BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   1 / 53

1 to 3K   out of 156.9K words

👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



*BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM*

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin ƙai. Ya Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma, ka kuɓutar da hannu na daga rubuta abinda zai cutar da wani na da ni kai na.


___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@watpadd Sultywrites22



STEP 1


PAGE _______1 & 2



Tsananin zafin ranar daya tsananta ne yasa ta sake duba wayarta a karo na ba adadi, daidai lokacin da agogon ya nuna ƙarfe 1:30pm, sautin ƙaraurawar tashin dalibai data jiyo ne ya sata sauke zazzafar ajiyar zuciya. Matashiyar budurwa ce mai matsaƙaitan shekaru, kyakkyawar gaske, olive skin colour ne da ita me matuqar ɗaukan ido, fuskarta ta kasance oval shaped, ga wasu deep eyes dake gare ta masu matuqar haske yayin da eyeballs ɗin suka kasance masu dan tsini domin ba flat suke ba gabaɗaya, tana da yalwar gashi wannda hakan ya gaza ɓoyuwa saboda wasu kwantattun gashi da suka zagaye goshinta har zuwa gefen kunnuwanta, haka zalika gashin girarta da na idanunta kamar Wadda tayi fixing, tana da hanci dan daidai tare da ƙaramin baki me launin light brown.

Kaɗan kaɗan take buga wayar hannunta a Kan lips ɗin ta tana kallon yaran dake rububin fitowa daga makarantar, wata kyakyawar yarinya ce da baza ta wuce shekaru 7-8 years ba ta fito tana kalle kalle. "Shazeen". ta ƙwalawa yarinyar Kira Wanda hakan yasa ta juyowa da sauri zuwa saitin da taji kiran, kwasowa tayi a guje tana zuwa ta faɗa jikinta cikin jin daɗi ta ce, "Aunty Hushaima yau kinzo da wuri".

"Eh, Amma na sha dukan rana ai, maƙaryaciya kawai, kika cemin yanzu 1pm Ake tashin Ku? Yaya baya zuwa ɗaukanki har sai kowa ya watse yake zuwa?".

"Whl ALLAH Aunty Hushaima 1pm ne, yau ma assembly ɗin da aka sakeyi yanzu ne ya sa ba a tashemu kan lokaci ba, kuma ma munyi practical na tie and die ne, kinga ba". Ta ƙarashe Tana nuna Mata hannuwanta da gaban rigarta da sukayi staining.

Riqo tsintsiyar hannunta tayi suka fara tafiya tana faɗin, "Kun sha tie and die Kam, sai muje gida ki zauna ki wanke kayan tas".

"Aunty Hushaima ki siyamin aipo ki gani, whl tas zan fidda su, na fiki iya wanki ai". Ta faɗa tana ɗan cilla ƙafa irin yadda yara keyi idan wani Abu ya musu daɗi.

"Ai bakin ki ne aipo ɗi......" Maganar ta ce ta tsaya sakamakon caɓin da ya wanke su gabaɗaya har fuskarta, ba shiri ta saki hannun Shazeen tare da dage hannayen ta sama tana kallon white palazzo ɗin ta da gabaɗaya ya ɓaci. "Kam burauban can". Ta faɗa cikin ɓacin rai tare da ɗagowa idanunta suka sauka Kan wasu shegun motoci guda biyar baƙaƙe sidik kirar mercedes benz GLE class, dukkan su a rufe suke da tinted glass hakan yasa ba'a iya ganin na cikin sai dai na ciki yaga na waje, kana ganin motocin kasan ba na qananun mutane bane. Ganin yadda sukayi wucewar su yasa ranta ƙara ɓaci cikin zafin nama ta sunkuya ta wawuri wani qaton dutse ta seta motar dake ƙarshe bata ƙarasa barin layin ba ta wurga mata sai ji kake tass glass ɗin baya ya tarwatse, dama abunka da ya sha rana, salati mutanen dake wurin suka fara yi yayin da wasu suka dafe bakunan su cike da tsantsar fargabar abinda zai je ya dawo da kuma mamakin ƙarfin hali irin nata.

Wani dattijo da ya riqo hannu wasu yara biyu dake sanye da uniform ɗin makaranta irin na jikin Shazeen ɗin ya ce , "Ke kuwa jikata me ya kaiki taɓo irin wa'anna mutanen, da yawa yawan su basu san darajar ɗan Adam ba, yanzu haka kika bibiya ɗan wani babban ne, su na jin kansu da girma kamar su suka shimfida ƙasar sai sa suke yin yadda suka ga dama, su taka Wanda suka so a lokacin da suka so kuma su zauna lpy".

Cikin qunar rai ta ce, "To ai Baba daɗin ta ƙasar ta ALLAH ce ba mallakin wani ba bare yayi iko da ita, kuma mulki da arziki ai duk na ALLAH ne shi ke bada wa ga wanda yaga dama haka kuma jarrabawa ce ga duk wanda ya bawa, Kuma yana iya karɓe kayan sa a duk lokacin da yake so, kuma duniya bata da tabbas tunda rigar aro ce k........." Maganarta ta katse sakamakon motocin da sukayi parking a daidai saitin su, cikin rawar jiki dattijon nan yaja hannun yaran suka bar wurin.

Ita kuwa ba tare da wani fargaba ba ta nufi wurin su tana ƙara haɗe girar sama data kasa, wasu garadan mutane ne suka fito kallo ɗaya zaka musu ka shaida excort ne saboda shigar dake jikin su ta baqaqen kaya, fuskar nan kuwa in ka kalla sau ɗaya baza ka so sake kallo ba. Ɗaya daga cikin su ne ya matso inda take tare da fidda hannu ya zabge ta da marin da sai da tayi taga taga kamar zata faɗi tayi saurin dafe motar, hannunta akan kuncinta, wasu stars ne kawai ke kai kawo daga idanunta zuwa cikin kanta.

"Ke dabbar ina ce? Kinsan nawa ne glass ɗin motar da kika fasa? to ko duk dangin Ku aka haɗa baza a samu rabin kuɗin ba...." kasa ƙarasawa yayi saboda saukar marin bazatan da yaji, da mamaki ya ɗaga kai yana kallon yadda take huci, juyawa yayi ya kalli ɗaya abokin aikin nasa take sauran suka firfito suka zagaye su. Ba tare da ta dubi ko da ɗaya daga cikin su ba ta ce, "kai ɗin banza kai ɗin wofi, kana me gadi dakai har zaka ɗaga hannu ka mare ni sannan in tsaya kallon ka, ba'ayi wannan halittar ba Whl ".

Shi dai har lokacin bai fita daga shock ɗin marin ba tunani ma yake itan ce ta mare shi ko kuwa dai wani ne, dan ya kasa yadda cewa akwai mace mai ƙarfin halin da zata iya kallon sa sannan har ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari kamar haka, ballantana wannan yarinyar da dukkanta bata ƙarasa ko ƙirjin sa ba.

Gyaran muryar da akayi ne yasa duk suka ɗago suna kallon direction ɗin da sautin ya fito, wani kyakkyawan matashi ne tsaye kana kallon sa kasan ALLAH yayi halitta, duk da kuwa duk gulmar ka baka isa cewa ga kamannin sa ba saboda fuskarsa dake rufe, sanye yake da white kaftan ɗinkin monogram da yayi fitting ɗinsa sosai, kansa sanye da p cap black haka idanunsa suna cikin wani sunshade da ya cinye kusan rabin fuskar sa, daga kan hancin sa kuwa zuwa bakinsa noes mask ne wanda hakan ya ɓoye kamannin sa sai abin da ba'a rasa ba, ƙafarsa tana sanye cikin white prada wetlook loafers. "Aram! Meke faruwa?". Ya tambaya da wata irin nutsatstsiya kuma kamilalliyar murya.

Cike da ɓacin rai da har lokacin ya kasa ɓacewa akan fuskarta ta ce, "Kai har ka tambayi meke faruwa, au touu da alama kai ne shugaban azzaluma...." Haɗiye sauran maganar tayi dalilin wata mahangurba da ɗaya daga cikin excort ɗin ya kai mata, cikin kaushin murya ya ce, " Ke ki iya bakinki, kinsan kuwa waye a gabanki ?".

Tana ɗagowa taga jinin da ya biyo hannunta, tsuke bakinta tayi tare da tattareshi ta tofa akan white loafers ɗin nasa. Runtse ido yayi tare da ɗauke ta da wasu gigitattun maruka da sukafi wanda Aram ya mata dan har sai da ta Kai ga zubewa a ƙasa, ƙoƙarin hana idanunta tara ruwa tayi tare da furta, "ALLAH ya isa ban yafe ba"........ A harzuƙe securities ɗin sukayi kanta, saurin ɗaga musu hannu yayi hakan yasa duk suka qame a inda suke suna huci kamar wasu mayunwatun zakuna, ɗayan ya ce, "kee boss kike wa ALLAH ya isa".

"An masa ALLAH ya isan, mugaye , azzalumai, macuta masu matashin Kai da hakkin mutane".

"Boss......" Girgiza masa kai yayi hakan yasa wanda ya soma Maganar haɗiye wani yawu mai ɗaci, dan ba haka yaso ba, so yayi boss ya basu dama yau suci uban shegiyar yarinyar nan suga ƙarshen tsaurin idon nata.

Kallon Sama da ƙasa ya Mata na seconds kafin ya maida kallon sa Kan yaran nasa dake ta faman zazzare ido suna sauke numfashi cike da ɓacin rai, ɗan girgiza kansa yayi tare da sakin wani sirritaccen murmushi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa, cikin normal Muryar sa mai sanyi da saukar da nutsuwa ga mai sauraro ya ce, "Ku je da ita ta biya kuɗin glass ɗin data fasa, sannan a tabbatar min da waye ya sata".

Da sauri ta ce, "Tsaya Malam waye Kai a faɗin ƙasar Nifaz? Miye inkiyar ka da in anji za'a shaida ka, me Ka ajje me Ka bawa wani ajiya da har zaka fara tunanin turo ni akayi wurin ka? Me kake taƙama dashi? Wannan kayan wutar? to bara kaji ko a kwalar riga ta dan ka sa a tafi dani, muje har birnin sin, amma ni ma Whl sai an biyani kayan mu da aka ɓata da cabi yauwa". Ta ƙarashe tana tankwashe ƙafa daga zaune da take akan ƙasa.

"Meye kayan naki da aka bata". Ya tambaya still idanun sa a kanta ta cikin munafukin shade ɗin nasa.

Juyawa tayi tare da kwala kiran Shazeen dake rakabe bayan poll wire, a tsorace ta taho. Janyota tayi tare da nuna masa kayanta sannan ta nuna wandonta da goshinta, "Ina fatan kana gani dai da kyau. Ko mu ba mutane bane ? ko kuma bamu da Yanci, to whl nima ba zan yadda ba ".

Ba tare da yayi magana ba ya juya zai koma mota, tsalle tayi ta dire gaban sa, "Kai shugaban azzalumai, Whl ko ku kun haƙura ni bazan haƙura ba, dole ne a biyani hakkin kayana da aka ɓata, ko nai ta ja maku ALLAH ya isa har duniya ta naɗe kuma whl ALLAH ya isa guba aya ce me hana kwanciyar kabari".

"Ku janye min ita daga nan ". ya faɗa Yana keɓewa ya wuce ta gefenta gudun kar ta ƙara tunzira shi, dan in banda self control irin nasa da ba abinda zai hana ya bar su Aram suci ubanta, saboda yadda tayi masifar ɓata masa rai, saidai ba zaiyi hakan ba saboda wani dalili, Marin da ya mata ma baisan lokacin da yayi shi bane saboda shi mutum ne me tsananin kyankyami.

Ganin yadda suka nufo ta gadan gadan yasa ta yi kwafa ta wuce tare da ɗaga murya ta ce, " Whl bana yafi ya kuma s......" Haɗiye sauran maganar tayi tare da jan hannun Shazeen da niyyar tafiya taji an wurgo Mata Abu a fuska, bundle din 1k ne ya sauko Kan hannunta, juyawa ta yi ta bisu da kallo har sun shiga motocin su sun fara tafiya. Kuɗin ta ɗauka tare da jujjuya su sai kuma taja kwafa ta zura su a jaka . Abun hawa ta tsare musu suka hau ba tare data damu da ta kaɗe ƙasar jikinta ba.

"Madam ina zamu ne?". Mai tuk tuk ɗin ya tambaya bayan sun fara tafiya. "Kwanar chiriku".......... "Gsky Hajiya ba can nayi ba"....... Sai da ta watsa masa harara sannan ta ce, "Au dama ba Sana'a Ka fito yi ba, ko akwai iya wuraren daka ware kake yin Sana'ar taka?".

"Kinga ni fa da zaki hau baki ce min ga inda zaki ba, dan haka yanzu ki sauka kawai ki tari wani abun hawan ni ba can nayi ba".

"Kai kama isa, uban kuturu yayi kaɗan whl yadda Ka ɗauko mu sai Ka kai mu ko na tara ma jama'a".

"Ke ni zaki nunawa jan wuya, whl sai na farfarɗe ki, baki sanni bane a ƙasan gada nake kwana in gaya Miki". Ya faɗa yana zaro wata ƴar ƙaramar wuqa daga kugunsa.

"Kallo nan"........ ta faɗa tana ɗage masa gefen rigarta itama wanda hakan ya bayyana wata zungureriyar wuqa dake soke a gefen wandon nata. "Baza ka buɗe min ido ba cikakkiyar yar ƙasar Nifaz nake, ina yawo da ita ne saboda kariya daga irin Ku, dan haka kar kace zaka nuna min duniya, dan ko da nazo cikin ta idanuwa na a buɗe nazo, gwara Ka wuce mu tafi salin Alin karatun yan yankan kai, in ba haka ba na gwada ma nawa tashancin whl".

Girgiza kai yayi tare da Jan kwafa ya maida tasa wuqar, ya bawa machine ɗin wuta suka wuce ba tare da ya sake cewa uffan ba, dan yasan lalle yau ya ɗauko yar hau daidaishi, kwatance ta dinga masa har suka ƙarasa Kan layin sannan ta ce ya tsaya, sauka sukayi ta zaro ɗari biyar a jakarta ta bashi, bata tsaya sauraren me zaice ba ta ja hannun Shazeen suka wuce, unguwa ce irin ta talakawa dan babbar mota ma in ta shiga sai ta maqale amma duk da haka layin tsab yake ba kamar irin sauran unguwanni na talakawa ba Wanda warin kwatami ma da bola sun ishe Ka.

Ƙofar wani madaidaicin gida suka tsaya tana kokarin ciro makullin Shazeen ta ce, "Aunty Hushaima gidan a buɗe yake".......... Ta ƙarashe tana tura ƙofar ta shiga tana rangaɗa sallama, bin bayanta tayi suka shige. A ɗan ƙaramin tsakar gidan ta tarar da wani saurayi durƙushe yana wanki, kallon tulin kayan su da ya ɗaibo tayi kafin ta ce, " Sahnish kayan nan basu ma yawa ba, ai da jira na kayi na dawo sai muyi tare".

Ɗagowa yayi Yana goge fuskarsa da omo ya fantsama, sosai yake tsananin kama da su biyun. "Whl kawai na dawo ne naga ba abinda nakeyi to dama akwai yar ɗari uku da na samo, shi ne fa na ɗauki ɗari da hamsin na siyo omon nan, nace bari na wanke kayan dan dama tin shekaran jiya naga sun taru. Amma lpy na ganku kamar wanda sukayi wasan ƙasa? Ke kuma me ya sameki a fuska?".

Ba tare data bashi amsa ba ta zaro kuɗin da mutanan da bata san ko su waye bane suka bata, firfita ta shigayi dasu tana ɗan wani ƙasaitaccen murmushi. Saurin ɗauraye hannun sa yayi ya nufo inda take tsaye. "Hushaima ina kika Sa....samu kuɗi masu yawa irin wanna?". Ya ƙarashe yana Mata kallo me cike da tarin tambayoyi.

Gyalen dake wuyanta ta cire ta ɗaura Kan igiya sannan ta wuce yar inuwar dake kofar dakin su ta zauna tare da faɗin, "karaso mana, kayi tsaye a wurin kamar wani bafade". Cikin sanyin jiki ya ƙaraso ya zauna a gabanta tare da zuba Mata ido. Labarin abinda ya faru ta bashi sai da ta gama, ya ce, "Me ya kaiki Hushaima, baki san ko su waye su ba, yanzu idan kuma suka cutar dake fa ina kike so in sa kai na, ya kike so ayi da Shazeen". Ya karashe cikin tashin hankali.

"Dadi na dakai raguwar zuciya kuma a matsayin ka na namiji, whl Ka daina tsoro Sahnish, kuma ni ban ma san zasu bani kuɗi ba, kawai dai nasan na musu ɓarna dan gsky raina yayi masifar ɓaci ne, kuma ina neman hanyar da zan fidda Kai na saisa kawai na tsiri wanna borin kunyar".

"Dubi fuskar ki fa Hushaima, ji yadda lebenki ya kumbura". Ya ƙarashe yana kai hannu kan kumatunta da shatin yatsu yake nan shimfiɗe a fuskarta ta. Kwafa taja tare da shafa kumatun nata ta ce, "Ai Whl sai na rama Sahnish ka rubuta ka ajje ka kuma zuba ido ka gani komin daren dadewa, ni ni ni dai har za'a wawwanke da maruka har uku"........... Ta ƙarashe tana me girgiza kanta ta sake jan Ƙwafa. Sahnish da ya saki baki yana kallon ta ne ya ce, "Da kika samu suka barki basu tafi dake ba shi ne kika samu damar fadin sai kin rama ko, wai da ALLAH Hushaima yaushe zaki barmu mu zauna lpy ne? Ina rabaki da kalmar saikin rama ɗin nan, ba fa komai bane ake nasarar rama shi, a wani wurin hakuri da yafiya sune j........." Shiru yayi sanadiyar kallon da take wurga masa. Sautin "hmmm" ya fidda ba tare da ya ƙarasa maganar da ya faro ba.

"Kaga yanzu dai duk ba wanna ba kasan muna da buqatar kudin nan, dan ka san jibi ne ranar da Malam Ado ya bamu mu bashi kudin hayar sa ko mu bashi gidansa, dama abinda muka hada bai wuce dubu talatin ba kaga sai a bar wancan yaso a cire dubu sittin din a nan a bashi ko ya kace?".

"Eh hakan yayi saura dubu arbain kenan ".

"Akwai kudin makarantar Shazeen da za'a fitar dubu goma sha biyar, dama abun na rai na dan na san nan da sati biyu zasu fara magana akai su ma".

"Saura ashirin da biyar".

"Toh sai a siya kayan Abinci na dubu goma, kai ma Ka dau goma ni na dau biyar, wancan talatin din kuma baza mu taba ta ba yanzu saboda bamu san matsalar da Ka iya taso wa ba wanda zamu buqaci kuɗin".

Kallonta yake cikin wani yanayi me wuyar fassarawa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Gsky Hushaima bazan karɓi komai daga kuɗin nan ba ke da Shazeen kunfi kowa buqatar sa dan haka Ku riqe kawai ".

"Me sa zakace haka Sahnish, duk abinda ya shafe mu ne ai, in babu kuma ai kai ma me nemowa Ka kawo ne".

"Eh ni ya Zama dole na Nemo

1 / 53