ya faɗa yana juyawa wurin matar ya ce, "Ni fa ba wannan bace wadda nake nema".

"Kai malam karfa ka rainamin hankali, wannan dai itace Hushaima kaɗai a unguwar nan".

"Hushaima ne sunan ta amma ba wannan bace"......... Carpenter ya faɗa, Hushaima data maidasu TV ta buɗe baki zatayi magana dan tuni ta gano wata ce kawai ta damfare shi a layin ta kuma yi amfani da sunan ta, Kuma duk yadda akayi ta mata farin sani ne, bata kai ga yin Magana ba ta hango wata matashiyar budurwar na fitowa daga wata arniyar BMW i5 sedan, tana sanye da wasu shegun English wears riga da wando, fuskarta manne da wani makeken glass, kyakyawa ce sosai gashi kallo ɗaya zaka mata ka hango class a tare da ita daga yanayin takunta ma. Da wani irin kallo tabi mutanan dake ƙofar gidan kamar taga wasu sabbin halittu daga wata duniyar kafin ta maida kallon ta ga Hushaima data ɗan saki fuskar ta duk da ba wai murmushi take ba. "Mutan new york saukar yaushe? Bismillah shiga daga ciki mana Ina zuwa".

"Ke dai bari tun last week na dawo ban faɗa Miki bane saboda dama surprise nake son miki"......... Ta ƙarashe tana sake kallon mutanan sannan ta shige ciki tana faɗin, "Saikin shigo".

Ita kuwa Hushaima baquwarta ta na ida shigewa ta fara tijare mutanan nan tare da yin jam'u ga dukkan mutanan unguwar ta musu tas sannan ta ce ALLAH yasa wata ta sake amfani da sunan ta whl sai taci mata uwa, duk ta tara mutane a ƙofar gida daga karshe ta ce, "ku Kuma ku daibi kafuran ƙafafunku ku bace min daga ƙofar gida tun kafin rai na ya ida bacewa"...........sumi sumi suka wuce, da kallo ta bisu kafin ta ce, "Munafukan mutane da ana ruwa suna irgawa tsabar sa ido, ALLAH yasa wani me tsautsayin ya sake daibo kafa yazo ƙofar gidan Nan"..........Ta Ƙarashe tana juyawa ta shige tare da gabzo ƙofar.

A tsaye ta samu baquwarta ta tana danna waya, ɗaki ta wuce ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa tana faɗin , "Ya hakuri Amla na barki a tsaye kina jira".

Sai da ta zauna sannan ta kalli Hushaiman data zauna ita ma, ta ce, " ƙawata meke faruwa Wai?".

"Mtwee barni kawai, mutanan unguwar Nan ne suke neman su tsokano ni, kinsan mutane baka shiga harkar su ma nema suke su taqale ka, wai wata ce akayiwa kayan ɗaki bata cika kuɗin ba ta gudu Kuma Wai sunan ta Hushaima shi ne suka kawo carpenter nan".........."Yanzu ya kukayi dasu?"

"Ai kema kin sani, na saita musu hanya mana, to ni akwai wata sabuwar buɗewar ido da za'a nuna min ne".

Dariya Amla tayi da faɗin, "ƙawata kenan baki da dama, nayi missing dinki sosai whl".

"Ki bari kawai, ai Ina ganin videos ɗin ku a yanar

10 / 53