BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   23 / 53

66K to 69K   out of 156.9K words

wani file tare da faɗin, "Hushaima muje ki rakani, Sahnish kai sai ka dawo nan driving seat ka zauna Ka jiramu ko".......... Da "to". Ya amsa sannan suka buɗe ƙofa suka fice suna sake ƙarewa tsarin gidan kallo especially Hushaima data zama wata yar ƙauye a wurin, dan gsky tsarin gidan ya haɗu matuqa gashi dai gida ne amma kuma gefe guda an ware an fitar da ɓangaren office office.

Gaban building ɗin ofisoshin suka tsaya, wurin wani mutum dake tsaye sanye da uniform, Amla ta ce, " Am ko zaka yi mana jagora zuwa wurin me gidan"..........."Me gidan ai ya daɗe ba lpy sai ɗansa Oga Amjad dake zuwa shi ma ba kullum ba, amma dai yanzu kunyi Sa'a yana ciki".

"To Dan ALLAH yi mana iso, saqo na kawo masa".

"Muje to" .......... Ya faɗa Yana wucewa ciki. "Ni Kam Amla je ki fito kawai, wurin nan ya min kyau Ina so na ɗan zagaya kafin ki fito". Ta faɗa tana bin wurin da kallo cike da shaawa dan har cikin zuciyarta wurin ya burgeta.

"Ah ah in baza ki shiga ba to ki koma mota, ai ba haka mukayi dake ba, haka kawai kije ki ɓacemin in zo tafiya in rasa inda kike". Amla ta faɗa dan tasan halin Hushaima kar taje ta kwaso mata magana Saisa ta faɗi haka.

"To naji shikenan, barni na koma ɗin".........Ta faɗa tana juyawa ta nufi motar, girgiza kai Amla tayi tabi bayan security ɗin nan. Saida taga shigewarta sannan ta juyo cikin shauqi take bin flowers ɗin da kallo wasu ta shafa, wasu ta cira, wayarta ta ciro ta shiga Snapchat ta fara ɗaukan hoto har bata san lokacin data tsinci kanta a cikin wani ƙayataccen garden ba, sake gyara wayarta tayi tana cigaba da ɗaukan pics ɗin, wasu ƙananun karnuka ta hango irin na turawan nan da zaku ga suna tafiya gashin jikinsu na jan ƙasa, ɗan komawa tayi da baya ta laɓe ba wai dan tana tsoron karnukan ba sai dan tana gudun su ganta suyi haushin nan nasu, dan ba abinda ke saurin hargitsa mata lissafi irin Kukan Ƙare, daga inda take laɓe ta cigaba da ɗaukan hotonan view ɗin harda karnukan, kwata Kwata bata lura da mutum a wurin ba.

Amjad dake tsaye yana waya tunda ta shigo tana ɗauke ɗauken hoto yake kallonta ta ƙasan ido, juyowa yayi dakyau daidai lokacin da ta laɓe a jikin ginin saboda hango karnukan da tayi amma sai yaga still ɗaukar sa hoton take, hannayenta da gefen fuskarta ya zubawa ido tare da faɗin, "Ina sane da komai Hanash, Kai dai ka cigaba da aikin ka kawai, sannan ka tabbatar duk wani shige da ficen da za'ayi a sirrance ake yin sa, Kar kowa ya sani, tunda already an gama shirya komai, so ba wata matsala for now sauran maganganun zamuyi anjima, I'm going to attend to something now"..........Yana kai wa nan ya kashe wayar ba tare da ya saurari amsar na cikin wayar ba, ya nufi inda Hushaima take, ɗaya daga cikin karnukan ne ya fara haushi yana tsalle tare da bin ƙafar Amjad ɗin yana wasa, ai da wani irin sauri Hushaima ta bar wurin. Dakatawa yayi da tafiya tare da lumshe idanun sa ya buɗe, fasa bin wurin yayi ya juya ya shige ta ƙofar baya.

Ko da ta fita daga garden ɗin direct inda su Amla suka shiga ta nufa tana haki tsabar rikicewar da tayi har wani duru duru take gani dafe bangon tayi tana sauke numfashi. "Are you alright?"......... Ɗagowa tayi ta ga wata mata tsaye tana kallon ta.

"Da ALLAH ko kinga ƙawata data shigo yanzu Ina tabi?".......... Kallon rashin fahimta matar take mata dan batajin hausa, wani saurayi ne da ya fito daga wani office yana tsaye gaban wasu print server yana printing ya ce, "I think she's with the Oga Amjad guest, excort her, she's in that office".......... Saurayin ya faɗa yana ƙarewa Hushaima kallon tsaf, dan baza ka taba kallon ta kace irin yaran nan ne dako wuqa ƙasa musu a kai baza su iya ko da rubuta sunan su bane, saboda Hushaima ta samu wayewa sosai karatun ne sai a hankali, amma dai zamuji komai nan gaba.

"Okay let's go". Matar ta faɗa tana nuna mata hanya tare da shigewa gaba, bin bayanta tayi har zuwa wani madaidaicin office, ba tarkace sosai a cikin sa, table ne kawai da main chair sai guest chair guda ɗaya wadda Amla ke zaune tana ganin ta tayi saurin miqewa tana tambayar, "Me ya shigo dake kuma, ke da kikace kin fasa shigows?" .

"So you are together, right?"......... Matar ta tambaya.

"Yes". Amla ta amsa, bata sake cewa komai ba ta juya ta fita tare da ja musu ƙofar.

Gaban table ɗin ta Ƙarasa tana cire gyalenta ta hau firfita da hannunta. "Wai me ya faru ne?".......... Amla ta tambaya tana binta da kallon tuhuma. "Kare". Ta bata amsa har lokacin wata juya juya take ji.

"Mtweee wai Kare ke kin fiya tsoro whl, ni duk na ɗauka wani abun ne ma, ina Sahnish ɗin?"........."yana mota mana". Ta faɗa tana zagayawa ta zauna kan main chair dake office ɗin tanajin kamar zata kifa. Bata fi two minutes da zama ba aka buɗe ƙofa, shigowa yayi Philip biye dashi, da sauri Amla ta miqe saboda kwarjinin sa da ya cika office ɗin, "ina kwana?".......... Ta faɗa a ɗarare, Kai kawai ya ɗaga mata alamar lpy. Philip ne ya nufi wurin Hushaima da sauri cikin faɗa ya fara faɗin, "Come on, get up, who gave you the right to sit in the boss’s chair".

"Hushaima tashi mana, ko bakiga mai wurin yazo bane ". Amla ta faɗa da sauri.

Ɗagowa tayi ta kalla Amla sannan ta kalla Philip dake tsaye kamar zai Kai mata duka a fusace ta miqe tare da wurga kujerar baya da ƙafarta cikin fushi ta ce, "kujerar banza kujerar wofi, akan kujera zaku kamawa mutane ihu a ka, kujerar lu'u lu'u ce ko ta zinare aikin banza aikin wofi".........ɗaga hannu Philip yayi zai kai maketa Amjad ya girgiza masa Kai alamar Kar yayi sannan ya zagaye su dan isa ga kujerar tasa, saidai bai gama wucewa ba Hushaima ta tsirtar da yawu tare da jan tsaki. "Hushaimaaaa me haka? lpyr ki kuwa? Zo ki fita to, tafi ki jirani a can".

"Dama zan fita ai ko baki faɗa ba Kuma kema karki sake kice zaki ɗaga min murya yauwa"........ Philip ne yayi saurin shan gabanta da faɗin, " You can’t go anywhere, you disrespected the boss, you have to go, bend and tell him sorry before you leave".

"Dan ALLAH je ki bashi hakuri to".

"Whl ba'a haifi uban da zanje in bawa hakuri ba, gwara tun wuri ma ku cire wannan tunanin a ranku".

"Hey, you know who the boss is and his dad here?".

Cikin ɗaga murya kamar zata kai masa duka ta ce, "kaci durun uwarka da turancin, in ka Isa ka faɗa da hausa mana kagani".

Ɗagowa Philip yayi ya kalli inda Amjad ke zaune kan kujerar sa hankalinsa kwance kamar baisan meke wakana ba, kamar yasan Philip ɗin shi yake kallo, sai ya ɗago shi ma, da hannu ya masa alamar ya bata hanya ta wuce kawai.

Matsawa yayi Yana faɗin, "kinyi Sa'a whl amma da sai kinyi bayani ƙaramar marar kunya kawai"......... Juyawa tayi ta fice da sauri, komawa Amla tayi ta zauna tana satar kallonsa cike da mamakin wani abu data barwa kanta sani, haƙuri ta fara bashi ya katseta. "Go ahead and say what brought you here, I have things to attend"......... Ajiyar zuciya ta sauke a sirrance kafin ta miqa masa File dtin da faɗin, "Daddy na ne yace na kawo ma wannan".

Karɓa yayi da faɗin, "Alryt, you can go".

"Thank you". ta faɗa tare da tashi ta sake satar kallonsa suka haɗa ido da sauri ta juya ta fice.

Takarda ya yaga a gefe yayi dan rubuta akai ya miqawa Philip tare da yi masa thumb, "Good job".

"Thank you boss". ya faɗa tare da duba takardar sai Kuma ya juya ya fita .


______________A mota ta tarar da Hushaima sai ruwan masifa take kamar zata kama da wuta, shiga tayi da faɗin, "Gsky Hushaima baki kyauta ba ko kaɗan, kawai ki tofawa mutum yawu sannan kija masa tsaki, kinsan waye shi kuwa? Kuma ma tun farko ai da baki zauna a kujerar ba, ko kuma da kika jisu sai ki tashi ki bashi wurinsa, ALLAH ma ya taimakeki whl da yace a barki ki tafi dan nikam bani da ƙarfin fitar dake anan".

"Wai meke faruwa?".......... Sahnish ya tambaya dan shi bai gane Kan masifar Hushaiman ba, shi dai kawai yana jin ta ne.

Faɗa masa abinda ya faru Amla tayi bata ƙarasa rufe bakinta ba Hushaima ta ce, "In zaki maidani in da kika ɗaukoni ki maidani, in Kuma baza ki maidani ba in san inda rana ta min". Girgiza Kai Amla tayi tana cilla hancin motar ta Kan titi dan already ta saba da zafin zuciyar nan ta Hushaima.

Wayarta ta ɗauka tana driving ta lalubo wata number da akayi saving da ride or die tayi dialing, Saida ta kusa katsewa akayi picking, "Hello Amla!"......... Handsfree ta danna hankalinta akan titi ta ce, "Nashwa ykk?"

"Lpy kalau alhamdulillah".

"Ina Nayrah ɗin?"........."Muna asibiti whl jiya ta samu accident."

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wani asibitin ne Nashwa"........ta tambaya a rikice cikin tashin hankali.

"General hospital, A&E section ".

"Ina kusa da Asibitin bari na ƙaraso Nashwa ".......... Ta ƙarashe tana kashewa sannan ta ɗago da niyyar magana ta tsinci idanun Hushaima a kanta tana jifanta da wani kallon tuhuma, hankalinta ta maida titi da faɗin, "Besty ina friend ɗin nan tawa Nayrah da nake baki labari, to itace tayi accident, bari muje mu duba ta sai na kaiku gida ko".

Hushaima da har lokacin idonta ke kan Amla, a dake ta ce, "Ba zani ba, sauke ni a nan".........."haba Besty dubiya fa akace, ai ko dan ladan da zaki samu kya je".......... Faɗin Amlan, saidai kafin ta rufe bakinta Sahnish daga bayan mota ya karɓe da faɗin, "ki sauke mu daga nan ɗin kawai Amla".

Da mamaki Amla ta kalli Hushaima da yanayin ta yafi na ɗazu tsanani sannan ta kallo Sahnish ta mirror wanda shi ma daga kallon data masa ta fuskanci kamar mood ɗin sa ya canza, to meke faruwa? Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsar ta, sai kawai ta ce, "Shikenan muje na kaiku gidan sai na dawo".

Ba wanda ya ƙara magana a cikinsu sai Amla dake mamakin sauyawar Sahnish ɗin dan a iya tsawon lokacin da suka kasance tare baza ta iya cewa ga lokacin da taga wani yanayi na daban a kan fuskar Sahnish ɗin ba, to me ya sauya shi lokaci guda? Ni kuwa nace ummm inji me ciwon hakori.

Kowa da abinda yake tunani har suka ƙarasa gidan, tana tsayawa Hushaima ta Buɗe mota ta fice tayi shigewarta ciki ba tare da ta ko waiwaye su ba, Sahnish na ƙoƙarin fita shi ma Amla data ƙasa haƙuri ta ce, "Sahnish wai meke faruwa? Naga kai ma kamar yanayin ka ya sauya wanda kuma ba haka na shigo motar na sameka ba?"........... Dan jijjiga kansa yayi tare da faɗin, "Bakomai Amla, kai na ne ya sara whl, ina so ne dama naje na sake shan magani na huta "........... cikin gamsuwa da bayanin nasa ta ce, "Ayyah, ALLAH sarki, sannu kaji ALLAH ya baka lpy, dama sai a hankali zaka warware ". Ta ƙarashe tare da sanya hannu a jakarta ta ɗauko kuɗi masu yawa ba tare data irga ba ta miqa masa.

Dukda yasan suna da buqatar kuɗin saida yayi shakkar karɓa a yanzu saboda wani dalili nasu shi da Hushaiman, maganar Amla ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi. "Ka karɓa mana Sahnish ba yawa".

"Da kin barshi Amla, Kar mu ɗaura Miki nauyi da yawa ".

"Bakomai Sahnish, Dan ALLAH Ka karɓa, Ni da ku ai duk ɗaya ne "........... Ba yadda ya iya dan yana matuƙar jin nauyin Amla ko dan ɗawainiyar da take dasu, haka ya karɓa ya sa a aljihu dan bazai tunkare ta da kuɗin yanzu ba saita huce sai ya nuna Mata. Sallama ya mata sannan ya shige ciki shi ma.

Lokacin data shiga gidan bata ko kalli kowa ba ta shige ɗakinsu, kan yaloluwar katifar tasu ta zube tana jin kanta na wani irin Fisga ga zuciyarta dake tafarfasa, sunan ALLAH ta fara ambato kaɗan kaɗan ta fara jin nutsuwarta na dawo mata, abinda ya faru tsakanin ta dasu Amjad ne ya shiga dawo mata daki daki a ƙwaƙwalwarta kamar wadda aka tsikara ta zaune, "Shi ne, tabbas shi ne ko da a wancan lokacin ban ga fuskar sa sosai ba, amma ku ma suma Boss suka kira shi dashi".........Shiru tayi tana recalling scent na perfume nasa, na lokacin da suka fara haɗuwa da na yau. Hushaima akwai matuqar wayo take ta gane shi ne, tun daga kan yatsun hannunsa da Saida suka kwanta a kumatunta zuwa yanayin jikinsa, turaren sa tare da sunan da suke kiransa dashi. Dan baza ta kwanta da muryar sa ba tunda a yau baiyi Magana ba ballatana kuma fuskarsa wadda baza ta iya cewa ga kamanninta ba a haɗuwar su ta farko sai yau.

"waye shi?"........... Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsar ta, wayarta ta ɗauka ta hau neman layin Amla amma bata ɗaga ba, cillar da wayar tayi tare da miqewa tsaye tana faɗin, "wataƙila wannan itace damar da zan samu ta ɗaukan fansa".

Readers in baku manta ba ai Hushaima ta ɗau ƙudirin ramuwar abinda Amjad ɗin ya mata a ranar da suka fara haɗuwa to yanzu fa an tada tsohon giɓi ko ya zata kaya oho.

Shuru tayi tana ɗan buga hannunta cikin na juna, wayarta da tayi ƙara ce ta dawo da ita duniyar mu da sauri ta matsa ta ɗauka ganin Amla. "Hello Ƙawata ".......... Cikin jin dadin jin muryarta haka alamun ta sauko Amla ta ce, "Besty w......" Tarar ta tayi da faɗin, "Waye wannan wanda mukaje wurin sa ɗazun?"......... Shuru Amila tayi kafin ta ce, "lpy dai?"

"Lpy ni dai, dan ALLAH ki bani amsa ".

"Amjad Hashim Darwin shi ne sunan sa mahaifin sa shine mamallakin HD AURUM MINING da Kuma HD REFINERY ai baza ki ƙasa sanin sa ba saboda sannane ne gidajen television na gida dana ketare duk suna yawan nuna su shi da mahaifin sa, saisa nayi mamakin abinda kikayi masa saboda Babban mutum ne".

"Amla abinda na tambayeki daban amsar da kika bani daban, cewa nayi waye shi ba waye mahaifin sa ba".

"To Besty ni abinda na sani ai shi na fada Miki k........." Bata ƙarasa ba Hushaima ta kashe wayar tana jan siririn tsaki. komawa tayi ta zauna ta shiga tunane tunane, a haka Sahnish ya shigo ya sameta ta zuba wa wuri guda ido, shigowar sa ya sata ɗagowa ta zuba masa ido har ya ƙaraso ya zauna gefenta tare da faɗin, "Anya ba su ba ne?"........... ɗaga masa kai tayi sannan ta ce, "Ba wai Sahnish su ne, ni lokacin da Amla take bani labarin ta ban taɓa kawowa su bane sai yau da naji muryar ɗayar".

"Yaushe suka dawo garin nan da zama to"..........Shiru tayi ba tare data bashi amsa ba, hakan yasa shi ma yaja bakinsa, kowanne da abun da yake tunani can kuma Hushaima ta miqe ta ɗauki gyalen ta da waya tana faɗin, "Ni zan fita, in Barka a ɗakin ne ko ya?".......... Ganin yanayin ta ba yadda yayi tunani ba ya sashi zaro Kuɗin dake aljihun sa ya miqa mata, "Gashi nan Amla ce ta bayar".



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️




___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22


STEP 1


PAGE _______32


Karɓa tayi ta irga dubu hamsin ne, talatin ta ɗauka ta miqa masa ashirin sannan ta juya da niyyar fita, kallon kuɗin yayi kafin ya ce, "Hushaima tsaya, wanna ai yamin yawa ke ce fa dawainiya take kanki, ki Ƙara ragewa"..........juyowa tayi ta kalle shi, "Wai kana nufin ni zan cigaba da wanna Kai kawon ne, dole fa Kai ma ka miqe ka san abunyi, zaman hakan ba zai ma ba, ya kamata ace komin ƙanƙantar sa kana samowa, dan yanzu hatta Shazeen in za'a saya mata wani abu saidai a haɗa in ba haka ba ta haƙura"............. Ta ƙarashe cikin faɗa tare da juyawa ta fice dan tasan in ba haka tawa Sahnish ba bazai taɓa miqewa ya tsaya da ƙafarsa ba yadda take so, gashi dai akwai zafin nema amma abu kaɗan sai ya hanashi neman, abu kaɗan ke rikita shi, yayi ayyukan ƙarfi da yawa amma daga ɗan abinda bai kai ya kawo ba sai ya ce shi ba zai koma ba ya bar wannan aikin, haka kwanaki ya samu aiki wurin mechanics amma daga su karafiya suka ritsa shi shikenan ya tsorata ya bar aikin, yayi aikin wanki da guga a wani gida shi ma ba'ayi nisa ba ya zube rashin lpy wai pneumonia ya kamashi, yayi aikin sayar da ruwa na jarka amma kwata kwata ya ƙasa iyawa da gwagwarmayar dan yana tsaye sai abokan aikinsa suzo su cike kurar ruwansu suyi gaba yana kallo bayan kuma shi ne akan layi. Ita Kuma ba wai ta gaza bane ah ah, kawai dai tana so ya zama me juriya, saboda yau da gobe ba abinda ta bari, gatan da zata masa shi ne ta nuna

23 / 53