BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   37 / 53

108K to 111K   out of 156.9K words

ba wani abu bane"....... Godia ta masa sannan ta fita daga motar, ta wuce ciki, shi kuma Zubairu da yake maqale jikin katanga kamar ƙadangare yana jira su gama, ganin ta fito ya sashi ƙarasawa ya buɗe motar ya shiga, ya tada suka bar layin.

Da daddare kuwa suna zaune a ɗaki dukkansu suna hira, zubairu ya ƙwankwasa ƙofar ɗakin nata, tashi tayi ta buɗe ba tare data tambayi waye ba saboda tasan Wanda take expecting, shi din ne kuwa miqa mata ledar dake hannun sa yayi da faɗin, "Gashi inji alhaji yace idan kin haɗa Yana jiran kiranki"........" Okay ka mashi godia dan ALLAH"........ " Ba damuwa". Zubairu ya faɗa tare da barin ƙofar ɗakin, ita Kuma ta koma ciki tare da cillawa Sahnish kwalin wayar, ɗauka yayi ya buɗe da mamaki a fuskar sa ya ce, "Hushaima sabuwar waya nake gani Ina kika samu haka?".

"Wani alhaji ne ya saya min fa ".........."kice duka ɗaya kika wanko shi tass, wannan wayar ai me tsada ce, iPhone 17pro fa kinsan kuɗinta kuwa. Hmmm amma dai ki kula, a tsaya dai a iya wanke wanken dan nasan wannan fagen kam kin haddace shi amma kar a wuce gona da iri".......... Batace komai ba sai ɗaukan tsohuwar ta ciro sim ɗin ta miqa masa da faɗin, " Haɗata a kirashi yanzu".



---------------------√



Duk da baiyi niyyar fita ba a lokacin saboda so yake anjima yaje gida yaga su Anah da jikin Dada amma halin da Nayrah ɗin take ciki a yan kwana biyun na damuwar abinda ya faru tsakanin ta da mahaifan ta ya sashi fito da ita night date. Zaune suke a wurin daga ita sai shi, wuri ne da ba kowa yake zuwa ba akasari manyan masu kuɗi ne ke zuwa su huta saboda waje ne me saurin comforting soul, atmosphere ɗin wurin is so relaxing, akwai sport center, akwai bangaren wurin cin abinci akwai cinema da sauran su, a yanzu ma fitowar su kenan daga wurin sport ɗin suka zauna aka kawo musu refreshments suna sha suna hira cikin nishaɗi.

A waje Kuma wata shegiyar mota ce ta sako kai zata shige ciki, Amma sai aka tsareta tare da faɗin anyi reserving wurin gabaɗaya har sai Wanda ke ciki ya fito, sauke glass ɗin motar yayi tare da yafito Kamal dake tsaye can gefe jikin motocin nasu, da sauri Kamal ya taho ganin Awais ne me Kiran, yana ƙarasowa ba tare da Awais ya amsa gaisuwar sa ba ya ce, "Waye a cikin Nan?"........ Ɗan shafa Kai Kamal yayi kafin ya ce, " Boss ne da madam".

Shuru yayi can Kuma ya ce "Kaje kace su buɗe min ƙofa, yayan wanda yake ciki ne"....... Ba musu Kamal ya wuce wurin securities da kuma sojojin nasu dan yasan halin Awais yanzu sai yaci mutuncin sa, ko da ya faɗa musu saida suka Kira Amjad suka sanar masa, murmushi yayi kawai tare da faɗin ba damuwa su barshi ya shigo.

Buɗe masa akayi ya wuce can nesa ya yi parking cikin dan duhuwa, sannan ya juyo wurin yarinyar dake zaune a gefensa tare da faɗin, "Karki fito, mun fasa zaman a nan ɗin ma, bari kawai na je na gana dashi sai nazo mu tafi, qani na ne".

"Okay". Da sauri na juyo jin muryar Hushaima, da gasken kuwa itace hakimce a passenger front seat na motar Awais.

Buɗe ƙofar yayi ya fita, a hankali itama ta buɗe ta fito ta bi bayan sa dan sai taje taga qanin nasa da saboda yana ciki aka hanasu shiga sai kace wani shugaban ƙasa. Wajen ba haske sosai hakan yasa Awais bai san tana binsa a baya ba har suka kusa isa inda su Amjad suke, tasowa Amjad yayi wanda hakan yasa Hushaima saurin shigewa lungun dake hannun damanta, wurin Amjad yabi da kallo sannan ya miqawa Awais ɗin hannu yana faɗin, "Yau Kai kaɗai ka fito kenan?".

Miqa masa hannun Shima Awais yayi suka gaisa ya amsa da, " Na gaji da yawo da driver ko wani escort ne, Kuma kasan Ina da damar na zagayawa ba tare da takura ba "......... ya faɗa cikin sigar shaguɓe. Murmushi yayi da faɗin, " Haka ne ". Ya ƙarashe yana satar kallon lungun da Hushaima ta shige Sannan ya ce, "ƙarasa ku gaisa da Nayrah bari nasa a kawo ma wani abu".......... Kamar zaice ah ah sai Kuma ya wuce table ɗin da Nayrah ɗin take .

Ta kawo Kai da niyyar komawa mota dan taji abinda suka faɗa saboda saisa tayi ƙoƙarin barin wurin kafin ya zagayo ya ganta saidai ina ta makaro tana kawo kai shi Kuma yazo shigewa kallon kallo sukayi irin na cikin ido ɗin nan kowa da abinda ke cikin zuciya da kuma kwakwalwar sa...............



*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 NE KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______ 51 & 52



Ta kawo Kai da niyyar komawa mota dan taji abinda suka faɗa Saisa tayi ƙoƙarin barin wurin kafin ya zagayo ya ganta saidai ina ta makaro tana kawo kai shi Kuma yazo shigewa kallon kallo sukayi irin na cikin ido ɗin nan kowa da abinda ke cikin zuciya da kwakwalwar sa, da sauri sauri ta wuce wurin motar tasu, bin bayanta yayi da kallo na wasu yan seconds sannan ya juya ya wuce ciki ya masa order refreshments ɗin da ya faɗa sannan ya koma inda ya bar su yana faɗin, "Amma Awais yau fitar nan ta musamman ce ko? Danni nayi zaton ko kai da hajiyar taka ne".......... ta ƙasan ido Awais ya maka masa Harara sannan ya ce, " Nothing special fa, kawai na ɗan fito na zagaya ne, yanzu ma tafiya zanyi banaso dare yayi min sosai".

"Ko dai bakaso ta gaji da jiranka"............ Amjad ya faɗa yana ɗan Smirking tare da tsare shi da ido yana sipping mocktail drink ɗinsa da ya ɗauka akan table ɗin hankali kwance ya wani karkace kai yana binsa da wani kallon ƙasa ƙasa. Cikin alamun rashin gsky Awais da ya miqe ya ce, "Wa.... Wacece kuma, nace ma Ni kaɗai na fito k........." Saurin tareshi Amjad ɗin yayi da faɗin, "Calm down, Ni fa Hajiya nake nufi, kar ta gaji da jiranka baka koma gida da wuri ba ta kulle ma ƙofa". Ya ƙarashe cikin sigar zolaya yana wani tsuke baki tare da yiwa drink ɗin wata yar iskar zuqa.

Kame kame Awais ya fara saboda yaso ya kwafsa, "To... to ai kai ne baka taɓa yi wa mutum magana kai tsaye "......... taɓe baki Amjad ɗin yayi daidai lokacin waiter ɗin ya ƙaraso. " To ai ka tsaya ka sha wani abu ko?"............ "Na sha in naje gida". Awais ɗin ya amsa yana barin wurin ba tare da ya ƙara kallon in da suke ba, da hannu Amjad ya yiwa waiter alamar yaje kawai, sake sipping mocktail drink ɗin yayi da dan dama a bakinsa sannan ya juya wurin Nayrah data tafi wata duniyar saboda maganganun da Awais ya faɗa mata a dunƙule wanda ta kasa warware su, straw ɗin da Amjad ya tsokala mata a kumatu ne ya dawo da ita duniyar mu, Ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta wurinsa. Bakinta ya nufa da straw ɗin hakan yasa ta ɗan buɗe ya shige, ɗayan bakin straw ɗin ya sanya a cikin nasa bakin sannan ya Fara transferring ɗin juice ɗin da ya guntsa zuwa bakinta through straw ɗin.........


_______________Shi kuwa Awais yana shiga Mota ya samu Hushaima zaune tana game tayi baya da kujerar ta harɗe kafafunta ta ɗaura kan dashboard ɗin kamar motar ubanta. "Sorry na barki ke ɗaya ALLAH yasa zafi bai damar min ke ba?".......... Wani irin juya kwayar idanuwanta tayi sannan ta musu masauki a kansa kafin ta ce, "Eh kam ya takura min matuqa......." Take ya shiga bata haƙuri amma sai ta katseshi da faɗin, "Sa'a ɗaya yaci kawai dan baka kusa dani ne amma ko a kan tukubar tsire zan zauna in dai kana kusa dani to fa ba zanji komai ba face sassanyar iska me kaɗawa cike da begen ka".......... Wani irin murmushin jin daɗi Awais ya saki ba tare da ya shirya masa ba sannan ya tada motar yayi horn aka buɗe musu suka fice daga wurin.

Sai wurin 12am Awais ya yi parking a bakin layin nasu saboda yana sauri ya koma gida dan in dai ba ƙaryar tafiya yayiwa matar sa ba baya kai wa kamar wannan lokacin a waje amma gashi yau Hushaima ta riqeshi har zuwa wannan lokacin ga kuma matar tasa tana ta kira ya kasa ɗagawa. Ɗan karkatowa yayi wurinta tare da faɗin, "To kwalisata sai yaushe kenan? ".......... Shuru tayi tana rolling wa'annan firgitattun idanun nata kamar me tunani, can kuma ta tsayar dasu wuri ɗaya ta kalleshi tare da faɗin, "Duk lokacin da kaji kana buqatar gani na, ni ɗin a ko yaushe a shirye nake da amsa kiranka"......... cikin jin daɗin kalaman ta ya ce, " To baki da matsala sai munyi waya kawai, ga wanna".......... Ya faɗa Yana miqa mata bundle biyu na 1k, karɓa tayi ta sanya a jaka sannan ta ce, "ALLAH ya Karo wanin su, Amma da ALLAH in tambaye ka mana".........."Eh to da inaga idan tambayar ba wai dole yanzu kike son amsar ta ba mu bari sai gobe mana, ko kuma muyi waya in naje gida". Ɗan girgiza kanta tayi da faɗin, "Alaji kana tsoron matar ka ne?". Saurin gyara zama yayi yana faɗin, "Wane ita, ita ɗin banza, Inajin ki ALLAH yasa na sani ". Ɗan taɓe baki tayi a sace sannan ta ce, "Wanna qanin naka ya kuke dashi ?".

"Step brother na ne, shi ne autan mu a maza, Wani abun ne?"........... ɗan girgiza kanta tayi kana ta ce, " Bakomai kawai dai ina daga mota naga wani kallo ne da yake ma kamar dai......" Shuru tayi kuma yayin da Awais ya danyi wani gajeren murmushi sannan ya ce, "Ai baza ki gaza jin suna sa ba, Shi ne ake zargi da safarar mutane a ƙasashe da dama".......... wani iri tayi da fuska kamar wadda ta sha wani abu me ɗaci sai kuma ta yi saurin sakin fuskar tana wani tunani a ranta saboda ko da ace sunan kaka suka haɗa zaiji kunyar faɗar haka a waje amma sai taga har kamar Alfahri yake ma da faɗar. Jama'a wani abu dake birgeni game da Hushaima akwai zurfin tunani, a cikin seconds sittin kacal zata warware komai ta cilla shi ma'aunin sa, wato Baiwar ƙwaƙwalwa ba wai sai me ilimi ba kaɗai, wanda bai taɓa zaman aji ba ma sai kaga ALLAH ya bashi. Irin su Hushaima ne in suka samu masu tsaya musu sai kaga sun zama wasu kuma abun Alfahri a cikin al'umma da kuma duniya gabaɗaya.

Katse tunanin nata tayi da faɗin, "Ohh ohkk Tabbas naji labarin, ance har yayi wa wata yarinya fyade ma suka Kai kotu yanzu haka ya ɓatar dasu ba'a san in da yarinyar da iyayenta suke ba"........... Da sauri ya ce, "Haka ne, gashi yana neman bata mana sunan gida, ko wanna sojojin da da kika gani hukuma ce ta sanya su dinga tsaronsa har sai an gama tattara bincike sannan suyi ram dashi a yanke masa hukunci daidai dashi".

Zubawa Awais ido tayi har ya gama ɓatancin sa akan Amjad ɗin sannan ya ce, "To kwalisata idan har ita kenan tambayar ina iya tafiya?". Ya ƙarashe da sigar neman umarni. Gira ɗaya ta ɗage tare da kafaɗunta biyun sannan ta ce, "Me zai hana, Sai da safe, ALLAH ya tashemu lpy"......... ta ƙarashe tare da buɗe ƙofar motar ta fita tana ɗago masa hannu har yayi reverse ya bar layin sannan ta wuce gida tunanika fal ranta.

Tana zuwa ta shige Dan dama ba'a rufe gidan da wuri. A ƙofar ɗakinta ta samu Sahnish tsaye sai faman danna waya yake a gaggauce da alama ita yake nema, yana ganin ta ya taho da sauri yana faɗin, "Hushaima daga Ina kika fito?".

Tsayawa tayi tare da faɗin, "Sahnish ban gane daga Ina na fito ba tsaro na kake ko me?".

"Haba Hushaima Kar zaman gidan nan ya rinjayi tunanin ki mana, ni nasan ba haka kike ba Amma wanna shi ne Karo na biyu da kike ƙoƙarin ɓoye Min wani Abu, Ranar Lahadi haka kika fita tun rana sai karfe tara na dare kika dawo, na tambaye ki, kikace min abokiyar aikin ki ce ta haihu, Hushaima! Na fa sanki fiye da yadda na san kai na ba abokiyar aiki ba ko ita me wurin taku ce ta haihu ba zuwa zakiyi ba amma na bar maganar ta wuce, yau kuma tun da akayi sallar magriba kikaci kwalliya Kika fita sai yanzu kike dawowa, ina kike zuwa?".

"Na shiga uku ni Hushaima, to Sahnish kamani ka daka sai na fada ma kaji"..........Ta Ƙarashe tana wucewa ta buɗe ɗakinta ta shige ta bar Sahnish ɗin baki sake, cike da damuwa ya juya ya wuce ɗakin sa ya ɗauko Shazeen ya dawo mata da ita ɗakinta ya juya ya fice tana masa magana ma ko juyowa baiyi ba.

Shi kuwa Amjad Bayan tafiyar su Awais da kamar 30 minutes ya ce da Nayrah ta tashi su wuce ya Kai ta gida akwai inda zashi, tashi tayi tana ɗan kumbura fuska jin cewa zai Kaita gida ya barta shi kuma ya sake fita maybe ma ba a gidan zai kwana ba kamar yadda yai musu lokacin da ya kawo su ita dasu Nashwa. Har suka je gida tana kumbure kumbure ko da aka buɗe mata ƙofar mota ma qin fita tayi ta juyo tana kallon sa ganin kamar hankalinsa ma yayi wani wuri ya sa ta riqo hannun sa tare da ɗan leqo fuskar sa, dawo da kallonsa yayi kanta tare da yi mata ɗan murmushi ya shafo gefen fuskarta da faɗin, " Ya akayi ne Madam ?"......... Zumɓuro ɗan bakinta tayi kafin ta ce, " Me ke damun ka ? Na lura tunda ya Awais ya tafi mood ɗin ka ya sauya".

"Bakomai kawai dai zanyi missing ɗin ki ne, bana so nayi nesa dake ko na minti ɗaya my Ninie, ina buqatar Jin motsinki a kusa dani a ko da yaushe"......... Ya karashe yana jan fluffy kumatun ta. Ajiyar zuciya ta sauke maganganunsa na ratsa jikinta, a shagwabe ta ce, "To to ka fasa fitar mana, ka bari sai da safe, ni tsoro ma nake ji".......... Yana ƙoƙarin magana wayar sa tayi Ƙara alamar shigowar saqo, dubawa yayi yaga Philip ne hakan ya sashi faɗin, "Akwai aikin da dole a daren nan zan kammalashi, amma in na gama zaki ganni ko nan da jibi ne".

"What next tomorrow fa ?". Ta faɗa a rikice. Cike da tabbatar wa ya amsa da. "Yes"....... A zuciyar sa kuwa yana matukar tausaya musu shi da ita, a matsayin su na sabbin aure da ko 1 month basu cika ba, ace basu samu damar kasancewa da juna ba ko da na tsawon sati biyu ne, saurin kawar da tunanin yayi saboda Kar hakan ya kawo masa nakaso a ayyukan sa sannan ya sake cewa, "Shiga gida sai na wuce, kinga an fara nema na". Bata ƙara ce masa komai ba ta sauka jiki a sanyaye, zagayowa tayi ta ɓangaren sa cikin dauriya ta kamo fuskar sa da hannuwanta duka biyun tana kallon cikin idon sa ta ce, " ALLAH ya Kare min Kai gaban ka da bayan ka, ya ma katanga daga duk wasu masu sharri". Ta ƙarashe tana me manna masa peck a both cheeks ɗin sa sannan ta juya ta shige ba tare data tsaya jiran amsar sa ba, da wani irin kasalallen murmushi ya bita har ta shige sannan ya basu umarnin tafiya.

Direct family house ɗin su suka nufa, ko da aka Buɗe masa ƙofa bai fita ba saida ya gama waya da Philip sannan ya ziro da ƙafar sa ɗaya waje cikin nutsuwa ɗayar ma ta biyo baya sannan ya fito gabaɗayansa ya nufi Ƙofar part ɗin mahaifiyar sa, bayan ma'aikatan sun buɗe masa ya wuce ciki. A falo ya same ta tsaye tana duba agogo tana ganin shigowar sa ta sauke ajiyar zuciya dan dama saboda ya sanar Mata zai zo yau ɗin ne yasa ta ki kwanciya tun ɗazu dan tasan Amjad baya Alƙawari ya karya komin matsi in dai ya faɗa to ko yaya sai ya kwantanta shi. "Ya hakuri Dan ALLAH Anah na barki kina ta jira whl bansan zan Kai dare haka ba sai sa na faɗa miki gashi kuma kin hana kanki bacci kina jira na ".

Murmushi tayi tana kallon Ɗan nata cike da so da ƙauna ta ce, "Yanzu ma na

37 / 53