Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
sai da lokacin fita salla yayi, ta tashi abu ya gagara ta ji gaba ɗaya tamkar an saka sarƙoƙi, an nannaɗe mata ƙafafuwanta.
Duk wani ƙoƙari da za ta yi domin ta tashi abu ya gagara, kawai ta fashe da kuka.
Amira ta dubeta ta ce "Nana, menene ki tashi an tafi salla".
Cikin kuka ta ce "Amira na kasa tashi ƙafata ciwo take yi mini, kamar ana karya ni"
Ganin yadda Nana take kuka, sai jikin Amira yayi sanyi, a baya da yawa ana zaton Nana ƙarya take abubuwan da take yi, amma yanayin da take ciki yanzu dole mutum ya tausaya mata.
Amira ta fita ta kirawo malam Auwal, suka dawo tare, ko da suka dawo suka tarar ta mimmiƙe tamkar gawar da ta jima da rasuwa.
Cike da tausayawa shi ma ya tsuguna a kanta, ya kalli bakinta na ta fitar da kumfa, yatsunta daga na hannu har na ƙafa, sun lanƙwashe.
Ayoyin suratul jinn, ya fara karantawa yana tofa mata, ya idar ya koma ayoyi biyar ɗin farko na suratul baƙara, ya ɗan jima yana yi mata karatu kafin jikinta yayi saki, sai dai ba ta tashi ba.
Sosai tausayin Nana yake ratsa Auwal, Nana tana buƙatar kulawa ta musamman daga namiji mai addini, da haƙurin gaske, idan Allah ya taimake ta tayi aure, tasirin larurarta zai ragu idsn aka dagewa addu'a da kulawa sosai. Kwanakin nan jikinta ya tsananta, kusan kullum ba ta da lafiya.
Ganin ta yi bacci, ya sanya ya cewa Amira ta tafi wurin salla, su ƙyaleta ta huta.
Ayshercool
08081012143
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA(002
7
Wunin yau Nana, a ɗaki tayi shi, ta ɗauki azumi tana tawasalli da azumin da fatan Ubangiji Allah yaye mata larurar da take damunta ya ba ta lafiya.
Saboda ita kanta yanzu lamarin yana matuƙar ba ta tsoro.
A tsakar gida take ji yo radion mama, wani likita yana ta bayani, a kan cutar depression cutar damuwa, anxiety disorder cutar fargaba, shaye-shaye da farfaɗiya.
Shiru tayi, tana nazarin alamomin cututtukan baki ɗaya, cike da fatan ta gano wanne ne yake damun ta a ciki. Sai ta ji tana da wasu daga cikin alamomin anxiety disorder, wato cutar fargaba, sai kuma ta ga wasu alamomin na ciwon damuwa ne yake damunta. Tabbas akwai abubuwa da dama na ƙaluble daa suke binne a cikin zuciyarta, wanda galibi marasa daɗi ne. Ba ta tunanin akwai wani abu na farinciki da ya faru da ita, da za ta ce ba zata manta ba, gaba ɗaya rayuwarta a kan siraɗin ƙaddara take. Sai dai ta na godewa Ubangiji, da ya bar ta da imaninta.
Haka kurum sai ta ɗan ji salama a ranta, ta fara saka ran larurarta ta asibiti ce, idan ta je za ta samu mafita.
Tayi ajiyar zuciya, ta lumshe idsnaunta, kawai ta ji an bushe da dariya.
Ta buɗe idonta da sauri, ta waiwaya ba ta ga kowa ba. A take ta tuna da ire-iren mafarke-mafareken da take yi, da yadda mutumin nan yake tilasta mata yarda da sharaɗinsa na sai ta bayar da magani. Ta tuna ire-iren gane-ganen da take yi, a zahiri kuma ba ta ji likitan ya yi bayanin makamantan wannan alamomin a cikin bayanin cututtukan da ya yi ba, a take ta karaya ciwon dai da ba ta son ace shi ne da ita ya tabbata shi ɗin ne dai, ko ta na so ko ba ta so aljanu ne suke damunta.
Ko ta yi yinƙurin kawar da tunanin, sai ta tuna yadda take ganin mutumin nan a mafarki, da irin maganganun da suke yi da shi.
Kawai ta fashe da kuka, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a halin da take ciki, dan wasu sun gaza yadda ciwo ne Allah ya jarrabe ta, kawai ta ɗorawa kanta ne, dan samun attention ɗin mutane wato hysteria a turance.
Ta tashi ta ɗaukko bagcon kayanta, ta din ga ciro magungunaa, kala-kala da ake ba ta, da sunan maganin aljanu, leda-leda ta din ga fito da su. Ta gama tattare su wuri guda, ta fita tsakar gida ta din ga tura su a murhu ɗaya bayan ɗaya. A take gidan ya kaure da ƙauri da hayaƙi mara daɗin shaƙa.
Mama ce ta fito tana faɗa "Ƙaurin meye haka mara daɗi kamar gidan 'yan bori?" Ta tarar da Nana a bakin murhun ta na ci gaba da ƙona kayan.
"Ke meye haka? Uban me ki ke tura mini a murhu?" Nana ta ɗago ta kalleta, ta yi shiru ta ci gaba da abin da take yi.
Tari mama ta hau yi, ta ce "Idan ma uwarki ce ta aiko miki da wata tsiyar ki ke babbaka mini, to baƙar aniyarku ta koma kanku, dan na fi ƙarfin ku daga ke har ita" gaba ɗaya hankalin Nana ba ya kan Mama, zancen zuci kawai take yi, tana kallon yadda kayan ke babbakewa a cikin murhu.
Ganin Nana ta mayar da ita mahaukaciyar ƙarfi da yaji, ya sanya ta koma gefe ta zauna, ta na cigaba da ƙananan maganganu.
Ko da Nana ta yi buɗa baki, kunun tsamiya kawai ta samu ta sha, hakan bai dame ta ba, ta mayar da hankali sosai wurin roƙon Allah samun lafiya, da miji na gari.
Yaro ne yayi sallama, ya ce ana kiran Nana a waje.
Jamila ce ta ce masa ya ce tana zuwa.
Nana ta fito ƙasan zuciyar ta cike da murnar, malam Auwal ya dawo, akwai yiwuwar ya fito ayi auren, tun da ya dawo.
Sai dai tayi turus, da hasken fitilar wutar lantarki ya haske mata fuskar Saleh, ƙanin mijin Ummi.
Wani takaici ne ya kama ta, amma ta dake ta ƙarasa fuskarta babu yabo babu fallasa.
"Hajiya Nana, barka da fitowa ya ki ke ya gida?"
"Lafiya ƙalau, ya su Anty Ummi?"
Saleh ya ce "Duk su na nan lafiya" ya ɗan yi shiru, sannan ya numfasa ya ce "Na san dai Ummi, ta yi miki bayanin komai ko?"
Nana ta kalle shi ta ce "Wane bayanin kenan?"
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ba ta kawo miki kaya ba, ta ce in ji ni?"
"Ohh na tuna, na gode sosai da sosai"
Yayi murmushi ya ce "Ai ba wani abu, ta ce Baba ya ce ba sai na wahalar da kaina ba ma, na yi miki kayan ɗaki kawai ba sai an yi lefe ba. Kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai mu tafi can lagos tare wurin sana'ata, akwai ɗakin da nake haya komai akwai a ciki na buƙata"
Nana ta sake kallonsa ta ce "Baban bai gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba?"
Ya gyara tsayuwarsa ya matsa kusa da ita ya ce "Ai duk wannan ba wani abu ba ne ba, muddin za a samu fahimtar juna da ni da ke. Wallahi a matse nake ne Nana, ni ko wannan juma'ar ta jibi, a ɗaura ki tare a gidanmu kan na gama shirin tafiyarmu ikko" yayi maganar cikin numfarfashin rashin gaskiya, yana ƙoƙarin ya kai hannunsa jikinta.
Ja da baya ta yi, cike da takaici sai dai kafin ta yi magana, ta hango Auwal a tsaye, hannunsa riƙe da leda ya tsaya sak yana kallonsu.
Ta kalli Saleh da yake ƙoƙarin kuma matsowa, ta kalli in da Auwal yake, kawai ta juya ta shiga gida, gabanta yana faɗuwa, ba ta san ma me yakamata ta yi ba.
Kawai ta shiga ɗaki ta kwanta. A waje kuwa Gaddafi ne ya tarar da Saleh, suka gaisa Gaddafi ya ce "Mutumina yau kai ne a gidan namu?"
Saleh ya ce "Wallahi kuwa, na zo wurin Nana, kuma mu na cikin magana ta shige gida, ba ta ce mini komai ba"
"Ita Nanan?"
"Eh wallahi, ina so mu fahimci juna da ni da ita, ayi a wuce wurin kawai"
"Ka kwantar da hankalinka, kamar ka aureta ka gama ne, har wani zaɓi take da shi, kai da zaka taimaka mata. Ka manta da ita kawai ka turo a kawo kuɗi"
Saleh ya washe baki ya ce "Allah mutumina"
"To me za a jira, kawai ayi abin da ya dace" Nan ya tsaya suka ci gaba da hira, saboda Gaddafi ma a Lagos yake neman kuɗi, kuma su na haɗuwa da Saleh sosai.
Sai da suka gama hirar, sannan suka yi sallama, Gaddafi ya shiga cikin gidan, ya dira wa Nana bala'i da cin mutunci a tsakar gida. " 'yar gidan uban waye ke, da za ki hurawa mutane hanci, ke da da za a taimakawa, mahaukaciyar banza da ta wofi. Ki na yawo a kwararo ki na wannan tamɓelen ki hana jama'a bacci, kowa ya san mahaukaciya ce ke a unguwar nan, kin samu ana sonki, amma ki bujire. To wallahi ba ki isa ba dole ki auri Saleh, ki fita ki bar gidan nan ƙila ma rashin aure ne ya sanya ki ke wannan haukan "
Nana ta toshe kunnneta, saboda zafi da tururin da zuciyarta take yi, ji take tamkar ta ɗura masa ashariya, ta rama cin mutuncin da yake yi mata, amma ta din ga maimaita Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Baba ne yayi sallama, ya tarar da Gaddafi yana bala'i, da ya tambaye shi ba'asi, ya ji da Nana yake, sai ya karɓa ya ɗora shi ma.
Nana ta rasa wannan jaraba, babu wanda aka tsangwama yayi aure a gidan sai ita, saboda su ga babarsu a gidan, ita kuma ga rashin uwa, ga larura ga shi duk wata hanya da za ta samu mahaifiyarta ko a waya, Baba ya datseta, har yana nema ya yi mat baki.
'meye na damuwa ma, matar da ko in da ku ke ba ta zuwa, ta ga halin da ku ke ciki, balle ki gaya mata halin da ki ke ciki, ta saka ki a addu'a, ko kuma t nema miki magani' wata zuciyar tayi mata tunin, abin da ba ta so, domin in dai tana ire-iren waɗannan tunanin, ta na jin zafin mahaifiyarta a ranta.
"Ke Nana, zo ga waya Atine za ta yi magana dake" maganar Baba ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula.
Gabanta ne ya faɗi, wata sabuwa in ji 'yan caca, ba ta ƙaunar duk abin da zai haɗata da matar nan a rayuwarta.
Ba tare da ta amsa ba, ta tashi ta fita.
Baba ya miƙa mata waya, ta karɓa hannunta na rawa ta saka a kunneta, ta yi shiru.
"Ke ma'u ki na ji na?"
"Eh" ta amsa a cunkushe.
"Dan ubanki sai ki yi mini shiru, ko gaishe ni ba za ki yi ba, har kya yi wa mutane ƙaryar iskancin aljanu, mu da a ka yi gadon bori a gidanmu.
Nana ta yi shiru, tana mamkin yadda jahilci, ya sanya yaya Atine alfahari da harkar shirka, da shi ne musababbin gadar mata da bala'i, kamar yadda mutumin da take mafarki da shi, yake iƙrari.
"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, ranar asabar ki yi kuɗin mota, ki taho gidana, akwai gidan wani mai magani da zan kai ki. A baki maganin aljanu da na farin jini, aure dole ki yi shi babu fashi, ko shi wanda ba kya so ɗin ko wani daban. Ke wannan baƙin jinin kamar an jiƙa hatimin jaɓa an baki, daga nonon babarki ki ka shawo shi. Mu zuriyarmu farin jini ne da su wallahi, babu mai nauyin jini"
"Yaya atine, idan ni a nonon uwata na sha, su suwaiba a naki nonon suka sha? Tun da Uwar tawa ba ta nan, menene na sakota a zancen ki, koma wani bala'in ne ya same ni, ba duk a dalilin shirka da iyayenku suka yi ba ne, da har ki ke alfahari da ita" ita kanta Nana ba ta san yaya aka yi, suke fita daga bakinta ba, saboda yadda ranta ya ɓaci zuciyarta take tafasa fiye da kima.
"Ma'u ni ki ke gaya wa haka?"
Gaddafi ne ya yi kan Nana, amma Baba ya tare shi, ya ce "Rabu da ita, ka na taɓa ta babu lallai, mu yi bacci mai daɗi a gidan nan, wataƙila ma ba ita ba ce ba, ƙyale ta"
Ta ajiye wa Baba wayarsa, ta koma ɗaki.
****
Cike da damuwa Auwwal ya koma gida, 'yar tsarabar da ya yi wa Nana, ya bawa ƙannensa, wani irin kishi ya addabi zuciyarsa, sai dai kuma yanayin kallon da ya ga tana yi wa wanda suke tsayen ne, bai gama gane kansa ba.
"Auwwalu" Umma da ta gama kasa gurasa da naman gabanta.
Ya kalleta ya amsa da "Na'am Umma"
"Magana nake son mu yi da kai ta fahimtar juna. A matsayina na mahaifiyarka".
Ya tattara mata hankalinsa baki ɗaya cike da ladabi.
"Ka zo mini da maganar aure, na ce maka ka dakata, ba yanzu ba tukuna. Karo na farko abin da ba ka taɓa yi mini ba, ka kai ƙarata wurin kawunka ƙanin mahaifinku. Ya zo har gidan nan baka nan, mun yi magana ta fahimta da shi sosai na kuma fahimce shi, har ya gaya mini ka gaya masa sunan yarinyar da gidan mahaifinta. Na ce masa to ya ɗan saurare ni. Na zo da kaina na saka ayi mini bincike, shi ma kawun naka na saka yayi ta nasa ɓangaren. To magana ta domin Allah ba zan yadda ka auri wannan yarinyar ba, ashe ita ce wadda ka ke bani labari mara lafiyar nan. 'yan unguwarsu sun tabattar da ba ta da wata matsala sai wannan iskokai, kuma ana kyautata zaton kakaninta 'yan bori ne, ni kuma gaskiya ba zan yadda a ɓatawa tsatsonmu suna ba, a sa a gada wa zuriya masifa ba. Dan haka mun gama magana da shi, shi ma zai neme ka ya kuma yi maka magana. Ya ce mini ya saka wani abokinsa ya yi naka hanyar tafiya Qatar ko Allah ya sa a dace da kyakyawar sana'a. Idan Allah ya sa ka tsaya da ƙafarka ka samu wata yarinyar mai kyakyawar nasaba da lafiya ka aura. Ba cin mutunci ba amma an ce yaran gidan ma galibi su ne suke ciyar da kansu, uban ba ya sana'ar komai, yarinya budurwa kuwa duk in da aka bari ta ciyar da kanta, ai an samu matsala. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka" da ƙyar Auwwal ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa. Mama tana da gaskiya amma idan aka ce waɗannan abubuwan kacokan za a duba a ɗora mata laifi shikenan ba za a aure ta ba kenan? Nan aka zo neman auren ƙamwarsa aka ce ba za a aureta ba, 'yar mace ce, aka yi ta ɗauki ba daɗi kafin auren ya yiwu, amma Umma ta manta da wannan, ita ma tana hango aibun da ba ya cikin jerin abin da zai iya hana aure a shari'a a yanzu".
"Auwalu ka yi shiru, ko baka yarda ba zaka bujire ne?"
"A'a subhnallah, na amince Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi, amma Umma, da a bar maganar Qatar ɗin nan, idan Nana ce na haƙura amma..
Ta tari numfashinsa ta ce "Ai mun gama yanke hukunci, biyayya ce kawai taka Auwal"
Ya risuna ya ce "Shikenan Allah ya wuce mana gaba" ya tashi jikinsa a sanyaye ya bar ɗakin Umma, ya koma shagonsa.
Washegari da safe, ta je gaida Baba, bayan ta shirya za ta tafi wurin aiki, amma ya ƙi amsawa, ya ma tashi ya bar wurin.
Cikin damuwa ta koma ɗakinsu, ta ɗauki jakarta, ta kalli Jamila, da ke ta danna waya ta ce "Jamila, dan Allah ko kin san laifin da na yi wa Baba, ya ƙi amsa gaisuwata?"
Jamila ta ɗago ta ce "Lallai Nana, jiya da ki ka gaggaya masa magana, da shi da yaya Atine, ko har kin manta?" Shiru Nana ta yi, ta fara jin wata ƙara a cikin kanta, ta jingina da bango ta dafe kanta ta ce "Subhnallah"
Jamila ta tashi zumbur, ta ja da baya ta ce "Ya dai?"
"Wallahi Jamila, ban san ya aka yi hakan ta faru ba, da na tashi daga bacci, tunanin abin nake yi kamar mafarki ba a gaske ya faru ba, gaba ɗaya na kasa gane kan rayuwata, amma shikenan" kawai ta fita daga ɗakin, ta saka takalmanta ta fice.
A ƙofar makarantar, danƙareriyar motar ta yi parking, gilasanta baƙaƙe ne ƙirin, ba a ganin wanda yake cikin motar.
Yaro ne ɗan shekaru uku, ya fito daga cikin motar, ya zura hannunsa ya ɗaukko akwatin abincinsa, bai tsaya rufe motar ba ya nufo wurin da Nana take tsaye, yana washe baki cike da murna.
Sakin fuska ta yi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ɗaga shi tana murmushi. Sai dai yayi shiru yana kallonta, ganin alamun damuwa a fuskarta.
Ta shiga da shi cikin makarantar, ta fara tafiya da shi aji, in da take ajiyewa ɗaliban nata, kwanukan abincinsu, ta juyo za ta kama hannunsa su fita, amma ya ƙura mata ido.
Cikin harshen turanci ta ce "Muhsin let's go" (Muhsin mu tafi)
"Anty sorry" (Anty ki yi haƙuri) ya furta cikin damuwa.
Kallon sa tayi ta ce "Meyasa ka ke bani haƙuri?"
"Anty waye ya dake ki, ki ka yi kuka?" Ya faɗa cike da yarinta. Haɗiye hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata tayi, ta ce "Atishawa na yi, mu tafi assembly ground"
Ko da suka je wurin assembly, an yi tsit ana addu'a, amma ɗalibanta na ganinta, suka fara tsalle, su na kiran sunanta.
"Anty, ko ki saka 'ya'yanki su yi mana shiru, ko ki ja su ku tafi" vice principal ya gargaɗeta. Cikin hikima ta sanya yaran yin shiru, yaran da take jin ƙaunarsu, har cikin zuciyarta.
Lokacin tashin yaran, duk an zo an ɗauke su, saura muhsin da ta biyewa, take yi masa lilo, kafin a zo ɗaukarsa.
Daga ita sai shi a harabar wurin nishaɗin yara, ta ɗora shi a wannan lilon ta sauke shi a wancan.
"Laa Anty kin ga Daddy" yayi maganar yana nuna bayanta.
Ko da ta waiwaya, mutumin nan ne da suka haɗu a ofishin director, ta sauke muhsin, ya nufi wurin babansa da gudu, ita kuma ta ɗaukko masa jakarsa da lunch box ɗin sa.
Har ƙasa ta risuna ta gaida shi, ya amsa cikin sakin fuska ya ce "Ya yaran naki, ya ƙoƙari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
"Madalla mu na ta goɗiya, mun yaba da ƙoƙarin da ki ke yi wa yara, Allah ya saka da alkhairi"
"Amin na gode sosai"
Har zai juya su tafi ya ce "Amma yaran naki, sun tashi gaba ɗaya ko?"
Ta ce "Eh, sun tafi dama Muhsin ne ya rage, zan tafi nima"
"To mu je, sai mu sauke ki a hanya mana"
Nana ta ɗan yi turus ta ce "Bakomai na gode, ai babu nisa sosai"
"A'a bakomai, ai ni na ce muje sai