Author : Young Writer Category : Tknovels
ido ba, gsky Amjad ya kamata ace kana daurewa kana leqowa kullum duk da yanzu kayi aure ka ware kanka, amma Ka san mahaifin Ka fa ba Wanda ya fi shaquwa dashi kamarka, kaga ɗazu da aka gwada jininsa ya hau sosai whl".
Cikin yar damuwa ya ce, "Amma Anah bata faɗamin ba"............."Eh to ai ba lalle ta gaya ma ba maybe bata so ta tada ma hankali ne, ko kuma itama ɗin bata sani ba tunda ba leqowa take ba idan mugun halin ya motsa. Wai saboda kwana na ne sai tace baza ta shigo ba, Yo mutumin ma da bashi da lpy har wani kwana za'a raba"........... Ta gefen ido ya kalle ta sarai yasan Hajiya zunaira na yar tsama da mahaifiyar su amma fa su duk ɗaya ne a wurin ta, dan bata nuna masu banbanci tsakanin su da su Julaybin ɗin data Haifa kawai dai ita matsalarta ta kishin da takeyi da mahaifiyar su ne, kuma a wurin ta hakan bai shafi yaran ba. Saidai tana sane da zazzafar ƙiyayyar dake tsakanin su Julaybin ɗin da su Amma ta nuna ita ba ruwan ta ba kuma abinda ya shafe ta bane, faɗa ne na yan uwa ita miye nata dan haka Ko su Julaybin ɗin zasu kashe su binne a gabanta baza ta ce musu ci Kanku ba kawai dai ita baza tace suyi ba ko su bari duk yadda sukayi can ta matse musu, haka kuma da ace shi kansa Amjad ɗin zaizo gabanta yayi zancen cewa su Julaybin ɗin sun masa kaza ko sai ya rama ko yace shi ma zai aikata musu wani abun, to fa ba zata ce masa kanzil ba in ya iya allon sa ya wanke.
"Yanzu dai hajiya ki dubamin ko bacci yake"
............. "Haba Amjad Kai da mahaifin Ka ai ba mai ma iyaka dashi kaje Ka duba in idon sa biyu to, Dan ni tun dazu ina nan ina wani Abu ne ban shiga ɗakin ba da zan fito dai na barshi yana bacci"......... A Nutse ya ce, " To Hajiya in yana buqatar wani abu fa kinga ai ba yadda zaiyi ya Kira wani yace ya masa ko, ke kuma kina nan ai baki sani ba"......... Dan buga tsakiyar kanta tayi da hannu tana juyawa ta wuce cikin falon tana faɗin, " Abin ne ai da gajiya Amjad kuma ragon azanci nayi da ban tsaida Sufi ba tunda dama shi yake zama kusa dashi "..........Takaicin da ya kamashi shi ya hanashi magana, abinda Anah sa baza ta taɓa yi ba kenan, bata taɓa nuna gajiyawa da Dadan su ba tunda abun nan ya faru, dan haka baice komai ba ya wuce ɗakin, a hankali ya tura ƙofar ya shiga ɗakin so quiet bakajin komai sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki Wadda ta gauraya da room freshener take bada wani cool sanyi, a hankali ya taka zuwa gaban gadon sai a lokacin ya lura idon mahaifin nasa biyu zama yayi gefen sa fuskar sa na wanzar da wani murmushi Wanda ya fito daga can cikin zuciyar sa, dan Amjad bayan Anah ba wanda yake so sama da mahaifin sa saboda shi ne first friend ɗinsa a duniya, riqo hannun sa yayi cikin nasa kana ya ce, " Dada kaci abinci kuwa?"........ Da ido ya amsa masa da eh. "kanajin ƙishi?"......... Ya sake tambaya, nan ma da idon ya masa alamar ah ah . "To akwai abinda kake buqata?"......... alama ya masa da babu, numfashi ya sauke a hankali sannan ya ce, " Dada sirikar Ka na gaishe Ka, kuma Dada kasan me? na siyo ma ostrich daga US, suna nan ina maka kiwon su a gida na, amma akwai wani me faɗa a cikin su ni dai da nace kawai zan bayar dashi, sai yai ta bin Ninie da gudu ita kuma tsoron su take tayi ta ihu, rannan ina wanka Dada naji ihun ta na ɗauka wani Abu ne ya faru kawai ina fitowa na gansu har tsakiyar ɗaki ta dale Kan gado tana ta zunduma ihu".......... Dariya Dada yayi har saida hakwaran sa suka bayyana, Murmushi yayi shi ma cikin jin dadi ya sake damqe hannun Dadan cikin nasa ya ce, "Dada akwai wani abu da nake so Ka min addu'a akai ALLAH yasa nayi nasara".......... Da ido ya masa alamar zaiyi nasara kuma yana masa addu'a. Miqewa yayi tare da rungume Dada daga kwancen da yake yayi kissing ɗin hannunsu dake cikin na juna ya ce, " Zan tafi Dada bana so Ka dinga damuwa dan baka ganni ba akwai abubuwan da suka sakoni gaba da yawa Amma inaso Ka dinga Ji a ranka ina lpy matukar Kana min addu'a. Yanzu dai na kunna ma TV ko zakayi bacci?"......... Alama ya masa da zaiyi bacci dan dama yana cikin baccin yayi mafarkin Amjad ɗin shine farkawar da yayi, yanzu kuma da ya ganshi hankalin sa ya kwanta. Gyara masa kwanciya Amjad yayi sannan ya rage masa gudun AC ya juya ya fita zaune ya samu hajiya Zunaira ta kishingiɗa ta harde tana goga screen ɗin waya tana kora lemu alamar bata da wata damuwa, sallama ya Mata tace ya gaishe da Nayrah sannan ya fice.
Yana fita direct gidan sa da su Philip suke ya nufa, Yana shiga ya tarar dasu Ashely gabaɗayansu wanda isowarsu kenan a Daren, bayan sun gaggaisa Ace ya ce, "Tun ɗazu muke jiranka ka shanya mu kana can kana tsinkar fure".......... Murmushin da bai yi niyya bane ya ƙwace masa ya ɗago yana kallon Philip dan yasan shi ya sanar musu, sunkuyar da kai Philip yayi yana ɗan shafa kai. Maganar Ace ta katse shi, cikin serious tone ya ce, "To yanzu dai kasan bamu da time ɗin da zamu ɓata, ya kamata ace munyi komai mun gama"............ Ƙarasawa yayi ya zauna yana ɗan satar kallon Widad ko nace Jey da ya hakimce sai wani taunar chewgum yake kamar mace, "Ya Ake ciki ? Fatan komai ya kammala?"........... Ashley ta ce , "Yes mutanen da suka buqata duk sun kammala, so yanzu miye next?"........... "Amm abinda za'ayi Next shi ne zamu tuntuɓe su, su faɗa mana inda za'a Kai mutanan da inda zamu karɓa cikon kuɗin anan ne zamu kafa musu tarkon farko"......... Sauqe ƙafar da ya ɗaura Kan ɗayar Widad yayi tare da faɗin, "Bafa tarko muke neman kafa musu ba, saboda Kai kasan da tarko ne da wancan mutumin BB LALO shi zamu kama, to amma ko mun kamashi bashi da wani info da zai bamu akan Shadow saboda shi ma bai san waye shi ba, abinda ya kamata shi ne tunda yanzu mun tsallake first step, bincike zamuyi na ganin taya Ake shigar da mutane garin ba tare da sanin gomnatin su ba, waye kuma wanda ya ke isar dasu ga shadow ɗin".
Dukkansu sun bashi full attention nasu suna sauraron sa har ya gama sannan Kiara ta ce, "Yes binciken da ya kamata muyi kenan, yaso idan muka haɗa musu tarko da mutanan dake wurin mu, sai mu kama Wanda dama munsan bamu da haufi zai jagorance mu zuwa wurin shadow ɗin"........... Nisawa Amjad yayi yana me aminta da shawarar su dan yasan clique ɗin nasa duk zaqaƙurai ne kuma akwai sharp brain saisa baya da haufi a kan kowannen su, sai kawai ya ce, "Ina so kowa daga cikin mu yayi nasa binciken ya kuma samo wa'annan amsoshin within 24 hours"...........Tashi duk sukayi suka masu sallama wuce ɗakin su da already Philip ya nuna musu masaukin da aka gyara musu a cikin gidan, Dan kamar yadda kuka sani Ace da Ashely ba yan ƙasar bane aiki ne yake haɗasu, Ashley mutumiyar UK ce yayinda Ace kuma ya kasance mutumin Italy, Kiara kuwa tafiyar awanni ma a mota zata iya kaita garin su kawai dai tana bakin aiki ne. Falon ya rage daga Philip dake tsaye sai Widad da Amjad da duk suka tafi kurman tunani, can Amjad ya ɗago ya kalli Philip tare da tambayar. "Akwai wani abun ne?" .
"Eh Boss batun yaron nan da aka kashe kamar yadda kace muyi bincike, wanda suka kasheshi suna da hannu a hatsarin da Madam ta samu, Amma ga file na bayanan da muka tattara". Ya fada Yana miqa masa, karɓa yayi ya duba sai da ya gama ya saki wani one side smiling da yafi kama dana takaici, ɗan jijjiga kansa yayi tare da biting lips ɗinsa sannan ya rufe file ɗin ya ajje gefen sa. "Sai me kuma?". Ya sake tambaya ba tare da ya bar wata alama ta halin da yake ciki ba akan fuskarsa.
"Sai batun yarinyar nan Boss, ban samu wani bayani Kan ahalin ta ba domin duk wani bayani da za'aban saidai a bani akan su ukun, unfortunately babu info akan abinda ya shafi dangi ko mahaifanta, sannan kuma bata da haɗi da mahaifin madam haka kuma su Hajj zawaad kawai friend ɗin yar sa ce sai dai........." Ɗan shuru yayi yana murza maganar da zai faɗa a bakin sa, ƙureshi da idon da Amjad ɗin yayi ne ya sashi furta, " Sai dai akwai boyayyar alaqa tsakanin ta da Oga Awais"......... Slowly ya maida kansa jikin headrest ɗin tare da rufe idanun sa na wasu minutes hannun sa ya Kai fuskarsa ya shafa sannan ya Buɗe idanun, tunanin sa kenan yarinyar karuwa ce tunda shi kaɗai yasan waye Awais da kuma wanna boyayyar halayyar tasa ta neman Mata wadda yakeyi a boye to Amma.......... katse tunanin yayi tare da kallon Philip tin kafin yayi magana ya juya ya fice dawo da kallonsa yayi Kan Jey da hankalinsa ke kan wayar dake hannun sa ga ɗan bakin nan dake motsi cikin salo me jan hankali, takaici ne ya sake kumeshi dukda ƙoƙarin kauda kansa da yake sai da ya yi magana. "Haba mana widad ". Ɗagowa yayi Yana yin kwai da chew gum ɗin dake bakin sa cikin wani salo ya riqe Kwan da gefen baki kana ya ce. "Ya ne?".
"Please Ka daina wanna abun mana ba daɗi, Kai ta chin chew gum sai kace karuwa "..........Ya faɗa Yana kallon Jey ɗin a yatsine kamar yaga wani abun kyankyami saboda a duniya in akwai abinda Amjad ya tsana bai wuce yaga anacin chew gum ba. Hannuwan sa biyu ya ɗaga tare da faɗin, "Is okay, yanzu akwai sauran wani Abu ne?"...........Sai da ya maka masa harara kafin ya ce, "Baka samu wani haske Kan mutumin naka ba ?".......... Yar nutsuwa yayi cikin wanna maqalalliyar murya tasa Mai kama da an masa dole ya ce, " Babu wani abu special a tare dashi saiii da........" Abinda ya faru na ranar da Hushaima ta hanashi karɓar kuɗi a hannun sa ne ya dawo masa to amma ya zaice da Amjad, taya zai sako Hushaima a aikin nasu bayan babu wanna tsarin infact sai ma Amjad ɗin ya raina shi yace zuwa yayi yana kula mata . "Sai dai me?" Amjad ɗin ya tambaya.
"Zan sake bincikawa"..........." Shikenan ba damuwa, zaka tafi ne ko anan zaka kwana?"........ Girgiza kansa yayi alamar ah ah tare da miqewa ya ce, "zanzo da safe in sha ALLAH".........." ALLAH ya kaimu ". Amjad ya faɗa shi ma yana tarkata file ɗin ya ɗauka ya wuce ɗakinsa.
------------------√
Ko da ta tashi yau bata bi ta Kan Sahnish ba ta dai shiga da asuba kamar yadda ta saba ta tarar dashi yana sallah, tun daga nan bata sake bi ta kansa ba saida suka gama shirin su da Shazeen suka fito sannan ta wuce dan miqa masa abun Karin sa, saidai da mamakin ta ƙofar ɗakin nasa a rufe, Meenakshi ce ta ce, "Ai Sahnish ya kusa minti ashirin da barin gidan nan"......... takaici ya sata faɗin, "To yawa kansa bari na nemi almajiri na bashi"....... Da sauri Meenakshi ta ce, "Wani almajiri in dai ku bakwa da buqata kawoshi nan"......... Dama ba wani Abu bane Heinz beans ne da bread Wanda Awais ya Mata shopping ɗin su jiya sai tea data dafa ta haɗa masu dashi, miqa Mata tayi tare da faɗin, "In kin gama ki barmin kwanun a wurinki in na dawo zan karɓa". Daga haka taja hannun Shazeen suka fice. A makaranta ta ajjeta kamar yadda suka saba sannan ta wuce wurin aikin ta.
Wuraren 11:30 am Awais ya kirata ɗauka tayi tana sakin murya bayan sun gaisa ya ce, "ki na gida ne?".......... "A'a ina wurin aiki". Ta bashi amsa Kai tsaye. Ɗan shuru yayi kafin ya ce , " wurin aikin da nisa ne? Ina ne? ".......... Yayi tambayar a haɗe, faɗa masa tayi ya ce, "To ai ina kusa da layin ma, ki fito ina son ganin Ki, ina layin da yake kallon inda kika tari abun hawa kusan magriba ranar da muka fara haɗuwa to layin zaki shigo ki ɗanyi tafiya kaɗan zaki ga motata pake, saboda nan ɗin kamar unguwata ce inada mutane sosai a wurin"......... Ba tare da wani tunani ba ta ce, "Okey, gani Nan".......... Ta faɗa kana ta kashe ta zaro powder dake jakarta ta sake shafawa, ta sake murza oil perfume a gaggauce ta maida kayan jaka ta fito, ta leqa domin ta sanarwa Hajiya zataje ta karɓo saqo ta dawo ta tarar bata nan reception ta wuce tare da faɗin, "Am Jumayma zan fita nan bakin layi na karɓo saqo ba nisa zan ba, na leqa na sanarwa hajiya kuma na tarar bata nan".
A wulakance Jumayma ta ce, "Baki da ikon fita sai tazo ki tambayeta da kanki tunda ai bani na ɗauke ki aiki ba"........." Dake kurkuku na shigo? To sai na fita kuma na riga na sanar Miki tunda kince bake kika ɗaukeni aiki ba kinga Baki da ikon hana ni fita ai"......... Tana kai wa nan ta sa Kai tayi waje, kwafa Jumayma taja sannan ta cigaba da ayyukan ta tana shirya abinda zata faɗawa Hajiya idan ta riga Hushaima shigowa.
A inda ya faɗa mata anan ta same shi wurin ba kowa saboda sabuwar unguwa ce yanzu ake gine gine a layin, buɗe Mata ƙofar baya yayi ta ɗayan side ɗin, tana zuwa ba ɓata lokaci ta shige tare da rufewa, fita zubairu yayi ya bar musu motar a kunne saboda AC wani gini ya shige saboda Kar ma mutane suzo wucewa su ganshi su fara cika duk da ba Awais ɗin suka gani ba amma sun san duk inda Awais yake to fa Zubairu yana nan, gashi kuma ya riga ya ɓata mutanan da raba musu kuɗi a duk lokacin da ya shigo.
Wani Mayen kallo yake binta dashi har saida ta gaishe shi sau biyu baiji ba, haɗa yatsunta tayi a saitin fuskarsa suka bada sauti sai lokacin ya dawo nutsuwar sa, murmushi yayi da faɗin, "Gsky ke din me kyau ce Hushaima".........." Na Saba jin wannan ai Alaaaji na".......... Wani ƙayataccen murmushi ya saki saboda yadda zuciyar sa take wani yarr yarr a duk lokacin data kirashi da Alajin ta ɗin nan, gashi yadda take furtawa da wani irin salo. "A gsky naji daɗin yadda kikayi saurin bani matsayi a zuciyar ki".......... Wani farr tayi da idanuwan nan nata masu rikita bawa tare da faɗin, "Ko nayi gaggawa ne ?"......... Harda datse harshe wurin saurin amsa ta da, "Ina ina naji dai daɗin wanna matsayin a wurin kyakyawa, zinariya, ɗawisuya kamar ki, ".........." Kai Alaaaji wai sai kace yau Ka fara ganin me kyau, Ku ai kun saba Hulɗa da turawa, labarawa, Indiyawa to kuma wani kyau ne zai ruɗe Ku".
"Kyau kyau ne Amma kyan Hushaima daban yake, zan so na mallaki wanna kyakyawar halittar cikin gida na ni kaɗai in dinga kalla ina jin daɗi"......... Ɗagowa tayi ta zuba masa idanuwan nan nata tana kallon cikin kwayar idonsa direct har cikin zuciyar sa wanda hakan yasa shi faɗin, "Kiyi hakuri ƙwalisata ki daina min irin wanna kallon dan baki san ya nake ji bane a duk lokacin da kika zubamin wa'annan idanuwan naki masu haske gabana har faɗuwa yake, a dinga tausaya min mana"......... ya ƙarashe yana ɗan kwantar da kai gefe, murmushi ta ɗanyi tare da ɗauke kanta ta rasa meysa mutane basa so ta ringa kallon su wanna shi ne Karo na ba adadi da ake faɗa mata haka, ba ga Matan ba ba ga Mazan ba ta rasa miye aibun idanunta.
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Alaji muje Kai tsaye Kan abinda yasa Ka nemi mu haɗu bayan kuma jiya da daddare muka rabu, dan banyi tsammanin kiran ka ba a irin wannan lokacin".
"To yanzu laifi ne dan na buqaci ganin masoyiya? Kuma dai ba wannan ba Magana ta gsky son ki nake Kuma ina so ne muyi aure, dan haka ki Bani dama na zanta da mahaifin ki"......... Kai tsaye ta ce, "Ban shirya aure ba".
Wani ɓoyayyen murmushi ya saki dan dama ya san komai gami da ita kawai latsi ne irin nasu na yan duniya dan haka ya ce, "To yanzu ya kike so
Ayi?"........."Duk yadda kace". Ta bashi amsa kai tsaye idanunta akan window tana bin layin da kallo.
"Zaki iya amsa gayyata ta zuwa guest house ɗina yau da daddare?".
"Yayi wuri da yawa dan har yanzu ba wai na gama sanin Ka bane gabaɗaya, dan ku sanannu ne ba hakan ke nuna baku da ɓoyayyen hali ba, na sani ma ko kana yankan Kai ne Ka kaini gidanka Ka ciremin ido ko wani sassa na jiki na ka kaiwa dodon tsafin ku"........ Dariya wawan yayi sosai saboda yadda tayi Magana tsakanin ta da ALLAH amma shi sai ta bashi dariya, dan haka ya ce, "Dama kina tsoro ?".
"Ahh Alaji rayuwar nan fa ɗaya ce, kuma daga ita sai mutuwa, sannan ba'a mutuwa a dawo, tsoro akwai inda yake da kyau akwai inda bashi da kyau, kamar yadda Ka faɗa hasashen Ka gsky ne bani da tsoro, amma a inda nasan zan iya kare kai na, ba wai kawai dan na yarda da kai na bazan yi waiwaye ba in ina tafiya".
Jinjina Kai yayi a lokacin data gama maganar sannan ya ce, "Amma meysa kika ce haka ?"......... kai tsaye ta ce, "Baka sauraren labarai ne, ai yanzu abinda ke faruwa kenan saboda da kunga shukar da babu Mai ita