BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   47 / 64

138K to 141K   out of 190K words

kyautu mu sani"

Baba ya taso kamar zai dake su ya ce "Kin ga ku bi hanyar da ku ka shigo mini gida ku fita".

"Dan Allah Malam Isa ka yi haƙuri, abin duk bai kai haka ba, ka bari a kaimu ko gidan nata ne, mu ga ɗakinta, mu gaisa da ita, mu ba ta saƙon mahaifiyarta"

"Na yi muku iyaka da 'ya ta, ba zaku taɓa ganinta ba, ba ta buƙatar ku, ku bar mini gida, kafin na yi muku ɗibar albarka"

Ganin babu mutunci a lamarin Malam Isan, ya sanya suka kwashi kayan da suka zo da su, su ka fice.

Ayshercool
08081012143

40

Hargowa da bala'in da Baba ya yi wa su Adda Rakiya, ya yi masifar ɓata musu rai, a zaton su duk abubuwan da suka faru a baya sun riga sun wuce, dan aure ya mutu ba ya nufin a wanzar da gaba a tsakanin yara da mahaifiyar su, ko a yanke duk wata da za su yi alaƙa da ita.

Ga gajiyar tafiya da su ka sha a mota, amma Baba ya yi musu wannan mummunar tarbar.

Can gidan su Nana kuwa, ana ta neman Yusra, ba a ganta ba, hankalin Hajiya Halima ya yi mugun tashi, suka fito neman ta harabar gidan tare da Siyama.

Gurin Sayyid su ka nufo, Hajiyar take tambayarsa "Dan Allah yarinya ba ta zo ka buɗe mata ƙofa ta fita ba? Wata 'yar fara haka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"Na shiga uku, ni kuwa ina yarinyar nan ta shiga haka? Kirawo mini Nuradeeni a waya, ko sun fita tare?"

Siyama ta ce "Su fita tare su je ina, su da ba shiri suke yi ba, ina zai kai ta? Wataƙila tana cikin gidan nan wani gurin ta samu ta shige kawai"

"To tana cikin gidan nan, mu ganta mana"

"Ki yi haƙuri mu koma, mu ci gaba da duddubawa"

Nana kuwa ba ta san me ake yi ba, tana zaune a gefen Yusra, tana bin karatun Alkur'ani da ta kunna a wayarta. Ta ji daɗin yadda take raira karatun yau, ba tare da ta ji kanta ya fara ciwo ba, ko ta fara jin sanyi ba. Yusra kuwa baccinta take yi da gaske.
A ƙalla ta kai awanni biyu tana bacci, har Nana ta idar da karatun Alƙur'anin, ta ɗora girki. Ta kammala babu jimawa ta farka daga baccin. Nana ta saka ta yi alwala, ta ba ta hijjabi ta yi alwala ta yi salla. Ta sake zuba mata abinci ta ci, sannan ta ce "Mu je na raka ki cikin gidan, zan zubawa mijina abinci shi ma na ba shi"

Ta kalli Nana ta ce "Ki na da miji?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh, ina da shi, shi ne a waje yake yi muku gadi"

Yusra ta ce "Mhmm ni da na fara rashin lafiya, shekara biyu kenan, mijina ya sake ni, ya ma yi aure ba zai zauna da ni ba. Ba wanda ya san me nake ji, amma ke na ga kamar kin san me yake damuna, ke ba za ki ce ƙarya nake yi ba. Mami ta ce "Ina sane na kashe aurena, na ji haushi sosai da sosai"

Nana ta riƙe hannunta ta ce "Ki yi haƙuri, na ki ƙalubalen kenan, tabbas na san ciwon nan, na san babu daɗi, kuma babbar jarrabawa ce a ce na kusa da mu sun kasa fahimtar mu, su din ga ganin muna sane muke yin abin da muke. Dan haka dolenmu ne, mu dage mu yi ta adduo'i da azkar domin Allah ya bamu lafiya"

Ta jinjinawa Nana kai ta ce "Na gode sosai da sosai"

Nana ta tashi suka fito daga ɗakin, dama Sayyid a matse yake ya shiga ɗakin, zaman Yusra a ɗakin ya hana shi shiga.

"Wannan ne mijin naki?"

"Eh shi ne"

Ta ce "Sannu dattijo"

Ya ɗago ya kalle ta, ya ɗaga mata hannu. Ta yi murmushi kawai.

Nana ta ce "Dattijo kuma?"

"Eh, ke matashi ki ke gani, ni kuma Dattijo nake gani, duk da kema ki na ganin haryanzu dai ki na wasi-wasi ne"

Nana ta ce "Haula"

Ta amsa da "Na'am uwar gijiyar Ƙaisar"

"Amma me yasa za ki yi mini haka? Matar ta farfaɗo ta samu ta ci abinci, ta yi bacci kuma kawai sai ki zo za ki sake burkita ta"

Yusra ta yi murmushi ta ce "Tuba nake, wallahi ba da wata manufar na zo ba, gaisuwa na zo kwasa kuma na yi sai anjima"

Nana ta ɗan ƙura wa Sayyid ido, amma ya ƙi kallonta, ya tafi ɗakin su. Ta jinjina kai a hankali ta ce "Biri ya yi kama da mutum"

Har cikin falon Nana, suka shiga tare da Kubra. Hajiya Halima na ganinsu ta miƙe ta ce "Laa a ina ki ka ganta? Tun ɗazu muke bulayin neman ta a cikin gidan nan"

Nana ta ce "Subhnallah, wallahi ban sani ba, gani na yi za ta fita na hana ta, mu na tare da ita a ɗakina, kuma na yi ragon azancin ban zo na sanar miki ba".

"Mami ta bani abinci, kuma na yi bacci ma"

"Ikon Allah, yau kin yi baccin kenan?"

Yusra ta ce "Eh, na yi bacci sosai mai daɗi, na ga ma Sagir a baccin"

A fusace Hajiya Halima ta ce "Ba za ki daina maganar Sagir ɗin nan ba ko? Mutumin da ya riga ya sake ki, ba zai zama da ke ba, mene ne na zancen sa "

Siyama kuwa da ranta ya ɓaci ta ce "Amma baiwar Allah wannan shiga hakki ne, tun ɗazu mu ke neman ta fa, kuma saboda wulaƙanci da rashin mutunci mijinki ya ce bai ganta ba, wannan ai gidadanci ne da rashin hankali"

"Laifina ne, ba nasa ba ki daina zaginsa dan Allah, ba na jin daɗin hakan"

Hajiya Halima ta ce "Siyama ya isa haka dan Allah, amm Nana sunan ko? Mun gode sosai da sosai"

Nana ta juya za ta tafi, Yusra ta ce "Ƙawata sai anjima"

Nana ta yi mata murmushi ta ce "Kar ki manta abubuwan da na gaya miki fa"

Ta amsa mata da "To"

*****

An ɗaga Shukura daga kwanciyar da take yi, an yi mata wanka, aka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, tana zaune tamkar gawa.

"Shukura yanzu haka rayuwa za ta kasance mutum babu tawakalli kenan? Da Allah ya baki lafiyar ba za ki gode masa ba kenan?"

"Mummy"

"Naam"

"Kin ga gawar abin da na haifa?"

Hajiya Amina ta ce "Eh mana, awansa shida a nursery ya rasu, sai da na gan shi sannan Sagir ya tafi da shi ya binne."

Hawaye ya gangaro kan kumatunta, ta ce "Amma me yasa ba a bari na gan shi ba?"

"Shukura ba kya cikin hayyacinki, za a yi ta zama da gawa ne ba a binne ba? Ai ba zai yiwu ba"

Ta ce "Haka ne, amma ina baban Haidar ɗin yake?"

"Bai daɗe da tafiya ba ki ka tashi, kuma da na san za ki farka da wuri an jira, kin gan shi. Amma na san ya ɗaukar miki shi a hoto ai. Na tura family group ma, amma dai na ƙara gaya musu, ban da zuwa dubiya ba kya jin daɗi"

Ta ce "To Mummy na gode sosai, tun da dai kin ce mini kin ga gawar babyn shikenan, Allah ya sanya mai ceto ne. Ke ma Allah ya baki ladan ɗawainiyar da ki ke ta yi da mu"

Cikin jin daɗi Hajiya Amina ta ce "Amin ya Allah, ko ke fa Auta, dan Allah ki ci abincin ko na ji daɗi"

"To Mummy amma saboda ki ji daɗi zan ci kaɗan, ba na son cin komai"

"Ba komai, hakan ma na gode sosai da sosai Autar Mummy"

Haka Shukra ta din ga yaƙi da zuciyarta, da ƙoƙarin kawar da tunanin mafarkan da take yi.

*****
Har Gaddafi ya gota matan, da suke zaune a kan barandar ƙarshen layin, sai kuma ya dawo da baya ya ce "Sannun ku"

Su ka amsa masa da "Yauwwa sannu"

Ya ce "Kamar 'yan uwan babar su Imrana"

Adda Rakiya ta ce "Laa Gaddafi kai ne?"

Sai ya gyara tsayuwarsa, su ka gaisa. Ya ce "Ya na gan ku a nan?"

Adda Rakiya ta so ta kare, amma Fati ta gaya masa abin da ya faru.

Ya girgiza kai ya ce "Ku yi haƙuri, abu ne da ya faru ya riga ya wuce, amma an ƙi bari ya wuce, ake ta nanatawa, bari na nemo muku Nasiru, ya raka ku."

Bayan tafiyar sa Rakiya ta ce "Fati, wannan ba Gaddafi ba ne ba, mai cewa zai daki Mai Jidda, yau shi ne da gaishe mu"

Fati ta ce "Wallahi nima abin ya bani mamaki sosai da sosai"

Su na cikin tattaunawa, Gaddafi ya kawo musu ruwan sanyi da lemo, ya nemo Nasiru, ya tarar musu abin hawa, ya biya kuɗin suka tafi.

*****
"Sayyid"

Ya ɗaga ido ya kalle ta.

Ta ce "Ko dattijon ne?"

"Wane dattijon?"

"No ba komai"

"Ki daina kallona, kamar ki na tuhuma ta"

Ta ce "Tuhumar ta ka nake yi ai"

Ya tsaya da cin abincin ya ce "Da me?"

"Ci abincinka, zan gaya maka"

Ya ci gaba da ci, ta sake kiran sunansa.

Ya ɗago ido ya kalle ta.

Za ta yi magana, su ka ji an buɗe gate ɗin gidan an shigo.

"Laa a buɗe ka bar gate ɗin?"

Ya ce "Eh na manta ne"

Sallamar Nasiru ta ji, ta yinƙura ta tashi ta leƙa.

Kasancewar jikinta babu hijjabi, ko ɗan kwali babu a kanta, kafin ya yi magana tuni ta yi wani irin ihu, ta yi waje da gudu. Tashi ya yi da sauri, ya bi bayan ta, domin ganin abin da ya sanya ta wannan ihun haka.

Gani ya yi ta rungume ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da Nasiru. Ya koma da sauri ya rufe abincin da yake ci, ya kawar da kwanukan ya koma gefe ya tsaya.

Tare suka shigo da matan, ɗayar na share hawaye ita ma. Su na shigowar ya fice daga ɗakin.

Nana ta kasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfinta.
Adda Saude ta ce "Nana kukan ya isa haka"

"Adda ina mamanmu?"

"Yanzu dai ki yi haƙuri, mu gaisa mana Nana"

Ta basu gurin zama, sai dai ta kasa daina kuka, ta kawo musu ruwan roba, ta koma gefe ta zauna ta cigaba da kuka.

Anty Fati ta ce "Haba Nana, ki yi shiru mana"

"Dan Allah ina Maman take? Yanzun ma ba za ta zo ba?"

Adda Saude ta ce "Ki yi haƙuri Nana, auren nan na ki ma ba mu sani ba, waiwai mu ka ji, tare za mu taho da ita da, amma mijinta ya hana, yanzu haka ma babanki da korar mu ya yi, Gaddafi ne ya haɗo mu da yaro ya rako mu, har ya biya mana kuɗin mota"

Cikin kuka Nana ta ce "Na kira ta, Baban su Walida ya ɗauka, bai haɗa ni da ita ba"

"Ki haƙuri Nana, lamarin iyayen naki ne sai haƙuri, ita kanta babu yadda ba ta yi ba ta zo, amma ya hana har da barazanar saki. Amma ga kayan aurenki nan da ta bayar a kawo miki, mu ma da abin da Allah ya yassare mana. Yanzu zamu haɗa ki da ita a waya, zan kira Lawan ya kai mata sai ku gaisa"

Nana ta ci gaba da kuka, tana jin kewar mahaifiyarta, amma gaba ɗaya ba ta da maraba da marainiya.

Anty Fati ta ce "Nana, mijin naki buzu ne kenan? Ke kuwa yaya aka yi ku ka haɗu har danginsa su ka bari, ya aure ki, ai ba sa auren bare da wahala. Har gara matan su, idan ka na da kuɗi za su baka, amma mazan dai ba sa auren wasu matan idan ba na su ba".

Ras gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ce "A gidan da yake gadi mu ka haɗu"

Adda Sauda ta miƙo wa Nana waya, Nana ta karɓa jikinta yana rawa.

"Salamu Alaikum Nana, ki na ji na?"

"Mama" ta furta cikin rauni, tana fashewa da wani irin kuka tamkar za ta shiɗe.

Maijidda ma kukan ta saka ta ce "Nana ki yi haƙuri, na san ni mai laifi ce a gurinku, dan girman Allah ku yafe mini an fi ƙarfina ne, na rasa yadda zan yi. Imrana ma ya daina zuwa inda nake"

"Mama dan Allah ki zo, ni ba na son na zo na saka ki a matsala ina son na ganki, dan Allah"

"Nana in sha Allah zan zo Nana, da gaske an yi miki auren ko? Kodayake daga majiya mai ƙarfi na ji, Babanku bai kyauta mini ba. Ga ɗan abin da na tara miki nan babu yawa, ki yi haƙuri Nana, ki ba wa ɗan uwanki haƙuri dan Allah ku yafe mini. Wallahi ku na raina ban taɓa mantawa da ku ba, babu yadda na iya, mijin da nake aure ba shi da fahimta, kansa kawai ya sani shi ma" Nana ta kasa magana sai wata irin sheshsheƙar kuka da take yi.

Ta sake cewa "Ki na ji na Nana, ki yi haƙuri da rayuwa, jariri ma ana haihuwar sa, mahaifiyarsa ta koma ga Allah, kuma ya rayu cikin ikon Allah, ki zama mai juriya, ki yi wa mijinki biyayya. Har yadda aka yi aka yi auren ki, an gaya mini, amma ko 'yan uwana ban gaya wa ba, kowace mace ko na ce ko wane dan Adam akwai kalar tasa jarrabawar. A raina, ban taɓa jin za ki aikata, wani abu da zai tozarta ki ba. Ki yi haƙuri ki rungumi auren ki Nana, shi ne mutuncinki da suturar ki.
Yaya jikin ki kuma?"

"Da sauƙi" ta faɗa muryarta na fita da ƙyar.

"To ki riƙe Addu'a, ki riƙe Allah. Ki riƙe auren ki da kyau, ki yi haƙuri Nana, ki yi haƙuri ku yafe mini. Dan Allah kar ki yi fushi da ni, kamar yadda ɗan uwan ki ya yi, wallahi ku na raina."

"To Mama, na gode sosai, na gode" suka yi sallama, Adda Saude na ta rarrashinta da ba ta haƙuri.

Gyaran muryarsa ta ji a ƙofar ɗakin, Nana ta tashi da ƙyar ta nufi ƙofar ɗakin.

Zuciyarsa ce ta buga da ƙarfi, a razane ya ajiye ledojin hannunsa ya ce "Mene ne?"

Nana ta yi shiru tana kallon sa.

"Yi magana Husna, mene ne?"

Nana ta goge hawayenta, ta ce "Babu komai fa"

"A'a launin idonki ya canza, ba kuka ne kawai ba, akwai matsala ne"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka kwantar da hankalinka, zan yi maka bayani bari baƙina su tafi"

"Zuciyata babu daɗi, ki daina kuka na roƙe ki"

Cike da jarumta, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Na daina" ya jinjina kai, ya ɗauki ledojin ya ba ta.

Ta koma cikin ɗakin, su ma fruit ne, da fura da Nono ya kawo.

Ta hau fafutukar ɗora musu girki, a hankali ta ɗan ware, su ka yi ta hira, Nana ta ce "Me yasa ba a zo mini da ko Walida ba, rabona da su tun su na yara sosai"

Anty Fati ta ce "Wa zai ɗaukko su, ya zo ya yi ta jaraba, mussaman ya san in da aka tafi da su. Ai Maijidda ba ta yi dacen mazaje ba, daga Baban naku, har Iliyasun.

Suka yi salla, Nana ta kammala girki, ta ɗebarwa Sayyid nasa, su na ta yi wa Nana hira, sai dai zuciyarta cike da damuwa.

Nana ta fita ta samu Sayyid, ya miƙe tsaye yana kallon kumburarriyar fuskarta cike da damuwa.

"Sayyid ka zo za ku gaisa da 'yan uwan Mamana, su ne suka kawo mana ziyara ka zo mu je ku gaisa. Amma idan da hali ka yi musu magana dan Allah"

Ya ce "To, amma idan ina kallon fuskarki a haka, ba zan iya magana ba"

Ta yi murmushi ta ce "Ba na son rigima, mu je to"

"Ina jin kunya, wuce gaba na biyo ki"

Ta yi murmushi, ta yi gaba ya bi bayan ta.

Ya yi sallama sannan ya shigo, ya tsugunna, ya sauke takunkumin fuskar sa ya ce "Barkanku da zuwa, ya hanya?"

Jin gaisuwar ta sa suka yi banbarakwai, amma Adda Saude ta ce "Lafiya ƙalau, mun same ku lafiya? Ya iyalin?"

Ya ce "Alhamdilillah mun gode Allah"

"To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, bamu samu mun halarci taron biki ba, sai yanzu muka zo. Allah ya baku zaman lafiya. Sannan a yi ta haƙuri, shi aure ɗan haƙuri ne, ba farkon auren ba, sai zama ya yi zama ake gane haƙurin. Ubangiji Allah ya yi muku albarka, dan Allah ka yi haƙuri da ita ka riƙe ta amana"

"In sha Allah"

Anty Fati ta ce "To ina fatan dai ba za ka yi mata kishiya ba, tun da ta ciri tuta ka aure ta, tun da dai an ce ba kwa auren wanda ba ƙabilar ku ba? Dan ni 'ya ta daidai take da mata huɗu, har da ɗoriya."

Miƙewa ya yi yana murmushi, ya nufi hanyar fita. Nana cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid ba fa ka ba da amsa ba"

Yatsansa manuniya ya nuna mata, ya ce "Ke kaɗai ce Ma vie"

"Anty Fati ki zama shaida"

Ya fice yana murmushi, Anty Fati ta ce "Ke babu ruwana, namiji na mata huɗu ne, wasa nake yi kar ki saka a hakan a ranki"

Nana ta basar da maganar, dan wani irin zafi ta ji ya fara taso mata.

Adda Saude ta ce "Nana an baki 'yan abubuwa kuwa na gyara, ko kuwa haka kawai su ka ninko ki, su ka kawo ki?" Nana ta yi shiru, tare da sunkuyar da kai, wa ya tsaya bin ta kan ba ta wani abu, har gara Ummi ta kawo mata, ranar da su ka zo da su Jamila, ta rubuta mata yadda za ta yi amfani da shi, amma tun da ta jefa ledar a drower, ba ta sake bi ta kan su ba, saboda pressure gabanta ta ishe ta, ba ma ta taɓa tsammanin wani abu zai shiga tsakaninsu ba.

Anty Fati ta yi wa Nana tambayoyi, a kan matsalar sanyi, Nana ta ce ita ba ta jin komai na alamar sanyi.

"To duk da ke kaɗai ce a gurin mijinki, amma kar ki zauna ki miƙe ƙafa Nana, kar ki ga ba shi da ƙarfi, tsaf 'yan mata za su din ga kawo masa farmaki, ki na ganinsa tubarkallah da shi. Nana ki yi addu'a, ki yi gyara kuma ki yi biyayya, za ki zauna lafiya in sha Allah. Nana ki yi kissa, kar ki zauna haka sai abin da ya zo miki, ki zama mace mai tunani Allah ya baku zaman lafiya"

Suka yi ta yi mata nasiha, har aka yi sallar la'asar. Su na yin sallar la'asar, su ka ce za su tafi, saboda kar su yi dare a hanya.

Nana ta ce "Bari ya dawo

47 / 64