Author : Young Writer Category : Tknovels
da zamu qalubalance ta, kasan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi"........ Shuru Haisha'an yayi baice komai ba, ganin haka yasa Omaine tashi ya wuce bathroom dan wanke hannunsa.
____________A bangaren Queen Hirut kuwa ta aika ne a Kira Muru akan Haisha'an, lokacin da Muru ta iso palace sallamar duk mazan sukayi sannan suka rufe ƙofa kamar yadda sukeyi in zasuyi wata magana a tsakanin su. A kujerun dake wurin Muru da sauran bayi suka zauna, dan su bayin su mata basa zama a ƙasa cox ana daraja su sosai. Sunkuyar da Kai tayi alamar girmamawa sannan ta ce, "Gani ya shugaba ta".
"Muru!"....... Queen Hirut ta Kira sunan ta a kausashe.
"Abun bauta ya sanyaya zuciyar shugaba ta"....... Muru ta faɗa still kanta na kallon ƙasa.
"Ɗanki ya kasance babban me laifi a masarautar Nan, ba Kuma dan wani dalili ba da yanzu baya takawa a wanna doron duniyar tamu".
"Tuba nake shugabata, haqiqa ni bani da ja kan duk abinda kika yanke akan Haisha'an ko da kuwa za'a yanke masa hukuncin kisa ne saboda lalle Haisha'an ya keta doka dole jinin sa ya halatta wa Abun bauta domin ya aikata saɓo ".
Murmushin Jin daɗi Queen Hirut tayi saboda bata taɓa yanke hukunci ko Kuma tayi shirin aiwatar da wani abu kan Haisha'an ba Muru ta bata hakuri kan kartayi Wanda ita Kuma take ganin hakan matsayin tsantsar girmamawa da Muru ke mata.
"Masarauta tana alfahri dake Muru dan haka kije bangare na ki jirani"......... Cikin jin daɗi Muru ta ce, " Ina godia shugaba ta"........ Miqewa tayi sauran bayin ma da suka zo tare suka miqe tare da risinawa alamar girmamawa ga Queen sannan suka rufawa Muru baya, suna fita wani bafade ya shigo, daga bakin Ƙofar ya zube, Mrs Ruthy kanwar Queen ce ta ce, " Kana iya shigowa Kibrom".
Tashi yayi sannan ya ƙaraso tsakiyar palace ɗin da faɗin, "Abun bauta ya sanya miki albarka, an samu su Hailu a guardroom cikin fitar hayyaci bayan sun shiga tare da Haisha'an dan bashi horo, a yanzu haka suna cikin wani mawuyacin hali"......... Chief Benish ta ce, "Ina shi Haisha'an ɗin?"
"Mun barshi a ciki baya motsi"........ Girgiza Kai tayi tare da kallon Queen Hirut sannan ta ce, "Kibrom Kaje kaji dasu".
Miqewa yayi da fadin, "An gama legna". (mekakelegna, wato chief minister). Tashi yayi tare da sake durƙusawa alamar girmamawa ga Queen sannan ya juya ya fita.
-----------------√
Anan wajen Amla tayi sallama da barrister sannan ta nufi inda su Hushaima suke tsaye ta buɗe musu motar ta hanyar danna remote ɗin dake hannunta tare da faɗin, "Ku shiga mana"........ Ita da Hushaima da Shazeen suka shiga gaba, baba ilerika da Sahnish suka shiga baya, Saida suka dau hanya ta ce, "Amma Hushaima kin Kira wani ne?".
Itama Hushaiman da take cikin qullewar Kai ta ce, "Whl ban Kira kowa ba Amla, da nasan da Wanda zan Kira ya fidda ni a nan wurin ai da bazan Kai wanna kwanakin a ciki ba".
Sahnish ya ce, "Amma fa Abun ya ɗaure min Kai, Kuma duk wanda yasa a saki Hushaima to lalle sama yake da su wannan Awais ɗin, kiga fa yadda DPO ya fito a rikice ko ganin gabansa ba yayi".
"Gsky ba ƙaramin mutum bane Kam, saboda nima da na nemi ya min ƙarin bayani cewa yayi kawai daga sama ne, to daga sama aljanu ne?"....... Amla ta faɗa, baba ilerika ya amsa da, " koma dai minene ai sai mu godewa ALLAH tunda har ya fito da ita lpy".
Amla ta ce , "haka ne baba, ALLAH dai ya tsare gaba Kuma Hushaima Dan ALLAH ki kiyaye ki dinga tausar wannan zuciyar taki, kinga dai wahalar da muka Sha ba Dan ALLAH ya taimake mu ya yanke mana wahalar ba da har yanzu muna ciki. Sahnish ka dinga bawa yayar nan taka ruwan buta tana sha ko ALLAH zai sa wannan zafin zuciyarta ta ya ragu".
"In Sha ALLAH"........ Ta faɗa fuskarta na kallon titi, shi dai Sahnish uhummm kawai yace dan ya san Hushaima ba ruwan buta ba ko butar aka guggutsira aka bata in zuciyar nan ta motsa sai tarihi ya maimaita kansa.
"To nifa inaga in kin samu wuri zaku sauke ni a nan dan ba gida na nufa ba"........ Faɗar Baba ilerika.
"Baba za'a shiga majalisa kenan"....... Hushaima ta faɗa tana ɗan sassauta fuskarta.
"To Hushaima abunki da me iyali ai saida buga buga, zama wuri ɗaya ai na Wanda ya Tara ne"......... Ya faɗa daidai lokacin da Amla tayi parking gefen titi ya buɗe Ƙofar ya fita.
Ita kuwa Hushaima girgiza kanta kawai tayi da jin maganar baba ilerika, to mutumin da baya ciyar da gidan sa baya shayar dasu baya tufatantar dasu wani nauyi ne a kansa, juyawa tayi da faɗin, "Sahnish in akwai kuɗi a wurinka bani".
Ragowar kuɗin dake jikinsa duka ya zaro tare da irgawa ya miqa mata su yana faɗin "Dubu huɗu ne suka rage dama".
"To Sahnish ALLAH ya kaiku gida lpy"....... Baba ilerika da ya leqo ta window ya faɗa.
"Baba ga wanna kayi kuɗin mota"....... Amla ce ta ce, " kinga riqe dubu huɗun zakuyi wani abu dashi, ungo miqa masa wanna"....... Ta ƙarashe tana miqa mata dubu goma.
Karɓa tayi ta miqa masa. " Kai Hushaima harda wata wahalar Kuma?".
"Bakomai baba, mun gode da karamci sosai, ALLAH ya saka da alheri".
"Ni ne da godia ai Hushaima. Hajiya Nagode fa ALLAH ya tsare hanya"........ Ya faɗa yana ɗaga musu hannu tare da zaro karar sigarin sa da lighter ya kunna sannan ya tsallaka titin ya ɗauki hanya da Ƙafa.
Amla ta ce, "Ni whl a farko kallon mutumin banza nake masa Amma ganin yadda yake ta Kai kawo tare da Sahnish sai naji ya burgeni whl".
"Amla ai ko mutumin banza ma yana da ranar sa, bar ganin mutum haka kace bashi da amfani whl kowa da irin amfaninsa da Kuma ranar sa"....... Faɗar Hushaima.
Sahnish ya amsa da, "Gsky dai baba ilerika ya mana rana, ko da ace bashi da Abun taimakon mu ya mana Kara Kuma ya kasance a tare damu da Kuma shawarwari".
Amla ta ce, "Nima na gani whl, Amma dai daga gani har yanzu baiyi retire ba"........ Ta ƙarashe tana Yar dariya.
Dariya Sahnish yayi shi ma yayin da Hushaima ta ce, "Baba ilerika ai sai shi, ALLAH dai ya shiryeshi".
Haka suka cigaba da hira har suka ƙarasa gida, parking tayi a ƙofar gidan, fita Sahnish yayi tare da mata sallama , Hushaima ma buɗewa tayi Shazeen ta fita tana ƙoƙarin fita itama Amla ta tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta, "Hushaima"......... tsayawa tayi daga ƙoƙarin sanya ƙafarta a waje da take ta juyo tana kallonta. "Hushaima nayi wani tunani ne, ya kamata ki zama cikin shiri, domin ko ma waye yasa aka fito dake to zaizo gareki ko kuma saqonsa, saboda ya sanki".......... Tayi Maganar idonta akan layin. "Ya San ni?"...... Hushaima ta Tambaya da ɗinbin mamaki.
Dawo da kallonta kan Hushaiman tayi tare da faɗin, "Tabbas ya sanki, saboda haka kawai daga sama ba zai taimaki mutumin da bai sani ba. Ni dai na faɗa Miki ki zama cikin shiri saboda bamusan da wacce zaizo Miki ba".......... Hushaima data shiga ruɗin tunani ta girgiza mata kai sannan ta juya ta fita ba tare data sake cewa komai ba. A ƙofar gidan ta tarar da Sahnish da Shazeen tsaye suna jiranta, wucewa tayi kawai ba tare data ce musu komai ba, Sahnish dake riqe da hannun Shazeen ya rufa mata baya yana faɗin, "Duk sallamar ce awa guda".
Tun daga soro sukeji ife ife har suka ƙarasa ciki, tsayawa sukayi suna kallon yadda Yarinyar baba ilerika da yarinyar kawu adamu ke dokuwa a filin tsakar gidan, gefe Kuma iyayen su ne ke ta musayar baki suma kamar zasu kaiwa juna hannu, ga lady cyama data saki sauti a MP ɗin ta suna cashewa dasu yar charas.
Juyowa Hushaima tayi ta kalli Sahnish kafin ta ƙarasa da sallama, Amma ina ba wanda ya lura dasu ma bare yaji sallamar ta, itama dai kawai tayi ne Amma tasan ba ji zasuyi ba. Wucewa ɗakinta tayi Sahnish ya buɗe mata ɗakin ta shige sannan suka bi bayanta shi da Shazeen, tsab suka samu ɗakin dan kullum sai Sahnish ya gyara kafin ya fita.
Tsayawa tayi tare da faɗin , "Sahnish yanzu ruwa zakaje ka samo min nayi wanka, dan whl ni kaina kyankyamin kaina nake kusan sati guda ba wanka ".......... Wucewa yayi ya ɗauki bokitin dake ƙofar toilet sannan ya fita yana faɗin, "Yanzu kuwa".
Wayarta ta ɗauka a jaka tare da dubawa, sosai ta cika da mamakin ganin ba missed call na Alhaji Awais ko ɗaya, shuru tayi tana tunanin ko dai ya gano itace ta jiwa yarinyar sa ciwo, katse tunaninta tayi tare da rufo ƙofar saboda hayaniya ta wuce ƙuryar ɗakin sannan ta danna masa kira sai dai har ta katse bai ɗaga ba, ba ƙaramin fargaba ta shiga ba da rashin ɗagawar tasa, shiru tayi tana bubbuga wayar akan lips ɗinta, cikin rawar jiki ta sake kiran number tasa har tazo katse wa ya daga. "Hello Hushaima"......... Ɗan shiru tayi saboda jin yanayin Muryar sa kamar ransa a ɓace yake.
Tausasa Muryarta tayi da faɗin, "Alaji na kana Lpy?"............"Ina Lpy kwalisata ykk, kwana biyu"..........."Alaji lpy kuwa naji Muryar ka wani iri?". Tayi tambaye a ɗarare.
Cikin sautin dake bayyana fushin sa ya ce, "ki bari Hushaima wai wata yar iska can da ba kowan kowa ba kawai ma'aikaciya a wurin saloon ne ko whatsoever ma wai ta fasawa yarinya ta kai sannan ta ɗauki matsiyacin hannunta ta mari matata, imagine kamar ni a ƙasar nan ai min wannan cin mutuncin".
"Subahanallahi Alaji abinda ya faru kenan? an kama yarinyar amma?".......... Ta tambaya dan jin amsar da zaice .
"Ina ranar da muka rabu to ai ranar abun ya faru, tun a ranar aka kulle shegiya, na ci alwashin tozarta yarinyar nan in kuma ga gatanta a ƙasar nan dan gobe za'a shiga kotu daga can in Sa a wulla min shegiya gidan yari amma sai dai me........" Shiru yayi yana huci alamar abun yana masa ciwo.
"Kai alhamdulillah gsky Alaji gwara ka nuna mata waye kai a ƙasar nan, to in banda ma tsaurin ido irin na talaka ai ko makaho yasan bakin rijiya ba wurin wasan sa bane, ko daga kallon yar ka ma ai tasan ba tsarar ta bace amma har tayi mata irin wannan lahanin sannan ta mari Hajiya".
"To ai Baki sani ba"..........Ya tare ta. "Wai ɗazu kawai na samu labari an sallame ta ba tare da izini na ba, wai na tambayi dalili amma saidai ace min inyi hakuri daga sama ne, duk wanda nasan zan kira kan batun nan na kira amma amsar ɗaya suke bani sannan anqi faɗamin daga saman waye, wai ni za'a tozarta a garin nan ".
"To yanzu kai Alaji hukuncin me ka yanke?".........."Whl whl whl Hushaima jinin Hudaibiyya ba zai zuba a banza ba sai tasan cewa tsakanin sama da ƙasa akwai tazara ko uban waye ya tsaya mata kuwa sai na tozarta ta sai nayi watagigi da rayuwar ta"........... Shuru tayi can kuma ta ce, "Alaji baka tunani turota akayi?".
Dif Awais yayi ya ɗauke wuta domin sai da ta faɗa wannan tunanin yazo kansa kenan anyi amfani da ita ne don cin ma wani abu yanzu kuma da suka samu abinda sukeso suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka sa aka sake ta, jijjiga kansa yayi cike da gamsuwa da tunanin da yayi ya ce, "Kinsan kwata kwata banyi wannan tunanin ba, kai gsky kina da brain My ƙwalisa"........ Lumshe idanunta tayi ta buɗe tana sakin wani shu'umin smirk ta ce, "Alaji ina so Ka barmin komai a hannu na, na maka alqawari sai na gurfanar ma da ita a gabanka, da kaina zan kawo ma ita".......... Dukda yana cikin yanayin ɓacin rai hakan bai hana shi darawa ba saboda maganarta ta da yaji kamar tatsuniya, da har ya fara wani tunani daban sai kuma yaji ta shigo da wannan shirmen, dariya yayi sannan ya ce, "Kaji ki da wata magana dan ALLAH, ke da baki santa ba ta ina zaki iya nemo ta. Ni fa sai da kikayi maganar nan ƙwaƙwalwata ta kawo wuta saboda yarinyar da akace yar matsiyata ce gaba da baya bazawara kuma me ya'ya marayu kaiii akwai wani abu. Amma yanzu ke bakisan fuskar ta ba, baki san inda take ba sannan kice zaki kawo min ita?".
Wani silent smile ta sake saki tare da yin one step forward ta ce, " Alaji sanin talaka ai sai talaka, in dai har ka yarda dani da kuma alqawarin da na ma ni kuma sai na kawo ma ita cikin ruwan sanyi, kuma zan so duk wannan alwashin daka ɗauka ka aiwatar dashi a gabana. Amma inaso kafin nan ka sa a fara bincika ma ko turo ta akayi kuma ka sa ido a mutanan dake kusa dakai ".......... Ɗan shiru yayi yana sauraran ta da kuma tunanin Maganarta na ƙarshe, ba dan ya gama yarda da batun kawo yarinyar ba gabaɗaya amma dai yaji ɗan sanyi sanyi, dan haka ya ce, "Shikenan ƙwalisata zanyi duk yadda kikace, kuma na bar Miki komai amma fa in kika Saɓa alqawari kuma........."
"Hmm Alaji kenan karkayi mamaki in nace ma wanna shine alqawari na uku da na taɓayi a duniya, saboda bana ɗauka alqawarin da zan karya, na yanzu shi ne na uku kuma sai na tabbatar na cika ma shi saidai kai ka fasa abinda ka faɗi".
"I like your confidence, kina burgeni matuka whl, kinsan wannan rikicin ne ya hannani kiranki tun ranar, ke ma kuma sai yau kika tuna Dani".
"ALLAH Sarki Alaji, yau na fito daga asibiti fa kwana na shida acan bansan inda kai na yake ba, zazzaɓi nayi me zafi"........ A ɗan dame ya ce "Subahanallahi ya jikin naki ?".
Sake langwaɓewa tayi da faɗin, "Da sauki Alaji amma fa naji jiki ba ƙarya".........Ta ƙarashe tana kallon Sahnish da ya shigo da bokitin ruwan ya kai mata a ƙofar toilet ya Ajje saboda Shazeen dake cikin bayin, sannan ya dawo bakin katifarta ya zauna yana kallon Hushaiman dake tsaye tana waya.
"Zanzo anjima in sha ALLAH, ALLAH ya ƙara sauki kinji sannu, da ba dan wannan abubuwan da suka shige min kai ba ai da ko asibitin ne sai nazo, to bansani ba"........ Ya mata ƙarya dan Alhaji Awais duk wani iya shegensa a ɓoye yake kamar yadda kukaji Amjad ya faɗa shi kaɗai yasan wannan ɓoyayyen halin nasa dan ko su Nuhail da Julaybin basu sani ba ballantana kuma iyalinsa daga shi sai direban sa Zubairu wanda shi ne idon sa a harkar. "Bakomai Alaji Nagode sosai, sai kazo ɗin".
"Ba komai ki huta yanzu sai na shigo zuwa anjiman in sha ALLAH ".
TO FA JAMAA GA DAI HUSHAIMA TA DAU ALQAWARIN KAWO WA ALHAJI AWAIS WADDA TA FASAWA YAR SA KAI BAYAN KUMA TA SAN ITA CE , SANNAN TA CE YA SANYA A MASA BINCIKE SHIN KO TURO TA AKAYI KUMA YA SANYA IDO AKAN MUTANAN DAKE KUSA DASHI, SHIN BAKWA GANIN TA FAƊI HAKA NE DAN TA KAWAR MASA DA HANKALI WANI WURI? KO KUMA TAYI HAKAN NE ITAMA DAN CIN MA WANI NUFI NATA? TO WAI SHIN YA KUKE GANIN ZA'A ƘARE? ZATA KAI MASA KANTA NE KO KUMA YA ABIN ZAI KAYA ?
WANI ALQAWARURRUKA NE GUDA UKU DA TACE A TSAWON RAYUWAR TA SU KAƊAI TA TAƁA ƊAUKA?
YA BATUN ALWASHIN FANSA DA TACE SAI TA ƊAUKA AKAN HUDA WATO YARINYAR ALHAJI AWAIS?
WAYE YA SA AKA SAKI HUSHAIMA? MIYE DALILINSA NA SAWA A SAKE TA? SHIN YA SANTA NE DA GASKE KAMAR YADDA AMLA TA FAƊA ?
WAI SHIN SU WAYE SU MA? INA IYAYEN SU?
INAGA TAMBAYOYIN ZASU MUKU YAWA BARI DAI NA BARKU HAKA MU HAƊU A STEP 2, KARKU BARI A BAKU LABARI.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______ 68 & 69
AURELLON SULTANATE💎
Rouslan bai tarar da Reeslan ba sai a mota, shiga yayi kawai dan already an buɗe masa, baice da Reeslan komai ba shima baice dashi komai ba a haka motocin suka fice daga ɓangaren na su. Ɗan juyowa Rouslan yayi da niyyar satar kallon Reeslan daidai lokacin shi ma ya kallo Rouslan ɗin, kallon juna sukayi na tsawon second sittin kafin su sake ɗauke kansu still basu ce da junansu komai ba, can kuma a hankali kamar mai tsoron wani ya jisu Rouslan ya ce, "Meysa baka sanarwa Ummu ba?"......... Kallon sa Reeslan ɗin yayi kafin ya ce, "Kai meysa baka faɗa mata ba".
"I can't! "........ Ya faɗa muryarsa ɗauke da damuwa.
"Abun da kake tunani ba shi Ummu take nufi ba
Rouh, saboda akwai abinda ke faruwa d........" Shuru yayi tare da maida kansa kan glass ɗin window yana kamo lips ɗin sa na ƙasa. Juyowa Rouslan yayi gabaɗaya ɓangaren Reeslan cikin wani irin yanayi ya ce, "Akwai wasu abubuwan da suka fi wa'annan kenan ?"........ Juyowa Reeslan