Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ta sake ƙoƙarin kwanciya.
"Ki ci abinci, ga ƙosai" ya yi maganar yana nuna mata ledar da ke kusa da gas.
Ta girgiza masa kai ta nemi guri ta kwanta.
"Kin yi mini laifi ki na fushi da ni kuma? Na ce kar ki yi abu kin yi, kuma kina fushi?"
Ta kalle shi idonta fal hawaye ta ce "Kuma shi ne sai ka shaƙe ni? Har na yi maka laifin da za ka yi yinƙurin kashe ni, dama ba so na ka ke yi ba" A rikice ya zaro ido ya kalle ta ya ce "Ni? A'a ban shaƙe ki ba. Me yasa zan shaƙe ki kuma? Raina ya ɓaci ne, zuciyata ta kama da wuta, sosai da sosai amma ban shaƙe ki ba. Kamar bacci ma na yi daga lokacin"
Idonta fal hawaye ta ce "Bayan ga shaidar faratanka a wuyana"
Kamar ya yi kuka ya ce "A'a, kin manta kin yanke mini farce, amma ban taɓa ki ba ma, kalli hannuna" ya yi maganar yana nuna mata yatsun sa.
Ya miƙa hannunsa wuyanta, dan ya duba shaidar faratan da ta ce, amma ya ji jikinta zafi rauuu.
Sake rikicewa ya yi ya ce "Ma vie. (Rayuwata) tu as de la fièvre ? (Zazzaɓi ki ke yi?" Ya yi maganar a rikice.
Ba ta kula shi ba ta kwanta, tana jin yadda jikinta yake ɗaukar zafi, cikin ta yake yamutsawa.
Wayarta ya ɗauka ya danna, ya kara a kunnensa. Da French ya yi magana, ya ajiye wayar a kan mudubi, ya dawo inda take ya ce "Tashi ki saka kaya, na kira Habu"
"Sayyid da ba ka kira shi ba, zan warke fa"
"A'a jikin ki ya yi zafi sosai"
Ya nemi guri ya zauna a musa da ita, yana ci gaba da kallonta cikin damuwa.
*****
Sannu a hankali yake jujjuya wayar hannunsa, yana sake karanta saƙon da ya shigo wayarsa.
An shirya tsige shi, daga shugabancin 'yan kasuwa, bisa zargin sa da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe, na ƙananan 'yan kasuwa.
Tabbas akwai kuɗaɗen wasu a hannunsa, har da wanda kuɗinsu bai kai ba, da zai yi wa ciko ya ba su bashin kaya. Kuma ya tattara kuɗin ya yi order kayan, sai dai sun ƙara wata guda a kan lokacin da yakamata su zo, shima yana ta bibiya ne. Amma ya yi wuri a ce an ɗauki wannan matakin, duk da ba yau ya saba yi wa ƙananan 'yan kasuwan irin wannan tallafin ba, har ma da manyan, amma ba a duba hakan ba.
Fadila ce ta nufo shi, hannuna da ɗan ƙaramin tray, ɗauke da fruit, ta nemi guri ta zauna.
Ta ce "Daddy, ga fav ɗin ka, banana, ga kuma smoothie na yi maka, na ga kamar a gajiye ka ke"
Ya yi murmushin yaƙe ya karɓa ya ce "Na gode sosai da babyna"
Jiki a sanyaye ta ce "Daddy" ya kalle ta ya ce "Na'am"
"Me yake faruwa ne?"
Ya ce "A ina?"
"Damuwa ce a fuskarka, dan Allah gaya mini, meyafaru?"
Ya yi murmushi ya ce "Tsabar gajiya ce kawai, kin san yanayin harkokin namu, babu hutu"
Fadila ta riƙo hannunsa ta ce "Na san wataƙila har da damuwar kayan nan, da suma suka yi delay, amma dan Allah ka yi haƙuri ka daina damuwa, yadda wancan suka kuɓuta, wannan ma da yardar Allah za su tsira. Kar ka damar mini kanka dan Allah"
Maganganun nata sun ɗan ba shi ƙwarin gwiwa, shi bai damu da batun tsige shi daga shugabancin ba, shi haƙƙoƙin mutane da suke kansa, su ne suka dame shi. Yana jin daɗin tattauna matsalolin sa da Fadila. Duk da ba ta kai uwargidan sa shekaru ba, amma yau shekara bakwai da auren Fadila, ta tattara duk ta tsane shi, tana ganin ya ci amanarta, sun yi wahala tare ya ƙaro aure. Duk da duk wani abu na jin daɗi na hakkinta yana sauke mata. Ko ya gaya mata damuwarsa, sai dai ta taɓe baki kawai ta ce Allah ya kyauta, ko ma ta ce masa alhakinta ne.
Fadila kuwa ko sun samu saɓani, da ya shiga damuwa, take ruɗewa har sai ya samu mafita, sai dai a wannan karon, ba zai iya gaya mata ba, saboda ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba ita ma.
****
"Husnah" ta buɗe idonta ta kalle shi, lokacin agogon ɗakin ya nuna ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe.
"Tashi ki saka kaya, ga Habu can ya zo, za mu je a duba ki"
"Na ce ka daina gaya musu, mu daina saka su ɗawainiya"
"Tashi ki daina yi mini jayayya" ya yi maganar, yana tsuke fuska.
Ta tashi da ƙyat, ya taimaka mata ta saka kaya, ta saka hijjabi, a harabar gidan suka tarar da Habu. Ya yi mata sannu suka fice.
Tun da ya kira Habu ya sanar masa, dama da adaidaita sahu ya zo. Wani ƙaramin asibiti suka je. Buzu yana tare da Nana, Habu ya yi ta shiga yana fita.
Ya sayo kati aka duba ta, aka ba ta gwaje-gwaje. Sun ɗan jima a gurin ɗaukar jinin, ta gaji da zaman, ta zame tana ƙoƙarin kwanciya a gurin, amma ya riƙo ta tsam a jikinsa.
Suka koma gaban likita da sakamakon, ya duba ya kalli Nana ya ce "Yaushe rabon ki da Al'ada?"
Tamkar ya sokawa Sayyid mashi, ji ya yi ina ruwansa da zai yi mata wannan tambayar? Amma ya dake bai yi magana ba.
Nana ta gaya masa, ya ce "Ok, to akwai ciki ne, sai kuma malaria++ bai kamata a ce, ga juna biyu ba kuma ga malaria ki na fama ba. A kula sosai. Zan rubuta ruwa da allurai a saka miki, za ki ɗan ji ƙwarin jikin ki in sha Allah"
Ya yi rubuce-rubuce ya basu, Sayyid ya karɓa suka fito.
Ya miƙa wa Habu katin, aka nuna musu inda za su kai Nana.
Habu ya kalle shi ya yi masa magana da yaren su, ya cewa Habu "Tsaya" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya ba wa Habu"
Habu ya kalli kuɗin ya kalle shi, ya ce "Da can kuɗin yi wa Nana amfani da su.
Wani ma'aikaci ne, ya shigo ward ɗin zai sanyawa Nana cannular. Nana ta miƙa masa hannun, ya kai hannu zai kama ya saka mata Buzu ya riƙe hannun Nana.
Ma'aikacin ya ce "Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne" ya yi shiru ya ƙi magana. Nana ta kalli yadda launin idonsa ya canza. A ranta ta ce "Allah ya yaye maka wannan azabar kishin Sayyid"
Habu ya yi gyaran murya, ya "Ka yi haƙuri, a saka mata, ka ga tana shan wahala sosai.
Ya yi mursisi, ya murtuke fuska, ya riƙe hannunta gam, ya ƙi saki.
Sai da Habu ya zauna ya din ga yi masa bayani da yarensu, cikin tattausar murya. Ƙarshe ma'aikacin gefe ya koma, ya zubawa sarautar Allah ido.
Tamkar gunki ya yi gum, ya ƙi motsi kuma ya ƙi magana.
"Ni idan ba zai yarda a saka mini ba, dan Allah ku mayar da ni gida, na je na kwanta na gaji" ta yi maganar a raunane, cikin yanayin rashin lafiya.
Da ƙyar ya saki hannun Nana, sai dai ya kawar da kansa gefe, saboda yadda zuciyarsa ke tafasa da ganin ya kama hannun Nana ya saka mata ruwa.
Har huɗu su na Asibiti, sai dai ta ji dadin jikinta, zazzaɓin ya sauka.
Aka gama saka mata ruwan, sannan suka tafi gida. Ba ya jin nauyi ko kunyar Habu, haka yake rungume da Nana yana shafa ta, kamar zai lashe ta ya mayar da ita cikin sa.
Suka koma gida, Nana ta samu ruwa ta yi wanka, ta saka kankanar da ya saya mata a gaba, ta din ga sha, saboda itakaɗai ce ta ji ta yi mata daɗi.
Suna harabar gidan, Habu yana yi masa magana, sai ga babar su Yusra ta ƙaraso.
"Kai mai gadi, ina ka tafi baka yi wa kowa bayani ba? Zamu kai Siyama wankin ƙonuwar da ta yi, amma ka yi tafiyarka yawon ka?"
Habu ya ce "Ki yi haƙuri Hajiya, mai ɗakin nasa ce babu lafiya, ba a nuste yake ba, hankali tashe mu ka tafi Asibiti ki yi haƙuri dan Allah"
"Ni ma tawa 'yar babu lafiya ai, ba sai ya yi bayani ba. Tun da idan zai je wani guri yana rubutawa Jamil ba, sai Jamil ne ya buɗe mana muka tafi, ƙonuwar na ta jini"
Habu ya sake cewa "Ki yi haƙuri dai dan Allah"
Ko ɗaga kai bai yi ya kalle ta ba, balle ya kula ta, ko ta saka ran zai ba ta haƙuri, ya bar ta ita da Habu.
"Sannu"
Ta jinjina kai ta ce "Sayyid da ka sani ka ba ta haƙuri, ba na son wannan faɗan da ake yi maka"
"Ya jikin? Kin daina jin zazzaɓin?"
"Amma ka san mun yi laifi, bai kamata mu tafi ba su sani ba"
"Da suka buɗe ƙofar sun mutu ne?"
Nana ta sauke numfashi ta ce "Aishikenan, idan ka janyo aka kore mu, ka nemo mana inda za mu zauna ai" ya yi shiru, bai kuma cewa komai ba.
Daga bisani ya ce "Me za ki ci?"
"Ba komai, ba na son komai, kankanar nan ta ishe ni".
A hankali ya kai hannunsa, ya shafa gashin ta, ya saki murmushi ya ce "Kitson nan ya yi kyau sosai, ya dawo da hannunsa kan hannunta, ya jujjuya hannun, ya kai bakinsa ya sumbata ya ce "Kin yi mini kyau"
Ta kalle shi galala ta ce "A hakan da na fita hayyacina. Tun jiya na so ka kalla ka yaba ba, ka share ni ka yi ta yi mink faɗa"
"Idan na ce kar a yi, to a bari ne kawai, ba na so. Me yasa zan ce kar ki je guri ki je?"
Jiki a sanyaye ta ce "Na san na yi laifi, ka yi haƙuri. Za su ga kamar wulaƙanci ne, sun gaya mini abu na tashin hankali, amma na kasa yi musu jaje. Sayyid ban ji ka ce komai ba, a kan abin da aka ce"
"Wanne?"
"Da likitan ya ce... Sai kuma ta yi shiru.
"Ya ce me?"
"Ina da juna biyu, tsoro nake ji" ta yi maganar tsoron na bayyana ƙarara a kan fuskarta.
"Tsoron me?"
Abin da ta so furtawa daban, amma ta kauce faɗar hakan, kar ta tayar masa da hankali ta ce "Ban ga ka yi murna da hakan ba"
Ya gyara zamansa ya dubi Nana a tsanake ya ce "Wata irin wutar zafin, ganin wani ya taɓa ki ne, take ci mini zuciya. Amma wallahi ina cikin murna zamu ƙara yawa, nima Ahalina zai cika, ki haifi namiji mai kama da ni. Ko kuma mace mai kama da ke"
Murmushin dole Nana ta yi, ba dan ya kai zuciyarta ba ta ci gaba da tauna kankanar bakinta a hankali.
*****
Yanayin yadda aka banko ƙofar gidan, sai da Baba ya tsorata kamar ya zura da gudu. Ya dai tsaya ya ce "Kai wani mara hankalin ne ya ke yi mana wannan banzan bugun haka?"
Bai yi magana ba, sai ganinsa Baba ya a tsakiyar gida, tamkar ya faɗo daga sama.
"Uban me ya kawo ka gidana?"
"Gidan Ubana ne" ya faɗa yana ɗan rarraba ido yana kallon gidan.
"To uban me ya dawo da kai? Nan ka saka 'yan sanda suka din ga yi mini sintiri a gida, ka kai Gaddafi ƙara, kuma ka gudu, da yake kai duk inda ka tsuguna babu alkhairi tsiya ce take biyo baya. Ka bar mini gida kafin 'yan sanda su zo neman ka"
"Ni fa ban kashe kowa ba wanda suka yi abin ma an kama su, kawai ka wani din ga kora ta, idan na gama abin da nake yi da kaina zan bar maka gidan ai. Ka yi ta wani gidanka kamar wani gidan arziki"
Baba ya ce "Tun da ba na arziki ba ne ba, zo ka fice"
Imarana ya ce "Wallahi ba zan tafi ba. Ina Nana? Ke Nana"
Nasiru ne ya yi sallama a gidan, hannunsa riƙe da ledar kayan miya, yana ganin Imarana ya tafi da gudu ya rungume shi.
Imarana ya ce "Nasiru, na ga kana nema ka kamo ni a tsawo. Wai ina Nana ne?" Baba yana ƙiftawa Nasiru ido, amma tuni ya kwatsa wa Nasiru bayani.
"Ai an yi mata aure"
Turus Imrana ya yi ya ce "Kamar yaya? Uban waye ya yi mata auren ban sani ba?"
"Ni ne nan ubanta, idan kuma kai ka haife ta da sai an sanar da kai sai na ji"
"Kut.. aure fa, wa ka aura mata, ina fatan ba wannan ajawon bane Salisu yake ko wa?"
"Ba Saleh ba ne, wani Buzu ne mai gadi" Nasiru ya sake ba wa Imrana amsa.
Kai tsaye ya ƙundumo ashariya ya ce "Wane irin Buzu kuma? Kai ina ne gidan da aka kai ta?"
Baba ya ce "Wallahi ka taka ka je gidanta ban yafe maka ba. Kar ka kuskura ka je ka yi mata hauka ka kashe mata aure"
"Wallahi sai na je, dama kula ka ke da ni, shi ne za ka yi mini Allah ya isa ta kama ni, amma tun da ni nake kula da kaina ba za ta kama ni ba. Kai Nasiru wuce mu je ka raka ni"
Baba ya ce "Nasiru idan ka raka shi, sai na yi maka dukan tsiya"
"Kai mu je zan baka dubu biyu"
Nasiru ya waiga yana kallon Baba, ga batun kuɗi ya ji, ya maze ya bi Imarana suka fice, Baba na ƙwala masa kira amma ya fifita dubu biyu a kan kiran Baba.
Su na tafe a hanya, Nasiru yana ba wa Imarana labarin, abin da ya faru da yadda aka yi auren Nana. Ba ƙaramin fusata Imarana ya yi ba.
Mussaman da ya gaya masa, gadi Buzu yake yi.
"Uban me mai gadin zai tsinana mata, Allah na tuba mu dai ba mu yi dacen uba ba wallahi mu dai kawai ya kawo mu Duniya yana neman maraba da mu."
Sayyid na zaune yana shan shayi, a harabar gidan ya ji an taɓa gate. Ya rufe fuskar sa da sauri, ya tashi ya je ya buɗe, ya tsaya yana kallon Imran, saboda tsananin kamnninsa da Nana.
Babu jiran komai, Imrana ya ƙarasa hankaɗa ƙofar ya shiga, Nasiru ya bi bayansa.
Nasiru ya ce "Ga mijin Nanan nan" ya yi maganar yana nu na masa Buzu.
Imran ya ƙare masa kallo, ya ce "Ikon Allah, kai ka auri Nana? Tana ina?" Sayyid ya yi shiru yana kallon Imrana.
"Malam magana nake yi, ko kurma ne? Ina take?"
Nasiru ya ce "Kamar fa ba ya magana, amma Nanan tana cikin ɗakin nan"
"Dan Allah ji wulaƙanci, ɗakin mai gadi, ba ta samun arzikin a ajiye ta a gida ba ma, sai ɗakin daga shi waje, koma mene ne ya zo ya afka mata"
Nana tun tana banɗaki take jiwo, kamar muryar Imran, amma ta kawar da tunanin, a ganinta mai zai kawo shi yanzu.
Ta fito daga banɗakin ya shigo, Nana ta zabura ta ce "Imrana" sai kuma ta tsaya da tuna halin Buzu a kan kishin tsiya.
"Ke ashe ba ki da hankali? Ki ka zauna aka aura miki mutum kawai ki ka biyo shi yawon gadi? Gidan babanki ba mamora gidan miji ma haka? To wallahi sai kin bar gidan nan, sako hijjabinki mu tafi"
"Imarana mu tafi mu je ina?"
"Ko ma ina ne. Amma wallahi ba za ki zauna a gurin nan ba. Haka zamu zauna babu ci gaba?"
"To ka zauna mana, ka sha ruwa ka ci abinci, sai mu yi magana. Mama ma ta yi mini aike su Adda Saude sun zo...
"Dalla rufe mini baki, ina ruwana da wata? Addar wofi da can ba su zo ba sai yanzu. Ki ɗaukko hijjabinki mu tafi daga nan har human rights, na san biyayya kawai ki ka yi wa Baba ki ka auri mutumin nan, tun da dama ke ba sanin ciwon kanki ki ka yi ba"
Nana ta yi shiru, tana kallon in da Sayyid yake tsaye, ya tsare ta da ido. Tsoro take ji kar Sayyid ya yi wani abun da zai tunzura Imran, dan ta san ko zai kashe shi ba zai yi shiru ba.
"Imran na gode da ziyara, da kuma soyayyar da ka ke nuna mini. Amma ka yi haƙuri ina son aurena"
Wani irin takaici ya kama Imran ya ce "Nana me za ki zauna ki yi a shago, ɗakin nan meye marabarsa da shago? Na san zaman gidanm ne ba kya so, ba can za ki koma ba. Harkoki sun fara buɗe mini, karatu zan mayar da ke, kyakyawar rayuwa nake so na ga kin yi"
Ta sake kallon Buzu, da ya zubo mata idanunsa, Imran ya waiwaya ya ga abin da take kallo.
Sayyid ya shigo cikin takunsa na kamala da nutsuwa.
Ya sauke takunkumin fuskar sa, ya sakar wa Imrana murmushi, ya ce "Kun yi kama sosai, da alama ku na da alaƙa sosai" ya yi maganar yana miƙa wa Imran hannu su gaisa.
"Ba zan gaisa da kai ba, ƙanwata za ka sakar mini, Nasiru ya gaya mini duk wani abin da ya sani. Ni ban ji na gamsu da wannan auren ba ko kaɗan. Ya za a yi sama ta ka a aura miki mutumin da ba ƙabilarmu ba, babu wani dogon bincike. Ni jikina yana bani wani abu, ni ban yarda da auren nan ba gaskiya."
"Nima na fuskanci akwai sharuɗɗan da ban cika ba, aka yi wannan auren. Amma ko me za a yi mini, ba zan iya rabuwa da ita ba, tana ɗauke da ruhina a jikinta. Idan ka raba ni da ita, ni ya zan yi? Zan kula da ita, ka daina raina inda Allah ya ƙaddara zamana da ita, ba ka san gobe ba"
Imrana ji yake kamar ya mangare Buzun nan ya huta, haka kurum ya ji bai yi masa ba. Kuma ya san wannan kyawun ne ya ruɗi Nana, har take cewa ita ba za ta rabu da shi ba.
Ya sake kallon Nana ya ce "Kin zaɓi zama ko Nana?"
Idonta fal hawaye ta ce "Ka yi haƙuri Imran, Allah ne ya haɗa ƙaddarorinmu, ba komai zan iya yi maka bayani ba, amma ina son aurena. Sayyid na buƙata ta a rayuwarsa".
Imran ya haɗiye wata irin ƙwallar takaici. Ya zura hannu a jakarsa, ya ƙirgo kuɗi, ya tako gaban Nana, ya kamo hannunta ya saka mata ya ce "Ga wannan babu yawa, cikin abin da nake tarawa ne, domin na dawo gida na inganta rayuwar ki. Dama Saboda ke na dawo, daga nan ko gida ba zan kma ba, zan tafi inda na fito. Kai kuma tun da ta zaɓi zama da kai, idan ka ci amana na bar ka da mai hudowar rana da