BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   38 / 53

111K to 114K   out of 156.9K words

fito daga ɗaki ai, na manta ban faɗawa masu girkin nan abun da zasu girka da breakfast bane, Ya surukar tawa?"
.........Ta faɗa tana ƙarasawa cikin falo ta zauna a ɗaya daga cikin expensive cushion ɗin dake falon, a gefen ta ya zauna tare da ɗaura kansa Kan kafaɗarta yana kallon fuskarta.

"Um um Kai fa yanzu ba yaro bane karkazo Ka kassara min kafaɗu, kaje can kayiwa matar taka, ni yanzu na yaye ka, ace mutum sai san jiki da shagwaɓa kamar wani yaro ( ni kuwa nace ummu mu faɗa Miki waye Amjad a waje ko mu bari duniya ta sanar Miki).

"Anahhhh please mana". Ya faɗa a shagwabe. "To naji gyara zaman ka muyi magana ".......... Ɗan zakuɗawa yayi amma bai tashi ba, pillow ta ɗauka ta buga masa aka tana faɗin, "Zauna daidai nace ma, haba cikin daren ma sai ka sani surutu"....... Tashi yayi gabaɗaya tare da sauka ƙasa ya tankwashe ƙafafuwan sa a gabanta Yana kallon ta, wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Anah ALLAH ya gani tana mutuwar son Amjad duk cikin ya'yan ta, ko dan Shi kaɗaine namiji.

"Anah !"........... Ya Kiran sunan ta a tausashe ganin ta lula wata duniya . "Anah meysa kike sa damuwa sosai a ranki na faɗa miki in sha ALLAH babu abinda zai faru sai alheri, Amma in ina ganinki cikin damuwa to ni ma fa ba zan sami nutsuwa ba".

"Dole na damu Amjad, bazan ɓoye ma ba kullum da Kai nake kwana a rai nake tashi, abin nan yana tsoratani matuka baka da laifi amma meysa za'a dinga jan wani bincike, an takuraka da yauwa Amjad baka da sakewa kamar na da, baka da sakewa a cikin Al ummar ƙasarka, kuma ance baka isa fita wata ƙasar ba, kana cikin gidan Ka ana tsaron Ka a ƙofar gida, wanna wace irin rayuwa ce".

"Anah na Miki alqawari tunda bani da laifi duk daran daɗewa gaskiya zatayi halin ta, kuma ke kinsan da ace ina da laifi da tuni yanzu ba wanna zancen ake ba tunda magana ake ta duniya gabaɗaya kuma kinsan basa bincika abu sau biyu saboda cigaban su in ma mu nan suna ta jeka ka dawo ".......... Da wa'annan kamalan yayi amfani ya samu ya kwantar Mata da hankali sannan ya ce , "kotu fa ta sanya neman mutanan nan, saboda an zauna babu su ba wani tsayaye nasu, dama kuma can su ba lauya bane dasu".

"Kasan ni ma lokacin nan saida nasa Juraysh ya min bincike a kansu amma ba wani labari game dasu an ce su gudu, to Amma Kai ya akayi kasan sun gudu tun a lokacin daka faɗamin, Anya Amjad baka san wani Abu a Kai ba kuwa?"........ Yar dariya yayi da faɗin, "Anah gsky kin fiya rigima kema yanzu har juraysh kika sa bincike, fisabilillahi me ya haɗa sojan ruwa da bincike, ko da ke barin yi shiru, amma dai ya akayi kuma bai binciko sun ba"............. "Kai Bana son wasan banza wai ni kakar Ka ce da zaka sani gaba da tsokana".

Haɗa hannuwansa yayi wuri ɗaya alamar ban haƙuri sannan ya ce, "Ya hakuri Anah ta ba tsokanar ki nake ba, kawai dai ina mamaki na yadda kike sanya juraysh a aikin da yake nasa da wanda yake ba nasa ba. Amma Anah meysa kike tunanin ko inada masaniya a Kai, Anah whl ni ba ruwana kawai dai ina predicting abu ne tun kafin ya faru, nasan basu da hujjar da zasu bayar dama burin su su yaɗawa duniya ne to kuma sun yaɗa, kuma sunsan kotu zata Hukunta mutanen ne idan har ta kama su da laifin ƙarya da ƙazafi, whl Anah marar gaskiya ko a ruwa gumi yake ni nasan tabbas hakan ce zata faru kuma gashi hakan ne ya faru"........... Ita dai Anah kallon sa kawai take har ya gama bayanin sa sannan ta ce, "Ka dage da addu'a Amjad, ta ko ina Ka haɗa makiya da bansan me Ka tare musu a duniya ba, dan in a san ransu ne basu kaunar su buɗi ido su ga kana takawa a doron ƙasa. Abu na biyu Ka Kula da matar Ka Nayrah, dan ita ɗin amanar Ka ce, ban samu na kebance dakai ba ranar da Kuka zo amma inaso na faɗa ma duk rintsi duk wuya ka Kula da yarinyar nan, tayi ma halacci kuma itace irin matar da kowani namiji zai yiwa kansa fatan samu, a lokacin da kowa ke kyarar Ka ita kuma a lokacin ta nuna ma ƙauna, ta zaɓe Ka Wanda har hakan ya zama silar da iyayenta suka juya Mata baya, a yanzu Kai ne kaɗai hope ɗin ta, ina Mai Ƙara jaddada ma Ka Kula da ita"......... Muryar sa ce ta Ƙara yin sanyi akan ainahin yadda take, tunani ya shiga yi na yadda zai ainahin raba kansa biyu, yana cikin wanna tunanin maganarta ta dawo dashi, "Ka tashi kaje kaga dare yayi kuma Ka barta ita kaɗai, da ka sani ma ai ka bari sai da safe kazo ".

ALLAH sarki Anah ita ta ɗauka gida zai koma, to bari dai na kame baki na kar Agent Amjad yaji ni.

"To Anah Amma zan shiga naga Dada Dan inaso mu dan tattauna"..........Ya faɗa while a zuciyar sa kuwa cewa yake dole Ku min uzuri Anah. Ita kuwa Anah mamakin Amjad ɗin take yadda baya taɓa gajiya da tattaunawa da mahaifin nasa wanda shi tsakanin sa dashi ji ne kawai da ido, Amma sai ta ce, " Toh ALLAH ya tsare Ka gaida Nayrah ɗin in kaje". Ta faɗa tana miqewa, tashi yayi shi ma sai da ya rakata har ɗaki sannan ya Mata saida safe ya fito.



---------------------√



AURELLON SULTANATE💎



Cike makekiyar fadar take da duk wasu masu matsayi a masarautar tun daga Kan Mai martaba Sultan zuwa Kan hakiman North da south east da west wanda suka kasance ƙanne a wurinsa zuwa kan sauran yan uwan nasa, sai kuma su wazir, imam wato limamin fada, sai khaleep Wanda ya kasance kamar sarkin musulmin masarautar gabaɗaya, sai Amirul bahr wato kwamandan ruwa, sai Qadi Mai jagorantar shari'a a cikin masarautar, sannan Hajib Mai tsaron kofa kenan shi ne babban jami'in Sultan me kuma kula da shige da ficen mutane da kuma tsare tsaren fada, sai wali wato mai Kula da yankin masarautar, sai aminul Darb shi ku ma mai kula da dukiyar masarauta da muhimman hanyoyi na kasuwanci, sai katib wato sakatare kuma marubucin masarauta shi ke da alhakin rubuce rubuce na hukuma, wasiku da kuma dokoki da Adana bayanan gomnati, sannan Amirul jaysh wato commandan sojoji na masarautar, sai sheikhal balad shi ke da alhakin Samar da tsaro na gida da bin dokokin masarauta da kuma Kula da tsaftar masarautar, da dai sauran su dan idan nace zan tsaya lissafo dukka mutanan fadar nan to fa zamu shafe Babi biyu ba'a gama ba saboda suna da yawa sosai.

Wazir ne yayi gyaran murya tare da gyara mic ɗin dake maqale a rigarsa domin sautin maganar sa ya isa ga dukkan mutanan fadar cikin harshen larabci ya fara magana, " Assalatu wassalamu ala Nabiyyul Kareem, Assalamu alaikum ya ayyuhal mu'minin, ina muku barka da halattar wanna taro na gaggawa da aka kira, kamar yadda Kuka sani a yan kwanakin da suka wuce Maleekh Reeslan ya fita da mutanan sa domin shaqatawa, sai kuma aka Kai masa farmakin bazata Wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin mutanan mu".......... Dakatawa yayi kaɗan sannan ya cigaba, "To kamar yadda Kuka sani ne babu wanda zai mana hakan face mutanan SWORD OF FIRE KINGDOM, kuma hakan ce ta tabbata gashi nan kuji daga bakin waziril bahas (ministan bincike)".

Gyara zama Babil yayi tare da buɗe takardun dake gaban sa sannan ya soma magana kamar haka. "kamar yadda muka tsaya tsayin daka muka tabbatar munyi sahinhin bincike tabbas mutanan sword of fire ne suka kai wa su Maleekh hari, kuma ba kowa bane ya jagoranci wannan harin bazatar face li'iliti Anoosha, domin ko da suka kashe mutanen mu saida sukabi sahun Maleekh ɗin domin su far masa shi ma, ALLAH Bai basu sa'a sun gan shi ba"..........Waziri ne ya ƙarɓa da faɗin, "Tabbas ya kamata ace abinda suka aikata bai tafi a banza ba, domin hakan na nufin har yanzu Queen Hirut fa tana Kan bakar ta ne, kuma tunda suka fara bi ta Kan Maleekh to tabbas gobe Sultan zasu hara".

Take Yan surutai suka fara tashi cikin fadar, Gyaran murya Sultan yayi take fadar ta ɗau dumi kowa yayi tsit ana sauraren sa. Magana ya fara kamar haka, "Ni inaga a aika musu da wasiqa ta neman qarin bayani, dalili da kuma tuba, haɗe da neman gafara daga su zuwa wanna masarauta"............ " ALLAH ya taimaki Sultan ya Ƙara lpy, maganar Ka bata da ta biyu amma ni a tawa shawarar wanna harin da gangan suka Kai Shi, kuma wanna bashi bane na farko amma duk muna ɗaga musu ƙafa, nan gaba bamu san abinda zasu aikata gare mu ba ya Sultan, inaga kawai mu ma mu rama dan su san shuru shuru fa ba tsoro bane "......... Yana Kai nan yayi shuru.

Qadi ne ya karɓi zancen da faɗin, " Wazir ni inaga abinda Sultan ya faɗa shi ya kamata a aikata, a fara aika masu da wasiqar tukunna raddin su shi zai bamu amsar hukuncin da zamu dauka ".......... Da wanna kowa yayi na'am sannan aka rufe taro da addu'a, kowa ya tashi ya koma kan aikinsa sai mutanan fada dake zama tare da Sultan.

Fitowa Reeslan da Rouslan sukayi daga cikin fadar suna sanye da Kaya iri ɗaya haka gashin kansu da ya sha gyara sai ɗaukan ido yake ɗaure a bayan ƙeyar su sun saki jelar ta sauka har gadon bayansu. Rouslan ne ya ce, "Yanzu gashi Ka taso mu munfito idan Abbu ya neme mu fa?"......... Ya faɗa grey piercing eyes ɗin sa akan Reeslan ɗin. Taɓe Baki Reeslan yayi da faɗin, " Sai Ka koma ka zauna ai tunda ba riqe ka nayi ba, amma ni dai bazan iya wanna zaman jimamin ba, zuciyata zata iya tsayawa, ni yanzu ma Zanje naga Hirtik ne in zaka muje in baza Ka ba ka wuce muje in kaika gida". Ya ƙarashe idonsa na yawo akan wani bafade da yake kallon su ta ƙasan ido, da sauri ya kauda kansa ganin Reeslan ya tsaida idanunsa akansa saidai ya makara.

"Kai zo"......... Ya fada sharply. Cikin faɗuwar gaban abinda zai faru Rouslan ya ce, " Kai da wa kuma ........." Saboda yadda yaji muryarsa ta sauya a lokaci guda. Saidai kafin ya rufe bakinsa ma Reeslan ya wuce wurin wanna bafaden da jikinsa ya fara ƙerma cikin faɗa faɗa ya ce, "Ƙasa"............ rikicewar da yayi yasa bai ma san Reeslan ɗin ya ƙaraso gabansa ba har sai da ya tsinkayo Maganar sa, jiki na rawa ya durƙusa tare da buɗe baki da niyyar bashi hakuri ya buga masa guiwar ƙafarsa a haɓa, ji kake gab hakwaransa sun haɗu da juna, Bai bari ya gama dawowa hayyacin sa ba ya kifa masa wani wawan mari, da sauri Rouslan da ya iso wurinsu ya riqe hannun kana ya ce, " Kayi hakuri mana Habiby, muje Please" .........." Rabu dani Rouh, kallon bakin mu yake muna magana saboda ya ji abinda zamu faɗa yayi munafurci to duk kar nake kallon ku".

"Dan ALLAH Habiby ya isa, Muje kawai"..........."Whl bai isa ba, Ka bari in fidda masa hakora tukunna".......... Da yawan fadawan fadar suna kallo amma basu da damar ko ɗaga ido saboda kowa yasan tashin hankalin Reeslan. Akeem da yazo shiga fadar ya tarar da Reeslan na bala'i Rouslan na tausarsa ya sashi fitowa da sauri ya nufo wurin su, "Khali Rouslan meke faruwa ne?".

Dawo da kallonsa yayi kan Akeem ɗin yana huci ya ce, "Ina ruwan Ka ne? Kai kuma sakeni tunda ba mahaukaci bane ni".......... Ya ƙarashe yana fisgewa daga riqon da Rouslan ya masa, tausa murya Akeem yayi kana ya ce, "ALLAH ya baka haƙuri khalee, dama wai dan naga ranka a ɓace ne shi ne na tambaya "..........Tsaki yaja kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce inda motar su take. Ɗauke ido Rouslan yayi daga kansa bayan ya wuce tare da ɗan buga goshinsa kaɗan da hannu saboda kansa da ya ji ya wani mugun Sara masa, cikin ƙarfin hali ya ce, "Ƙar ka damu Akeem, wani abu ne ya ɓata masa rai, je ka kayi uzurin da ya kawo ka, bari na ƙarasa".

"In sha ALLAH ni ma anjima zan shigo wurin ummu ai"........." Ba damuwa sai kazo"...... Rouslan ɗin ya faɗa ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake ba.

Yana shiga motar Reeslan ya fisge ta kamar zai tashi sama. "Kar kace ban gaya ma ba amma kaga wannan shegen yaron Akeem daga shi har kakarsa ina tausayawa ranar da zan waiwayo su".......... Kallon sa Rouslan kawai yake kafin ya ce, "Kaiiiiii Habiby! Kakarsa fa uwa take a garemu saboda matar mahaifin mu ce, ka daina faɗar haka".......... Wani sharp look ya wurga masa na seconds kafin ya ɗauke kansa ya maida kan titi ba tare da ya sake cewa komai ba, shi kuma Rouslan ɗin ya cigaba da faɗin, "Bai kamata ace kana irin haka ba habiby, kai kenan ba wanda ya tsallake zagi ko zargi a wurinka kowa munafuki ne kowa ɗan iska ne, Ni gsky bana jin daɗin haka kuma Akeem ɗin nan, ɗan ka ne tunda ɗan babbar yayar ka ne".......... Ɗan jijjiga kansa yayi kafin ya ce, " Kaga Rouh, baka san komai ba kayi shiru kawai"............ " Ba wani abinda ban sani ba duk abinda ka sani na sanshi".

Iska ya furzar daga bakinsa yana ɗan bugar kan steering motar ya ce, "Akwai ranar qin dillanci, Ranar da kowa zai san SIRRIN ƁOYE. Komai yana da rana ko da yake tana da jinkiri"............ Zuba masa idanu kawai yayi, yayinda shi kuwa ya maida hankali kan tuqinsa hankali kwance kamar bashi yayi maganar ba, jan bakinsa Rouslan yayi ya tsuke ganin maganganun na neman fin ƙarfin tunanin sa, sai kawai ya jingina kansa dake masa ciwo jikin headrest har suka ƙarasa gida. Sauka Rouslan yayi Lokacin da aka buɗe masu ƙofar tare da leqowa ta window ya ce, "Take care of yourself, Karka daɗe". Bai jira amsar sa ba ya yi saurin juyawa ya wuce saboda wani sarawa da kansa yayi ba kuma ya son Reeslan ɗin ya gane saboda zai iya fasa zuwa ganin farin cikin sa wato Hirtik.

Da kallo yabi Rouslan ɗin har ya kusa shigewa part ɗin kawai ya buɗe motar ya fito, taku ɗaya biyu yayi ya cin masa dan Reeslan ba dai zafin nama ba, tsayawa Rouslan yayi tare da faɗin, "A'a ka fasa tafiyar ne ?". Bai bashi amsa ba sai shigewa ciki da yayi hakan yasa shi ma ya rufa masa baya cikin dauriya yake faɗin, "Magana fa nake ma"........... Ganin yadda hankalin hadimai ya dawo kansu inda suka fara zubewa suna miqa musu gaisuwa yasa Rouslan yin shuru tare da ɗaga musu hannu ya cigaba da bin Reeslan da ko arziƙin kallo basu samu daga wurin sa ba.

A falo na biyu suka tarar da su Albeena da kuma su Hibba, step sisters ɗinsu. Sannu da zuwa suka musu, Rouslan ya amsa musu sama sama saboda ciwon kan dake damunsa, Albeena baki abun magana cikin zumuɗi ta ce, "Yauwa ya Reesla........" Bai barta ta ƙarasa ba ya katsa Mata wata tsawa, "Ke karki dameni kinji"........ ba ita kaɗai ba dukkan su saida suka sha jinin jikinsu. "Kai kuma wuce muje Ka huta"......... ya faɗa calmly kamar bashi yayi tsawa yanzu ba, duk da Rouslan ɗin bai faɗa masa ya gane cewa baya jin daɗi saboda duk motsin Rouslan, Reeslan na sane dashi haka shi ma Reeslan ɗin duk motsin Rouslan yana sane dashi ba dan karkuce wani abu ba da sai na iya cewa daidai da bugun zuciya ɗayansu in ta sauya suna ji a jikinsu.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1


PAGE _______ 53



Ko da ya wuce bangaren Dada, a ƙofar falon sa na ciki ya tsaya tare da yin knocking, daga ciki Hajiya Zunaira ta ce, " Waye ne cikin daren nan?"........... Ba tare da ya bata amsa ba ya sake knocking, "Waye wai?" ........... Ta sake tambaya still baiyi magana ba kuma bashi da niyyar yi ɗin sai ma agogon hannun sa da yake ta dubawa alamar a qage yake. Tasowa tayi ta leqa ta peephole, kasancewar falon ba haske sosai yasa bata gane shi bane dan ya sunkuyar da kansa ne yana duba wayarsa, a ɗan fusace ta buɗe ƙofar tana faɗin, " Wai wannan wani irin iska........" Maganarta ta katse saboda idonta da ya sauka akan Amjad da ya ƙarasa tura ƙofar baya ya shigo cikin wani low deep voice ya ce. "I'm ".

Matsawa tayi baya kana ta ce, "Amjad kai ne kuma inata magana kayi shuru"........."Ni ne hajiya ai banason na ɗaga murya ne ban sani ba ko Dada yayi bacci ba daɗi a tashe Shi".

"Haba Kai kuwa ko yayi bacci ai zaiyi farin ciki ga duk Wanda ya tashehi ya ganka, yau kusan kwana biyu kenan fa bai saka a

38 / 53