Author : Young Writer Category : Tknovels
masa yadda zai dogara da kansa ba wai sai da ita ba.
______________ita kuwa Amla tana zuwa asibiti Nashwa ta fito ta mata jagora zuwa ciki, bayan ta gaisa dasu Mumu ta ƙarasa kujerar dake gefen gadon Nayrah ɗin da Mumu ta nuna mata ta zauna, "Sannu dear, ashe haka ya faru".......... Ta faɗa tana kallon Nayrah ɗin cike da tausayawa halin da taganta a ciki.
Cikin ƙarfin hali Nayrah ɗin ta ce, "Haka ALLAH ya qaddaro Amla sai dai muce ALLAH ya kiyaye gaba yasa hakan shi yafi alheri"..........." Alheri kuma? A irin wannan iftila'in?". Amla ta tambaya tana kallonta da mamaki. Murmushi tayi wanda bai kai zuci ba tana ɗauke Kallonta daga kan Amlan.
"ALLAH ya baki lpy ya tsare gaba".........." Ameen ya rabbi". Ta amsa.
"Kinsan da kiran me na Miki Nashwa ta sanar dani wannan abun da ya faru, saurayin ki fa na gano"............" A ina ?". Ta tambaya tana kallonta.
"Daddy ne ya aikeni na kai wa wani saqo, to ashe ni ban sani ba shi ne wanda zan bawa saqon, shi ne fa na kira na miki tsegumi"........ Satar kallon inda su Mumu suke tayi ganin hankalin su baya kansu ya sata faɗin, "Amla Ki rage murya dan ALLAH"........ ɗan kallon tuhuma Amla ta mata kafin ta ce, "Ya dai? Any problem?".
"Bari kawai Amla ke dai ki tayani da addu'a"........... Ta ƙarashe tana gyara kwanciyar ta saboda hankalinta da ya koma kan Amjad ɗin, shiru sukayi can kuma Amla ta ce, "Da tare zamuzo da besty na, to sai su.........." Saurin canza zancen tayi da faɗin, "To qanin ta ba lpy saisa, amma tana miki sannu".
Cikin jin daɗi Nayrah ɗin tayi Murmushi da faɗin, "Ni dai ALLAH ya nuna min ranar da zanga besty ɗin nan da aka hanani zama da zancen ta, gashi hotonta ma rowar sa akemin".
"Ke bari bestyn tawa ce sai ni, kwata ƙwata bata yadda da hoto amma zance mata ke kike so ko kuma duk ranar da naje na haɗaku a video call "...........haka suka cigaba da hira sama sama kafin Amla ta musu sallama ta tafi.
---------------------√
Sai da ya gama duba takardar sannan ya maidata cikin file ɗin ya ɗauka ya fita, main office dinsa ya koma tare da Kiran Nazbeer a waya, ba'a ɗau lokaci ba ya shigo, "Ungo Nazbeer ka maidawa Alhaji zawaad wanna file ɗin nasa sannan ka sanar masa cewa duk abinda su Julaybin sukeyi da sani na tare muke aiwatar da komai, dan haka kar ya wani damu kansa".............. "Okay boss". Nazbeer ya faɗa yana ɗan risinawa ya karɓa file ɗin. Bai ce komai ba ya ɗauki abinda zai buqata ya yi waje inda ya samu su Kamal suna jiran sa, shiga yayi Kamal ya rufe sannan shi ma ya shiga yaja suka fice zuwa Masallaci dan har lokacin sallar juma'a ya kusa.
Bayan an sauko daga masallaci suka nufi wani wuri, a gaban wani tangamemen gida suka tsaya, Horn sukayi me gadi ya buɗe suka shiga anan ya hango Juraysh da Hunaiz sai daddyn su Juraysh ɗin da Kuma uncle ɗinsa ɗaya wato brother Anah tare da wasu manyan mutane su uku. Yana fitowa juraysh ya baro wurin su ya nufoshi yana Murmushi ya miqa masa hannu yana faɗin, " Da ai cewa nayi ba zan zo ba tunda abin haka ne, har zaka nemi Hunaiz ka sashi aiki bayan ga ni"...........Hunnunsu cikin na juna suna musabaha ya ce, "kai fa oga ne, tunani na ko kana da wani aiki me muhimmanci a gabanka ne, nasan Kuma in dai na faɗa ma zaka iya katsewa kace zaka yi nawa aikin, kuma naga ga Hunaiz da ba abinda yake yi".
"To naji Amma ai ko kira kayi ka sanar dani, ba dan Anah ba ai da saidai naji labari"........... Shafa gemun sa yayi kadan da faɗin, "Bari kawai Juraysh kasan yadda abubuwan suke".
"Haka dai kullum baza ka taɓa canzawa ba, yanzu ma gashi saida ka makara, dan har an ɗaura, zuwan da kayi ma ka same mu tafiya zamuyi, dan haka sai munci tarar ka"............Ya ƙarashe cikin sigar zolaya. Smirking yayi da faɗin, "I know yallabai a mun afuwa, muje na gaisa dasu a gurguje, hospital zan wuce wurin amarya ta"........... Dukan wasa Juraysh ya kai masa a baya yana faɗin, "Ummm kaji sabon ango to ai Ka bari ta warware ko"..........."Mtweee kai whl ka fiya wasan banza".
Haka suka jero tare zuwa wurin mutanan, har ƙasa Amjad ya durƙusa ya gaishe su, Juraysh ya ce, "Wannan cousin brother ɗin mu ne".
"Masha ALLAH"............Ɗaya daga cikin mutanan ya faɗa yayinda ɗayan ya ce, "Wait wai wanna ba Amjad bane ?".......... Brothern Anah ne ya ce, "Shi ne mana ".......... Kallon juna sukayi kafin ya sake cewa, "ALLAH sarki, Amjad dama ana ganin ka ido da ido, na dauka sai a BBC dasu CNN?".
Dan murmushi yayi kawai Juraysh yayi saurin faɗin, "Daddy barin rakashi yace zai gaisa da mutanan gidan"...........Ya faɗa saboda gudin aja zancen wata maganar ta ɓullo kuma. Daddyn nasu ne ya ce, " To mu dai mun wuce, in Kun fito kwa samemu gidan Anah taku, Hunaiz kai sai ka jirasu ku taho tare ko".......... Hunaiz da ya ƙarasa suka gaisa da Amjad ne ya amsa da, "To Daddy".
A ciki ma Juraysh ne yayi introducing ɗin sa a matsayin cousin ɗin sa da yazo gaishe su, a tsatsaye suka gaisa da matan sannan suka fito daidai lokacin Dad ɗinsu Nayrah ya kawo Kai a fusace ko ganin gabansa ba yayi da alama dai labari yaje masa. Ja baya Amjad yayi dan bashi hanyar wucewa kallon kallo sukayi na kusan minti biyu kowa da tasa ma'anar kallon kafin Amjad ɗin ya keɓe ya fice ba tare da ya ce dashi komai ba haka Juraysh ma yabi bayansa suka fice, cikin tsokana Juraysh ya ce, " Ga sirikin naka fa, naga sai muzurai yake da alama za'a tada gidan nan gwara muyi mu bar wurin nan tun Kafin bomb din ya tashi damu"........... daidai lokacin da Hunaiz ya ƙaraso wurin su dan dama shi a waje ya jirasu, Amjad ne ya ce, "Nagode dude's, ALLAH ya bar zuminci, ina ga ba wuri ɗaya zamuyi ba dan zanje hospital ne kamar yadda na faɗa ma, ku Kuma naga kamar su Uncle na jiran ku ko" ..........ya faɗa yana ɗan susa girarsa.
"To ai harda Kai suke nufi".......... faɗar Juraysh ɗin. Duba agogon hannun sa yayi tare da girgiza Kai ya ce, " Bazan samu komawa gida yanzu ba, duk abinda ake ciki muyi waya da kai ko Hunaiz".
Rakashi sukayi har mota sannan suka koma wurin tasu motar, Saida suka ga fitar su sannan suka shiga cikin wadda suka zo Hunaiz ya ja suka fice.
______________Dad yana shiga ya tarar da mahaifiyar sa zaune tana rabawa jikokin ta alawowin ɗaurin aure da aka shigo dasu. "Iyani! Iyani me wanna tsinannnan yaron yazo yi gidan nan ?"........... Ɗaure fuska tayi da faɗin, " Wa kenan?" .
"Wanna yaron Amjad mana".
"Au, Yan uwan sa ya rako mana, ko bakasan yan uwa suke da sirikin naka bane ".
" Ba rako yan uwansa yayi ba shi ne sirikin nasa"........... Yayyun dad dake shigowa falon suka faɗa, ƙarasowa sukayi suka nemi wuri suka zauna.
"Whatttt Yaya Adam, kasan kuwa me kuke faɗa, Amjad Hashim Darwin shi ne siriki na?".
"Kwarai"......... Yaya Adam ya Amsa da alamun tabbatar wa.
"To whl ba wanda ya isa dole a warware auran Nan, tukunna wa ma yace a daurawa ya'ta aure ba izini na, bayan ina takawa a doron duniya ban mutu ba".
"Ita Yar taka ai da amincewar ta dan saida mukayi baki da baki da ita ta kuma tabbatar mana da ta amince. Domin jiya muna zaune yaron nan ya aiko ɗan uwansa ya same mu ya shaida mana tsawon shekara ɗaya da wani abu da yi musu baiko, yanzu Kuma ya buqaci a sanya ranar ɗaura aure kace baka amince ba, kai akwai wanda zaka aurawa ƴarka. Yara kuma suna san junan su tunda har yarinya na ɗaukan ƙafa ta bishi har inda yake, saidai dake shi ɗin ɗan albarka ne baiyi Amfani da hakan wurin cutar da ita ba, sai ma nema da yayi ta faɗa masa inda zai samu wasu daga cikin yan uwa domin ya kai abin wurin su, ita kuma ta masa kwatancen nan gidan"........... Yaya Najib ya ɗaura da, "Mu Kuma baza mu sake zubama ido kai da matarka ku sake irin rashin albarkar da tasa kayi a baya ba ".
A fusace dad ya ce, "Nifa ba gwanin ta aka min ba yauwa Kuma aure sai an raba shi ko Kuma na shigar da Ƙara, wai ko baku san waye yaron nan bane, yaron da ƙasashen duniya suke bincike a Kansa wanted ne fa, bayan haka Kuma matan banza yake nema ko baku da labarin iyayen yarinyar da suka shigar da Ƙarar sa bane, okay dake ba ɗaya daga cikin ya'yan ku bane ko ".
Iyani ce ta ce, "Wai dakata Nu'uman ada daka ɗauki yarka kayi mata baiko dashi ba ka yi bincike kasan waye shi bane? Ina cewa ko Neman mu baka yi ba tsakanin Kai da dangin matarka ku kayi abunku ko? Okay saboda a lokacin kana cikin inuwar arzikin sa, ni dama nace bana Ƙara shiga cikin harkar ka ko ta iyalin ka wanna ma da kaga na karɓa su Najib ne suka dinga bani baki, ba fata nake ma ba Nu'uman amma abinda ka aikata Ka biyewa son zuciyar Matar ka whl wanna hakkin bazai taɓa barin ka ba".......... Bai tsaya yaji karashin zancen Iyani ba ya juya ya fita ba tare da ya Kara cewa komai ba, asibitin ya koma dan yana da tabbacin can Amjad ya nufa.
Bayan fitar sa iyani ta kalli su yaya Najib kana ta ce, "Maganar da yake faɗa gsky ce Najib?"........... Saida ya sauke numfashi sannan ya ce, "Haka ne Iyani, dan a yanzu ma maganar da ake ance duk ma'aikatun su na gold da refineries ɗinsu ƙasashe sun dakata da mu'amala dasu, shi kansa yaron ance wai an tsayar da passport ɗinsa daga ƙetara ƙasa na wani lokaci dan har yanzu ana Kan bincike ne ".
"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun, to batun neman matan da yake fa? Shi ma da gaske ne?".
"Shi ma dai haka mutane suke faɗa amma baza muce gashi ba tunda bamu gani ba da idanun mu ba, Sunce wai ya yaudari wata yarinya ya lalata mata rayuwa har sanadiyyar hakan ta samu Matsala a ƙwaƙwalwa, yanzu haka dai ance suna gaban kotu, ance wai dan iyayen yarinyar basu da ƙarfi ne saisa har yanzu Ake jan shari'ar yau gobe yau gobe"...........Yaya Adam ne ya dakatar dashi ta hanyar faɗin, "Dakata Najib duk wanna bayanan da kake idarwa a gaban Ka akayi ne?"............." Yaya Adam bakaji abinda nace bane, bamu gani da idanun mu ba, ba kuma mu shaida ba amma ina faɗa mata abinda mutane suke faɗa da kuma abinda duniya ta shaida bama cikin ƙasar Nifaz ba kawai, kuma Kai ma kana gani kuma kana karantawa a news".
"Najib mutum kamar Amjad dole zaiyi tarin maqiya na ɓoye Da na fili, dan gsky Ni kam har yanzu zuciyata ta ƙasa aminta da wa'annan shaci faɗin da ake yayatawa"........... Juyawa yayi wurin Iyani da faɗin, "Iyani ni sanin da nayi wa yaron nan, yaron kirki ne dan duk cikin iyalan alhaji Hashim, ance yafi ji dashi saboda hankalin sa da nutsuwar sa kawai dai akwai wani Abu a ƙasa".
Ajiyar zuciya iyani ta sauke da faɗin, "To ya akayi kuka yarda akayi auran bayan kunsan haka abun yake, danni kwata kwata ban sani ba kawai kun shigo min da yaro ne cewa shi yake neman auran Nayrah mahaifin ta kuma yaqi har yarinya ta fara binsa gida".
Yaya Adam ya ce, "Haka ne Iyani daga jiya zuwa yau da safe Kai har lokacin da aka ɗaura auren mu kan mu bamu san ba yaron da yazo jiya bane mijin domin ko a wajen suna ma da suka ce Amjad Hashim bamu kawo komai ba saboda mun ɗauka ko sunan ne yazo ɗaya tunda su anasu sunan akwai Darwin a ƙarshe saidai zuwan sa yanzun shi ya bayyana mana cewa bashi bane, dan a gaban mu shi mahaifin yaron da yazo jiya ya kirashi da Hunaiz, yanzu ma kawai na rasa yadda zan cewa shi Nu'uman ɗin ne saisa na shirya masa cewa shi Amjad ɗin ne ya aiko ɗan uwansa, Amma a zahiri yaron da yazo jiya a matsayin zuwan kansa yayi ya rufemu".
"To duk ba haka ba ita yarinyar wa take so ne?"........... Iyani ta tambaya. Yaya Najib ya ce, "Amjad, dan saida na zayyane mata duk abinda ya fada min ta tabbatar min haka ne, sannan na sake ce Mata da izinin ki Amjad yazo neman a ɗaura muku aure tace eh, kin amince tace eh".
"Kenan akwai wani Abu tunda har bai bayyana kansa ba sai bayan an ɗaura auran, in kuwa haka ne ya kamata Ku bisu asibitin domin Ku tabbatar da gaskiya"............. Faɗar Iyani dan hankalin ta ya kasa kwanciya wannan yaro ya musu shiga shiga ba zurfi, yaya Adam ne ya kalli yaya Najib da faɗin, "Nima tunanin da nake kenan inaga muje mu ji Kar ya zama mune marassa gsky, tunda kaga bamu ma sanar masa ba saida aka ɗaura muka ce yazo ya ƙarɓa sadakin ƴar sa "............ Iyani ta cafe da faɗin, "Ai ba laifi kukayi ba dan shi Nu'uman ba sanin ciwon ɗa yayi ba bai damu tabi shi ba ya gudu da ita indai wanna matar na ƙarƙashin sa ba abinda ya dameshi duk ta gama mallake shi". Miqewa yaya Adam yayi yana faɗin, "Bari muje muji abinda ake ciki iyani".
"To sai kun dawo ALLAH yasa muji alheri, amm Nafi'u ya tafi ko? ".
Yaya Najib ya ce, "Eh bayan an ɗaura aure ya wuce, yace yana da wani uzuri ne, har yake cewa mey sa ma ba'a ɗaura auren a masallaci ba bayan anyi Sallah. Kuma ma dai Ni whl sai yanzu abun ya dawo min Mey sa sukace lalle sai a gida".
"Kaga da ALLAH Najib wuce muje, kai akwai ka da son ayi gaba ayi baya, iyani mu mun wuce".
"ALLAH ya tsare hanya, ku gaishe min da yaran. ina Amfani aure irin wanna, Nu'uman dai baiyi dacen mata ba sam........" Haka suka fita suka barta tana Mita ita kaɗai.
Lokacin da Amjad ya isa asibitin Mumu ya samu sai ƙannen Nayrah ɗin, ba laifi jikin da sauki dan tun asuba aka cire oxygen ɗin tana dai kwance hannunta maqale da drip, tura ƙofar yayi ya shiga da sallama bayan yayi knocking sau ɗaya, duk miqewa sukayi banda Nayrah dake kwance sai pale eyes ɗinta data zuba masa tana kallonsa cike da tsantsar so da ƙauna, gaisheshi su Nashwa sukayi ya amsa musu a sake sannan ya gaishe da Mumu, fuska a ɗaure ta amsa sannan ta ɗaura da faɗin, "Me ya kawo Ka bayan kasan kashedin da Alhaji ya ma".
"Wurin matata nazo "...........Ya faɗa kai tsaye ba tare da wata shakka ba. Kallon Nayrah dake kwance tayi sannan ta kalli Amjad ɗin, "Wace matar taka ? Kai wai ko Ka fara haɗawa da kurɓe kurɓe ne"........... Ni kuwa nace Mumu Anya bakwa wuce gona da iri kuwa ke da Dad.
Bai ɗaga ido ya kalle ta ba haka zalika bai bata amsa ba sai wayar sa da ya zaro daga aljihu ya buɗe yayi playing wani video ya miqawa Nayrah kasancewar volume a ƙure yake yasa Mumu ta gama jin komai, video ne na ɗaurin auren sa da Nayrah ɗin harda sadakin da aka biya da silillikan gold's masu nauyi na companyn HD AURUM MINING. Video na ƙarewa mumu ta buɗi Baki da niyyar magana Dad ya banko ƙofar kamar zai balle ta Wanda har saida Mumun da kanta ta zabura, ita kuwa Nayrah wani sassanyar murmushi tayi tare da gyara kwanciyar ta dan a yanzu bata da wata sauran fargaba kuma jinta take kawai she's safe, ni kuwa nace Anya kuwa Nayrah? To bari dai mu gani.
"Kai sakar min ya'ta tunda bani na aura ma ita ba kuma banga uban da ya isa ya ɗaurawa ya'ta aure ba ina raye"............." Amma ai kai ka Bani auran nata ko?"............ Amjad ya bashi amsa Yana ɗago kansa tare da zare p cap din da ke kan nasa. "Ko da na Baka ai lokacin bansan waye kai ba, yanzu kuma da duniya ta fito da ɓoyayyen halin da kake ɓoyewa nace na warware, kuma na fasa" .
"Bai warwaru ba, bai kuma fasu ba "........... Amjad ya bashi amsa Kai tsaye . "To Baka isa ba kuma zanga in duk duniyar nan akwai wanda ya isa ya zo ya ɗaukar min ya, ko ya cilastani kan abinda banyi niyya ba".
Dan gajeren murmushi yayi da faɗin, "Dad a yanzu fa ina tsaye ne a gabanka matsayin sirikin Ka kuma miji ga yarka wanda yafi Ka iko da ita "............ Ɗaga hannu Dad yayi da niyyar kai masa Mari me ya tuna kuma yayi saurin sauke hannun yana jan kwafa, murmushi Amjad ɗin ya sakeyi tare da girgiza kansa ya ce, "Dad bana bukatar yin doguwar jayayya dakai Amma abinda nake so Ka sani wani yana cin albarkacin wani, Haka zalika duk da zaki ya kasance shugaba a dawa yasan damisa na iya fito na fito dashi , shuru shuru ba tsoro bane iya taku ne, Andddd silence is not weakness it's power"........... Yana kaiwa Nan ya juya ya kalla Nayrah sannan yayi waje.
"Ke kinajin dai abinda kika janyo min ko, a gabanki ya tsaya ya kalla idanun mahaifin ki ya gaya min magana, to shikenan mu zuba mu gani "............ Ya faɗa yana juyawa zai bishi mumu ta ce, "A'a Alhaji karka bishi ya isa haka, inaga lokaci yayi da zamu zubda makaman yaqi tunda bakin alqalami ya riga ya bushe kasan dai ba fin ƙarfin yaron nan mukayi ba, da Kai da duk wanda kake tunanin yana bayanka whl in da ya ga dama zai iya batar daku a doron ƙasa dan haka yanzu ka bari mubi Abun nan a sannu a samu ya sakar mana Yar mu kawai ba tare da wani tashin hankali ba, Kuma