Author : Young Writer Category : Tknovels
furzar kafin ta ce, " Batun yarinyar nan ne da iyayen ta, ɗazu nayi waya dashi ina faɗa masa zancen shiga kotun nan kasan ya tafi KM to shi ne yake ce min wai baza ayi zaman kotu a satin nan ba, ni abun ya ɗaure min Kai".
Dan shuru yayi kafin, "Gsky bani da wani labari game da wanna"............"To da ALLAH inaso Ka sa a min bincike akan hakan".
"Shikenan Anah, in sha ALLAH za'ayi".
"Nagode juraysh ALLAH yayi albarka, Ka gaida min da Aunty batoola".
"Zataji in sha ALLAH".........Daga haka suka yanke wayar. Kallon Adla da suka shigo ita da Esham tayi, ganin su cikin shiri ya sata faɗin, "ina zuwa haka?".
"Zamu Ɗan je shopping ne daga nan zamu biya gidan Durrah tun shekaran jiya take cewa tana son gani na".
"Shikenan kuje karku daɗe Ku Kula, amma wa zai kaiku?".
Dan shuru tayi kafin ta ce, "Ni zan ja mu mana Anah........"
"Kanki yana rawa ko Adla, ki wuce kuje amma su dabee su rakaku".
"To "......... tace sannan suka Mata sallama suka fita.
-----------------------√
Wurin Juma me kanti yaje, shago ne dake gaban layin su kaɗan yawanci ma duk abubuwan da zasu saya a wurin sa suke saye, Dalilin da yasa kuwa ya kai masa shi ne juma yayi karatu har matakin HND dan sau da yawa su kanyi hirar da Sahnish ɗin Saisa ma yanzu baiyi tunanin kowa ba saishi. Ganin da mutane a shagon ya sashi ɗan tsayawa har saida ya gama sallamar kowa sannan ya ce, "Malam juma dan ALLAH so nake Ka taimaka kayi min irin wanna rubutun".
"Tooh Malam Sahnish wani irin rubutu ne da zai gagare Ka ni kuma na iya"..........Dariya kawai Sahnish yayi ya miqa masa, saida ya duba sannan ya ɗago tare da faɗin, "yanzu komai irin wanna za'ayi?".
"Eh kawai kuɗin zaka Ƙara nan dubu ɗari zaka sa "............Shuru Malam juma yayi kafin ya ɗauko biro da takarda ya fara rubutun, miqa masa yayi bayan ya gama . "Kai amma nagode sosai Malam juma ".
"Bakomai Sahnish fatana dai ALLAH yasa ba rigima bane".
"Kai ma kasan bazan saka a rigima ba ai, bari naje, ina sauri ne"............Ya Kai ƙarshe yana sa Kai ya fice daga shagon, gida ya koma inda ya sameta a tsakar gidan tana jiran sa, tana ganin sa ta ce, " Juya muje".
Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya ce , "ina kuma?".
"Okay so kake in barka Ka zauna Ka huta ni kuma ina titi ina neman yadda zanyi ko? tsakanin ni da Kai wa ya kamata yayi wanna abun da nakeyi? amma Kai Ka zama macen ni na zama namijin ko" .............. Yadda ta hayyaƙo take masifa yasa Sahnish ce wa , "ALLAH ya Baki hakuri muje"........ Saboda sanin halin yadda ya ganta a tunzure ɗin nan tana hayaqi kaɗan take jira ta kama da wuta.
Tare suka fita suka kulle gidan, Shi dai binta yake kawai kamar wani yaronta, Sahnish irin mazan nan ne masu sanyi sosai kafin kaga zafin sa a daɗe.
Abun hawa ta tsare musu tare da faɗin inda zai kaita, a ƙofar police station ya sauke su, tana sauka ta ciro kuɗin sa ta bashi ko tsayawa ciniki batayi ba ta wuce ciki .
Da corpor Hambali suka fara haɗuwa cikin wasa da dariya suka gaisa shi dai Sahnish Yana rakuɓe a bayanta kamar wani marayan ɗan tsako, kallon ikon ALLAH kawai yake dan shi ko hanyar police station ɗin ma bai sani ba bare kuma cikinta. "Amm Sergeant Ubayd fa ?"
"Kai anya Sergent Ubayd ya shigo yau kuwa, amma lpy dai ko?".
Gyara tsayuwa tayi da faɗin, "Ai idan aka ga gemun kaza, an ga ranta. Ba lpy ba, wani ne muke haya a gidansa............." Zayyane masa komai tayi ta rufe da fadin, "ya kuma ce duk abinda zanyi nayi kuɗi ya cinye".
"Kai Kai ashsha wanna mutum bai kyauta ba, yanzu ina receipt na shaidar kun bashi kuɗi ko wani shaida na zahiri ma'ana mutum".
"Ga dai takardar da yake bamu nan, kuma ga qani na nan shi ya bashi kuɗin da hannun sa"......... Ta Ƙarashe tana miqa masa.
Karɓa yayi Yana faɗin, "Eh ga takarda Kam, Amma kuma ɗan uwanki bai isa yayi shaidar ki ba, ba wani a wurin lokacin da aka bashi kuɗin, dan wannan ma takarda ce kawai ba receipt ba".......kai tsaye ta ce, "Ita dai wannan takardar ita yake bamu tun asali ma, sannan kuma akwai wani abokin sa ma da suka zo tare a lokacin da zai ƙarɓi kuɗin"............ Ta faɗa without second thought.
"Yanzu dai me kike so ? Saboda akwai hurumin da yake namu akwai kuma Wanda dole saidai rent tribunal".
"Ni kawai ya dawo mana da kuɗin mu, mu kama wani mu basu gidan su tunda su sunce da safe suke son makullin, kuma baza su iya Ƙara notice ba saboda sun daɗe da biya ".
"Shikenan, yanzu kinsan inda zamu samu shi abokin nasa ?".
"Inama da number sa ai sai a kirashi yazo".
"Okay ki kirashi, bismillah ga waje Ku zauna".......... Ya faɗa yana nuna musu bencin dake ciki. Wucewa tayi ta zauna shi dai Sahnish yana daga Bakin Kantar a tsaye . Kira ɗaya tayiwa Baba ilerika ya ɗaga, " Hello".
"Yauwa hello"..........."Ina magana ne da Baba ilerika?" . Ta tambaya domin tabbatarwa.
"Ni ne mana hajiya, harkun yanke shawarar ne?".
"Kazo police station ta gangare Kan batun Malam ado"........... Bai ma Bari ta ƙarasa ba ya ce, " Au to to, ta tashi kenan, to gani nan zuwa yanzu kuwa"............Kashe wayar tayi sannan ta shaida musu Yana zuwa, ba'a dade ba kuwa sai gashi Mai tuk tuk ya sauke shi, shigowa yayi Yana washe baki kamar gonar auduga kaucewa Sahnish yayi ya bashi hanya. "Assalaaaaamu alaikum"............. Ya rangaɗa wata sallama kamar yan kawo amarya sun kawota gidanta.
"Wa alaikum salam"............ Corpor Hambali ya amsa .
"Barkan Ku dai, ya aikin?".........Tasowa Hushaima tayi da faɗin, " yauwa gashi nan ma ya karaso".
"Kai ne abokin Wanda suke haya a gidan sa ?".
"Eh ni ne yallabai amma ALLAH yasa dai ba kuɗin wani ya sake ci ba aka kulle shi, dan ni whl na gaji da zuwa bailin Malam ado a rayuwata gsky ranka ya dade, ku kaishi kotu kawai nifa aminin sa ne ba uwa ko uba muka haɗa ba, ai ni da nasan ma wata rigimar ya tsokano ba zanzo ba".
"Bata gaya ma dalilin kiran naka bane?"..........." Ah ah ranka ya daɗe kawai tace nazo police station ta gangare Kan Maganar malam ado, to Bansan wannan maganar bace ai".
Daga Hushaima, Sahnish harsu corpor kowa da mamakin da yake. Hushaima mamakin ta bai wuce na yadda Baba ilerika ya ƙware wurin iya shirya makirci ba, shi kuma Sahnish mamakin sa na shirin da Baba ilerika da Hushaima sukayi ne domin shi tunanin sa Hushaima ta shiryawa Baba ilerika wanna abun, su kuma Yan sanda mamakin su na Malam ado ne kenan dama an shaide shi ɗan rigima ne kuma ya saba taro rikici tunda gashi har aminin sa yace ya gaji da zuwa bailin sa.
Katseshi Corpor hambali yayi da faɗin, "kanaji duk ba wannan bane "...........Abinda Hushaima ta faɗa masa ya kwashe ya zayyane masa sannan ya karashe da tambayar, "hakane?"
"Kwarai da aniya ranka ya daɗe a gabana suka bashi kuɗi akayi rubutu ya basu takarda ".
"Shikenan yanzu Kai zakazo muje azo dashi ke kuma Hushaima Ku zauna Ku jiramu dasu corpor babba, wanna ai kince qanin ki ne ko?"........."Eh ranka ya dade".
"Kuma kikace shi ya bada kuɗin da hannun sa?" Ya sake tambaya.
"Eh ". ta amsa .
"To zamuje tare dashi mu taho da shi Malam ado ɗin yanzu "............. Ya faɗa Yana wuce wa wani office Jim kaɗan ya fito suka tafi, Shi da Baba ilerika da Sahnish sai kuma wani dan sandan da yake sanye da fararen kaya, ya tukasu a motar police ɗin suka tafi.
Ko da sukaje gidan Malam Ado basu sameshi ba ganin zasu ɓata lokaci suka bar sallahu sun juyo zasu taho Kenan sai gashi, tsayawa yayi ganin motar yan sanda a ƙofar gidan sa, "Officer lpy?".
"Lpy ce ta kawo mu zamu je dakai ofishin mu ne ka ɗan amsa mana wasu tambayoyi".
"Ah ah officer kaga ni ba wani amsar dana sani bare har a tambayeni, meye ma zai haɗani da bayanin da zai kaini har offishin ku".
"Karka damu ba jimawa zakayi ba yanzu zaka dawo".
"Ni Wai m......" Maganar sa ce ta maqale sakamakon idon sa da ya sauka akan Sahnish da baba ilerika. "Au thooo kune, to Kai Kuma a wa?"......... Ya faɗa Yana nuna baba ilerika da hannu.
"Kaga malam ba hayaniya muka zo yi ba, kazo muje kana bata mana lokaci".......... Ƙwafa yaja ya shige suka tisashi a gaba har mota saida ya shiga sannan suma suka akaja suka wuce .
Har suka ƙarasa banda jan kwafa Babu abinda malam ado yake, bayan anyi parking suka firfito suka shige ciki, anan kan bencin dake bayan kantar suka zazzauna Corpor hambali ya koro jawabi sannan ya ida da tambayar, " Haka akayi?"
"Hakane Amma su suka matsa sai na karɓa, na riga na faɗa musu saida gida na zanyi su tashi suka nace kamar da kuɗin ubansu na gina gidan".
"To ai da sai ka bar mana kuɗin mu nemi wani ko, kuma saika karɓe? sannan ai baka ce mana a notis muke zaune ba cewa kayi zaka saida".
"Wancan shi yaga dama ya baku amma ni kuma dole na karɓa kuɗin kwanakin da kuka ƙara, yoo in banda ma cuta irin ta yahudu taya mutum zai saya gida ace sai an bada wani notis ai duk kwanan da mutum zai ƙara karɓi kuɗi kawai. Ku wai baku ma da dangi ne ko daga sama kuka faɗo in ma baku da iyaye......."
Tare shi tayi da faɗin, "Um um malam Ado kaga karkayi kuskuren shiga hurumin da ba naka ba, bar ganin ka haka whl Ina iya fidda hannu na sharara ma mari billahillazi"........... Ta ƙarashe tana miqewa daga zaunen da take.
"Ni zaki mara ? Ranka ya dade Kuna dai ji ".
"Kai zan mara ɗin, kafi ƙarfin a mare kan ne tsohon banza kawai"..........Sahnish ne ya riqo hannunta yayin da corpor ya ce, "Kunga duk ku tsaya sulhu ne ya zaunar damu anan ba wai tashin hankali ba, Kai malam ado yanzu sun ce ka biyasu kuɗin su, su tashi su bawa masu gida gidan su gobe da safe".
"Ai kuwa bani da ko asin da zan iya biya saidai su nemi wani wuri su fake in na haɗa kuɗin na basu, Kuma ma ai sai ayi lissafin kwanakin da sukayi a gidan dan ni ban yarda da wani notis ba yauwa".
Cikin ɗaga murya Hushaima ta ce, "ka ma Isa, ka Isa? whl tlh billahillazi huwar rahmanu baka motsawa ko Ina in baka fito da kuɗin nan ba, kuma Naira biyar bata ciwon kai a ciki tasss zaka dawo dasu yadda aka baka, notis kuma wannan ba da mu zakayi ba, hukumar data Shar'an ta notis ɗin zakaje ka ƙalubalanta ".
"To sai ki ɗauki Babu tunda ana haifo abinda Babu shi".
"Ranka ya daɗe nazo nan ne saboda a ƙwatar mana hakkin mu dan haka ku sashi ya fitomin da kuɗi na dubu ɗari cifff ko Naira ɗari ce bata cika ba whl ba ina zaije".
Wata bahaguwar juyowa malam Ado yayi, "dubu me banji sosai ba, dan sake faɗa?".
"Ka jini Sarai ai, bani Kuma Kara maimaitawa".
"Wa kika bawa dubu ɗarin tukunna, ai ni ainahi ma abinda kike biyan gidan dubu sittin ne".
"Eh Amma wanna shekarar ai da muka samu matsala kace sai an Ƙara ma muka Ƙara ma Kuma yanzu zaka ce baka san zance ba".
Corpor hambali ne ya ce, " A jikin takardar shaidar biyan dubu ɗari ne ga Kuma abokinka da suka bayar a gaɓansa, " Malam nawa ta bashi?"........... Ya ƙarashe yana duban Baba ilerika.
"Dubu ɗari ta bashi sannan ta bani la'adar dubu goma".
"To Kai kaji".
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, dama nasan za'a rina tunda aka dauyko wanna tsohon najadun tsohon ala tsi alatsitsi ala tsine".
"Ka dinga sa minjaye malam ado tsoffin najadu dai, Kai ma ai ba tsohon arzikin bane, wace miyar ce ba'a sha dakai ba".
"Kai Kai ka kiyayeni fa yasin Ina iya sauke ma hakwaran da suka rage ma a duniya".
"Shege ka fasa"........... Baba ilerika ya faɗa yana murmushin mugunta.
Tsawa Corpor ya musu ganin baza su saurara ta lumana ba. "kukace faɗa zaku mana anan Ina iya saka ku a cell na rufe whl. Kai kuma ka biyata kuɗin ta kawai a wuce wurin".
"Nifa Ranka ya daɗe nace ma kuɗin nan bani dasu, a caje ni in karya nayi".
"Ranka ya daɗe nafa riga nayi rantsuwa".......... Hushaima ta faɗa tana wani ƙanƙance firgitattun idanun nan nata sannan ta waro su lokaci guda wanda hakan ya ƙara mata wani sirritaccen kyawu.
"Ai ko aradu kika haɗiya saikin saurara whl t.....".......... Kafin ya Kai zancen da yake son faɗa kawai yaga tayi caraf ta zare wayarsa dake gaban aljihun rigar sa . "Kam bura uba"......... Ya faɗa Yana miqewa .
"Ku saurara mana haba".
"Ranka ya daɗe zamuje wurin saida waya da wani anan wajen, in mun saida zan ɗauki kuɗi na abinda yayi ragowa na bayar a kawo masa"..........ta faɗa saboda tasan ko banza wayar tasa tafi ƙarfin dubu ɗari.
"Ki fa bani waya ta, Ranka ya daɗe Ina akeyin haka?".
"Wanna shi ne abinda zamu iyayi in kana da kuɗin ta ka bata in Kuma babu aje a saida a kawo ma ragowar ".
"Naji ta bani wayata zan biya".
"Au ashe dai ta tabbata cutar daka saba yiwa mutane kake so ka gwada a kansu"............"Ba ruwanka dani ilerika, karka kuskura ka shiga sabgata na gayama"...........Malam Ado ya faɗa a fusace.
"Ya isa haka, Kai ka gama naka kana iya tafiya ma"..........Corpor ya faɗa yana nuna Baba ilerika.
"To ranka ya dade nagode"......... Baba ilerika ya faɗa Yana tashi ya fita.
"Ina kudin yake yanzu?".........."Saidai muje ATM ko wurin me pos a zara amma fa ni dubu sittin na sani".
"Bafa batun dubun sittin malam kuɗin su dubu ɗari ne ga dukkan shaidu sun shaida in Kuma kace dubu sittin ne Kai ka kawo taka shaidar".........Shuru yayi tare da jijjiga kansa yaja Ƙwafa, "Shikenan muje bakomai".
Haka suka fita gabaɗayansu harda Corpor Hambali sukaje ya cira dubu ɗarin ya miqa musu sannan ta bashi wayar sa ya tafi. Dubu goma ta fitar a ciki ta ce, " Ranka ya daɗe ga wanna Kai ma ka Sha ruwa".
Ita kuwa Hushaima ba komai ya sata ƙara dubu arba'in ɗin nan ba akai saidan cin mutuncin da Malam ado ya dinga musu tare da nuna ita ɗin bata isa yin komai ba, da kuma rashin sanar dasu ya sayar da gida da baiyi ba kuma ya karɓi kuɗin su. WANNAN KENAN.
"Ai dama kin barshi, wanna ai aikin mu ne , kuma kina daga cikin wadda hukuma ke alfahri da ita duk abinda zakiyi bakya daukan doka a hannun ki"......... Ya Kai ƙarshe yana tura dubu goman sa a aljihu.
"To Ranka ya dade nagode sosai".........."Zaku wuce ne ko Kuma a rage muku hanya".
"Ah ah karka damu zamu samu abun hawa ".......... Daga haka sukayi sallama sannan suka bar wurin ita da Sahnish, "Sahnish inaga mu wuce ɗauko Shazeen kawai nasan kafin mu ƙarasa Sha biyu tayi, bana son su fara sallah a rufe hanya".
"Duk wanna Abun da ake yanzu ki samu ki saya wani abu kici tun safe ko ruwan shayi baki kurɓa ba fa".
"Kai kake ta wani ruwan shayi Sahnish idan ka ce zaka zauna Kuma zaka nuna sanyin jiki whl wulakanta zakayi a rayuwa, saboda ita rayuwa kamar caca ce babbar riba tana zuwa da babbar kasada ne iya ribarka iya kasadar ka, ko zaka mutu kayi kokarin ganin baka wulakanta ba Ina Ƙara jaddada ma, baka buqatar wani ya tsaya ma domin kare mutuncin kanka. "............ Shi dai Sahnish Bai Ƙara cewa komai ba sai maganganun ta dake Kai kawo a cikin kansa da Kuma tunanin yadda suke rayuwa tsawon lokacin da Hushaima takai tana sacrificing abubuwa da dama saboda shi da Shazeen. Har suka tare tuktuk suka hau tunane tunanen da yake kenan. Basu sallami me tuktuk ɗin ba dan already an tashi su Shazeen ɗin lokacin da suka ƙarasa makarantar dan haka ɗaukota kawai Hushaima ta sauka tayi suka juyo. Sai a lokacin ta ɗauko wayarta ta Kira Ilerika bayan ya ɗaga ta ce, "A ina zamu haɗu ne ALLAH yasa bakayi nisa ba?"..........."Eh yanzu dai na fito zan fita".
"To in ba damuwa ka jiramu kan titin yellow chain".
"To ba matsala hanya ta ce ai"........Daga haka sukayi sallama.
Suna sauka a bakin titin kuwa ta hango shi tsaye Yana busa sigarin sa, "Riqe hannun Shazeen ku wuce gida Sahnish, bari naje na ji yadda za'a yi".
"Ah ah mu dai jiraki anan ɗin Amma ki kula daga ganin mutumin can tsohon Dan duniya ne Kuma kinsan yan bariki basu da amana ".
Wani silent smile tayi da fadin, "Kai ma kayi wanna tunanin Sahnish bare kuma ni".
"To ni din me kika maidani?"............Bata bashi amsa ba ta wuce , ganin ta yasa ya fara ƙoƙarin kashewa ta katseshi, "Karka takura kanka baba ilerika ni bani da matsala ai. Zancen ɗakunan hayar daka faɗamin ne yasa na neme ka"..........Washe baki yayi, "tou tou Ina sauraren ki kuɗin sun samu kenan? yanzu zuwa zamuyi kiga ɗakunan ko Yaya?"........... Ya tambaya a jere.
"Ah ah ba sai naje ba ai nasan baza ka tallata min Abun banza ba, yanzu zaka ban lambar Acc ɗin ka sai a tura ma kuɗin".
"Too Amma da cash ne da sai yafi sauki fa"........"ai bani da cash ɗin ne amma kana bani za'a tura ma yanzu".
"To ba damuwa "...........Ya faɗa soke sigarin tasa a gefen baki ya sanya hannu ya ɗauko wayar tasa ya tura mata. Duba wayarta da tayi ƙara alamar shigowar saqo tayi tare da faɗin, "In an tura zan kiraka in faɗa ma".
"To in kin tura ɗin a ina zamu haɗu na baki makullin".
"Ah ah kaje ka sa a share a wanke, in an gama saika Kira ka fadamin kawai, yanzu ga wanna".......... Ta ƙarashe tana zaro kuɗi daga jakarta ta miqa masa, karɓa yayi tare da karkacewa aka wani ɗage kai sama ana irgawa. "Goma cirr"..........."Ka Sha ruwa da ita".
"Yiii huuuu sai da ni, au ya hakuri na shaafa, godia nake irin albarka, kina turowa za'aje a fara aiki".
"Ba damuwa sai ka jini "............ta