Author : Young Writer Category : Tknovels
sa ko Kuma Kai da kake cousin ɗin sa".
"Whl ku canza hali, Sam wanna bashi bane abinda ya kamata ku dingayi matsayin ku na yayyun sa, abinda ya shafe shi ai ya shafe ku ne duka".
"Ya isa haka juraysh"......... Anah ta faɗa tana ƙoƙarin tausar zuciyarta dake zafi.
"Ka dai yi min gurguwar fahimta ne kawai Juraysh Amma ba damuwa, Anah ni zan koma".......... ya karashe Yana miqewa ya musu sallama ya fita.
Waya Anah ta ɗauka. "Anah me zakiyi?".......... Juraysh ya katseta.
"Juraysh so nake naji ko da gaske da sa hannun sa a ɓatan yarinyar da iyayen ta, hankali na gabaɗaya ya kasa kwanciya, zuciyata ta rasa sukuni".
Girgiza kansa yayi da faɗin, "Haba Anah Kar ya zama kema ana influencing ɗinki mana, Anah idan har Amjad zaisa a batar dasu kenan bashi da gaskiya kuma ya aikata laifin da ake zargin nasa dashi"........... Shuru tayi ya sake faɗin, "kiyi tunani sosai fa Anah, ni whl ko wa'annan Yan uwan nasa ba wai na yarda dasu bane, ki duba fa yadda yake Ƙara wani sussunkuyar dakai, shi fa munafiki baya zuciya duk abinda zaka masa zai shanye ne".
Shuru Anah tayi tana tunanin maganganun Juraysh ɗin Kuma da alama suna tasiri a tattare da ita.
_____________Zaune suke a wani madaidaicin falo su biyu ne sanye da ƙananun kaya polo t shirt da sweet pant irin na sport, t shirt ɗin ta bayyana ƙwaryar tumbin nan nasu ras dashi. "Dalilin da yasa na buqaci ganin ka Alhaji Huzaif daga ni sai Kai ba tare da ko su Abid sun sani ba shi ne nasa an ɗauke yarinyar nan da iyayen ta"............Saurin kallon sa Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, " Mai sa zakasa a ɗauke su, yanzu in kotu ta zauna aka nemi ganin su fa, ai sai mutane suce dama ƙazafi suka masa".
"Eh ai gudun tonuwar asirin sa ne yasa ya ɓatar dasu"......... Kallon sa yake cike da Neman Ƙarin bayani.
"Saboda a wannan zaman zasu bayyana shaidun da kotu ta buqata mana sunan sa zai ida baci ".
Shuru Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, "To naji, amma ai tare ake komai dasu Alhaji Abid mesa yau Kuma kace mu haɗu mu kaɗai daga ni sai Kai?".
Gyara zama yayi da faɗin, "Abinda ya tara mu anan daban ne, bana so mu bawa Ahuoyzah haɗin Kai ya samu wanna karɓuwa a majalisar man fetir ta duniya, domin fa mu yan kallo zamu dawo".
"Ehhhh Kuma haka ne, amma Kuma ai zai biyamu sannan yanzu in mun masa haka miye namu"......... Ɗaura ƙafarsa yayi ɗaya kan ɗaya yana murmushi ya ce, "Zamu barwa Ramphant Juwaira filin domin shi ya dace ya samu wanna karramawar ta wanna shekarar".
"Canza hanya zamuyi dasu kenan?"....... Alhaji Huzaif ya tambaya yana gyara zama .
"Ko ɗaya muna daga nan ɗin zamuyi komai Amma bana so su Hammoud su sani, na janyo ka ne saboda Kai ma ka samu alheri a tare dashi, saboda shi babu wanda yafi mu shiga gabansa kuma kasan bai taɓa samun ko da star ɗaya ba so yana cikin ɗokin samu, zai sakar mana ragamar komai ne".
Cikin jin dadi Alhaji Huzaif ya ce, "Dama ai munafukai ne, ni dama tun can na lura sun ɗaukemu kamar wasu yaran su, Kuma mu zamu bisu ta ƙarƙashin ƙasa saidai su gansu kasat wanwar"...........Dariya sukayi tare da tafawa Hajj zawaad ya ce, "kanka na ja Mutumi na".
"Amma fa wani hanzari ba gudu ba".........."Ehh wanne kenan?".
"Batun yaran HD".
"Ina sane da su barsu, dama nake basu kawai suyi nasu tunda yara ne kuma kasan ai su basu san Kan harkar ba, wancan yaron ne ya sani yanzu kuma sun tsige shi gefe, so ba abinda zasu samu wahalar banza zasuyi karshe zasu bace a kasuwar duniya gabaɗaya".
Girgiza Kai Alhaji Huzaif yayi Yana Dariya ya ce, "Baka da daɗi Hajj Zawaad".
_____________Tsaye yake a ɗakin mahaifin nasu
Yana Kai da kawowa waya ce maqale a kunnen sa yana faɗin, "Awais karka min wasa mana kai ma da nake gani me ƙwaƙwalwa, kasan Amjad yana da basira sosai, yana iya bincikosu in ka ajje su a kusa, san samu a fitar dasu daga ƙasar gabaɗaya, ni fa duk wanna shirun da yayi akan komai hankali na bai kwanta saboda na tabbatar akwai abinda yake shiryawa ta ƙarƙashin ƙasa".
Daga ɗaya bangaren Awais ya ce, "Julaybin fitar da wa'annan mutanan ba ƙaramin aiki bane a yanzu kai ma ka sani al'ummah sun san fuskar su hakan kamar tonuwar asirin mu ne ai".
Shuru yayi can Kuma ya ce, "ka shirya su ka sasu a mota su tsallake iyaka mana a baɗɗa musu kammani kawai"..........Awais zai sake magana ya ce, "ka ga karka kuskura ka sake kirana in ba wanna labarin zaka bani ba"...........Yana kaiwa nan ya katse Kiran yana sauke naunauyan numfashi tare da duban mahaifin nasu dake binsa da kallo idanunsa taf da hawaye. Dariya yayi cike da rashin Imani ya ce, "Ohhh I'm so sorry daada an taba na gaban goshi ko? Whl karka ga laifin mu shi yake shiga gaban mu. Amma kasan wani Abu Dada na ɗauka ma alqawarin tozarta Amjad a gaban idonka da idon duniya sai ya wulakantu irin ƙasƙantacciyar wulakantar da Kare ma bazai shinshina ba, sai mu gani ko soyayyar da kake masa zata iya ceton sa"...........Ya ƙarashe da sautin dake bayyana tsananin wutar gabar dake zuciyar sa sannan ya juya ya fice a fusace.
_____________shigowa masaukin nasa yayi wanda baisan wa ya kama ba ma daga airport kawai aka bashi Address card da key ko fuskar wanda ya bashi bai gani ba. Zubewa yayi kan gadon Yana sauke numfashi dawowar sa kenan daga yawon zaga garin da ya fita, sosai yake sake jin son yin aiki tare da Shadow dan daga gani kamar yadda yake hasashe akwai riba a tare dashi, to amma tsarin su fa, ta ya zaiyiwa Wanda bai sani ba aiki, ya daɗe Yana lissafe lissafe kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya janyo system ɗin sa, jadawalin aikin dake gabansa ya shiga tare da dudduba abinda ya kamata, saboda so yake ya koma gida a satin nan dan can ma akwai abubuwan dake gabansa. Saida ya gama duk wasu abubuwa masu mahinmanci sannan ya kashe komai ya wuce bathroom ya watsa ruwa ya fito ya fada gado don gobe da yamma zai bar kasar Denmark .
TO JAMA'A NASAN KUN DASA AYOYIN TAMBAYA A WANNA PAGE ƊIN, TO NIMA DAI HAKAN TAKE A WURI NA ALQALAMI NA NE KAWAI ZAI BAYYANA MANA AMSOSHIN MU.
-------------------------√
Tun bayan lokacin da ya kira ya shaida Mata kuɗi ya shiga bai ƙara kira ba saida akayi sallar la'asar sannan kiransa ya shigo wayarta, tsame hannunta tayi daga cikin ruwan da suke ƙarasa wanke kayayyakinsu tare da karɓar wayar da Shazeen ta kawo Mata, amsawa tayi inda ta tsinkayo Muryar sa na faɗin, " Hello".
"Hello Baba ilerika ya ake ciki?"............." yauwa hajiya gashi na ɗauko motar ɗaukan kayan ki turomin addreshin gidan".
"kaga ba fa wani wuri bane da nisa titin da muka haɗu dazu, wannan dai layin da ya shiga ciki, kuna shigowa ma Ka kirani zan fito saboda ba lalle motar ta iya ƙarasowa ƙofar gida ba".
"To tou shikenan"............Ya faɗa tare da kashewa, Shazeen ta miqawa wayar, "Ungo riqe in ya Kira ki faɗamin bari na fito da kayan, Kai kuma Sahnish kayi Ka haɗa ƙwanukan nan gasunan zuwa da motar ɗaukan kayan"...........Ta ƙarashe tana wucewa ɗaki ta fara fito da kayansu kasancewar ba wasu kayan kirki bane yasa kafin su ƙaraso duk ta firfito dasu suna shigowa bakin layin ya kirata, dankwalin Shazen dake kan igiya ta zara ta rufa a kanta sannan ta zira slippers ɗinta ta fita.
Na gaya muku wani abu? Hushaima sam bata damu da ta wani suturta jiki ba a cikin unguwa Saisa yawanci yan unguwar suke mata kallon karuwa yar iska, ita kawai duk abinda zuciyarta ya raya mata to fa bata tsayawa wani tunani kai tsaye takeyin sa ba ruwanta da kowa kawai rayuwarta take kamar ita kaɗaice a cikin duniyar, tana kuma sane da kallon da yan unguwar suke mata, amma sam hakan bai dameta ba, ba kuma ta damu da gyara tunanin kowa ba tunda har ita ta san kanta. WANNAN KENAN.
A nan farkon layin ta hango su hakan yasa ta Ƙarasa tana faɗin, "Anan kuka tsaya ashe, dama na faɗama ai, motar baza ta samu shiga ciki ba, saidai muje dasu su kwaso kayan ".
"Layin naku ne sai hakuri amma ba damuwa, Kai sauko muje a ɗauko kayan"........ Ya fada Yana wucewa gaba, suna zuwa ta shige gidan, ganin sun tsaya ya sata faɗin, " Ku shigo Ku fita dasu mana ".
"Kuje Ku kwaso, Bari na jiraku anan"............Ya Ƙarashe Yana matsawa jikin wani kango dake opposite da gidan ya kunna lalitar sa yana ja Yana kallon su suna kwaso kayan har suka gama sannan ya kashe ya koma ƙofar gidan inda Hushaima ta fito. "Zaku tafi da Sahnish sai yaga gidan, nawa ne kuɗin motar?".
"5k ne, nama ɗauka tare zamu tafi ai gabaɗaya".
"Ah ah karka damu zamu shirya sai mu taho anjima in sha ALLAH, ga wanna 4k ne anjima zan baka ɗayar in kana dashi Ka ranta min ".
"Ba damuwa hajiya sai kun karaso, muje ko?"...........ya faɗa Yana kallon Sahnish da ya fito Yana dandabe ruwan dake hannunsa a bayan wandon sa. "Bari muje ".......... Sahnish ɗin ya faɗa yana wucewa.
"Tom sai kun dawo"..........Faɗar Hushaima tana me gyara tsayuwa, daga nan bakin Ƙofar take hango su har saida suka shiga motar suka tafi sannan ta koma ciki .
Lokacin da Sahnish ya dawo zaune ya samesu sun gama shiryawa, gefen su ya zauna yana faɗin, " Wai ALLAH gamu gare ka".
"Menene kuma?"..........ta tambaya tun kafin ya kai ga zaman.
Ɗan tsayawa yayi tare da kallonta sannan ya gyara zaman sa yana girgiza kai ya ce, " To ai kya bari na zauna Azagwai. Wai ni dama Hushaima mutumin nan bai kaiki kinga gidan ba kika zuba masa kudi har wurin 70k".
Juyowa tayi gabaɗaya gareshi tare da ragewa manyan idanuwan ta girma ta ce. "Me ya faru? karka cemin tarihi ya maimaita kansa?".
Murmushi yayi me kama dana ƙarfin hali ya ce, "Amma kinyi kuskure babba d........."
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______20
Murmushi yayi me kama dana ƙarfin hali ya ce, "Amma kinyi kuskure babba da baki fara zuwa kinga gidan ba, dan whl zancen da nake Miki ni dai bazan iya cewa dake komai ba saidai kin gani da idonki kawai ".
"Kai dallah Ka min bayani Yadda zan gane mana Ka dinga wani shige da fice".
"Ayya kwantar da hankalin ki, gida dai akwai shi, ɗakuna ma akwaisu amma sauran labarin sai idanun ki sun gane Miki"...........Tsaki taja ta tashi ta bar wurin saboda takaicin sa.
Saida sukayi sallar magriba sannan suka fito, kulle gidan sukayi suka taka zuwa titi suka tsare abun hawa suka hau. Saida suka tsaya gidan Malam ado dan bashi ɗan makullin. A fusace ya karɓi makullin yana binta da harara har ta koma tuk tuk ɗin suka wuce. Kwa na ce kawai ta raba gidan Malam Ado da gidan baba ilerika, tun daga farkon layin Hushaima take bin irin mutanan dake wurin da kallo, layin babba ne dan yana da faɗo, ba takura kuma, ba wuta amma hakan bai hana mutanen unguwar harkar gabansu ba, wasu da fitilar wayarsu wasu da touchlight hakan ya rage ƙarfin duhun dake unguwar, mutane ne ta ko ina kamar yanzu gari ya waye amma fa kallo ɗaya zaka musu saidai kace ALLAH ya shirya kawai.
A ƙofar wani gida Sahnish ya umarci Mai tuk tuk ɗin da ya tsaya, shi ya fara sauka sannan ya ce, "ku fito mun iso".........saukowa sukayi sannan suka sallami me tuktuk ɗi , dakalin kofar gidan tabi da kallo inda a can ƙarshe wasu yam Mata suke zaune suna buga whot babu mai ko dankwali a cikin su. "Har kun iso kenan ?"........ Maganar Baba ilerika da basu lura dashi ba ta dawo dasu daga duniyar kalle kallen da suka tafi.
"ALLAH yayi mun karaso baba!"...........Hushaima ta faɗa. "To bismillah Ku shigo mana".......... Ya faɗi yana wucewa gaba.
A baya suka bishi soro suka fara ratsawa, ɗakuna ne birjik a ciki yayinda wasu matasan samari ke zazzaune kana ganin su kaga yan zauna gari banza, da ƙafa Baba ilerika ya shuri ƙafarsu ya wuce yana faɗin, "Ana nan ana ƙarawa suminti dumi ko. Gafaran Ku dai"..........ya ƙarashe Yana doka kyauren da ya raba soron da cikin gidan.
Ina bama wanda yaji dan wata danbarwa suka tarar a cikin gidan anayi, wasu dattawa ne suke faɗa, ɗayan a ɗan karkace yake alamun yana da lalurar shanyewar ɓarin jiki, ɗayan kuma lpy Lau yake shi ke ma riqe da kwalar rigar marar lpy yana faɗin, "Whl kayi wasa ina iya cillaka cikin rijiyar nan, kana fama da ƙafa ɗaya hannu ɗaya zaka addabi mutane da bala'i a cikin gida".
Dunƙule hannunsa me lpy yayi yana wani zabura shi ala zai kai duka gashi sai haki yake yana faɗin, "Jefani kaga whl saidai mu nitse tare, ni zakawa iskanci da buraubanci Adamu".
"Kai Kai ni kake zagi"............Kaca kaca kokawa ta ɓalle, dawo da kallon ta tayi Kan mutanan da suke tsakar gidan wasu suna ƙofar ɗakunan su wasu kuma sunyi shimfida ƙarƙashin manyan bishiyun mangwaro dake tsakar gidan. Gyaran murya Baba ilerika yayi tare da ƙarawa muryarsa ƙaudi, ya shiga faɗin, "Tohh ya ahlul fituntunu ina muku sallama tare da yawun bakin sabbin baƙin da mukayi, wanda dazu kukaga an shigo da kayan su, to yanzu sun samu ƙarasowa, Kar naji Kar na gani kun dai san Halina yauwa. hajiya bismillah"......... Ya ƙarashe Yana nunawa Hushaima hanya, har ƙofar ɗakunan ya kaisu.
Hushaima ta leqa ɗakunan nasu dake maqota da juna sannan ta ɗauki na farkon me haɗe da toilet itada Shazeen. Daga nan sukayi sallama da Baba ilerika ya juya ya fita su kuma suka shiga Kimtsa dakunan.
Saida ta kimtsa ko ina ta musu shimfida sannan ta bar Shazeen data fara bacci ta fita tare da jawo Mata ƙofar ta rufo, kamar yadda suka shiga haka ta fito ta samesu saidai yanzu ba faɗa ake ba kawai suna zazzaune ne suna hira, gidan gabaɗaya ƙaurin hayaqin kayan bushe bushe yake, ga wasu mutanan da bata gansu bama a lokacin shigowar su, yanzu taga sun ƙaru hakan ya tabbatar Mata da cewa lalle sun shigo gidan yawa, kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta ta wuce ɗakin Sahnish, Yana zaune Yana linke kayan sa ta shigo, ɗagowa yayi da faɗin, "Yanzu nake son zuwa wurinku ma".
"Maganin sauro zaka tashi Ka siyo mana".......... Ta faɗa tana zama gefen katifar tasa da ko zani bata dashi, marabar ta da suminti kaɗan ne.
"Ku shiga net mana ko baki ɗaura ba".
"Kana mantawa da cewa Shazeen bata zama cikin net ko".
"Oh na manta whl, Amma yanzu dare fa yayi kuma ni bansan kan unguwar nan ba ki Kira tsohon can mana ".
"Kai dai kawai kace kaga Yan daba sun firgitaka baza ka iya fita ba kawai".
Yar dariya yayi kana ya ce, "Su ɗin ai abun tsoro ne kuma duk me hankali dole yayi gudu da ransa, mutanen da gabaɗaya kansu a juye yake, hanyar lafiya ai a bita da shekara".
"Yanzu dai a takaice baza Ka fita ɗin ba".
Dan susa kansa yayi da faɗin, "Ni fa nama gaji bacci nakeji whl ".
"To yama kyau saida safe".......... Ta faɗa tana miqewa ta fice, bin bayanta yayi da kallo kawai Yana mamakin yadda ALLAH ya bawa Hushaima taurin zuciya da rashin tsoro wanda yayi imani ko a cikin mazan ba kowa ke da irin jarumtar ta ba.
Tana fita bata tsaya ko ina ba sai ƙofar gida nan ta tarar da wata sabuwar tashar da aka kafa a ƙofar gidan, gefe guda motocin masu kuɗi ne sunyi layi yan mata sai kai kawo suke, gefe guda kuma kungi kungi ne kowa da clique ɗinsa ga wani kida dake tashi irin na yan tasha, yadda kasan kasuwa akeci. Ƙare musu kallo tayi can idonta ya sauka kan wani container tare da hango wannan marar lpyr da ɗazu suka tarar ana faɗa dashi zaune a ciki, da alama container tasa ce . Sauka tayi daga kan dakalin ƙofar gidan ta tsallaka wurinsa. "Salamu alaika".
Kallon sama da ƙasa yai mata ba tare da ya amsa sallamar ba ya ce, " Wacce zaa baki excel ko bensin ko rotmans".......... Hararar ƙasan ido ta aika masa tare da tabe baki ta ce, "Burkutu nake so kana da ita?".
Dariya yayi, "Ashe hajiyar babban Kai ce babu saidai ki Ƙara gaba".
"Kaga Malam maganin sauro na igiya zaka bani in da akwai".......... Tashi yayi Yana jan ƙafa ya ɗauko yana faɗin, "Akwai mana " .
Karɓa tayi tare da ɗauko naira ɗari ta miqa masa ta juya zata tafi ya tsaida ita. "Tsaya mana ga canjin ki".
"Barshi kawai "........... Ta faɗa tana ƙarasa barin wurin zuciyar ta cike da mamakin wanna bawan da ƙafa ɗaya a duniya ɗaya a lahira Amma maimakon ya koma ga ALLAH ya nemi lahirar sa, ya ƙare a saida sigari da goro.
------------------------√
Wani tsararren falo ne da ya gaji da haɗuwa, bashi da girma sosai haka zalika babu wasu tarkace da yawa a cikin sa. Wata kyakyawar matashiyar budurwa na hango zaune riqe da waya ta kurawa hoton wani kyakyawan saurayi ido, kyakyawa ce ajin ƙarshe in nace kyakyawa ina nufin pure beauty,