BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   33 / 53

96K to 99K   out of 156.9K words

A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️




___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd Sultywrites22



STEP 1



PAGE _______45 & 46




Tsaye take a ƙofar gidan misalin 11pm tana kallon mutanan gidan nasu da su lokacin ne ranar su ta fara, sun ƙure kiɗa akan layin, masu rawa nayi, masu ƙarawa sama hazo nayi, masu fira nayin tasu masu zance da samari nayi, masu cinikin abinci nayi, masu poker nayi kowa dai da abinda yakeyi, in banda hayaniya ba abinda ke tashi yadda kasan tasha ko kasuwa.

Bata cika fitowa a irin wanna lokacin ba saboda baccin ta ma take kwanciya tayi, amma gabaɗaya yanzu zaman ɗakin zafi yake mata, tunani daban daban ne suke kawowa ƙwaƙwalwarta farmaki a duk lokacin data kaɗaice ga Jey da har lokacin tana jinsa a ƙasan zuciyarta, dan yanzu ma har ta kwanta bacci ta ƙasa, shi ne ta tashi ta fito domin ta samu sukunin abinda ya dameta. Sanye take da Palazzo peach colour sai armless T shirt milk mai matuƙar taushi, kanta yane da wani yalolon ƙaramin gyale, gefen ta kuwa Mahrazu ne abokin su Wulu sai wani ƙoƙobarewa yake yana magana shi a dole nigga, ita kuwa sam ma hankalinta baya kansa kamar ma bata san da wanzuwar mutum a wurin ba ta tafi wani tunanin daban.

Wani irin taku sukaji kamar za'a girgije ƙasa, ga wata ƙura data taso kai kace girgizar ƙasa za'ayi, kafin kace me mutane sun fara gudun ceton rai, sai ihu wasu na faɗin ya'juj wa ma'juj ne suka bayyana, wasu na faɗin zaizayar ƙasa za'ayi, tsabar bala'i wasu ta cikin murhu suka dinga bi wasu ta cikin Kwanun Mai, wanda suka bugu sukayi maƙil kuwa ƙwata suka shige, gabaɗaya wurin ya hargitse karo kawai kake ganin anayi duk wanda ya faɗi kuwa ta kan ruwan cikinsa ake bi. Ita dai Hushaima kaucewa kawai tayi ta bawa masu gudu hanya dan Kar ayi gaba da ita, amma ita ko a jikinta ba ma alamar wani tashin hankali a tattare da ita dan sai taga abinda ya ture rawanin buzu, komawa tayi ta jingina da wata ƙaramar katanga dake jikin dakalin nasu wadda tayi kamar makari. Raba ido ta shiga yi daga gabas zuwa yamma, wasu ingarman giwaye ne suka sawo Kai kan layin suna tafiya suna ihu tare da dage dogon bakin nan nasu sama, sai da suka zo daidai saitin ta suka tsaya, kallo Hushaima ta Kai kan mutanan dake kan Giwayen maza ne sanye da wasu irin kaya kamar na fata dukkan su fuskar su ba alamun imani a tattare dasu, wuyansu sarkafe da sword tare da archery, dawo da kallon ta tayi kan Giwar da take sahun farko wadda ta banbanta da wa'ancan tun daga kan ado, wani irin faɗuwa gaban ta yayi wanda bata taɓa jin irin sa ba har saida ta motsa daga jinginar da tayi, daidai lokacin matashiyar budurwar ta juyo bangaren Hushaiman idonta ya sauka akanta, sanye take da dogon wando da riga marar hannu na Cashmere goat, rigar ta sauka har Kan cinyoyinta amma a yanke take daga both side haka ma ta gaba, kanta ba ko dankwali sai long brown curly hair ɗinta da ta ɗan kama rabi a tsakiya sauran duk ya sauko kan kyakyawar fuskarta, ƙafarta Kuma sanye da wani boot me kyau, dirƙo wa tayi ƙasa still idanunta akan Hushaima ta tako zuwa gabanta tana binta da wani irin kallo me wuyar fassarawa, ita ma Hushaima baki buɗe take kallon ta ganin irin fuskarta a jikin wanna budurwar, a tare suka Kai kallo jikin su wanda shi kaɗai ne kawai ya banbanta su shi ma ba wani da yawa ba, kawai dai Hushaima zata ɗan fi wancan cika ne da kaɗan, Amma bacin hakan komai nasu iri ɗaya, kalar skin ɗin su, doguwar fuskar su, wannan kwayar idanun tasu masu rikita marassa gsky kai harda masu gskyr ma, sirancin karar hancin su, dan brown lips ɗin su duk irin ɗaya.

Da hannu yarinyar take nuna Hushaima kamar tana so tayi magana sai Kuma ta juya da sauri ta kama giwar ta ɗale kamar wata tsuntsuwa, su ma sauran mutanen da suka sauko ganin ta sauko suka koma tare da motsa giwayen nasu suka fara tafiya kaɗan kaɗan har suka bar layin, ita dai Hushaima ta ƙasa yarda da abinda idon ta ya gane mata shin ko dai ta zautu ne? Dafe kanta tayi da dukkan hannayenta saboda yadda yayi wani irin masifar sarawa, Nishin da taji ne ya sata sauke hannun data riqe kan nata dashi, a Hankali ta juyo tare da fira ƙafarta ta bi inda take jin nishin tana zuwa taga kamar mutum raɓe, Bismillah tayi tare da Kai hannu ta ɗan tabo shi, ɗagowa yayi wanda hakan ya tabbatar mata da mutum ne kamar yadda tayi tunani. Fari ne tass kamar ka taɓa jini ya fito, yana da dogon hanci kamar an zana da biro, haka dark red lips ɗin sa wanɗanda ke zagaye da wani kwantaccen baƙin saje tare da tsararren gashin baki da ya ƙara ƙawata fuskar tasa, kallonta yake da grey piercing eyes ɗin sa da suke nan kamar ya sanya musu kwalli amma in ka lura da kyau zaka san natural ne ba wai kwallin bane, haka gashin girarsa dana idanunsa kamar zasuyi magana, uwa uba gashin kansa da ya wani baje har fuskar sa kasancewar sa me tsayi da laushi haɗi da santsi.

Ɗan ja baya Hushaima tayi tana sake ƙare masa kallo dan bata taɓa zaton ganin irin wanna halittar anan wurin ba, ganin sa dafe da kafaɗar sa ga jini da ya bata yellow t shirt ɗin jikinsa ya sa cikin tausayawa ta ce, "Sannu kaji ciwo ne ?"............ Sai dai a maimakon ya bata amsa sai ya dafa bangon ya miqe, still hannunsa dafe da kafaɗar tasa dake zubda jini. Ganin sai ya kalli hanya ya kalleta kamar me son tantance wani abu ya sata faɗin, " Muje cikin gida a samu Abinda za'a sawa ciwon naka, kana zubda jini sosai".

Ƙura mata ido yayi kawai ko kiftawa ba yayi kamar wanda yaga wata sabuwar halitta. " Ni ba cutar dakai zanyi ba in ma tunanin haka kake, gidan mu zamuje a sa ma magani".......... Ta ƙarashe tana nuna masa kanta tare da shi sannan ta nuna mashi gidan su ma'ana ta masa maganar kurame. Nan ma bai yi magana ba sai wucewa da yayi ya nufi gidan nasu data nuna, da sauri tabi bayansa tare da saurin shigewa gaba suka shige cikin gidan da yake tarwai kamar anyi yasa ko motsin kirki bakaji, ɗakinta ta wuce dashi tare da faɗin, " zauna barin je in samu Toshi (tissue)"............ Ta faɗa tana masa alama da hannu na abinda zata samo a goge jinin, Da kallo yabi ɗakin yana yatsina fuska ba tare da ya zauna ba ya wani tsirtar da yawu ya juya ya fice, baki buɗe Hushaima ta bishi da kallo har ya fice kafin ta juya ta kalli inda ya zubar da yawu sannan ta bishi wajen, a tsakar gidan ta same shi sai raba ido yake kamar wanda yaga wasu sababbin abubuwa.

Ɗakin Sahnish ta nufa tare da bubbuga masa ƙofar, Ƙara ƙanƙame Shazeen Sahnish yayi tare da fara karanto duk Addu'ar da tazo bakin sa, Jin shuru ya sata faɗin, "Sahnish in kana ji na ka zo ka buɗe min"......... Ai da wani mahaukacin sauri ya miqe tare da zuwa ya buɗe mata ƙofar ba tare daya saurari wani abu da zata faɗa ba ya jawo ta ciki yana kokarin maida sakata ta bige hannun sa da faɗin, "Kai bana son shashanci me hakan, zo muje da ALLAH "............." Ina ?"........... Ya tambaya kamar bai yadda dai ita ba. Jan hannun sa tayi suka yo waje, ai idon sa na sauka a kan sa yayi wani u turn ya dawo bayanta Yana faɗin, " innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahamanir Rahim".

Ɗagowa yayi yana binsu da kallo, tsaki Hushaima taja tare da faɗin, " Je ka ɗaibo masa ruwa ya wanke ciwon "..........." Au Wai dama kema kina ganin sa?". Sahnish yayi tambayar tsakanin sa da ALLAH, dan shi whl ya ɗauka gamo yayi.

"Bana san iskanci Sahnish zan saɓa ma whl, mutum ne kamar ka ɗan kauye kawai".

(Jamaa kuji Hushaima fa sai kace itama bata ruɗe ɗin ba).

A ɗan tsorace ya wuce yana keɓe keɓe, nufar inda yake Hushaima tayi tana zuwa ta ce, " Cire rigar ka wanke wurin"........... Ta faɗa tana nuna masa abinda zaiyi dan ita tafi tunanin yana da larurar magana ne, amma a mamakinta sai taga ba musu ya zare rigar wanda hakan ya bayyana murɗaɗɗen jikinsa da yake nan fari tas ga wasu kwantattun gashi masu laushi dake kwance a kirjinsa sun biyo layi ta tsakiyar cikinsa har zuwa cibiyarsa, ɗauke idanunta tayi zuciyarta na skipping beat ta maida kallonta wurin kafaɗar tasa inda shatin yankan ya ke nan rafkeke ga jini har lokacin zuba yake sosai ta jinjina ƙarfin halin wanna bawan dan yankan ya shiga sosai, "Sahnish bashi ruwan in ka ebo bari na ɗauko hijab naje wurin Dr misbah na kirashi"..........." Ah ah ke dai ki tsaya anan ɗin ni  bari naje na zo dashi sai na fiki sauri ai "........... Ya faɗa yana sakin gugar ya fice da sauri dan whl ba zai yarda ta barshi da wanna aljanin ba dan shi har yanzu ya ƙasa yarda mutum ne, zuwa tayi ta ƙarasa ɗaibo ruwan ta kawo gabansa tare da faɗin, "Gashi Ka wanke wurin kafin Dr yazo"........... Ɗauke Kai yayi kamar bai gane abinda take nufi ba"........."To Ka wanke hannun Ka".......... Ta sake faɗa tana nuna masa. Da wani irin daddadan sauti me kama da busar sarewa a hankali cikin natsuwa, da Arabic accent ɗin sa ya ce, "Bani so"........ Zuba masa idanunta kawai tayi cike da mamaki kenan dama yana magana, cikin son sake sauraran melodious voice ɗin sa ta ce, "Baka son me?"..........ɗauke kansa yayi ma kamar bai san da mutum a wurin ba, numfashi ta furzar kawai tare da riqe waist dinta da hannayen ta can kuma ta sunkuya ta ɗauka rigar tasa daya jefar ta karkaɗe tare da wanke gefe guda sannan ta ɗan jiƙa ta nufo shi da niyyar goge jinin dake binsa, warce rigar yayi tare da wurga Mata a fuska a fusace ya ce, "Stop this shit".

Haushi taji sosai, daga tana son taimaka masa a shi ne zai dinga wasu abubuwa kamar wata baiwar sa a fusace itama ta nuna masa hanya da faɗin, "Fitar mana daga gida to, kaje can in ma kasheka zasuyi su kashe Ka, yanzu haka Kai Ka tsokano su ma da bala'in ka".

Jama'a har kura tace da kare maye, yau Hushaima ke kiran wani da ɗan bala'i, eh to lalle abun ya yi tsamari.

Amma ina ko nuna yasan tanayi baiyi ba haka ta cigaba da bambamin faɗa kamar zata kama da wuta, faɗi take kawai yazo ya fice musu a gida, idonsa a kanta kuma yana jinta amma ko motsi baiyi ba har su Sahnish suka shigo shida Dr misbah .

Saida ta harare shi sannan ta ce, "Sannu da zuwa Dr"........."yauwa Hushaima yaki ke".

"Lpy kalau? Ga wanda zaka duba nan yanka ne ya samu a wurin kafaɗa ".

Matsowa Dr misbah yayi a ɗarare dan har ga Allah shi ma tsoron tunkarar sa yake saboda wani irin kwarjini da ya masa. Kallon sa da ya dawo dashi kan Dr misbah yasa ba shiri yaja birki, hannu ya miqa masa alamar ya bashi first aid box ɗin, kallon hannayen nasa Dr Misbah yayi ganin ba komai sai first aid box ɗin da yake riqe dashi ya sashi miqa masa hannun sa na rawa ya koma can baya ya tsaya. Zuba masa ido sukayi su duka ukun, tsugunnawa yayi tare da Buɗe first aid box ɗin ya dauko cotton da spirit ya dangwala ya fara goge wurin yana ɗan bata fuska har ya goge wurin tass ya sake ɗauko antiseptic ya sanya a wurin, sannan ya ɗauko surgical needle da suture thread ya sanya ya fara ɗinke wurin kamar ba jikinsa yake ɗinkewa ba cike da kwarewa da kuma nutsuwa har ya gama, sterile gauze pad ya sanya sannan ya manna medical tape, ba tare da ya maida kayan da yayi amfani dasu mazaunin su ba ya ture first aid box ɗin da ƙafa.

Ajiyar zuciya Hushaima ta sauke tare da ƙarasawa ta haɗa abubuwan ta maida ta rufe sannan ta miqawa Dr misbah da faɗin, "ina zuwa"......... Ɗakinta ta shiga ta ɗauko dubu ɗaya ta miqa masa da sauri ya karɓa yayi godia ya fice yana waiwayen su. Juyawa tayi ta kalli Sahnish sannan ta maida kallon ta kansa da faɗin, "zaka tashi Ka shiga ɗakin ne ko yaya?"........  Ko kallon ta baiyi ba ballantana ya nuna yaji maganar ta, juyawa tayi wurin Sahnish da faɗin, "Shiga Ka kwanta Sahnish saida safe Ka turomin Shazeen ma tazo ta kwanta". Tana gama faɗa ta wuce ɗakin ta, da sauri Sahnish ma ya wuce ɗakin sa suka barshi anan. Samu yayi Shazeen tayi bacci dan haka bai tasheta ba kawai ya ɗauko ta .

A tsaye ya samu Hushaima hannunta ɗaya akan waist ɗinta kamar me tunanin wani abu, kwantar da Shazeen yayi sannan ya wuce wurin Hushaiman tare da jawota daga bakin Ƙofar ya ce, "Hushaima me ya faru wai? Ina kikaje ɗazu da ake cikin wanna tashin hankalin? Waye wancan kuma?". Duk a lokaci guda yake jero mata wanna tambayoyin.

"Wani abun mamaki Sahnish wata halitta na gani sak kamar ni, abun ya ɗaure min kai ya sanya ni a ruɗu, dama ana samun irin haka? dan ni nasan ana samun masu kama ɗaya amma wannan kamar ta wuce kama sai naga kamar ni ce "............."A Ina wau?". Sahnish ya tambaya yana binta da kallon tuhuma.

"Yanzu mana, abinda kaji anawa gudu wasu mutane ne akan giwaye suka shigo Kan layin Kuma ga dukkan alama wancan mutumin suka biyo, Kuma su suka ji masa wannan ciwon, Amma whl yarinyar sak ni ce". Shuru tayi tare da dafe kanta da hannu ɗaya sai kuma ta ce, "Sahnish ina son sake ganinta, amma bansan a wace duniyar zan ganta ba, ina so kai ma ka ganta domin ka gani ko muna kama ko kuma ni ce na zauce sahnishhhhhh". Ta ƙarashe tana runtse idanunta, ita tasan abinda ta gani amma kuma wani sashin na zuciyarta yafi bata kamar ba daidai take ba.

Shiru Sahnish yayi dan shi yafi yadda da gamo Hushaima tayi. Hushaima na ƙoƙarin sake magana sai ganin mutum sukayi ya faɗo ɗakin, saurin matsawa Sahnish yayi ya bashi wuri, da ƙafa ya dinga ɗaɗɗage shimfiɗar dake ɗakin kamar me neman wani abu ganin haka yasa rai ɓace Hushaima ta ce, "Kai malam da ALLAH dakata nan fa ba gidan ku bane, in kaga zaka iya zama ka zauna in baza Ka iya ba ga hanya nan wuce ka tafi inda kafi wayo, ni taimakon ka kawai nayi ba hakkin ka bane a kai na, kuma mu abinda ALLAH ya bamu kenan"............ Da wani irin voice da saida yasa Sahnish riqo hannun ƙofar yana jiran ƙet ya zura waje ya ce, "Mind your tongue, baki da Matsayin da kowacce irin magana tazo bakin ki zaki faɗamin. Akan wannan ƙazamin ban ɗakin da ko in da dokuna na ke kwana yafi shi"........ Zaro idanunta waje tayi tare da ƙare masa kallon tsab sannan ta ce, "Ɗakin nawa ne ma banɗaki, to whl summa tlh sai ka fita ka tafi gidan ku, ai ka iya yin laifi ka biyo jikin gatangar mutane kana mannewa kamar kadangare, meysa su ka kasa tsayawa ka gaya musu maganganun s........."....... Wata irin juyowa yayi wadda saida tasa Hushaiman ta matsawa baya, gabanta na ɗan faɗuwa, da hannu ya nuna ta alamar warning sannan ya ce, "Ki shiga hankalin ki in ba haka ba zaki fuskanci hukunci da tsawon rayuwarki zaki ƙareta a dana sani, zan miki uzuri yanzu saboda bakisan waye ni ba amma......" Ya ƙarashe yana watsa musu wani kallo da ya ƙarashe faɗar abunda bakinsa bai faɗa ba, sannan ya ɗora da faɗin, "Fita a nan wurin kafin nayi fatali dake".

"Jar buuuu........." Toshe mata baki Sahnish yayi sannan ya fara janta dan yasan ko za'a kasheta baza tayi shuru ba shi Kuma ya tsorata da furucin wannan aljanin ganin da iya gaskiyar sa yayi maganar amma dukda haka Hushaima sai da ta ƙarashe faɗar abinda ta soma, daƙyar Sahnish ya turata waje, a fusace ta ce, " Whl sai ya fito mun daga ɗaki, ai ba ɗakin ubansa bane".......... "Dan ALLAH kiyi hakuri Hushaima, baki san waye shi ba. Ki tuna in fa wani abu ya sameki da ni da Shazeen ne zamu shiga matsala, ke kaɗai mu ke da, wanna mutumin daga ganin sa wani babba ne Kuma zai iya aikata abinda ya faɗa ɗin nan, dan haka ki barshi ba dai ɗaki bane kizo mu koma nawa mu zauna zuwa safe ai dole zaisan in da rana tai masa".

"Sai ka wuce ai ka je ka ɗauko mun yarinya, dan bansan mugun Alkaba'in dake tare dashi ba, saboda whl in na shiga Ina iya Ƙwada mai mar........" kafin ta rufe bakinta ma Sahnish ya faɗa ɗakin duk da dukan da kirjin sa yake yi, ko kallon in da yake baiyi ba ya sake ɗauko Shazeen ya fito .

Ranar kusan duk gidan kwanan ido biyu sukayi dan ba wanda ya rintsa, da asuba bayan sunyi sallah ta tashi ta fita, ƙwanƙwasawa mutanan gidan ƙofa ta dingayi dan duk sun ƙasa fitowa, a hankali suka fara leqowa kowa ya ganta sai ya fito da sauri yana tambayar abinda ke faruwa tace musu ba komai kawai suyi abinda ke gabansu sannan ta wuce ɗakin su, a tsaye ta sameshi yana danna wayarsa goldstriker iPhone

33 / 53