BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   31 / 53

90K to 93K   out of 156.9K words

ka bar nan wajen ".......... Miqewa yayi a zabure tare da riqo tsintsiyar hannun ta da niyyar janta su bar wurin saidai ko gezau batayi ba wanda hakan ya bashi mamaki, wani irin kallo ta wurga masa sannan ta juya wurin mutumin ta ajje masa kuɗin a gefe, ta juya dan kanta ta bar wurin .

"Ya hakuri jiddu yarinyar ce batajin magana ko kaɗan".........." Ba damuwa Alhaji sai goben Amma dan ALLAH gobe karka zo da ita"..........." In Sha ALLAH yanzu ma hanya ce ta biyo da mu tare da ni kaɗai zanzo ai"............" To ba matsala a gaida gida, ALLAH ya Ƙara girma"............ Da "Ameen". Ya amsa sannan ya bi bayan Hushaima.

A kan kwanar layin su ya same ta tsaye tana ganin sa ta rufe shi da faɗa kamar uwar sa, shuru yayi kawai ya zuba mata ido karta tara masa idon mutane dan Sahnish ya faɗa masa idan ta hau tana masifar nan ba'a mata magana dan tana iyayin komai. Saida ta gama cikin ƙoƙarin danne bacin ransa ya ce, "Meysa kika hana na bashi kuɗi? Kin sanshi ne? Meye tsakanin ki dashi?"........... Tsaki taja sannan ta ce, "Kanka na rawa whl, to ka sani da na bari ka bashi kuɗin nan da hannunka da baka Ƙara 24 hours a duniya "........... Tana kaiwa nan tayi wucewar ta, zaro ido yayi da jin kalaman ta. Kamar wanda aka sassaqa haka ya ƙame a wurin yana nanata maganganun ta me take nufi ? Wata tambaya ce ta dawo masa, "Shin miye dalilin da yasa aka bada sunan sa ? Juyawa yayi ya kalli hanyar da suka baro sannan ya kalla kan layin nasu da sauri yabi bayan Hushaima, yana zuwa ɗakin sa ya shige ya fara haɗa duk wasu important abubuwan sa, jin Kiran sallar magriba ya sashi zuwa yayi alwala sannan ya wuce masallaci, bai shigo gidan ba sai goma na dare, ɗakin sa ya wuce tare da kulle ko ina ya rage haske sannan ya qule can ƙuryar ɗakin ya Kira waya kusan two missed call ba'a ɗaga ba, tsaki yaja tare da datse hakoransa cikin jin zafin Kiran da yayi ba'ayi picking ba, yunkurawa yayi da niyyar tashi Kira ya shigo wayar, kalla yayi ya ɗauke Kai tare da komawa ya zauna saida akayi missed call huɗu ana biyar ya ɗaga, da ga ɗayan bangaren akace, "Sorry widad ka Kira, wayan baya kusa dani ne ".

"Nima naga kiranka na fara wani aiki ne".......... Ya faɗa cike da iya shege, Murmushi Amjad yayi daga ɗayan bangaren ya ce, "Ya akayi to ?" .

"Na gama komai sai Abu ɗaya"............sai da Amjad ya nisa kafin ya ce, "Inajin ka"........... "batun samo dalilin da yasa aka bada sunan sa".......... katsesa yayi da faɗin, " ALLAH yasa Ka samo dalilin dan hakan zai taimaka mana akan aiki sosai". Girgiza kansa yayi kamar yana gabansa kafin ya gyara zama yana faɗin, "Ban samu ba amma zan ma rubuto ma wani text yanzu"..........." Wani text Kuma widad bayan gashi muna waya, let be serious plz".

"Game da case ɗin ne fa shi ma, in Ka duba ba sai ka kirani ba"........... Daga haka ya kashe wayar ya shiga rubuta masa message ɗin bayan ya gama ya tura masa, ya kashe wayar sannan ya tashi ya fita, ɗakin Hushaima ya nufa, a buɗe ya sameshi sai hayaniya ce ke tashi daga ciki, ita dasu bonbon ne suke ludo su biyar ne sai ihu suke idan ɗaya taci, bayyanar sa yasa sukayi tsit kamar ruwa ya cinye su, yar charas tayi ƙarfin halin faɗin, "Ya Jey sannu da zuwa ".......... hannu kawai ya ɗaga musu tare da faɗin, "ku dan jira a waje". Ba musu suka tashi suka fita, turmi ya ɗauko ya zauna yana dan sake fuskar sa ya ce, "Yau kuma ina kika kai Shazeen?".

"Tana ɗakin Sahnish ai, can na korata"..........."shi ne Kuma ba'a neme ni ba?"............" To Kai ba gashi ka kawo kanka ba"..........." Ummm dogaron ki Kenan saisa kika qi zuwa ko saboda kinsan dole zan biyo baya". Satar kallon sa tayi ta ƙasan ido sai dai ta makaro dan ya ganta, murmushi yayi da faɗin, "Ɗago ki kalla da kyau yadda ko a mafarki baza ki manta kamar ba"............" Ina Abun yake ?". Dariya yayi kamar bashi ba sannan ya ce, "kin rama 1/1, yauwa wata tambaya zan Miki Please, ɗazu meysa kika hana na bawa mutumin nan kuɗi da hannu na?".

Wani wuri ta ƙurawa ido kafin ta ce, "Meye haɗin ka dashi kai ?"............" Kawai muna mutunci ne sosai, so Ina ɗan taimaka masa kinsan yanayin rayuwa kuma dai ana tare tunda duk maqota muke"............"To Ka nisance shi da Kuma duk abinda zai sanya kayi hannu dashi". Ta ƙarashe tana juyo da kallonta kansa.

"Meysa kika ce haka? Yana da wata illa ne?" ............" Babba ma kuwa ".

"To ki faɗamin mana saboda na kiyaye"............" Abinda zan iya faɗa ma kawai kayi nesa dashi ". Shuru yayi cikin ɗaurewar Kai, sha'anin Hushaima na ɗaya daga cikin abinda ke bashi ciwon Kai a yan kwanakin nan, can Kuma ya ce, "Hushaima zan sake Miki wasu yan tambayoyi, ba Kuma zan Miki hakan bane dan ranki ya ɓaci ki gayamin gsky dan ALLAH, Hushaima wacece ke Ina nufi background dinki? Miye asalin ki? Ina iyayen ki? Meysa kuke rayuwa haka shin ba dangi in ma ba iyaye?"........... Ya karashe a ɗarare saboda yasan halin birkitacciyar saidai da mamakin sa sai yaga tayi ɗan Murmushi da faɗin, "Shegu ne"............"shegu Kuma? ". Dariya ya kwashe da ita saboda yadda ta fadi kalmar, sosai yayi dariya kafin ya ce, "Please be serious mana".

Kallon data watsa masa ya sashi faɗin, " Sorry Amma ki bar batun wasa, kuma bakyau, be kamata ki sheganta kanki da kanki ba".........." Baka yarda ba ko, to da gaske nake ma bamu da iyaye haka muka buɗi ido muka tsinci kan mu a duniyar mu"............"kenan ku ba Yan uwan juna bane?"

"Tsakanina da Sahnish shekara ɗaya ne "........." Kamar ya bangane ba?"............" Mu bar zancen nan Jey zuciya na ya fara ɓaci, Dan ALLAH ". Numfashi ya fitar Yana sake kallon ta yayin da ta ɗauke Kai daga garesa. Shuru yayi yana kallonta shi kaɗai yasan saƙe saƙen da yake, sun daɗe zaune a haka kafin ya zaro kuɗi daga aljihun sa masu yawa ya miqa Mata, "Ga wanna Hushaima nasan zaki buqace su".......... yanayin yadda yayi Maganar yasa ta ɗan waiwayo suka haɗa ido, a sanyaye tayi ƙasa da nata tare da karɓa ta ce, "Mun gode sosai Jey, ALLAH ya Kara arziki"........... Da "Ameen". Ya amsa sannan ya miqe da niyyar fita har yaje bakin kofa ya juyo suka sake haɗa ido, kusan second 60 sannan ya juya ya fita, ɗakin Sahnish ya nufa, shi ma bai wani daɗe ba ya bashi kudi sannan ya masa saida safe ya koma ɗakin sa.

Yadda Jey bai rintsa ba haka Hushaima kowa da abinda yake yi, shi Jey aikin gaban sa yake haɗawa ita kuma Hushaima tunanika ne suka Mata yawa. A Kan kunnen Jey Hushaima ta fito ɗiban ruwa da asuba, Miqewa yayi tare da ɗaukan jakar sa ya saɓa a baya, a jikin window ya tsaya yana kallon ta harta gama ɗiban ruwan, har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo tana kallon ƙofar ɗakin nasa, kaucewa yayi daga jikin window har sai da yaga ta shige sannan ya buɗe ƙofar a hankali ya fito ya nufi soron ƙofar gidan yana tafiya a hankali kamar wani ɓarawo har ya Ƙarasa ya buɗe kofar ya fice sannan ya maida ya rufe.



-----------------------√



Lokacin da driver yaje wa Mumu da batun wani yazo ya tafi dasu Nashwa harda sojoji, kwashe shi tayi da mari ba tare data duba dattijantakar sa ba, "Kai baka da hankali ne, akan idon Ka aka tafi da ya'yan nawa Ka kasa Kira Ka sanar min ko Ka sanarwa alhaji, shi ne Ka kwaso ƙafa yanzu kazo kake faɗamin dan baka data ido, to whl Ka jira Ka gani sai ka yiwa yan sanda bayani "............. Jiki na rawa Baba jamilu ya durƙusa Yana bawa Mumu haƙuri, Amma kwata kwata bata saurare shi ba sai ma ɗaga waya da tayi ta kira yan sanda ta sanar musu abinda Ake ciki, sannan ta cigaba da zazzaga masa har saida yan sandan suka ƙaraso, "Officer gashi nan, Ku tafi dashi har sai ya faɗa muku inda ya'ya'na suke, Dashi aka haɗa baki aka ɗauke su, yanzu zamu biyo baya in alhaji ya dawo"............"karki damu ranki ya daɗe, zamuje dashi muyi bincike kafin ku iso".

"Shikenan Nagode, sai mun ƙaraso"........... Haka aka tisa ƙeyar Baba jamilu aka wuce dashi, Sai a lokaci ta Kira Dad wanda yaje sadakar bakwai na Farshad, tana sanar masa hankali tashe yace gashi nan zuwa, bai ɗau lokaci ba ya karaso har yana cin tuntuɓe a ƙofar shigowa garin sauri, "Garin ya haka ta faru hajiya Latifa?"..........." To Alhaji ni ai bana wajen dama na aika Nashwa da breakfast ne sai nasa Malam jamilu ya kaita a zuwan in Ka dawo daga wurin sadakar sai muje, to shi ne kuma yanzu Malam jamilun ya dawo yana sanar min wai wasu mutane da sojoji sunje sun tafi da Nayrah da Nashwa, to na Kira yan sanda sun tafi dashi nace sai munzo tukunna"............."Dauko ɗauko gyalen ki maza, mu fara zuwa asibitin tukunna "......... Ya faɗa yana juyawa ya ficewa da sauri, itama Mumu wucewa tayi ɗaki ta ɗauko gyalenta ta fito suka wuce Hospital ɗin.

Suna shiga office ɗin Dr suka nufa, riqo wuyan rigarsa Dad yayi a fusace ya ce, "Kai tsohon munafuki ina ya'ya'na suke?"..........." Haba Alhaji menene hakan, Ka sake ni mana wanna ba halin manya bane fa ".......... Dr ya faɗa ba wani alamun damuwa a tare dashi, wato abinda ya kamata mutane su gane in ana ganin mutuncin ka Karka yadda ka ɓata wannan kallon a idon mutanan dake mutuntaka, ku dai duba girman Dad da kuma muqaman da ya riqe, amma kace nace ɗin da sukeyi yau da gobe a cikin asibitin ya zubar musu da mutunci.

"Idan na kaika lahira acan saika faɗi halin manyan mutanen, nace ina ya'ya'na suke? wato dama daku ake haɗa baki ana ɗauke ya'yan mutane ko, okay bayan jariran da kuke ɓatarwa yanzu kuma kun koma kan manya ko".

" To Ka sake in ma bayani mana".........." Baza a sake Ka ba"......... Dad ya faɗa kamar zai Kai masa duka, Mumu ce ta ce, "Ya hakuri Alhaji barshi muji me zai faɗa". Sakin sa dad yayi ba ɗan yaso ba sai dan baya iyawa Mumu musu. " Ina ya'yan mu suke ?". Mumu ta tambaya. Gyara zaman rigar sa yayi da faɗin, " Mijinta yazo ya tafi da ita mana".

Kallon Dad Mumu tayi shima ya kalle ta . " Wani mijin nata, mijin da yake garƙame hannun hukuma ".......... Dad ya faɗa ba tare da tunanin yanzu duk abinda ya shafi Amjad ya shafe su bane tunda yana auren yar'su.

"Alhaji Amjad Hashim Darwin, Ka tambayi kowa a asibitin nan Shi yazo da kansa ya tafi dasu "............." Okay kenan Kai ma yaron sa ne, to sai Ka nuna min inda ya'ya'na suke don ubanka ".......... Dad ya faɗa yana kaiwa Dr naushi, nan fa faɗa ya kaure daƙyar securities suka banɓare Dad sukayi waje dashi, a fusace Mumu ta ce, "Ka jirayi sammaci, zaka amsa Kiran kotu dan sai munyi kararka".......... Murmushi Dr yayi da faɗin, "Ba damuwa hajiya a kowani lokaci a shirye nake in sha ALLAH". Kwafa Mumu taja sannan tabi bayan mutanan da suka lallaɓa dad sukayi waje dashi. Kaii Jama'a Dad dan bala'i ne.


________________Haka take a bangaren su Awais labarin da ya iske su shi ya gusar da farin cikin da suka kwana dashi. Kira Nuhail ya samu inda ake shaida masa cewa lalle fa an saki Amjad ya koma gida .........." Ban gane an saki Amjad ba, kasan me kake fada kuwa?"..........." Ranka ya dade ban Kira Ka ba saida na samu tabbacin abinda nake faɗa, an sake sa tun a jiyan da daddaren amma an haɗashi da jami'ai su tsare shi har sai an tabbatar da zargin da ake masa ".

Ajiyar zuciya Nuhail ya sauke kafin ya ce, "Har Ka firgita zuciya ta Raska, yanzu ya mutanan nan kuna dai tsare dasu har yanzu ko?"..........." Ai ranka ya daɗe ba wasa suna nan an killace su"..........." To ba damuwa in da wata matsalar Ka sanar dani, yanzu zan ɗan amsa wata wayar". Bai Jira amsar Raska ba ya kashe tare da Kiran Awais dan yasan Julaybin mutum ne me uzururruka ba kasafai Ake kiransa a waya a same shi ba ko da kuwa maganar urgently ne. Bayan Awais ya ɗaga Nuhail bai saurari gaisuwar da yake masa na ya tashi lpy ba ya ce, "Awais Ka Sami labarin an sako wancan tsinannan?".......... Ba tare da wata damuwa ba Awais ya ce, "Ban samu labari ba, Amma me ya faru?".........." Ya zakace mun me ya faru, Kai nama ji kamar Baka damu ba"..........." To nuhail ai dama kasan baza su rike shi ba akan laifin da bai aikata ba in dai har sunyi binciken gsky, ni fa dama a jiya kwana nayi da tunani in dai har aka riqe Amjad, to whl da gaske yana aikatawa kawai faɗuwa ce tazo daidai da zama, ba wai qagen da muka masa bane, saisa ma abun ya dameni Amma yanzu faɗa min ɗin nan da kayi yasa nasan to lalle akan kaiɗin mu yake tafiya, Dan haka muje next sai menene kuma?".

Shuru Nuhail yayi yana digesting ɗin maganar Awais dan kwata kwata shi tunanin sa bai ma Kai nan ba, jin Awais yana hello hello ne ya sashi faɗin, "Amma fa Awais kanka na ja kasan kwata kwata ni banyi wanna tunanin ba in fact nama mance da cewa wai mu muka ƙirƙira kawai na tafi a zuwan cewa ya aika ne"............"hahahaha". Awais yayi wata dariya me cike da Alfahri kana ya ce, "To yanzu ya Ake ciki?".

" Eh sun sake shi ɗin Amma wai sun haɗa shi da jami'ai, wai dan Kada ya gudu har sai an tabbatar da hakane ko ba haka ba"..........."To yanzu duk ba wanna ba kayi magana da Julaybin, ya sukayi da mutumin ya kamata ace munyi komai da zafin nama kafin a gama bincike a gano gsky ya kamata ace zuwa wanna lokacin ma'aikatar mu ta tsaya da ƙafarta sannan mu rushe batun Duk wani Abu na Dada a duniya sai muga miye dogaron nasa, tunda dama kaga already batun AURUM COMPANY sun tsaya saboda babu kasuwa, kaga dai komai na Dada ya fara tashi aiki sai mu kuma sunan mu ya fara yawo a iska yana zaga duniya, shi kuma kaga ko da ma an wanke shi ba kowa bane fa zai yarda dashi daga nan komai zai sake tsaya masa cak".

"Wato in na tuna wanna Abu yana bani nishadi Awais, yanzu in na gama da gida zanje na sameshi dan kasan shi ba'a cika samun sa a waya ba "..........."To hakan yayi karkayi sanyi Nima zuwa anjima in rana ta fito zan leqa gidan wurin su hajiya na jiyo meke tafiya a can".......... Da haka sukayi sallama sannan kowa ya kashe.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd SultyWrites22



STEP 1



PAGE _______43 & 44


Washe gari kamar yadda suka saba bayan ta gama dafa musu jallof ɗin spaghetti a yar ƙaraman stove ɗin da Jey ya siya musu, ta zubawa Sahnish da Shazeen sannan ta zubawa Jey nasa ta fita dan kai masa, gaisawa sukayi da mutanan gidan data samu a filin tsakar gidan nasu sannan ta Ƙarasa ƙofar ɗakin Jey ɗin, saidai da mamakin ta ƙofar a rufe, ɗan bubbugawa tayi amma shuru Aunty Barma dake wanke wanke bakin rijiya ta ce , "Tity anya kuwa yau Jawaad na nan, dan tunda na fito yau ƙofar nan a rufe na ganta "............. Ɗan shuru tayi tana kallon ƙofar kafin ta ce, "Aunty Barma Anya kuwa? ko dai bacci ne ya ɗauke shi har ya makara"........... Ta ƙarashe tana sake doka ƙofar da karfi, buɗewa ƙofar tayi wanda yayi sanadiyyar hantsilawar ta cikin ɗakin saboda ta saki jiki sosai, kwanun data zubo abincin ya zube mata a jiki, saidai ko takan zafin ƙonuwar da tayi batabi ba saboda tashin hankalin data tsinci kanta a ciki na lura da babu Jey babu kayan sa, ƙarasa shiga tayi ta fara daddage tarkacen da ya bari, ganin da gaske fa babu shi babu alamar sa bare kayansa ya sata fita da gudu tana Kiran sunan mama Atine wato matar Baba ilerika ta farko, fitowa mama Atine tayi daga ɗaki sanye da Kaya daban daban, riga daban zani daban an kai shi har ƙirji, dankwalin nan a gaban goshi take faɗin, "Tity meke faruwa irin wanna Kira da fara kainar safiya?"......... Riqo kafaɗunta tayi a ɗan rikice ta shiga tambayar, "Ina Baba ilerika"............"Ashsha, zancen banza, yoooo wanna kuma da yawo kamar yaci ƙafar kare, ai kema kinsan ba kullum yake kwana gida ba tunda raba mana kwanan yake da yan tasha, Hala wani kuɗin ya cinye miki ?"............. Ɗan dafe kanta tayi ba tare data bawa mama Atine amsa ba ta yi waje tana warware ɗan kwalin kanta, dan sanye take da doguwar rigar

31 / 53