Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ne na Allah, maganar aure tsakanina da ke, ba zai yiwu ba yanzu haka Qatar zan tafi da wani ɗan ƙanƙanin lokaci"
Murmushi ta yi, duk da hawayen da ya cika mata ido, ta ce "Ko kai fa, ka ga yanzu da ka gaya mini gaskiya zan fi samun nutsuwa sosai da sosai. Ina yi maka fatan alkhairi amma dan Allah ka ci gaba da yi mini addu'a, na san larurata ce ta saka ka fasa aurena, ka yi mini addu'a Allah ya bani wanda zai iya aurena da larurata a haka"
"A'a Nana, idan baki manta ba, tausayinki da halin da ki ke ciki, ya sanya na ce zan aure ki, ban ƙi auren ki saboda larurar ki ba"
Ta share hawayenta ta ce "Eh, da fari tausayina, daga baya ka koma so na, dama na san zaka rabu da ni, dama na fi so na ji daga bakin ka ne, tun lokacin da aka ce ba zaka iya riƙe aure ba, na ga komai a bacci, har rabuwar nan tamu na yi mafarki na gani, ba zaka aure ni ba. Hakan ba ya nufin zan manta tarin alkhairin ka a gare ni, Ubangiji Allah ya baka mace ta gari lafiyayyiya"
Zai yi magana ta girgiza kai, ta fice daga ofishin, zuciyarta na zafi hawayen da take ƙoƙarin dannewa, su ka ƙi dannuwa.
Auwal bai taɓa tunanin yana son Nana har haka ba, sai da Umma ta hana shi aurenta, kuma abin bai tsaya a nan ba, sai da Umma suka tura shi Qatar.
Nana ta tafi rijiya, ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta, sannan ta koma ajinsu aka ci gaba da tilawa da ita.
Sosai rabuwa da Auwal ya shigi Nana, duk da ta yi mafarkin hakan, amma ba ta bari ta gasgata hakan ba.
Har aka tashi daga makaranta, hankalinta ba ya kan abin da aka ƙara musu sam.
Da daddare, bacci ya gagari idanun Nana, sai tunani da zancen zuci, ya din ga ziyartar zuciyarta, har ta rasa wane tunani ya kamata ta yi.
Jamila ce ta zo da abinci daga gidan maman khairat, ta cewa Nana ta tashi ta ci, amma ta ƙi.
Sai da ta takura mata, sannan ta ci kaɗan, ta sha lemon ta kwanta, sai dai abincin ya tsaya mata yaƙi wucewa.
Tana daga kwance, tiryan-tiryan, yadda aka fasa aurenta na farko ya dawo mata, yadda take samari, su na tafiya, duk da galibi mutanen banza ne suke bibiyarta. Amma Suleiman ya zo da gaske zai aure ta.
Sai dai Baba ya din ga zubar mata da mutunci a idonsa, ta hanyar roƙe-roƙen kuɗi, kuma wani abin mama ce take ziga shi yake yi, har ita ma wasu lokutan sai ta tura ta ce ya bata kuɗi, sun wuni ba su ci abinci ba. Tun yana bayarwa da marmari, har ya gaji ya fara mita. Ya san da Nana ba ta da cikakkiyar lafiya, duk da a lokacin abin ya lafa, amma mama ta zaunar da shi, ta din ga karanta masa Nana aljanu har sun fara haukata ta. Matarsa ta zo har gida ta ci mutuncin Nana, har da an gaya musu babarta ce take biye-biyen bokaye, abin ya koma kanta take fama da aljanu.
Duk da dama Mama ta saba faɗar wannan maganar, idan ta so cin mutuncinta, amma abin yayi mata zafi ya mata ciwo.
Wuni ta yi tana kuka, Suleiman da kansa ya je gida ya ba wa Nana haƙuri, bayan ya samu labarin abin da matarsa ta zo ta yi mata, sai dai tun da matar ta koma gida, ya aka rasa gane kanta, ta kwanta rashin lafiya.
Ta din ga fama da matsanancin ciwon kai, idan ta fara sai ta fita hayyacinta ko gani ba ta iya yi, suka je asibiti ba a ga komai ba.
Ya koma gidansu Nana, ya ce idan ta san wani abu ta yi wa matarsa, ta bari uwar 'ya'yansa ce, ba zai so lafiyarta ta taɓu ba, tun da ai ya zo ya bata haƙuri.
Nana ta din ga rantse-rantsen ita babu abin da ta yi mata, ƙarshe dai matar kamar za ta haukace, ya zo ya ce a dawo masa da kayan aurensa, tun a waje Nana ta cutar da iyalinsa, ina ga idan ya aureta, dama kuma an ce masa mahaifiyarta na biye-biye.
Duk yadda Nana take son ta yi aure, ko dan saboda tarin ƙalubalen da take fuskanta, amma fasa aurenta da Suleiman bai wani dame ta ba, domin tana fargaba mussaman yadda aka gama zubar mata da mutunci a wurinsa.
Ajiyar zuciya ta sauke da ta zo nan a tunaninta, sai da kanta ya sara, ta sauke ajiyar zuciya. Ga abubuwa da dama su na cin zuciyarta, tana buƙatar abokin shawara da tattaunawa, amma rashin yardarta bai sanya ta bawa wani damar, hakan a rayuwarta ba. Mutanen da suka cancanci hakan a rayuwarta duk ba ta ita suke yi ba. Babbar damuwarta a yanzu, bai wuce yadda ta san ko ba ta so, Baba sai ya ƙaƙaba mata Saleh ba, dan ta fuskanci zamanta ne kawai ba a so cikin gidan, duk ga su Suwaiba da Jamila, su babu wanda yake takura musu a kan aure sai ita.
Sosai take jin zafin rashin Auwal, ko ba komai mutum ne ma'abocin Alqur'ani da kuma riƙo da addini, ta san abu ne mawuyaci a iya cutar da shi, ta sanya ran idan tana tare da shi, za ta samu sauƙin wasu abubuwan.
"Ke baiwar Allah" ta ji an kirata. Ta ɗaga kai, ta hangi wata mata bararoji a tsaye, ta yi kwalliya da tarin tsummokara, da wasu irin tarin sarƙoƙi na zare a wuyanta, da ƙullin kaya a hannunta, ta burtso da gashin ta gaban goshin ta.
Nana ta ɗaga kai ta ganta a wani wuri, da ba ta san ina ne ba.
Matar ta ce "Zo na baki magani"
Nana ta ce "magani kuma, na me?"
Matar ta sauke mayafin da ta rufe fuskarta, ko ina tsagu ne a fuskarta, har baka iya tantance kamaninta, saboda azabar billayen da ke fuskarta.
Matar ta ciro wani magani a cikin, ƙullin kayanta ta ce "Ki zuba a tafin hannunki, ki lashe"
Nana ta ce "To ai ba ki gaya mini na mene ne ba?"
"Idan ka sha, ba zaki ganin Ƙaisar ba, zai daina bibiyar ki yana takura wa rayuwarki, zai rabu da ke har gaban abada. Dukkanin damuwar ki za ta kau, babu wanda zai sake zuwa auren ki, yayi nasarar korarsa ko ya saka miki wani ciwo. Dan yan daf da fara kashe mutane, domin wata ƙungiyar asiri ce suke nemansa ido rufe yayi musu aiki. Idan suka sadaukar masa da jini, zai fara kisan mutane ne, kuma zai fara da mutane mafi soyuwa a gare ki"
Jiki na rawa Nana ta miƙa mata hannu, domin karɓar maganin.
Matar ta yi murmushi, haƙoranta suka bayyana baƙaƙe ƙirin da su, ta kama tafin hannun Nana, ta zuba mata maganin, da yawa.
Tana kama hannunta, Nana, ta ji tamkar an zare mata lakar jikinta, jikinta yayi wani irin sanyi, da ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ta kai garin maganin bakinta ta fara sha...
Ayshercool
08081012143
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002
P9
Ko da Nana ta sake lasar maganin, sai ta ga fuskar matar tana komawa baƙa ƙirin, tana ta fito da dogon harshe, tamkar na macijiya, wani abu mara kyan gani na futa daga bakin nata.
Iya ƙarfinta Nana take son ta yi addu'a, idan mafarki take ta farka, amma ta ji tamkar an saka dutse an tokare maƙogwaronta zuwa huhunta.
Babu tsammani, ta ga wata irin guguwa ta haɗu, Ƙaisar ya bayyana a tsakaninsu yayi wani irin mugun cilli da matar a gefe. Yayo kan Nana, ya zubar da sauran maganin hannunta, ya shaƙe mata wuya.
Wani irin kakari ta din ga yi, ta na amai dunƙunlen jini yana fitowa ta hancinta da bakinta. Ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa.
Ita ma Nanan, ya yi jifa da ita gefe, ta riƙe wuyanta tana numfashi da ƙyar.
Ya kalle ta a zafafe ya ce "Idan ki ka ci gaba da irin wannan gangancin, za a kashe ki a haka, babu wani mahaluki da zai iya raba ni da ke. Guba ta baki za ta kai jininki ayi tsafi da ke saboda tasirin taurarinki. babu wanda zai iya baki wani magani ya raba ki da ni, idan ki ka ci gaba da yinƙurin rabuwa da ni, za ki kashe kan ki da kan ki" yana maganar tartsatsin wuta na fitowa daga jikinsa, yana ƙona Nana.
A hankali ta buɗe idonta, ta ganta a kan shimfiɗarta, ta takure jikinta yana ta rawa, numfashinta yana fita da kyar. Wuyanta sai raɗaɗi yake yi mata, haka ma jikinta.
Ta kai hannu ta ɗauki fitilarta ta kunna, tana haska ɗakin, ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai. Jikinta ya ba ta wani abin tayi, su Jamila suka gudu suka bar ta a ɗakin.
Ta yinƙura da azama ta tashi tsaye, amma jikinta sai raɗaɗi yake mata, kafaɗunta kamar ba a jikinta suke ba.
Ayatul kursiyyu ta din ga karantawa, ta fita ta ɗauki buta, ta shiga banɗaki.
Tana fara fitsari ta ji ƙarnin jini, tana dubawa ta ga fitsarin jawur, jini a maimakon fitsari. Gashi ko kwana bakwai ba ta yi da gama al'ada ba. Ta wanke jikinta tayi alwala, ta koma ɗaki, gaba ɗaya ta kasa yadda har yanzu ba a cikin mafarki take ba.
Da safe ta fito ta yi aikace-aikace da za ta yi, Jamila ta ce "Nana me ya same ki haka?"
"A ina?"
"Jiya da daddare ki na ta kakarin amai, ki na kuka a bacci, yanzu kuma kalli jikinki, kamar an zane ki da bulala" Baba da ya fito daga banɗaki, shi ma ya kalli Nana.
Jikinta duk kwanciyar bulala, gashi ta ɗashe ta yi haske, kamar mara jini a jiki.
Nana ta kalli jikinta, ta ɗan taɓe baki ba ta ce komai ba, ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki domin yin wanka. Sai dai wannan karon ma, fitsarinta jini ne kawai yake zuba.
Kawai ta jingina da jikin banɗakin, ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta ta fara yin wankan. Sai dai tana zuba ruwan a jikinta, ta ji kamar fatarta za ta zazzago, jikinta ya hau kyarma.
Duk da a cikin banɗaki ta yi, haka ta furta a'uzubillah, ta cigaba da zuba ruwan a jikinta tana wanka, har ta kammala ta fito.
Ta yi alwala, ta shiga ɗaki ta shirya, tana kallon Baba yana kallonta, amma ba ta gaishe shi ba, haka kurum ta tashi da matsanancin ɓacin rai, ko ganin Baban ba ta son yi.
Ba ta kula kowa ba, ta fice ta tafi makaranta.
Gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga jiri tana fama, dan haka a cikin aji ta yi zamanta, ta kifa kanta a kan tebur, tana ta kewar rashin Auwal.
*****
"Safiyya"
"Na'am Hajjaju"
"Yaya kin yi magana da Jamila kuwa?"
"A'a yanzu dai nake saka ran zuwanta"
"Dan Allah, ki ɗan bugi cikinta ki ji, yarinyar nan ta sha lemon kuwa?"
Maman khairat ta ce "In sha Allah, zan bugi cikinta zamu yi magana da ita"
"Amma ina fatan, ba ki gaya mata ko na mene ne ba"
"A'a haba Hajiya, ya ma za ayi na gaya mata, ai kin ce ko wani ma ya ci ba komai, ita ɗin dai ake so ta ci, zan tambaye ta idan ta zo"
"To shikenan, na gode sai na ji ki"
*****
Ƙamshin turare ne ya cika wa Nana hanci, sai dai ba ta motsa ba ko ta buɗe idanunta ba.
Teburin da take kai, ya ɗan bubbuga, sai a lokacin ta buɗe idonta a hankali. Dishi-dishi ta fara gani.
A hankali idonta ya washe, ta ɗaga kai ta kalle shi.
Yayi murmushi ya ce "Anty ya dai ki ke bacci, ko babu lafiya ne?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli agogon ajin nata ƙarfe biyu. Tunani ta hau yi, tun da ta shigo da safe take wannan baccin, ko kuwa?
Maganar Muhsin ce ta dawo da ita hankalinta ya ce "Anty kin ga na gama" yayi maganar yana nuna mata littafin sa, da ya cika page guda da A.
"Afuwan Anty Nana, direbansu ya yi tafiya ne, mahaifiyarsa babu lafiya, ni kuma ba ni da isasshen lokaci, na shiga wani meeting ne, shi yasa na daɗe ban zo ɗaukarsa ba, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci". Jinjina kai kawai ta yi ta tashi, ya ce "Mu je sai mu sauke ki a hanya" sai dai haryanzu ba ta yi magana ba, ta bi shi su ka tafi.
Jamila na zaune, tana ta zaman kashe wando a gidan maman khairat, kamar yadda ta mayar da hakan ibada, tana tayata aiki su na hira.
"Ni kuwa jiya kin ci abincin jiya Jamcy?"
Jamila ta ce "Lallai ma Anty Safiyya, me zai hana ni ci, na yi abincin kuma na kasa ci?"
"Wallahi ni gaba ɗaya kasa cin abincin na yi, na ce da na sani, na ce ki tafi da shi duka"
Jamila ta ce "Subhnallah, ko dai Khairat za a yi wa ƙani"
Tayi murmushi ta ce "Rufa mini asiri, wallahi sai da ki ka tafi na ga kamar abincin ba zai ishe ku ba, kuma har su Nana duk sun samu sun ci?"
Sai da Jamila ta yi mamakin tambayar, amma ta ce "Eh mana, Nana ce ma babu lafiya, ba wani ci ta yi ba, kin san 'yar ƙi faɗi ce, sai na je da abu sau shurin masaƙi amma babu lallai ta ci"
"Eyya, to ai ba komai, mun riga mun zama ɗaya Allah ya ba ta lafiya, ta sha lemon ma?"
"Eh amma ba da yawa ba"
Safiyya ta jinjina kai ta ce "Dan Allah ki yi mata sannu"
Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "To, za ta ji, kin san ita kullum cikin ciwo take ne, abin nata ba na ƙare bane ba"
Suka ci gaba da hira, ƙasan zuciyar Safiyya, cike da farin ciki
*****
Ƙarfe huɗu da rabi na yammaci, sannu a hankali yake ƙarewa garin kallo, duk ya kwana biyu baya garin, amma ba wani abu ne ya canza ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin kewar Kanon dabon.
Tun daga can babban titi ya sauka, ya saɓo hanya, domin ya samu isashshiyar damar ƙarewa garin kallo, yadda yake so.
Dandazon mutane ya hango a wani wuri, mutane na ta surutu da hayaniya.
Har ya yi gaba, kawai ya dawo da baya domin ganewa idanunsa abin da ya tara wannan cincirindon al'ummar.
Ya din ga kutsawa, yana ture mutane.
Kawai ya tarar da wata matashiyar budurwa a kwance a wurin, sai dai ta juyar da fuskarta ba a iya ganin fuskarta.
Ya taɓa wani mutum ya ce "Malam lafiya, me ya faru don Allah?"
Mutumin ya ce "Wallahi tun azahar, muka ganta a kwance a wurin nan, an zata ma ko ba ta da hankali, ko kuma ba ta da lafiya, amma jikinta fes babu datti ba alamar hauka a tare da ita. An yi anyi ta tashi ko motsi ba ta yi, kuma tana da rai. An duba jakarta babu waya sai maka da kuɗi, yanzu ma dai an kirawo 'yan sanda".
Bai ce uffan ba, cikin azama ya nufi kanta, mutane na ƙoƙarin hana shi, amma bai saurari kowa ya je kanta ya ɗago ta.
Idanunta a rufe, sai dai hawaye da yake ta fita ta gefen idonta, ga jikinta zafi tamkar wuta.
A sanyaye ya ce "Nana" shiru ba ta amsa ba.
Miƙewa yayi yana ƙoƙarin ɗaukarta, wani ya ce "Malam lafiya, ina zaka kaita?"
"Ƙanwata ce" ya faɗa a taƙaice, ya fita ya taro adaidaita sahu. Bai sake tsayawa yi wa kowa bayani ba, ya saɓa Nana ya shiga adaidaita sahu, ya tafi da ita.
Mama na tsakar gida tana tankaɗen tuwo, sai ganinsa tayi a tsakiyar tsakar gida.
Suwaiba da take jan ruwa ya kalla ya ce, "Shimfiɗa mini tabarma a tsakar gida"
Ta ajiye gugan, ta ɗaukko tabarma, ya kwantar da Nana a kai.
Ya ɗebo ruwa a kofi, ya zo ya zauna a kusa da ita, yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame sosai da sosai.
Cirko-cirko mutanen gidan suka yi, su na bin sa da kallo, kowa da magana a bakinsa, amma babu damar furtawa.
Ya tofa ayatul kursiyyu, da falaqi da nasi, kowacce da bismillah, ya shafa mata ruwan a fuskarta, da tafukan hannayenta. A hankali yake bin jikint da kallo, yana mamakin shaidar duka ce, ko ta ƙonuwa a jikinta.
"Nana" ya kira sunanta. Cikin sa'a sai ta buɗe idonta a hankali, ta sauke a kan fuskarsa.
Shiru ta yi tana kallon sa, kamar ba ta taɓa ganin sa ba, zuciyarta na raya mata kawai tarkacen mafarkin da take yi ne. Ta yi shiru, ta tuna ta shiga motar baban Muhsin, su na tafe a hanya, a kunnenta ta ji ana ce mata, ga Auwal can a marrraba, nan da mintuna goma tirela za ta taka shi.
Babu shiri ta tsayar da baban Muhsin, bai gama parking ba, ta buɗe motar ta fita daga nan kuma, sai ta ɗimauce ta rasa gane gaba da baya.
Mayar da idanunta tayi ta sake lunshewa.
"Ma'u" ya kuma kiranta yana matsa hannunta.
Ta sake kallonsa a hankali ta ce "Wai da gaske kai ne?"
"To da waye? Dama haryanzu ba ki warke ba, ki na wannan ciwon Nana? Kuma uban waye ya dake ki duk jikin ki ya tashi haka?" Ta yinƙura ta tashi zaune, kawai ta fashe da kuka.
"To kukan uban me ki ke yi kuma? Na ce uban wa ya dake ki?"
"Ba dukana aka yi ba" ta bashi amsa tana share hawayenta.
"To me ya kai ki yin bacci a titi, maza sun baibaye ki, kamar ƙudaje sun ga mangwaron Binta suga"
Ba ta bashi amsa ba, ta ci gaba da kuka.
Ya tsuke fuska ya ce "Dalla yi mini shiru, ina yi miki magana ki na wani kukan banza"
"Me yasa ka tafi ka bar ni?" Ta yi magana cikin kuka.
Guntun tsaki yayi, ya ce "To dai ba ga ni na dawo ba? Uban me ake tsinana mini a gidan idan na zauna, yanzun ma tunaninki ne ya addabe ni, nake ta mafarkinki shiyasa na taho, kuma ina zuwa na tarar da dandazon mutane, ina dubawa na ga ke ce. Allah dai ya tsinewa wannan matsiyatan aljanun naki banzaye marasa imani"
Za ta yi magana, Baba yayi sallama suka amsa, sai dai ya ja tunga ya tsaya, ganin wanda bai taɓa zato ba a gidan.
"Kai imrana, uban me ka ke yi mini a gida? Me ya kawo ka gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana