BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   45 / 53

132K to 135K   out of 156.9K words

ya sake jan tsaki ya ce, " Yan wahala kawai"............ " Su wa?". Juyowa yayi wurin Omaine da ya ƙaraso ya nemi wuri kusa dashi ya zauna, "Ina zasu ne?"......... Ya tambaya yana dawo da kallon sa gabaɗaya kan omaine.

"Ina tunanin zasu tafi maida takardar raddi ne wa Aurellon"..........."Dama sun aiko da wata takardar kenan?".

"Sun Kara aiko wata ne?".......... Shi ma omaine ɗin ya maida masa tambayar yana kallon sa, ɗauke kansa yayi da faɗin, "Ita kuwa waccan matar dake rawar jiki ko da yaushe tana kan gaba wurin assasa wuta wata rana sai ta faɗo ta karye, munafukai kawai, wata cocumber da ita kamar wadda aka dire"......... Dariya sosai Omaine ya shiga yi shi kuwa Haisha'an ko murmushi baiyi ba kamar ma bashi yayi maganar ba sai arrow ɗin da ya zaro ya shiga zane zane akan dutsen kamar me haɗa wani abu. "Amma whl Haisha'an baka da kirki, yanzu me matar can tayi ita fa kawai yar aike ce".

Ba tare da ya daina abinda yake ba ya ce, "Ai ban ma fara rashin kirki ba whl, yanzu ba mai Ƙara kulle ni dama can ba wai ikon ta ko ƙarfin mulkin ta bane yasa take sawa a rufeni, dan da na ga dama ko hour ashirin da huɗu ba zanyi ba zan fito, to yanzu ba zan ƙara komawa ba na fito kenan, amma ɗaya bayan ɗaya zanci uban duk wanda ya sake ya shiga harkata, itama wanna me zubin shansherar tara ta nake, duk lokacin da ta kai ni bango sai na shayar da su ruwan mamaki ".

"Kaga Haisha'an Ina rabaka da li'iliti Azal, kasan yadda kaji sunan ta Azal to whl idan kuka haɗa hanya, Azal zata zame Maka a rayuwa. Ni dai kawai kayi hakuri Ka ɗauke idonka daga kan lamuran masarautar nan".

"Inah bata neme ni ba ko?". Ya tambaya, sunkuyar da Kai Omaine yayi saboda baisan abinda zai faɗa masa ba game da tambayar da ya masa na cewa ko mahaifiyar sa ta neme shi.

"Shikenan ba sai kamin ƙarya ba Omaine na samu amsa ta, bakomai tashi muje ni in ganta".

Kamar omaine zai ce Kar yaje sai Kuma yayi shuru saboda yasan ko sunje ma wulakanta su zatayi taita faɗar maganganu marassa daɗi akan Haisha'an ɗin kamar ba ita ta haifeshi ba, Amma ba yadda zaiyi bai isa ya nunawa Haisha'an ɗin baya san zuwa wurin mahaifiyar tasa ba dan yasan hakan zai iya sawa su samu matsala a abotar su. Dan Haisha'an duk da mahaifiyar sa bata son sa shi yana son ta, duk da ta tsaneshi shi yana kaunar ta, duk da ta wofanta da rayuwar sa shi Kuma tana zuciyar sa, akanta zai iya samun matsala da kowa.




-----------------------√




Sahnish na nan tsaye shi da Shazeen har baba Ilerika ya iso. "Suna Ina?". Ya tambaya. "Suna ciki"......... Sahnish ɗin ya amsa masa, kallon cikin police station ɗin yayi kafin ya ce, " Akwai yan kuɗaɗe a wurin ka ne?"......... Da sauri ya laluma aljihun sa gabaɗaya kuɗin kasuwancin na sa ya ɗauko dubu sha biyar ne ya miqa masa, karɓa yayi sannan ya ce, "Biyoni muje"........ sai da ya tsaya ya zuge biyar ya canza musu aljihu ba tare dasu Sahnish ɗin sun lura ba sannan ya shige. " Salamu alaikum"....... Baba ilerika ya faɗa lokacin da ya shiga.

"Wa alaikum Salam"......... Suka amsa suna binsu da kallo idonsu na sauka kan Sahnish suka haɗe rai, Constable Junaid ya ce, "Kai wai ba munce Kaje bane sai gobe ".

Baba ilerika ne ya amshe da faɗin, "Ai tare muke officer, dashi da Wadda kuka tsare ɗin ai duk ya'ya na ne, a taimaka mana mu ganta Dan ALLAH officer, ya min bayanin komai Kuma in Sha ALLAH da safen zamu zo muga DPO amma yanzun muna so mu ganta"............"Ka ga baba na riga na faɗa masa ba zai yiwu ku ganta ba sai an sanar da DPO".

"Shikenan ba damuwa, amma officer Ina son ganin ka ya za'ayi ne ?".......... Kallon abokan aikin nasa yayi kafin ya ce, " Muje daga waje"..........ya ƙarashe yana fitowa daga bayan kantar suka fita waje tare da baba ilerika, kuɗin ya zaro daga aljihunsa a dunƙule, yana faɗin, " Ranka ya daɗe ga wannan ka sa kati, ɗan minti biyar ma yayi yawa"........ Ɗan basarwa yayi da faɗin, "Ahh ahh ka barshi kawai, muje tunda minti biyar kace".

"A'a baza ayi haka ba Ranka ya daɗe ka karɓa ɗin dai ba yawa".......... Ya faɗa Yana zura masa a aljihu, washe baki yayi kana ya ce, " Ai baba shi yaron naka ne duk bai yi wanna bayanin ba, yazo ya dage sai ya ganta mu Kuma kasan dole mu bi dokar DPO ".

"Karka damu officer kasan Yara, abinda yasa ma aka samu matsala bai Kirani bane da wuri"........Ya faɗa Yana bin bayan Constable suka wuce ciki, jan rigar Sahnish yayi da faɗin, " Muje "....... Binsa sukayi inda ya nuna musu wani table da faɗin su zauna bari ya fito da ita.

Hushaima kuwa tana tsaye cikin cell ɗin banda sauro ba abinda ke garzar ta ga wurin gabaɗaya daga ta zauna sai kuɗin cizo ya fara gallara mata gashi ba ruwa ba abinci, Amma tsabar zuciya ko yunwar bata ji kawai tunanin ta yadda zata rama wanna cin mutuncin da yarinyar ta mata, ko tunanin tana raye ko ta mutu batayi ba. Kai jamaa ni kaina zuciyar Hushaima ta fara bani tsoro fa, maganar Constable ta ji Yana faɗin, "Ke fito ga Yan uwanki sunzo ganin ki, minti biyar kuke dashi"......... Batace komai ba ta fito ya wuce gaba tabi bayansa, da gudu Shazeen ta nufi wurin ta tare da rungume ƙafafunta tana faɗin, "Aunty Hushaima Ina kika tafi kika barmu yau mun Sha wahalar neman ki ni da yaya"......... Murmushin yaqe tayi tana riqo hannun Shazeen ɗin tare da kallon Sahnish da ya karaso wajen su. " Hushaima ya akayi hakan ta faru?"......... ɗauke kanta tayi tana kallon wani wuri kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta shiga bashi labarin abinda ya faru a taƙaice, kafin ta dawo da kallonta kansa. "Whl summa tallahi na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai Sahnish yarinyar nan sai tayi nadamar rayuwarta, tunda ta sake ta ƙetara iyaka ta sai tasan ni daban nake da sauran mutane, sai na rama ramuwa mafi muni, sai na sata kukan da sai hawayen ta ya qafe"........... Ta yi Maganar cikin qunar zuciya. Da wani irin yanayi Sahnish yake kallon ta shi ya san wacece Hushaima bata rantse bama aka ɓata mata saita rama ballantana wannan da tayi rantsuwa me girma haka, sai kawai ya rasa abun cewa sai kallon ta da yake kamar wata hoto, Baba ilerika da yazo wurin ne ya ce, "kiyi hakuri Hushaima".

Wani one side smiling tayi tare da juyawa wurin Baba ilerika ta ce, "Baka san abinda aka min bane baba ilerika, amma bakomai ina ɗan sandan nan, Sahnish kaje ya baka jakata ka ɗau makullin ɗaki na saboda Shazeen ko zata ɗauki kayanta saboda na makaranta....... kaga wani abu zai shiga kunnen Ka"........Ta ƙarashe tana ɗan matsawa ta kama kunnen kamar zata cire masa wani abu a hankali ta ce, "Akwai kuɗi a jakar ku ɗauka ko zaku buqaci wani abu"........ Kwata kwata Baba ilerika bai ankare magana Hushaima ta wa Sahnish ɗin ba .

Constable ne ya zo yana faɗin, "Lokaci fa yayi"........." Eh ai yanzu zasu wuce"........ Hushaima ta faɗa tana gyarawa Shazeen hijab ɗin ta ta kalli Sahnish da faɗin, "Ka kula da kanka kuma ka kula da Shazeen".

"Hushaima yanzu anan zamu barki a gaskiya bazan iya tafiya ba saidai a haɗamu a cell ɗin duka".......... Sahnish Ya faɗa Muryar sa na karyewa. A dake ta ce, "Kai kallo nan karka sake kace zaka min kuka, namiji kake ko baka sani ba ne, ka nuna min haka ta hanyar ƙoƙari na fita anan wurin, dan shi ne kaɗai ƙaunar da zaka nuna min ba wai ka tsaya zaka min kuka ba".

"Wai tun yaushe kike nan Hushaima?".......Baba ilerika ya tambaya. "Tun wuraren 12pm ne"........ Ta bashi amsa sharply. "Kaii abu baiyi daɗi ba sam, yanzu tun wannan lokacin kike nan ba ruwa ba abinci".

"Zanje na siyo mata wani abu yanzu".......... Sahnish ya faɗa tare da duban Constable ya ce, " tace ka bani jakarta in ɗauki dan makulli a ciki ".

"To Shazeen ga yaya duk abinda kike so ki fada masa ni yau bazan kwana tare da ku ba kinji".........."Ni gaskiya bazan bi yaya ba aunty Hushaima kizo mu tafi tare dake"........ Ta ƙarashe tana jan hannun Hushaiman alamar tazo su tafi.

"Wuce wuce muje"......... Constable ya faɗa yana tisa ƙeyarta, bata ƙara cewa komai ba sai kallon Sahnish da tayi sannan ta juya ta wuce .



*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1



PAGE _______ 60 & 61



Ɗauke kai Sahnish yayi yana hana raunin zuciyar sa bayyana saboda maganganun Hushaima. Suna tafiya da Constable zai maidata cell ta ce , "Akwai kuɗi a jaka ta ka ja qanin nawa gefe ka bashi su duka kace ya baka wani abu a ciki".......... Take constable ya sake fuska harda faɗin, "Ba matsala in da akwai abinda kike buqata ma ki faɗa sai a kawo".......... Bata ce dashi komai ba ta yi shigewar ta. Komawa yayi wurin su tare da kiran Sahnish ɗin wani office, binsa yayi suka shiga ya ɗauko jakar tare da sa hannu ya ɗauko kuɗaɗen kusan dubu dari uku ya bashi tare da ɗan makullin sannan ya ce, "Tace ka bani wani abu a ciki"......... Ba musu Sahnish ya zaro dubu talatin ya bashi, hararar Sahnish ɗin yayi kafin ya ce, "To jeka dama shi ne abinda tace a baka ai"........ Saka kuɗin Sahnish yayi a aljihu sannan ya juya ya fita wurin su baba ilerika tare da faɗin suzo su tafi. Sai da suka fito ya ce, "Baba mun gode sosai da kulawar ka ALLAH ya saka da alheri".

"Bakomai Sahnish yanzu ina zaka ne?"......... Faɗar Baba ilerika a daidai lokacin da suka fito daga station ɗin, tirjewa Shazeen tayi tare da fasa kuka tana nuna ƙofar station ɗin da hannunta. Sahnish da shi ma yake jin kamar ya fashe da kukan ya daure ya ce, "Shazeen yanzu zamu dawo mu tafi da ita ai, ki daina kukan kizo mu tafi "........."Ni yaya ka barni anan wurin aunty Hushaima kaje ka dawo"........."Ah ah Shazeen nan wajen akwai karnuka masu cizo, kizo dai muje mu dawo"......... Sai dai Firr Shazeen taki tafiya a lalle sai dai a barta a wurin Hushaima ko kuma a fito da ita su tafi.

"Kaga Sahnish kana ƙara ɓata lokaci kuma kaga dare yayi kar ka rasa abinda zaka siyawa Hushaima ɗin, azo kuma ta kwana bataci komai ba ka ɗauki yarinyar nan mu wuce kawai"........ Shawarar baba ilerika Sahnish ya ɗauka ya sunkuya ya ɗauki Shazeen tana tirjewa tana ihu suka wuce. "Baba a ina kake tunanin zamu samu abinda za'a siyawa Hushaiman ".

"Ai Sahnish inaga yanzu saidai ka siya mata abun kanti kawai dan whl yanzu baza ka samu kowa ba sha biyu fa saura".........."To me za'a siya mata a kantin?".

"Ka siya mata ko kifin gwangwani da biredi ma "..........." To". Sahnish yace sannan suka cigaba da tafiya har suka samu wani kanti suka siya mata harda ruwa da maganin sauro sannan suka koma suka bawa Constable Junaid ya kai mata.

Abun hawa Baba ilerika ya tsaida musu sannan ya ce, "Sahnish kana da yar dubu uku haka ?".......... Saida ya shiga tuk tuk ɗin ɗauke da Shazeen da ta sha kuka ta gaji harta fara bacci baiwar ALLAH. Ya ce, "Ba gida zaka bane Baba?".

"Ah ah dama Kai na tsarewa abun hawan saboda ga yarinya a hannun ka karka wahala".......... Hannu Sahnish ya saka a aljihu ya zaro dubu biyar ya bashi, karɓa yayi tare da faɗin, "Ah tou madallah godia nake Sahnish, in kun ƙarasa zan kiraka naji kunje lpy".

"To". Sahnish yace sannan ya bawa me tuktuk ɗin umarnin tafiya.

Ko da suka ƙarasa gida ɗakin Hushaima ya buɗe suka shiga ya kwantar da Shazeen sannan ya zauna gefenta dan shi kam kwata kwata ba ma ya jin baccin, tashin hankali yayiwa zuciyar sa qawanya tunani kawai yake yadda za'ayi ya fito da Hushaima, wanna wace irin baqar Rana ce? ko da wasa bai taba zaton akwai ranar da Hushaima zatayi kwanan cell ba, yana cikin wannan yanayi kiran Baba ilerika ya shigo Wayarsa kamar yadda ya faɗa kira yayi yaji sun isa gida lpy sannan ya kashe.

Shi dai Sahnish yadda yaga dare haka yaga rana da safe ya tashi Shazeen ta yi shirin makaranta ya samo mata abinda zata karya dan shi bayajin akwai abinda zai iya sawa cikin sa bayan Hushaima na can kulle bataci komai ba. Yana miqa Shazeen makaranta ya wuce police station ɗin duk da sunce sai 10am DPO zai shigo hakan bai hanashi zuwa da wuri ba, tsayawa yayi ya saya musu kunu da ƙosai sannan ya wuce ciki, samu yayi su Constable na shirin shifting wasu zasu shigo, nan ya sanar da Constable Junaid yana son yaga Hushaima Sannan ya bata abun kari, ba musu Constable ya buqaci ya ɗanɗana duk abinda ya kawo kamar yadda doka ta tanada sannan ya shiga ya kirawo masa ita.

Fitowa tayi idanunta sun ɗan tasa ga alamun rashin bacci a tattare da ita, kwana ɗaya duk tayi wata firi firi da ita kamar kazar mayu Amma Kuma kallo ɗaya zaka mata kasan bata karaya ba Kuma babu nadama ko dana sani a zuciyarta sai ma wutar ɗaukan fansa dake sake ruruwa, cikin ƙoƙarin ɓoye damuwa ta ce, "Sahnish Kun kwana lpy?".

"Hmmm da sauki dai, dan ni dai kasa rintsawa nayi kawai tunani na a wani hali kike a wanna wurin".

"Karka damu Sahnish Kai dai kawai kayi min ƙoƙari na samu fita daga nan ɗin saboda a fahimta ta yarinyar iyayen ta nada ƙarfi Kuma kasan yanayin ƙasar Nifaz a gurbace take da cin hanci dole zamu fuskanci barazana. Ina Shazeen ta tafi makaranta ko?".

"Ta tafi, ga wanna Abun karyawa ne na taho Miki dashi "........ Kallon sa tayi da faɗin, " kai ma ai baka karya ba"....... ɗan shafa Kai yayi kafin ya ce, " Na karya mana".

Karɓa tayi tana faɗin, "Haba Sahnish na sanka fa dan haka Ka samu wani abu kaci kafin DPO ɗin ya shigo, kaga ba dama bare na zauna anan muci wanna tare".

"Shikenan zan fita in samu wani Abun Amma ba zanyi nisa ba Ina nan ɗin har yazo, ALLAH yasa Abubuwan suzo da sauqi"......... Da haka suka rabu Constable ya maidata cell shi Kuma ya fita Neman abinda zaici.

Ƙarfe goma dai dai DPO ya shigo kamar yadda suka faɗa, yayinda goman tayiwa Baba ilerika a ƙofar police station ɗin. Bayan Sahnish ya gaishe da DPO ɗin ya tashi da niyyar binsa, wani Sargeant ya dakatar dashi da faɗin ya tsaya tukunna sai DPO ya shiga office ya zauna, komawa yayi ya zauna a daidai lokacin kuma baba ilerika ya shigo. Bayan sun gaisa da Yan sandan ya ce, "Sahnish ashe Kai kana nan ma tun ɗazu nake gwada wayar ka bata shiga ai".

"Ba caji ne baba, Ina kwana ".........." Lpy kalau, to ya ake ciki ya shigo ne?"..........Ya ƙarashe Yana zama kan benci gefen Sahnish ɗin. Kafin Sahnish ya bashi amsa Sargeant ɗin nan ya fito tare da fadin suna iya shiga wurin DPOn. Tashi sukayi suka bi bayan sa har office na DPO, gaishe shi suka yi ya nuna musu wurin zama sannan ya bawa Sargeant umarnin tafiya.

"Ranka ya daɗe mune yan uwan Hushaima"........ Baba ilerika ya faɗa. "Okayy kunji abinda ya faru ko?" .

"Munji Ranka ya daɗe Amma muna neman alfarmar a bamu bailing ta yaso duk abinda za'ayi ma sai ayi daga baya"........... Baba ilerika ya sake amsa masa. Girgiza Kai DPO yayi da faɗin, "Baza mu iya baku bailing ta ba a halin yanzu domin batun fa da ake yanzu yarinyar da abinda ya haɗosu tana ICU ne ba'a sa halin da take ciki ba. Kuma ma kamar yadda kuka ji mahaifan wanna yarinya sun buqaci a turaku kotu domin a bi musu hakkin ƴar su".

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Ranka ya daɗe baza mu iya ganin ka ba a sasanta".

"Baba wanna ba batu bane na sasantawa mu aiki muke don Kare hakkin Al'umma, ƴarka me laifi ce domin attempting kisan Kai tayi".

"Ranka ya daɗe whl tsautsayi ne Hushaima ko Dabba baza ta iya kashewa ba bare mutum"......... Faɗin Sahnish cikin matsanan cin tashin hankali.

"Yaro wanna ba magana ta bace ni dama abinda yasa na neme ku saboda mu faɗa

45 / 53