Author : Young Writer Category : Tknovels
da tarzoma a ƙasarsa, inaso past life ɗin mahaifin ka ta zama inspiration ɗin ka".
Girgiza kansa yayi Yana sake Jin wata ƙwarin guiwa na shigar sa sannan ya ce, "in Sha ALLAH Ammie na gode da tunasar wa ".
"To ko Kai fa, Amma dai da gani baka samu breakfast ba, Dan nasan an kwashe komai na ɗauka kafin ka tashi zasu gama lunch ai".
"Ammie Ina so na samowa Bushra nanny saboda kinga Azhar ba zama take ba saboda yanayin aikin ta, Najmah Kuma tayi ƙanƙanta ace an bar ragamar rainon Bushra a hannunta sannan ga makaranta"..........Ya shigo da wata maganar a maimakon Wadda ammie tayi masa. Shi fa haka yake ba komai yake amsa shi ba kuma karku ce akwai Wanda yake zaɓa yakewa haka a'a general ne, dan shi ko magana idan tayi tsawo to baya bi ta kanta haka ko a chat in dai zaka masa VN to fa bazai buɗe ba Amma typing komin yawansa zai karance Maka ne kasa da mintuna bakwai ko biyar, ba fa dan karamin note ba, a'a irin wanda zakaga read more ashirin ko sama .
Shuru Ammie tayi can Kuma ta ce, " A maimakon Nanny me sa baza ka samo mata uwa ba Jawaad ya kamata Ka haƙura ka manta da abinda ya faru a baya, yau tsawon shekaru kusan uku kenan tun yarinyar nan batafi awa ɗaya a duniya ba. Ka haƙura da ita tunda har kaga tsawon lokacin nan bata waiwayeku ba ya kamata ace ko wani irin so kake mata ka haƙura ka aika mata da takardar ta, ka manta da ita ka auro wata da zata maye ma gurbinta ka fara sabuwar rayuwa".
Sai da ya gama sauraran ta sannan ya ce, "Ammie ina so in gaya Miki dama wancan mutumin Amb. mudassir ya mun magana kan Azhar ya kuma ce ita tace ya tuntuɓe ni, ya nemi mu basu rana zasu zo tambaya so nace ya saurareni, ya kike gani?"..........Wani irin kallo take jifan sa dashi kafin ta ce, "Jawaad baza ka taɓa canzawa ba ko? Kai dai duk lokacin da za'ayi gabas Kai yamma zakayi lokacin da za'ayi yamma Kai Kuma gabas zakayi, naji batun Azhar Amma ya Ina ma wata maganar kana kawo min wata".
A hankali ya sauke numfashe tare da faɗin, "Ammie ba wai naqi sakin matar can bane saboda ina fatan wata rana na dawo da ita, a'a haka kuma ba wai naqi aure bane dan wani abu sai dan kar na huce haushi na akan Wadda bataji ba bata gani ba dan har yanzu ban huce daga abinda mahaifiyar Bushra tayi ba"........ Ya faɗa mahaifiyar Bushra ne dan shi ko sunan ta baya son ji, har godewa ALLAH yake da Bushra ta ɗauko komai nasa sai farin ne kawai na mahaifiyar, matar data zaɓi ruɗin duniya sama da ƴar ta, matar da taso zubda gudan jinin ta tun kafin yazo duniya saboda wani buri nata na banza, matar da ta guji ƴarta tun kafin taji duminta bare tasan abinda ta haifa dan shi ya tabbatar in dai ba'a bakin nurses ba mahaifiyar Bushra bata san me ta haifa ba, tunda ko ganin ta batayi ba tace a miqa masa abinda yake nasa saboda ma karta ganta ta shiga ranta. Murmushin takaici yayi saboda abubuwan da ya shiga dawo masa a kwakwalwar sa kamar yanzu Abun ke faruwa.
"Shikenan naji, Kuma nasan komai me wucewa ne wataran Kai da kanka zaka kawo min Wadda kake so, Amma abinda zance ma shi ne ba sai ka kawo wata nanny ba Bushra zata dawo ƙarƙashin kulawata in Sha ALLAH dama kuma ai ba'a hannun Najmah kaɗai take ba, Dan haka karka damu ka tsaida hankalin ka wuri ɗaya kawai your baby is safe"......... Cikin gamsuwa ya gyaɗa mata Kai sannan ya miqe da faɗin, "Zanje nayi sallah"..........."To shikenan sai ka fito, ka fa fito kayi lunch".
"In sha ALLAH ". Ya faɗa yana barin ɗakin.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______59
SWORD OF FIRE KINGDOM🔥
Ƙaton prison ne daga can karshen yankin masarautar, prison ɗin zagaye yake da manya manyan katti ko riga ta kasa sakuwa a jikinsu sai sword da kuma Archery da suka rataya a wuyansu da kafaɗa in banda muzurai ba abinda suke. Ƙofar wani cell aka buɗe, wani kyakyawan matashin saurayi ne ya fito daga ciki, kallo ɗaya zaka masa kasan baya farin cikin fitowar sa daga jail ɗin, ba kuma alamun nadamar abinda ya aikata aka kawo shi wurin a tattare dashi. Honey skin tone ne dashi wanda hakan yasa na fuskanci duk yawanci kalar mutanan masarautar haka suke sai wasunsu da suka kasance dark brown, yana da broad chest, well built body, sharp eyes, pointed noes, sensible ears and strong arms. Ahmad Haisha'an kenan yaro ne matashi da bazai haura 28 - 30 years ba a duniya, shi ɗin ɗane ɗaya tilo ga amintacciyar baiwar Queen Hirut mai suna Muru wadda a duk duniya ba abinda ta tsana sama da Haisha'an, duk da tana mahaifiyar sa ba komai tsakanin su sai kyara da tsangwama. Tun yana ƙarami Queen Hirut tasa aka kashe Mahaifin sa saboda kawai sun gano shi ɗin musulmi ne kuma baya bin Addinin su na bautar rana, ya taso cikin kaɗaici, shi kaɗai yake rayuwar sa sai abokin sa guda ɗaya Omaine, shi ma ɗa ne ga wani bawa a masarautar. Haisha'an ya qullaci abinda akawa mahaifinsa saisa ya tsani Queen Hirut fiye da komai a rayuwarsa sa, sosai yake takun saqa da ita da kuma mulkin nata, baya shakkar ya tsaya gabanta ya faɗa mata magana kowacce iri ce tun bai kai haka ba, wanda hakan yasa rabin rayuwar sa a prison yayi.
Mahaifinsa a ɓoye ya shiga musulunci kuma a ɓoye yake aiwatar da addinin amma shi Haisha'an a bayyane yake aiwatar da addinin dan dama shi tunda ya taso a cikin Musulunci ya taso saboda ko da aka haife shi sai da mahaifin sa ya yi masa Adhan a kunnen sa a ɓoye, haka kuma ko da ya fara wayo yayi ƙoƙarin ganin ya koya masa duk wani abun da ya shafi Musulunci har zuwa lokacin da aka gano aka kashe shi a lokacin ne kuma Haisha'an ya ɗaura ɗamara ya cigaba da neman ilimin Addini sosai kafin ya fito fili ya nunawa mutanen nasu shi ma musulmi ne kamar mahaifinsa nasa, sai dai abun Mamaki Queen Hirut ta kasa sawa a kashe shi kamar yadda akawa mahaifinsa sai dai tasa a kaishi prison a bashi horo sannan ta fakewa mutanen ta da cewa Haisha'an yana da amfani a masarautar ko dan aikin da yake yi tuquru, saboda in ya tashi aiki kamar bai san ciwon kan sa ba, aikin da mutum goma zasuyi zai iya haɗawa a lokaci ɗaya, Amma a baɗini ba hakan bane, ko ma miye zamuji a gaba. WANNAN KENAN.
Bin Custody Officer ɗin yayi zuwa office ɗin su suka bashi kayayyakin sa ya canza ya ɗauki na ɗauka ya juya ya fita ba tare da yace dasu komai ba, a bakin qatuwar Ƙofar gate ɗin prison ɗin ya tarar da Omaine tsaye yana ganin sa ya taho da sauri cikin farin ciki ya rungume shi tare da faɗin, "Alhamdulillah ɗan uwa, ina tayamu murna a wannan karon ma, kasan da naji shiru har na fara tunanin ko na gota lissafi ba yau bane"....... Ya ƙarashe yana ɗagowa tare da bin Haisha'an ɗin da kallo, hannu Haisha'an ya kai kan kafaɗar Omaine ɗin ya ɗan bubbuga sai kuma ya ɗage kansa sama yana bin ko ina da kallo ganin canje canjen da aka sake samu, murya can ƙasan maqoshi ya ce, " Har yanzu matar nan bata mutu ba?"....... Da sauri Omaine ya rufe masa baki tare da riqo hannun sa ya fara ƙoƙarin jansa saidai ko motsi bai yi ba kamar wanda aka sassaqa ganin haka yasa Omaine ɗin faɗin, "Ka taimaka mu bar ƙofar prison ɗin nan Haisha'an, ka rufa mana asiri in dai ba so kake ka sake komawa ba".......... ɗage kafaɗunsa yayi cikin halin ko in kula ya ce, "Can yafi daɗi ai Omaine, saboda ƴancin da zaka samu a can babu shi anan".
Matsowa yayi kusa dashi tare da yin ƙasa da murya kamar me raɗa ya ce, "Dan ALLAH ka bar wannan zancen Haisha'an, ba ta yadda mutum zai ji dadi ya kuma samu nutsuwa yana garkame"..........Ta gefen ido ya kalli Omaine ɗin da duka dukansa a iya kafaɗar Haisha'an ɗin ya tsaya. "Kai yanzu da kake saken wani daɗi kakeji? Wace nutsuwa kake da ita? a yau ƙaramin kuskure kana iya yi ko iyayen ka ko wani mafi soyuwa a gareka ba ɓata lokaci ya baqunci lahira, Matar da babu imani a ranta, matar da ta maida ran mutum kamar ran kaza bayan ALLAH shi ne kaɗai me rayawa kuma shi ne me kashewa, amma kuma su suce su ne masu kashewa a lokacin da suke so? Ni da kai maza ne kuma mun san girman da ALLAH ya bamu, ya bamu matsayi na masu kulawa da shugabanni (Qawwamai) a kan iyalansu da al'ummarsu tare da jagoranci a gare su, amma ka duba yadda rayuwar mu ta kasance a Matsayin bayin su wanda basu da daraja a idanunsu".
Shi dai Omaine bai bi ta kan zancen ba duk da yasan Haisha'an ɗin yana kan gsky, amma yasan yana amsa masa to fa zai tayi ne har ALLAH ya kawo wanda zai tseguntawa Hirut yanzu azo a samu matsala, gashi shi ko zuwa akayi aka ce mata ya faɗi kaza to indai ya faɗa ɗin a gabanta zai maimaita, dan haka Omaine ya ce, "Yanzu ina muka nufa?".
"Zanje nayi wanka first sai mu zagaya bayan gari"......... "To abinci fa?". Omaine ɗin ya sake tambaya. Kallon gefen ido yayi masa suna cigaba da tafiya, kamar ba zai ce komai ba dan an dau kusan minti uku kafin ya ce, "Ai a wancan gidan sai na fara cin abinci na qoshi sannan a rarrabawa saura, tunda babu shegiyar da zata mulkeni saboda ni ne sarkin su a ciki"...........Ya faɗa cikin halin ko in kula shi kuwa Omaine jan bakin sa yaja ya zuge ganin Haisha'an ɗin kamar ma ƙara ƙeƙashewa zuciyar sa take.
Ɓangaren da ya kasance na ya'yan bayi suka nufa tare da wucewa ɗakin su Omaine ya buɗe suka suka shige. Kan gadon Omaine ya faɗa, shi Kuma Haisha'an ya wuce toilet ɗin bai jima ba ya fito ya bude sip ɗin da kayan sa ke ciki komai yana nan tsaf kamar yadda ya tafi ya barsu, kuma yasan aikin Omaine ne, a gurguje ya shirya saboda lokacin sallar la'asar da ya lura yayi, gaban gadon ya ƙarasa in da Omaine ke kwance ƙafafun sa a ƙasa. "Omaine! Omaine "........ Ya faɗa yana ɗan bugar ƙafar sa, buɗe ido Omaine da ya fara bacci yayi daƙyar tare da faɗin, "Har ka fito ne?".
"Eh, Kaje kayi Alwala lokacin Sallah yayi "........ Nasan zakuce shin Omaine musulmi ne? Eh Omaine ya musulunta dashi da wasu daga cikin mutanan masarautar ta dalilin Haisha'an, sai dai su a ɓoye suke komai.
Tashi Omaine ɗin yayi ya wuce toilet dan zuwa ya ɗauro Alwala, da wani irin kallon me kama da na tausayi Haisha'an ya bishi, dan daga ganin yadda yake baccin ma kasan irin na wanda yasha aikin nan tuquru ya gaji ne, katse tunanin nasa yayi ta hanyar wucewa ya shimfiɗa musu Abun sallar sannan ya tsaya jiran Omaine ɗin ya fito sannan yaja su Sallar bayan sun idar Omaine ya ce, "To ni dai a gaskiya zan wuce naje na karɓa abinci, Dan kasan fa in dai ka sake aka gama rabo baka je ba to fa Saidai ka jira na dare".
Gyada masa kai yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ce, "In ka gama ka same ni a can"........ Da " To". Omaine ya amsa sannan ya tashi ya fita, Shi ma Haisha'an ɗin tashi yayi ya dauka sword ɗinsa da Archery ya rataya sannan ya saka takalmin sa ya fita.
Tun daga nesa ya hango wata jar Ƙura data rufe hanya sai wani ƙara ke tashi daga can iyakar garin, ba tare da wani tsoro ba ya doshi wurin yana matsowa sautin kofatun dawakai na Ƙara ƙarfi a kunnuwan sa har yazo daf da iyakar yankin nasu sannan ya tsaya, suma suna zuwa basu ƙetara ba suka dakata a hankali Ƙurar ya fara raguwa, kallo ɗaya ya musu yasan daga Ina ne, ɗaya daga cikin su ne ya ɗaga abun busar sa zai busa kawai yaga kamar an yi sama da abun busar, da sauri ya ɗago idonsa ya sauka kan Haisha'an ɗin da ya sauke Arrow and bow ɗin sa ƙasa alamar shi ya harbi abun busar ya faɗi, kafin suce komai ya ɗaga murya yadda zasu iyajin sa tare da faɗin, " Sarauniya bata nan tayi tafiya, Dan haka in saqo ne Kuna iya bani domin na isar dashi wurin Crown princess".......... Kallon juna sukayi tare da danyin magana a junan su sannan ɗaya daga cikin su ya matso gaba kaɗan da dokin sa tare da ɗan kwantowa ya miqowa Haisha'an ɗin takardar dake hannun sa, shi ma takowa yayi Amma be ketara ba daga nan ɗin ya miqa hannu ya ƙarɓa shi Kuma mutumin ya juya akalar dokinsa sauran suka rufa masa baya .
Ɗaga takardar yayi ya kalla tambarin eagle dake jiki, rigar sa ya ɗage ta baya ya zira ta sannan ya juyo daidai isowar Azal tana sanye da skinny leather jeans tare da wata armless riga ta fata data kai mata har guiwarta, ƙafarta sanye da boot sai Daenerys's dress data ɗaura akan kayan nata tare da sanya hular rigar da akayiwa bakinta ado da gashin farar wolf. Deanerys dress wata riga ce me kamar alkyabba amma bata da kaurin alkyabba tana da ɗan maballi daga wuya.
Tafiya take cikin gadara da nuna isa gefen ta Siberian tiger ta ce me suna Simba bayan ta Kuma bataliyar yan rakiyar ta ne, a gaban Haisha'an ta tsaya suna kallon cikin idanun juna wanda ba abinda ke fita daga cikin idanun kowannen su sai tsantsar tsana wa junan su, dawo da kallon ta tayi kan hannun sa ɗaya dake riqe da Arrow, Bayan sa ta kalla inda har lokacin akwai sauran ƙurar da bata gama washewa ba, bin wurin tayi da ido kamar me nazari kafin ta dawo da kallon ta kansa da Kai ta nuna masa bayan sa sannan cikin gadara ta ce, " Kai meke faruwa anan?"......... Juyawa yayi ya kalli bayan nasa kana cikin rainin wayo ya ce, " A Ina ?"......... Wani kallon banza ta masa kafin ta ɗaga sword din ta Wanda yake daban dana kowa a kyawu da ƙarfi, Dan daga Sandar Queen Hirut sai sword ɗin ta saboda su komai nasu daban ne dan an riga an gama dafa shi da siddabaru.
A kan wuyan sa ta Ɗaura sword ɗin tana wasa dashi kafin ta nufi fuskar sa, a kan kumatun sa ta tsaya tare da juya fuskar sa tana taku a hankali har ta Juya Haisha'an ya koma yana facing iyakar garin nasu ita kuma tana tsaye gefensa, Kan kafadar sa ta sauke sword ɗin nata kafin ta ce, "Can nake nufi".
"Lion ne da Bengel tigers suka yi rikici "......... Ya faɗa idonsa akan yatsun ƙafar sa da yake motsawa a hankali. Ɗan shuru tayi can Kuma ta janye sword ɗin nata ta juya ta fara tafiya mutanan nata suka rufa mata baya. Bai juyo ba sai da ya tabbatar sun bar wurin sannan shi ma ya waiwayo, right side ɗin sa ya nufa, yayi tafiya me ɗan nisa kafin ya isa kan wani qaton dutse me matuƙar tsayi da faɗi dan kusan shi ya zagaye rabi garin ta bangaren gabas kuma a ƙarƙashin sa ne kurangina yake sassaqaqqen gunkin su Queen Hirut, zama yayi a kan dutsen yana kallon view ɗin masarautar tasu kafin ya sanya hannu a bayansa ya zaro takardar ya buɗe.
Lokacin da ya gama karantawa ɗaga takardar yayi ya rabata gida biyu sannan ya sake rabata huɗu, kuci kuci yayi da ita kafin ya turata bakin sa ya taune, tsaki yaja yana faɗin, "Ku Kuma in kunji shuru ku ɗau matakin da ya muku. ALLAH yasa ma aurellon ɗin ta yiwa garin tashi ɗaya kowa ya huta........" Bai ida rufe bakin sa ba yaga yar Aiken fada ta fito da masu mata rakiya akan giwayen su sunyi hanyar fita daga yankin nasu, da kallo ya bisu kafin