Author : Young Writer Category : Tknovels
material ɗinkin A shape da ya kama surar jikinta, kasancewar bata da rama ta ko ina a cike take.
Tafiya take sauri sauri gudu gudu bata tsaya ko ina ba sai shagon hayar da Baba ilerika ya kama a sirrance yake zuwa ya kwana idan kwanan gidan ya ishe shi ko kuma matan nasa sun hura masa wuta, tana zuwa ta shiga bubbugawa, wata ce ta buɗe kana ganin ta kaga fitsararriyar kilaki, kallon sama da ƙasa tawa Hushaima kafin ma tayi magana Hushaiman ta rigata da faɗin , "ina yake?"..........Gatsinawa tayi a ɗage ta ce, "Ina yake, kamar ya ina yake? Shi wa?".........Tsaki Hushaima taja dan a yanzu bata da lokacin wanna hayaniyar sai kawai ta ce, "Baba ilerika"........... Leqowa yayi daga shi sai vest da dogon wando na atampa Yana faɗin, "Waye da sassafen nan blacky ?"......... Idon sa ne ya sauka akan Hushaima dan jim yayi alamar baiso zuwan nata ba ko kuma yanayin data samesu ne oho, kallon blacky dake bin Hushaima da harara yayi kafin ya ce, "koma ciki Blacky ina zuwa"............ Zatayi magana ya ce, "Shige mana haa".
Wucewa tayi ciki shi kuma ya dawo da kallon sa Kan Hushaima cikin borin kunya ya shiga faɗin, "Hushaima me ya kawo ki nan? in kina nema na ai zaki iya Kiran wayata, kuma ma kinga kwata na faɗa shine wannan matar ta taimaka min na wanke rigar tawa, ina jira ta bushe ne in taho gidan. Tukunna ma wa ya kwatanta miki wurin nan har yace miki ina nan? ". Ya ƙarashe yana ɗan shafa bayan wuyansa. Dan sosai yake kunyar Hushaima, yana jin nauyin ta tun a farkon haɗuwar su saboda yadda take bashi girma, ko ya'yan sa baya kunyar su ganshi da mace dan sun ma saba saboda shi da su ɗin kar ta san kar ne.
Ba tare da tabi takan zantukan sa ba ta ce, "Baba shin ko Jey ya faɗa ma zai tafi ne"......... Shuru yayi kafin ya ce, "Baya nan ne?" .
"Baya nan ya ma kwashe kayansa gabaɗaya sai ɗan makullin ɗakin da ya bari a ciki".
"Eh to lokacin ƙarewar kuɗin hayar sa dai baiyi ba Maybe kuma ya canza shawara ne, Amma to da wani Abu ne ko akwai wani Abun ki a wurin sa ne?"........... Shuru Hushaima tayi ta rasa me zatace dan ita sai yanzu ma irin rikicewar da tayi ya dawo Mata. "To kin kirashi ne a waya?". Maganar Baba ilerika ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. Tabb to ita tama tuna da wata Abu wai waya . "Bai dai sanar da Kai ba Kenan?".
"Ina fa ai ni rabo na dashi tun ranar da na ganshi shi da Sahnish can majalisar su Amiru me shayi da daddare".
"Amma Baba, ya kamata ace fa kana bincike kafin ka bawa mutane wurin zama a gidan ka, domin a irin hakan tabbas wata rana zaka bawa wani ɗan ta'addan mafaka ba tare da ka sani ba".
"Eh to, za'a kiyaye na gaba kam, to amma shi Jey ɗin wani abun ya aikata ne?".
"Bakomai kawai dai na gaya ma saboda gaba, tunda kaga yanzu ma sai tashi akayi aka tarar babu shi, to haka in wani azzalumin ne sai ya gama aika aikarsa ya gudu ya Barka a wahala".......... Ta ƙarashe tare da juyawa ta bar wurin da ɗan sauri sauri, kawai tunani yadda rayuwar su ta kasance tare da shi take. A da in akace zata shaqu da wani har ta tsinci kanta a irin wannan yanayin dan kawai ya barta saita ƙaryata saidai kuma gashi hakan ya faru a lokacin da bata taɓa tunani ba, "Jawaad". Ta faɗa a hankali tana cigaba da tafiya, maganganun su na jiya da daddare suka shiga dawo mata, a haka har ta Ƙarasa gida, ba tare data bi ta Kan kowa ba ta wuce ɗakinta, bata tarar dasu Sahnish ba kuma tasan bazai wuce ya tafi Kai Shazeen makaranta ba.
Wayarta ta ɗauka ta gwada kiran layin Jey ɗin saidai baya tafiya, murmushi tayi me ciwo, bata taɓa sanin irin ginin da yayi a zuciyar ta ba sai yanzu da suka tashi babu shi, ɗage kanta tayi sama tana tunanin rashin adalcin da zuciyarta ta mata, wanna dalilin ne yasa take taka tsantsan da zuciyarta a kan kowani ɗa namiji da ya nemi ya raɓe ta saboda bata son shaquwarsu ta zame mata rauni saidai kash Jawaad ya shammace ta.
Ta jima cikin ɗakin zaune har Sahnish ya dawo ya sameta a haka, neman wuri yayi ya zauna yana faɗin. "Hushaima ina kikaje ne? daga fita Kai abinci kuma na jiki shuru, na fita na tambaya akace ai kin fita, sai nace Kar Shazeen ta makara bari kawai na kaita na dawo kafin nan kin dawo dan nasan ba nisa kikayi ba".
"Sahnish Jawaad ya tafi"..........."To ai zai dawo tunda kinsan wani lokacin yana fita da wuri "........... Girgiza Kai tayi tare da faɗin, "Ina nufin ya tafi, tafiyar da bana tunanin zamu sake haɗuwa".
Shuru yayi Yana kallon cikin idanun yayar tasa me cike da longing wanda yasa jikinsa yayi sanyi. "Kunyi sallama kenan, har ya gama NYSC ɗin?"........... Kallon wasu sec ta yiwa Sahnish ɗin kafin ta ɗauke kanta, sautin hmmmm ta fitar tana ɗan tsuke bakinta idonta akan wayarta ta ce, "Kawai yayi wasa da hankalin mu ne gabaɗaya Amma bana tunanin NYSC yake, aiki dai yazo yi". Ta ƙarashe tana dago idanunta da suka ƙara haske har wani sheqi suke ta zubawa Sahnish su.
"Wani irin aiki kuma?"............. "Baza Ka taɓa fahimta ba Sahnish dan haka bar zancen kawai. Ya bani wasu kuɗi jiya yace na ajje zasu min amfani wai ashe shi sallama ce yakeyi a dunƙule ".
"Nima ya bani wasu "............ Gyada masa Kai tayi tana haɗiye wani abu da ya tsaya Mata daƙyar ta ce, "Ka tafi wurin Sana'ar ka kawai, nima aiki zan wuce"............ Ta na Kai nan ta miqe ragowar abincin nata dake cikin tukunya ta kwashe ta zuba a container ta rufe ta saka a jakarta a zuwan in taje aiki taci, ta ɗauki waya da abubuwan buqatarta ta, miqewa Sahnish yayi shima suka fice tare, a dawo lpy ya Mata sannan ya wuce ɗakinsa dan ya shirya ya fita.
Ko da taje aikin yau komai tayi Jey ne ke yawo a ranta har aka tashi, Sahnish ta Kira taji ya ɗauko Shazeen dan already an canza mata makaranta yanzu tun safe in ta tafi sai 5:30 suke tashi, nan ya shaida Mata gasu a hanya ma zasu shiga gida, hakan ya sa ta tsari abun hawa domin wucewa gidan itama.
Hanyar da sukabi jiya ta bi a ƙofar gidan wanna mutumin ta tsaya tare da ƙwanƙwasawa, wata yarinya ce ta fito suna haɗa ido da Hushaima ta zuba a guje ta koma cikin gidan tana Kiran umma, ƙofar shiga gidan Hushaima tabi da kallo sai ga wata babbar Mata ta fito ɗan nesa da Hushaima ta tsaya tare da faɗin, " Baiwar ALLAH lpy? Daga ina?".
"Lpy kalau dama wurin Mai gidan aka aiko ni ko yana nan?"........... Da sauri Matar ta ce, "Dan girman ALLAH kiyi hakuri m.........." Tarar ta tayi da faɗin, "Dama wasu kuɗi ne yayana ya bayar yace na kawo masa ".......... Ajiyar zuciya matar ta sauke amma daga ganin ta a tsorace take. "Tun da safe ya fita ai, yaje wata ma'aikata ne za'a masa interview to har yanzu kuma bai dawo ba"............" Tun karfe nawa ya fita ne?".
"Tun bakwai ne bama ta Ƙarasa cika ba gsky"............."Kuma bakuyi waya ba?"..........." Ai bashi da waya whl".......... ajiyar zuciya ta sauke da faɗin, "To ba damuwa in ya dawo zan dawo ". Ta ƙarashe tare da juyawa ta bar ƙofar gidan dan ta samu amsar tambayar ta.
-----------------------√
Yau kimanin kwana biyar kenan tunda ya Kai su Nayrah gidan nan, bai sake bi ta kansu ba amma yana bibiyar komai dake tafiya, ya kuma aika musu dasu Aram suna Kula dasu da kuma yi musu duk abinda suke da buqata.
Shigowa yayi cikin wani tangamemen office me matuƙar kyawu, bayansa wasu mutane ne suma sanye da suit black and white su huɗu sai cikon na biyar amma shi ya cire rigar suit ɗin sai white shirt ɗin kawai ya bari, kyakyawa ne dan colour skin ɗin sa colour ce me matuqar ɗaukan hankali wato shiny light brown, Yana da manyan idanu tare da hanci madaidaici, bakinsa light pink sai maiqo yake kamar ya shafa lipgloss, gashin kansa da yasha gyara me matuqar laushi kana gani kasan jinsin Hausa Fulani ne. Riqe yake da wasu files suna tafiya yanawa Amjad ɗin bayani, wanda yayi kamar hankalinsa baya kan mutumin amma kuma shi yake saurare har suka ƙarasa gaban table ɗin dake office ɗin, tsayawa yayi tare da zage zip ɗin rigar ledar da ya shigo da ita wadda ta rufe ko ina na jikin sa sai kansa kawai, ɗaya daga cikin wa'ancan huɗun ne ya sunkuya ya janye masa ita daga ƙafarsa sannan suka ja gefe suka tsaya, karbar files ɗin hannun mutumin yayi ya bubbuɗe ya duba sannan ya ce, "Hanash kamar yadda Ka saba tafiyar da komai ka cigaba a haka kawai, bana ma so wani yasan na shigo office ballantana kuma batun fitar da kaya, already tunda har anyi magana dasu da kuma adadin da zamu basu to made up the percentage ɗin da muke buqata as usual every year, yanzu ƙasashe uku ne damu a ƙasa kowanne zamu basu 30.33 million barrels kai ne a tsaye a kan komai, so sai ka Kula"............ Ya Ƙarashe yana zaro pen daga gaban aljihun sa ya buɗe murfin da bakin sa idanun sa akan paper yayi signing in da ake da buqatar signing ɗinsa sannan ya buga stamp ya miqa masa. Murmushi Hanash yayi yana kallon sa ya ce, "Ba abinda zai gagara ai ranka ya dade .........." Kasa ƙarasawa yayi saboda harara da Amjad ɗin ya aika masa, "In baza Ka iya Kiran sunan ba Ka barshi".
Shafa kansa yayi da faɗin, "Sorry sir ". Juyawa yayi ya nufi hanyar barin office ɗin ba tare da yace komai ba, da ɗan gudu gudu Hanash ya bishi yana faɗin, "Wait bros tsaya kaji mana". Dakatawa yayi da tafiya har ya karaso, kallon fuskar Amjad ɗin yayi tare da ɗan yin dariya, sake hararar sa Amjad yayi, "Zaka Faɗi abinda ke bakin Ka ne ko nayi tafiya ta".
Amjad da Hanash kusan abokan wasa ne dan tare suka taso saboda mahaifin Hanash shi ne babban abokin sirrin Dada duk wani sirri na Dada ya sani kuma duk wani harkar kasuwancin dada mahaifin hanash shi ke Ƙara bashi shawarwari da kuma abubuwan daya kamata. Sunyi zama na amana, Dada shi ya dau nauyin karatun Hanash har ya gama sannan ya buqaci mahaifin sa da ya shigo dashi cikin aikin kamar yadda shi ma a lokacin ya shigo da Amjad, sai ya zamana tasu tazo daya har zuwa lokacin da mahaifin Hanash ya faɗi ya mutu, ba ƙaramin jimama mutuwar mahaifin Hanash Dada yayi ba kafin daga baya ya sanya Hanash ya maye gurbi mahaifin nasa shi kuma Amjad ya maye nasa gurbin, saidai ya dinga taimaka musu da wasu abubuwan idan bukatar hakan ta taso har zuwa lokacin da wannan abun ya faru shi ma ya kwanta. WANNAN KENAN.
"Ai kai ne kaƙi tsayawa kaji, tunda kayi aure sai wani sha min kamshi kake ni ma fa zanyi auren nan yauwa"..........." Ta tabbata dai baza Ka faɗa abinda zaka faɗa ɗin ba kenan sai kayi halin naka".
"Tsaya zan faɗa". Ya faɗa Yana nutsuwa sannan ya ce, "Da gaske nima na kusa aure". Tsaki Amjad yaja zai cigaba da tafiya, Hanash ya ce, "Batun su ya Julaybin, ya za'ayi dasu idan sunzo karɓa kasan last week sun min magana tare da fadin akwai mutumin da zasu bawa 10 million barrels a shirya musu"............"Ka basu mugani in zai wuce"............ Da alamun rashin fahimta ya Ƙarasa wurin sa yana faɗin, "Ban gane ba kamar ya kenan?".
" A shirya musun kamar yadda suka buqata amma ni na ce ma ba abinda zai motsa daga nan, wancan kuma Dama mun gama maganar da kai, dan haka muje ka rakani na wuce ina da wurin zuwa".
"I trust you sir". Hanash ya faɗa tare da Sara masa yana dariya.
" ALLAH ya shiryeka Hanash ya kawo lokacin da zaka girma"......... Fadar Amjad Yana shigewa. "Eh mana ai dole zakace ALLAH ya kawo lokacin da zan girma tunda kai ka shige daga ciki kasan da........." Shuru yayi yana dariya saboda wani kallo me kama da harara da Amjad ɗin ke masa. " Ka cigaba da sakin baki dai, da mutane a bayanka sunajin wannan shirmen naka zasu rainaka dan su bani bane daka saba yiwa iya shege".......... ɗan satar kallon sauran ma'aikatan dake bayansu Hanash ɗin ya yi kafin ya ce, "Basuji ba ai".
Murmushi yayi tare da ɗan jijjiga kansa ba tare da ya sake cewa komai ba har suka fito zuwa gaban wani private jet ɗin dake fake a wani makeken fili a jikinsa an rubuta HASHIM DARWIN, daga nan sukayi sallama da Hanash ɗin ta hanyar hugging juna sannan ya miqawa sauran ma'aikatan nasu hannu ya juya ya shige jirgin yana gyara zaman suit ɗin sa, Saida suka ga tashin su suna ɗaga musu hannu sannan suka juya ciki.
A cikin wani filin da yafi wancan girma private jet ɗin ya sauka, fili ne babba gaba da baya sai wani tangamemen gini na Factory, wani irin dogon gini ne me matuƙar kyau da ɗaukan hankali, anan ya tarar dasu Kamal suna jiransa, yana saukowa suka rufa masa baya zuwa cikin ma'aikatar, nan fa kallo ya koma sama dan faɗar tsaruwar cikin ma ɓata baki ne, noes mask ya sanya sannan suka wuce ciki shi da wasu ma'aikatan da suka fito tarbarsa saida suka fara shiga wurin wasu engines wanda ke narkar da dunqulallun gold da kuma wanda ke yankawa tare da fitar da shape na irin sample ɗin da ake buqata, sai da ya gama zagayawa sannan suka fito, sun danyi tafiya kafin su isa wani bangare shi kuma duk glass ne zagaye da wurin ba bango na bulo ko ɗaya, sample ne na golds ɗin su na HD AURUM MINING iri iri a cikin glass cube suna juyawa da kansu sai ɗaukan ido suke, gaba kaɗan kuma bangaren diamonds ne da wasu irin precious gems masu matuƙar kyau, wurin ta ko ina ka juya kana ganin fuskarka saboda glasses ɗin dake ɗaukan ido ga wani irin sanyi da kamshi na musamman dake tashi, sai da ya gama duba komai sannan suka fita, wani bangaren suka sake nufa ko nace store domin danyen golds ne da diamond da kuma sauran precious gems amma ba gyararru bane, dan a duddunƙule suke ba ayi shaping dinsu ba, nan ma sun daɗe suna zagaye kafin su fita daga wanna bangaren su wuce bangaren ofisoshi, nan ma office ɗin sa dake Ma'aikatar ya nufa sannan yace a kawo masa duk wasu bayanai, bayan ya gama dubawa ya kalli Baba Hakim, dattijo Mai riqon Amana da gaskiya shi ya tsaya tsayin daka wurin ganin baiyi wasa da amanar da Dada ya danqa masa ba tun lokacin da suka fara wanna harkar lokacin da jajayen sawayen su.
"Amm Baba Hakim a duk wa'annan record ɗin dana duba Aurellon sultanate sun fi karɓar diamond fiye da kowani customer na mu kuma naga kamar masarauta ce, me sukeyi dashi? Suna kasuwancin sa ne?"........... Murmushi Baba Hakim yayi irin nasu na manya kafin ya ce, "Ai Amjad Aurellon sultanate su ne customer namu na farko tun lokacin da mahaifin Ka ya kafa wannan masana'antar, baka cika zuwa bane kafi neman a turama komai ta waya saisa ba lalle Ka san irin wa'annan abubuwan ba tunda abu ne da za'a rubuto, amma a yanzu da komai yake a gabanka ai gashi Ka gani, ba kasuwancin sa suke yi ba gini sukeyi dashi"........... Da mugun mamaki Amjad ya ce, "Gini kuma Baba Hakim?"............" Kwarai kuwa Amjad, ita wanna masarautar ai babu ta biyunta a duniya a dai ƙarfi, qawa da kuma mulki, suna da ƙarfin arziƙin da duk wata masarauta ta duniya bata isa tsayawa gaba da gaba da su ba, su ke nada duk wani sarki haka kuma suna d............" Ganin dogon tarihin da Baba Hakim yake son daukowa yasa Amjad yin dan Murmushi cikin son tsagaita maganar ya ce, "Baba gsky zanzo har gida Ka ban wanna labarin, Amma yanzu mu koma kan aikin dake gaban mu, naga kamar akwai mutane da yawa da suka biya ba'a basu kaya ba ".
"Eh ai kasan kaikace ba kamar da ba da za'a basu direct, hanya ɗaya ce damu ta sirrin daka buqata, saisa muka fi son a haɗa gabaɗaya yaso a aika musu a lokaci guda, hakan ma ba ƙaramar wahala yake bamu ba wurin lissafi".
Nisawa Amjad yayi kafin ya ce, "Na ɗan lokaci ne ai baba a Ƙara hakuri damu dai".........." Haka ne muna ta addu'a Amjad, ALLAH ya bayyana gsky ya kuma toni asirin su"............ Miqewa Amjad yayi da faɗin, "Ni inaga zan wuce saboda hanya".
"To ba damuwa muje na raka Ka, in sha ALLAH nima da aiki ya ɗan ragar min zan shigo na duba jikin alhaji Hashim ɗin "............" ALLAH ya kaimu ". Ya faɗa suna fita har wurin motocin dake pake ta bayan Factory ɗin Baba Hakim ya rakashi, sai da yaga tafiyar su sannan ya koma.
Ƙarfe biyar daidai suka iso, a wani irin gajiye yake jinsa, dan tun 6am suka fito amma ko ba komai ya rage wani aiki, direct Bluevielle ya basu umarnin zuwa dan tun ɗazu yake ganin Kiran Nayrah kuma yasan ƙorafin da zata masa kenan.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*