Author : Young Writer Category : Tknovels
kallo ne bare aje ga girman gidan da ya kasance kamar wata unguwar guda, wasu irin murtuka murtukan sojoji ne da ba kasafai ake ganin su ba sai a filin yaqi kowannen su riqe da manyan bindigu ba alamun Imani a tare dasu, ballatana Kuma daga ganin su ba musulmai bane, kansu ya sha sankwal sai kyalli yake cikin hasken fitilun da suka haske ilahirin gidan daga ciki har waje. Bayan an Bude musu gate ɗin suka shiga wata miqaqqiyar tafiya suka sake yi ko Ina ka kalla sojojin nan ne sai fama zazzare idanuwa suke.
Tun daga farkon shigowar ka zaka hango wani tsararren gini da baza ka taba kawowa a kasar nan kake ba, saboda yadda plan din gidan ya fito dakyau, bangare uku ne ɗaya gefen dama, ɗaya gefen hagu sai ɗayan dake tsakiya Amma Kuma a haɗe suke, saidai Kuma kowa yana da kofar shiga bangaren sa daga waje ba tare da ya bi ta bangaren ɗaya ba, haka Kuma in sunso zasu iya zuwa bangaren ɗayansu ba tare da sun fito waje ba.
Parking lot ɗin dake shaqe da wasu irin jibga jibgan motoci masu numfashi suka nufa, kafin ma kamal ya fito wani soja har ya buɗe masa kofar yana masa barka da zuwa, ba yabo ba fallasa ya amsa masa, kamar yadda fuskarsa take a ko da yaushe ita ba'a ɗaure ba ita Kuma ba a sake ba. Ƙarasowa sauran ma sukayi suna ta miqa masa gaisuwa, Sai da duk ya amsa musu sannan ya ce, "Fatan ba wata matsala?".
" No sir ba wani matsala"...... Ɗaya daga cikin su ya amsa. Dan daga kansa yayi alamar yayi, sannan ya juya ya wuce su Kuma suka rufa masa baya har gaban building ɗin, ƙofar dake right hand side ɗin sa ya nufa Wadda itama masu tsaron ta daban suke, nan ma gaisheshi suka shigayi ya amsa sannan ya wuce ciki shi ɗaya Yan rakiyar tasa Kuma suka juya domin komawa bakin aikin su.
Ciki ciki yayi sallama dan yasan ba lalle ya samun wani a falon ba, hakan ce kuwa ta kasance dan ba kowa sai wani makeken television Mai kamar cinema dake ta faman aiki shi kaɗai an rage volume gabaɗaya, qaton falo ne da ya cinye set din kujeru uku, faɗar kyawun falon nan sai wanda ya gani amma zan baku dama ku kiyasta shi a kwakwalwar ku kawai.
Wata hanya yabi data sake fitar dashi wani falon da yafi Wanda ya baro haduwa saidai bai kaishi girma ba. Saida ya wuce faluka huɗu sannan ya bayyana gaban wata kayatacciyar staircase, hawa yayi saman, nan ma bakowa sai ma'aikata dake ta Kai kawo domin tabbatar da tsabtar muhallin, a bakin wata kayatacciyar ƙofa ya tsaya tare da yin knocking kusan minti biyu ƙofar ta buɗe da kanta, sa Kai yayi ciki da sallama, wani shiryayyen bedroom ne da yaji kayan alatun more rayuwa, gaban gadon ya ƙarasa inda na hango wata kyakyawar dattijuwa zaune tare da wata yarinya da baza ta wuce 13 years ba, ita yarinyar na zaune a ƙasa kan Italian rug ɗin dake shimfiɗe a ɗakin ta miqe kafafunta ta tisa litattafai gaba, ita Kuma matar tana zaune a saman idanunta sanye da farin medicated glass da ya karawa fuskarta kyau gabanta laptop ce take yan latse latse a Kai, shigowar sa ya sasu ɗagowa gabaɗaya, wani sassanyan murmushi ne ya wanzu a fuskar dattijuwar lokacin da Amjad din ya ƙaraso gefen ta ya zauna. Hannu ta Kai ta shafa kumatun sa, " Babban mutum! yau Ina ka shiga tun safe ban ganka ba? Ka fita baka shigo ba".
"Kai Anah sai kace wani yaro, Kuma ma na shigo baki tashi ba ai saisa nace karsu Adla su tasheki".
"Good evening Uncle"........Dafa kan yarinyar yayi da fadin, "Evening baby girl, karatu ake tayi ne haka".
Anah ce ta ce, "To tashi kije wajen Adla ku ƙarasa karatun tare in da akwai inda baki gane ba ta nuna Miki"...........Da "to". ta amsa sannan ta tattare litattafan ta fita. Juyowa tayi gabaɗaya wurin sa da faɗin, " First of all kaci abinci tukunna?".........." Banci ba Anah, kuma ina shigowa naji wata yunwa whl"........Ya karashe yana karyar da kai gefe.
"Ja'iri, to baka san hanyar dinning ɗin bane ko kuma zuwa kayi ka faɗamin na tashi naje na ɗaibo ma".........."Ayyah Anah ni ne fa".
"Kai ɗin, ka ga dama ina neman ka amma tunda yunwa kakeji tashi ka fara zuwa ka ci abincin sai ka dawo muyi Maganar".
"Gsky Anah sai dai a kawo nan whl, na gaji da yawa ne yau". Bata sake cewa komai ba ta danna wani abu a gefen gadonta, ba'a rufa minti biyu ba akayi knocking, remote ɗin da ke gefen ta ta dauka ta danna ƙofar ta buɗe wata maid ce ta bayyana sanye da uniform black and white, cikin harshen turanci ta ce, "Gani mah".
"Ki kawowa babban mutum abinci"...... " Okay mah". Ta amsa tana ɗan duƙawa sannan ta juya ta fita.
"Naje gidan mommy dazu".......Ya faɗa bayan fitar maid ɗin.
"Mommyn, Mommy". Ta maimaita kamar bata gane ba. "Mommy Fareeha maman khadeejah"..........."Ohhkkk Allah sarki to ko kai fa Amjad, ka same su lpy?"......... Ɗan taɓe baki kana ya ce, "Hmmm, da sauki dai".
"Nasan komai Amjad, kuma daman nasan a yanzu sai mun kai zuciya nesa, ada can ma ya aka ƙare ballantana yanzu da suka samu abun faɗa, Amma ka cigaba da hakuri komai me wucewa ne, in sha ALLAH, ALLAH zai toni asirin duk wanda suka ma wanna sharrin, muna nan muna kaiwa ALLAH Kukan mu kuma ALLAH baya bacci".
Dan shuru yayi kafin ya ce, "Anah meysa baza a barsu da halinsu ba, kamar yadda kika ce kawai mu barwa ALLAH komai shi yasan daidai Amma karmu roqi ALLAH ya toni asirin su".
Wani irin kallo ta watsa masa Wanda ya sashi sunkuyar da kansa ƙasa. " Amjad k......." Kiran dayan shigo system ɗin ne ya hanata karasawa , video call ne daga wata number da akayi savings da Afia, miqa hannu yayi ya amsa kiran. Wata kyakyawar macece ta bayyana a screen ɗin tana zaune dauke da wani baby boy da bazai haura 2 years ba akan cinyarta, "heiiii babbabb....." Shi ne abinda yaron ya faɗa cikin gwarancinsa yana ɗago musu hannu.
"Hello my love". Amjad ɗin ya amsa shi ma yanawa screen din wani irin tausassan kallo. Murmushi Afia tayi wanda ya bayyana tsananin kamar ta da Anah, ta ce, " kai gauron uncle ya kamata kayi aure mu tarkatoma ya'yan Ka mu kawo ma, duk sun bi sun addabi mutan........" Kafin ta karasa maganar wasu yara su biyu suka yo kanta ɗaya ta kai ɗaya kuma ta gabanta kamar zasu shige cikin wayar, sai fama ihun Kiran Uncle Amjad, Uncle Amjad suke.
"To tunda bani aka Kira aji ba, Bari na kashe laptop ɗi na sai Ku neme shi ta wurinsa"....... Da sauri Afia ta ce, " Afwan Anah, ni kinga ba ruwana ai, ni uwata na Kira naji muryarta".
"Umm masu uwa manya, kefa an riga an daɗe da yayeki, ki daina wani Abu kamar wata auta". Amjad ya fada Yana harara ta. "Oho dai dadin ta Kai ma ba autan bane ai ranka ya dade".
"Ni kuwa ai kinsan ba ya ni, tunda Ku kuna da yauwa ni kuwa ni ɗaya ne".
"Kaji goɗoɗo dakai uban su wane kakan su wance ko kunya bakaji. Anah ALLAH ki dinga wa yaron nan faɗa ".
"Whl ki fita ido na Afy ni zaki haɗa da uwata, yanzu sai na Kira mijinki na faɗa masa dan halin da kika koyo, naji in yana da sa hannu a ciki"..........."Anah kina jinsa ko, Yana mantawa cewa ni yayar sa ce".
"Ku dai Kuka sani, kai Mai gidan haka zamuyi dakai wato ko nema na ma bakayi to m......"
Knocking ɗin da akayi ya tsayar da ita ɗagowa tayi tana kallon kofar da har Amjad ya ɗauki remote ɗin ya buɗe, maids ne su biyu suka shigo niqi niqi da warmers suka jera a kasa sannan suka fita. Sauka yayi ya zuba abincin ya fara ci, idan Afia ta tsokano shi kuma ya rama har ya gama sannan ya dauki gorar ruwa . "Anah ALLAH ku daina bashi abinci, in yayi zuciya yayi aure". Hannu ɗaya ya kai kan Laptop ɗin ɗayan kuma ya sanya gorar ruwa a ɗan karamin bakinsa yana sha, ganin yana shirin rufe laptop ɗin yasa Anah bige hannun da faɗin, "Meye hakan kuma?"......Saida ya cire gorar ruwan sannan ya ce, "to Anah bakya ganin tsokanata take ne".
"Au tsokanar ka ma nake, tsakani da ALLAH haka kawai ka dinga zuwa kana cinye musu abinci, Anah har yanzu yana nan da cin nan kamar gara ko". Baice komai ba ya koma ya zauna yana cigaba da shan ruwan kaɗan kaɗan amma idonsa akan screen ɗin.
"Kinga Afia ki bar mutumin nan in ba so kike yayi gaba da laptop ɗin ba".
"Anah ki korashi kawai yazo ya wani samu gaba muna magana, yauwa Anah ina su Esham da Adla ɗazu na kira Adla ban samu wayar ta ba".
Amjad daya miqe riqe da gorar ruwan sa ya ce, "An dai ji kunya. Anah dama fa kira tayi tace Miki ta kira Adla taji muryar ƴarta bata samu ba shi ne ta lalubo ki a rashin option".
Kafin Afia tace wani abu Anah ta ce, "To ina ruwanka".
"Ni kunga tafiya ta ma"....... Ya faɗa yana nufar kofar, Anah ta tsayar dashi ta hanyar kiransa, "ina zaka kuma bayan nace ma ina son magana dakai"........."To Anah ai naga kamar yanzun waya kike".
"Nop tsaya". Ta faɗa tana maida kanta ga screen din laptop din ta ce, "Afia bari zan kiraki back ɗan ban 10 minutes".
"To". Ta ce yayin da Anah kuma ta kashe kiran tare da ture laptop ɗin daga gabanta ma gabaɗaya. Dawowa yayi ya zauna shi ma yana fuskantar ta.
"Amjad! Miye matakin daka dauka akan wannan abun ko kuma miye matakin da kake kokarin dauka?".
"Anah ni fa ban aikata abinda suke fada ba, dan ALLAH ki kwantar da hankalin ki mana".
"Hankali na bazai taɓa kwanciya ba a cikin wannan halin da ake ciki Amjad, kuma sanin baka aikata ɗin ba ne yasa nake tunanin me zai hana ka shigar da ƙarar gidan radio da kuma televsion ɗin da suka wallafa wannan labaran ba, sannan su fito da wanda ya basu wannan labaran bogi da naso nayi Magana da Juraysh sai naga ya kamata na fara tuntubar ka".
Shiru yayi yana wani tunani kafin ya ce, " Anah a yanzu bamu da damar yin hakan saboda hukuma ta shigo cikin lamarin, yanzu gabaɗaya idon duniya ya dawo kai na da duk wani motsina, Al'umma gabaɗaya sun zubawa ƙasar Nifaz ido ne domin ganin iya gudun ruwan su, muna wani motsi zai zama qarin matsala, gwara mu bari su gama binciken a lokacin da suka tabbatar bani da laifi, mu kuma lokacin sai mu ɗaukaka namu ƙarar".
"Kai ɗin ba me laifi bane Amjad". Riqo hannuwanta yayi duka biyun cikin nasa yana hango tsananin damuwa dake cikin ƙwayar idonta ya ce, " Ban aikata ba Anah, kuma addu'ar ki itace kaɗai zata iya fiddani a halin da nake ciki ba wai damuwar ki ba, Anah ni kai na tafiya kawai nake amma a yanzu rashin lpyr Dada ma tafi komai ɗaga min hankali, ke kaɗai nake gani na danji karfi a jiki na".
Girgiza kanta tayi da faɗin, "ALLAH zai bayyana Gsky , kuma in sha ALLAH duk wanda ke son ganin bayan ka ba zai yi nasara ba saidai kai kaga bayan sa, kuma ALLAH sai ya wulakanta rayuwar sa".
"Ah ah Anah, Ni Bana son ganin bayan kowa ina so kawai ki roqa min ALLAH da ya kareni yasa nafi karfin duk wani mugu ya kuma bani nasara da Sa'a. Anah dukda an halatta wa wanda aka zalunta ya yi addu'a kan azzalumin daidai gwargwadon zaluncin, amma an fi so ayi haƙuri, a yafe kuma a nemi shiriya ga azzaluman, domin samun lada a wurin ALLAH. Saboda kamar yadda addu'ar alkhairi take dawowa haka mummuna".
Murmushi tayi tana kallon sa cike da so da ƙauna kafin ta ce, "Nagode da tunatar wa Amjad , ALLAH ya ma Albarka, ALLAH ya tsareka daga duk wani sharri ya baka sa'ar rayuwa".
"Ameen Anah tah ko ke fa, to yanzu ina iya tafiya? Dan inaso naje naga jikin Dada ne".
"Saura abu daya, batun yarinyar nan da iyayen ta".
"Anah wannan ai kotu ce zatayi aikin ta, kuma barrister Nazar zaiji da komai, karki damu in sha ALLAH ba wata matsala".
"Sauri kake kaje kaga Dadan ka ko? Sai sa kake ta yanke min zance". Yar dariya yayi yana shafa kansa tare da tashi ya ce, "barin je Anah".
"To, a fito lpy". Ta faɗa tana binsa da kallo mai cike da ƙauna da kuma tausayin ɗan nata na miji kwara ɗaya.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______5 & 6
Ko da ya fita ta cikin sashen nasu ya shiga bangaren mahaifin nasa. Kallo ne ya Koma sama domin komai na wanna bangaren linkin wancan ne ko ma nace yafi wancan. Sojoji ne tsaitsaye ta kowani angle na kofar sashen yadda ko sauro ne yayi ƙwaƙwaran kuka sai sun ji. wucewa yayi ciki inda ya tarar da wani mutum zaune yana waya, kallo daya zaka masa Ka tabbatar da ɗan uwansa ne saboda kammani na jini dan basa wani kama a yanayin halitta, yana ganin sa ya kashe wayar da fadin, " Dama kana garin nan Amjad?".
Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya ce, "Kai za'a tambaya ai Awais, an kusa sati biyu bamu hadu ba".
"Eh tou, abubuwan ne da yawa muyi nan muyi can, Gashi ka ga kai yanzu baka komai duk nauyin ya dawo kan mu, shi kuma Julaybin Abubuwa sun masa yawa, so mu ne dai tsaye Kan komai ni da Nuhail, yanzu ma cewa nayi bari na shigo naga jikin Dada, da ranar ba samun dama ake ba".
Murmushin gefen Baki yayi tare da wucewa yana fadin, "haka ne ALLAH ya taimaka "....... Ɗakin mahaifin sa ya nufa tare da tura ƙofar ya shiga da sallama. Wani dattijo mai kamala ne ya amsa yana ɗaurawa da, "Barka da zuwa yallabai".
Jingina yayi jikin kofar tare da fadin, "Baba Sufi baza ka daina kirana da yallabai ɗin nan ba , Ni fa kamar ɗan ka ne"........... Ya fada hankalin sa kan wani wuri, kallona na Kai Kan inda yafi bada hankalin nasa, wani dattijo na hango kwance Kan wani ƙayataccen gado idon sa akan Amjad ɗin dake tsaye. Takowa ya shigayi cikin sanyin jiki zuwa gaban gadon , yayin da wanda ya kira da Baba Sufi kuma ya miqe daga zaune da yake a bakin gadon yana ɗan murmushi ya ce, "Bari na dan zagaya, kafin ka fito"........Ya ƙarashe yana ficewa daga dakin.
Gaban gadon ya durkusa tare da dago hannun dattijon ya sanya cikin nasa ya Kai bakin sa ya bashi peck sannan ya ce, " Barka da Daren my hero."
Murmushi ya masa tare da lumshe idonsa ya buɗe wanda hakan ya sake bani mamaki shin baya magana ne.
"Dada na, yau baka ganni ba ko? Na fita tun sassafe ne sai yanzu na shigo"..........Kallon da mahaifin nasa yake masa me alamun tambaya ne ya sashi faɗin, "Naje yin wani Abu mai muhimmanci ne, sannan na ma je Wurin mommy Fareeha, kuma tace in gaishe Mata da Kai itama zata zo in sha ALLAH. Yau na gaji sosai Dada kai na har ciwo yake .........." Haka ya cigaba da bashi labarai yana masa hira amma duk wanna Abun ba umm bare um um, saidai in abu ya masa yayi murmushi in tambaya ce ya lumshe idanun sa ya bude, babu magana sannan ba inda ke motsi a jikin sa . Bashi ya bar ɗakin ba saida yayi bacci sannan ya gyara masa kwanciyar ya fita.
A falon ya samu Baba Sufi zaune shi kaɗai riqe da kofin shayi. "Baba Sufi kuma shi ne ka gudo nan kayi zaman ka".
"Ai cewa nayi bari na barku ku gana"........." Ina Awais?".........Amjad din ya tambaya yana bin falon da kallon.
"Ai ko dana fito ma ban sameshi anan ba Gsky, Maybe ya tafi ne ko kuma ya shiga wurin Hajiya"....... Ɗan shiru yayi kafin ya ce, " Shikenan Baba Sufi bari naje, sai da safe".
"To Allah ya tashemu lpy, Nima ina jira ne in Hajiyar ta shigo sai naje na kwanta".
"Ai ya ma yi bacci fa"..........Amjad ɗin ya faɗa yana zura hannun sa ɗaya a aljihu, ya nufi hanyar barin falon. Ɗakin sa ya wuce tare da zaro wayar sa ya kira Nayrah, tana ɗagawa ya ce , "Niniyous ykk"..........Ɓata rai tayi kamar yana gabanta ta ce, "Sai yanzu ne ka tuna Dani ko".
"Ke dai ba'a rasaki da ƙorafi, yanzu ne na samu zama ai".
"To naji, me kakeyi yanzu"..........Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce, "Me zanyi ninie, yanzu na shigo ɗaki na kwanta"........Jin tayi shiru ya sashi faɗin, "Tunanin me kike?".
"Tunanin ka "..........."Ni kuma? Me nayi da na hana zuciyar Ninie hutu ta shiga tunani na?"......... Ya faɗa yana juyawa ya kwanta akan cikinsa saɓanin da da yake reran, pillow ya janyo ya daura kansa akai tare da ɗaura wayar saman kunnen sa .
"Mumu ce ke fushi dani"..........cike da ƴar damuwa ya ce, "Saboda ni ne ko?".........Ɗaga masa kai tayi kamar yana gabanta kana ta ce, "ɗazu ne ta ji