Author : Young Writer Category : Tknovels
faɗa tana juya dan komawa inda su Sahnish ke jiranta. "Me ya faru ?"........... Sahnish ya tambaya tana kallon yanayin fuskarta da ya canza Lokaci guda.
"Bakomai, ungo wanna kaje wurin me pos ka bashi ya turawa mutumin can kuɗin hayarsa ka karbo takardar shaidar turin"............ Ta ƙarashe tana miqa masa kuɗin hayar ɗakunan data ware tun a tuktuk.
"Yanzu maimakon ki bashi kawai ga kuɗin a hannun ki, kuma sai anyi wata wahalar zuwa wurin me pos"..........wani kallo tai masa kafin ta ce, "Kaga irin wayon naka da in anyi magana kake faɗa ko, kawai sai naje na bashi kuɗi bani da wata shaida? ai mu dashi yanzu kar ta san Kar ne ko daga abinda ya faru a police station ma".
"To shi kuma Kuɗin da naga kin bashi fa ?"........."Wanda zai Sha ruwa"..........."Meysa to?".
"Zai mana amfani"........ta faɗa tana maida wayarta jaka bayan ta tura masa Acc number ɗin Baba ilerika taja hannun Shazeen suka wuce shi Kuma ya wuce shagon Juma don zuwa turawa Baba ilerika kuɗin hayar.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______18 & 19
Ƙarfe biyu daidai ya tashi daga gaban system ɗin sa, daga shi sai short nicker, zuge curtain ɗin yayi glass wall din ya Bayyana wanda hakan ya bashi daman ƙarewa ko Ina kallo garin yayi shuru sosai baka jin motsin komai sai ƙaran kukan wolf daga nesa kaɗan kaɗan, maida curtain ɗin yayi ya rufe tare da yin miqa ya koma gaban system ɗin ya kashe, sannan ya wuce gaban wardrobe ɗin ya ɗauko kayan da zaisa, tsabar yauqi irin nasa saida yaja 30 minutes kafin ya gama shiryawa cikin Biker jeans dark brown tare da t shirt dark brown sannan ya ɗaura light brown trench coat, ƙafarsa sanye da Boot shi ma dark brown. wucewa yayi zuwa wurin bedside drawer ya buɗe ya zaro wata ƙaramar bottle kamar ta Syrup, buɗewa yayi tare da ɗage kansa ya kurɓe shi duka sannan ya cilla kwalbar cikin dust Bin, Jim yayi a tsaye na tsawon 4 minutes sannan ya wuce kan gadon ya ɗauki neck gaiter ya sa sannan ya daura fedoras a kansa, bug ya ɗauka ya maqala a kunnuwansa, wani file dake kan mirrorn sa ya wuce ya ɗauka ya sanya cikin trench coat din sannan ya fita ya kullo ƙofar ya sanya key a aljihun sa.
Tafiya yake yana waiwaye wanda hakan yasa kallo ɗaya zaka masa kasan bashi da gaskiya, wata kwana ya yanka wadda tayi daidai da connecting ɗin bug ɗin kunnen nasa, dafe kunnen yayi yana sauraran maganar da ake masa ta ciki, duk kwana da zai shiga in yazo sai a faɗa masa, yana zuwa kan wani layi muryar dake fita ta ciki ta fara rawa, sake dafe kunnen yayi saidai baikai ga jin komai ba ya yi disconnecting gabaɗaya. "Sh**t "........... Ya furta yana datse haƙwaransa tare da jujjuyawa yana bin layin da kallo, shuru yayi na wasu second sai Kuma ya ɗaga Kai ya kalli wani gida duk da a duhu ne amma yana iya hango mutanen dake tsaye suna shanya a balcony ɗin kasancewar ba ƙofa sai stairs kawai shi ma kamar na kasa ce, matakalar ya bi har ya hau wurin su, yana shirin yin magana, ɗayan cikin su ya garo bucket gabansa wanda ya gangara har ƙasan stairs ɗin ta other side, wurin yabi da kallo juyowar da zaiyi ba mutanan, da sauri yabi stairs ɗin yana kalle kalle, haka ya cigaba da tafiya ba tare da yasan inda hanyar zata kaishi ba amma kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar ba wata damuwa a tare dashi saboda tafiya yake cike da nutsuwa kamar ko yaushe.
A gaban wasu mutanen ya bayyana su huɗu ne kan kujera suna shan shisha, ɗaya daga cikin su ne ya taso yana faɗin. " Sai yanzu kake zuwa?".
Saida ya kalla sauran ukun da suke harkar gaban su kafin ya ce, "Duba agogon hannun ka"............"3am ne yanzu".........Ya amsa .
"Shi ne time ɗin da aka bani. Waye wanda zan gani?"........... Ya tambaya yana kare masa kallo cikin dan hasken dake wurin.
Juyawa yayi wurin sauran da faɗin, "Jam ga baqon fa ya ƙaraso".......... Tashi jam yayi yana faɗin, " Ina zuwa".
Shigewa yayi gaba sannan wanda ya fara tarar Amjad yabi bayansa, shi ma Amjad ɗin ya rufa musu baya, gaban wata ƙatuwar ƙofa suka tsaya makulli Jam ya ciro daga aljihun sa tare da buɗe ƙaton ƙwadon dake jikin ƙofar, wani babban falo ne ya bayyana a gabansu tafiya suka cigaba dayi har sai da suka ƙure ƙarshen falon, hannunsa ya ɗaura akai tare da faɗin, "Gamu munzo!"........wata murya ce da basu san daga inda ta fito ba ta ce, "Na ganku ai".
Tiles ɗin dake gabansu ne ya fara buɗewa slowly, wasu stairs zuwa ƙasa ne ya bayyana a gaban su. ( aiki ja, Mamaki ne ya sake kasheni, saboda daga waje in kaga gidan baza ka taɓa tunanin zai dauki wanna Wuraren ba, dan kallo ɗaya zakayi masa kace in akayi wata iska me ƙarfi tsab zatayi gaba da gidan).
Shiga yayi suka bishi a baya suna gama shiga tiles ɗin ya koma ya rufe wani shiryayyen falo ne cike da mata da maza kamar wani ƙaramin club, wani slow music ne ke tashi speakers kawai kakeji suna dukan kiɗa, wasu na rawa, wasu na zaune kujerun dake cikin falon suna hira haɗe da ciye ciye, wasu Kuma suna yan kurɓe kurɓen su, hayaqi ne kawai ke tashi sai ka zata wani abun ake babbakawa.
Dakatar dasu wani mutum yayi, baka ganin komai nasa sai idanunsa kawai Kai kace irin ninja ɗin nan ne. Wanda ya fara tarar Amjad ne ya ce, "Wurin BB LALO"........... baice komai ba ya wuce can ciki wurin wata doguwar kujera wanda wani mutum ke zaune ya ware hannuwansa kan headrest ɗin kujerar, ƙafarsa ɗaya Kan ɗaya, hannun sa riqe da tumbler na wine, gefen sa wata mace ce sanye da yar ƙaramar riga da wando Wanda dasu da babu duk ɗaya, ta ɗaya gefen ya matsa tare da raɗa masa wani abu a kunne, da hannu ya masa alama da yaje ya shigo dasu.
Zuwa yayi ya faɗa musu su ƙaraso sannan ya shige gaba suka bi bayansa zuwa wurin BB LALOn, Sai da ya Ƙare masa kallo sannan ya masa nuni da wurin zama da hannu, tare da duban matar dake gefensa tun kafin ma yayi magana ta miqe tabar wurin, zama Amjad yayi, yayinda BB LALO ya buɗi baki cikin murya irin ta uban daba ya ce, "AMJAD HASHIM DARWIN?"..........gyada masa Kai yayi alamar eh.
Bubbuga dantsen hannunsa yayi sannan ya ce, "buɗe!"......... janye dogon hannun trench coat ɗin tasa yayi bai ƙarasa ba yaji wani irin radaɗi a dantsen hannun nasa kafin ya gama dawowa nutsuwar sa har jam ya zare abun dake hannun sa me kama da syringe, da ido BB LALO yayi masu alamar suna iya tafiya, juyawa yayi ya bar wurin da sauri yayinda shi Kuma mutumin da ya fara taryan Amjad ɗin ya gyara tsayuwa da alama bai gane me BB LALO ya faɗa da ido ba.
Gyara zama BB LALOn yayi da faɗin, "Ina P I file din ka?"........... Zaro file ɗin Amjad yayi a cikin rigarsa ya miqa masa, mutumin nan da ya masu iso ne ya ƙarɓa sannan ya miqa masa, duddubawa yayi sannan ya ɗaga Kai ya kalli mutumin da sauri ya bar wurin, bai fi two minutes ba ya dawo da faɗin, "Gashi sir".......... Da Kai ya masa alamar ya miqawa Amjad ɗin.
Karɓar files ɗin guda biyu Amjad yayi tare da buɗe na farkon, saida ya gama karantawa sannan ya ɗago ya kalleshi da faɗin, "Kai ne shadow din k........."
Bai rufe bakinsa ba yaji harbin bindiga da baisan daga inda ya fito ba, da wani slow move ya Kai kallon sa gefensa inda mutumin nan da ya tarye shi yake tsaya Amma sai ya ganshi zube a kujerar dake gefensa goshin sa na fidda jini alamar shi aka harba, kafin ya gama tantance meke faruwa ya tsinci murya BB LALO in da yake faɗin, "Wannan shi ne hatsarin dake tattare da Shadow, an ma uzuri saboda wanna shi ne zai kasance aikin ka na farko dashi, kuma information da ya samu a kanka yasa ya buqaci yin aiki tare dakai, saboda shi yafi son aiki da wanted criminals irin ka, dan haka Ka kiyaye. Shi ɗin daban yake, inuwa ce da ganin ta sai a haske shi kuma duhu ke lulluɓe dashi, aiki dashi abu ne me matukar hatsari akwai rules a file ɗin dake hannunka, ka karanta sannan kayi signing, Kuma ka sani baka da samar canza ra'ayi tunda har ka zo nan to rayuwa ko mutuwa shine kawai zabin da kake dashi".
Wani shaiɗanin murmushi Amjad yayi Wanda ya sanyashi rikiɗewa ya saje dasu. "Ni da kake gani, zaɓi tsakanin rayuwa da mutuwa bashi bane a gabana, saboda dama ban fito ba saida na shirya tunda kaga har duniya ta shiga rudani a kaina Kuma still ina rayuwana yadda nakeso to ka tabbatar da ni ɗin zaɓi na ba ɗayan biyu bane, zuciyata ta kan kirkiri zaɓi sama da uku, ba buqatar nayi ma dogon bayani dan shi Wanda zanyi wa aiki ya riga da ya san waye ni"..........ya ƙarashe Yana zaro pen a aljihun sa yayi signing.
"Gebriel karɓi Ka haɗa da wannan Ka tabbatar sun isa wurin oga domin sanyasu a record".
Karɓa Gabriel yayi tare da haɗa files ɗin wuri guda. " Ka Kira azo a dauke min gawar nan".......... Faɗin BB LALO Yana sipping wine ɗinsa hankali kwance.
"Okay!"............Gabriel ya Amsa tare da barin wajen.
Gyaran murya yayi yana sake relaxing cikin kujerar ya ce, " A wanna file ɗin dake hannunka akwai paper work na iya adadin mutanen da ake buqata daga wajen ka sannan akwai wani specified person da ake buqata shi ma, akwai sunansa, address da kuma duk wani info ɗin sa a ciki".
"To batun payment fa? Dan ni farashi na per person ne ba wai grouping nake ba".
Girgiza masa kai BB LALO yayi kafin ya ce, "Ba'a tsadance kuɗi dashi dan shi duk wa'anda ke aiki dashi price ɗaya ke garesu, a yanzu za'a baka rabi in aiki ya kammala zaa cika ma."
Ɗan shuru Amjad yayi kafin ya ce, "Inajin kamar ban yadda dakai ba, Anya ba gadar zare aka shiryamin da sunan shadow ba, in ba haka ba ai shi zai ban aiki tsakanin ni da shi ba wai dakai ba" ...........Amjad ya faɗa yanayin sa na ɗan sauyawa haka zalika bugun zuciyar sa Amma a fuska baza ka taɓa iya cewa ga halin da yake ciki ba, Dan masu iya magana nacewa labarin zuciya a tambayi fuska Amma a wurin Amjad ba haka bane duk abunka baza ka iya karantar abinda ke zuciyar sa ba daga yanayin fuskarsa.
Wata irin dariya irin ta basawa BB LALO yayi kafin ya ce, "In dai akan shadow ne kar kayi tunanin ganinsa ko haɗuwa dashi har iya tsawon lokacin da zakayi aiki dashi, shin zaka iya yadda in nace ma tsawon shekaru ashirin Ina aiki tare dashi Amma ban taɓa ganin sa ido da ido ba"........... Ɗan dakatawa yayi tare da ɗaukan kwalbar wine ɗin dake gabansa akan table ɗin da ya raba tsakiyarsu tsakanin sa da Amjad ɗin, sake tuttulawa yayi a tumbler ɗin sannan ya cigaba, "Zaifi kyautuwa idan ka kawar da duk wani tunani dake kwakwalwar ka, ka maida hankali Kan aikin dake gabanka ba wai batun ganin Shadow ko wani abu ba. Akwai deadline na aikinsa yana nan a cikin file ɗin dan haka Ka Kula ka Kuma kiyaye dokar sa".......... Ya Ƙarashe yana ɗaukan wayar sa ya tura wani saqo, wani Ninja ɗin ne yazo sanye yake da kaya irin na Gabriel hannun sa ɗauke da wata babbar suitcase, da ido ya masa alamar ya bashi. A gaban Amjad ya ajje sannan ya juya ya bar wurin.
"Wanna shi ne rabin kuɗin aikin ka, kana iya tafiya".........Bai sake cewa komai ba ya ɗauki suitcase ɗin ya tashi.
Kunsan meysa suka harbe wanna mutumin dukda shi ɗin ya kasance Yana aiki a karkashin su ne, to saboda ya kuskure wurin fahimtar alamar da BB LALO yayi musu da ido, haka suke basu da sani ko sabo, kuskure kaɗan kayi a bakin Ranka.
_____________Shi kuwa Amjad Masaukin sa ya koma, bayan yayi locking ɗakin ya Ƙarasa bakin gadon tare da ɗaura suitcase ɗin akai ya buɗe shi, tozali yayi da bundles na wasu miqaqqun pounds masu uban yawa, dan zai iya cewa daga bank sai cikin suitcase ɗin nan saboda yadda suke wani daukan ido"...........wani light smile ya saki tare da lumshe idanun sa ya buɗe, ɗaukan suitcase ɗin yayi ya adana sannan ya faɗa bathroom.
_____________"Anah wato maganar gsky mutanan nan sun gudu, ni daman tun farko nasan basu da gaskiya shirya musu komai akayi".
"Hasbunallahu wani imal wakil, to Juraysh meysa baza a nemo su ba, in aka barsu sunci banza kenan sun ɓatawa yaro na suna Kuma sun gudu".
"Ai Anah ko mu bamu nemo su ba hukuma zata nemo su, inaga mu bar musu komai kawai dan dole za'a nemo su, in Kuma ba'ayi hakan ba mu sai mu dau mataki".
"Shikenan, amma gsky raina yayi matuƙar ɓaci whl wanna ai rainin wayo ne ma, wai dan ALLAH me mutane suke so da yaron nan ne? Me ya tare musu a rayuwa? Kowa bashi da buri da ya wuce su ɓata shi, ka duba fa sanadiyyar haka Alhaji ya kwanta ba baki ba ƙafa ba hannu wanna wani irin tashin hankali ne".
Cikin jimami Juraysh ya ce, "Anah duk wani Wanda ke nasara a kan komai kamar Amjad dama dole yayi maqiya a boye ai harma da filin, shi ɗin fa guguwa ce da in ya taso dole kowa yayi ƙasa da kansa, ALLAH ne kaɗai yasan iya adadin mutanan da Ƙurar Amjad ta shigarwa ido".
"ALLAH ya fisu, cigaban sa Kuma da basa so in Sha ALLAH saidai zuciyar su ta buga, ni gashi ma tunda ya tafi KM ɗin nan ban cika samunsa a waya ba".
"Kai Anah bafa yau Amjad ya saba tafiye tafiyen nan ba, Kuma kinsan dama duk lokacin da yayi tafiya to ayi sallama da samunsa a waya ".
"Amma Kuma yanzu ai a cikin ƙasa yake Bai kamata ace ana rashin samun sa ba kamar da da yake fita abroad. Me ma yaje yi to shi da yanzu ba wani aiki yakeyi ba, ba gwara ya zauna a gida ba Nima Ina ganin sa hankali na ai sai yafi kwanciya".
"Amma Anah abun zai masa yawa idan akace za'a takurashi sosai, sai ya zama rana zafi inuwa quna, kawai dai mu cigaba da addu'a har ALLAH ya bayyana gsky ".
Sallamar Nuhail ta katse musu zancen nasu, Juraysh ne ya amsa, bayan ya ƙaraso ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan ya zauna yana faɗin, "Anah barka da rana".
"Barka Nuhail ashe ka shigo, ya gida ya yaran?".
"Duk sunan nan lpy, ai ƙawar taki ma saida na mata wayo na fito dan in dai taji nan zanzo an dinga rigima da ita kenan saita biyoni".
"Allah sarki, Kai Kuma baka son kawo su ba".
"Ba haka bane Anah, Ina cewa zan taho da ita su ma sauran zasu ce sai sunzo ni kuwa bazan iya yawo dasu duka ba saisa sai nace su bari sai maman tasu zatazo saisu biyota".
"Allah sarki, ALLAH ya albarkace su gabaɗaya ".
"Ameen ya ALLAH!, ya wurin Amjad kuwa, kwana biyu bana ganin sa kuma bana samun wayar sa, dama akwai wata maganar da zamuyi ne?".
"Eh tou nima gsky ba kasafai nake samunsa ba tunda yayi tafiyar nan".
Ta tabbata dai yayi tafiyar kenan ya faɗa a zuciyar sa, ba tare da yasan zancen zucin da yake ya fito fili ba.
"Naam magana kake ne".........Anah ta tambaya.
Da sauri ya ce, "Ah ah bakomai cewa nayi mu bamu ma san yayi tafiyar ba ina yaje ne?".
"Khor maksar"..........Juraysh ya bashi amsa a daƙile Yana hararar sa ta ƙasan ido.
"Au ashe ma Yana ƙasar ai na ɗauka ko ya samu fita ne dukda har yanzu bamuji abinda ƙasashen suka yanke ba a Kan sa, kuma gashi abun yana son shafar yanayin aikin mu dan a yanzu babu zancen fitar da Kaya daga refinery's ɗin Dada haka kuma kasuwar ƙasashe masu shigowa HD aurum mining yanzu sunja baya, ga batun case ɗin sa da yarinyar nan Kuma naji an fara raɗe raɗin wai an batar da yarinyar da iyayen ta".
Kallon Anah Juraysh yayi kafin ya ce , "kamar ya? an batar dasu ko Kuma sun gudu saboda basu da gaskiya".
"Ei to ni dai abinda naji kenan cewa an batar dasu "..........."A Ina kaji?".
"Zancen duniya ai baya ɓuya malam Juraysh, ni dama abinda yasa nake neman sa mu tattauna kenan saboda wanna Abun qimar gidan mu ce gabaɗaya, batar da yarinyar da iyayen ta bashi bane solution kamata yayi a zauna ayi maslaha".
"Kai cema akayi shi ya ɓatar dasu kenan?"............ Juraysh ya tambaya yana tsare shi da ido.
"Haka mutane suke cewa, Wai saboda gudun tonuwar asirin sa".
"To kai mutane ne? Kai ai ɗan uwansa ne, kai me iya ƙaryata wa ne ma ba wai kazo kana cigaba da yayatawa ba".
"To yanzu wani wuri naje nayi zancen ne? Ina cewa anan wurin daga ni sai Kai sai Anah, waye bare a cikin mu Anah da take mahaifiyar